Showing 138001 words to 141000 words out of 171073 words

Chapter 47 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7838

tare da fad'in, "Omo see love" ya fad'a cikin zolaya.

A haka dai suke hira suna ta jan sa da hira sai dai ya d'an saki fuska in na ansa ne yace uhu ko A'a, a haka har akayi i'sha aka tafi masallaci, bayan an dawo ma tace ya dawo aci a abinci gabad'aya haka akayi kuwa duk da baici sosai ba amma yaji dad'in yadda familyn suke da karamci sosai Hajiya Kaka take burge shi.

Washe gari.

Kasancewar jirgin azahar zasu hau su koma bayan an karya da safe Ibteesam taje waja sa dan ta rako shi wajan Hajiya Yaya suyi sallama, jakar da take yiwa kallon k'arama wacce ya tawo da ita taga ya b'ude k'asan ta sai ga katuwar leda mai d'auke da tambarin kamfanin sa ya fito da ita cike da kaya, kayan da suke ciki ya d'aga ya sake d'auko wata ledar amma bata kai waccan girma ba ya kalle ta yace, "Muje ya fad'a yana d'aukar ledojin.

A falon Hajiya kuwa duka suna nan daga yaran nata har jikokin nata da alama basu fita ba ana jira ayi sallama dasu Ibteesam d'in, da sallama suka shiga suka zauna aka kuma gaisawa a karo na biyu, babbar ledar Zaid ya jawo ya mik'awa Abba yace, "Abba gashi product d'in mu ne a bawa kowa" ya fad'a yana kallon sa. Da mamaki da kuma farin ciki Abba yaja ledar ana godiya suka b'ude, takalma ne masu kyau da tsada wanda ya zana da kansa ga kuma tambarin compony sa a jiki, sai kuma yadi milk colour mai kyau mara nauyi wanda shima da kansa ya zana shi kusan yadi d'ari. Babu wanda kayan bai burge shi ba Ameer da ya kasa shiru yace, "Zaid yanzu kaika ka zana wannan?" Ya fad'a yana nuna masa kayan da mamaki. D'aga masa kai yayi yace, "Ku kad'ai aka yiwa irin su indai ba an sake zana irin sample d'in ba gaskiya baza kaga mai irin sa ba" ya fad'a cikin muryar sa mai sanyi a koda yaushe.

Kafin su sake magana ya mik'awa Hajiya kaka tata ledar yace, "Ga naki". Bud'ewa tayi aka ga plat d'in takalma guda biyu masu bala'in kyau sai wani lace wanda bashi da hayaniya da yawa amma yayi bala'in kyau, zatayi magana yace, "Pls kar kuce komai". "Haba Zaid kaima kasan muyi shiru ai bazai yu ba wannan hidima haka?" Abbie ya fad'a yana kallon kayan. Nan aka fara yin masa godiya da addu'a ga iyayen sa yana amsawa da amin yana jin dad'in hakan sosai, kallon y'an matan yayi yace, "naku ba'a gama aikin sa ba da an gama za'a kawo muku". Da farin sukaa amsa suna yin godiya.

Ibteesam kuwa kallon sa kawai take dan bata zaci haka daga wajan sa ba gaskiya, bata d'auka zaiyi tunanin kawo musu wani abun ba balle har irin wannan kyauta haka lallai Zaid yana sonta sosai, lokaci d'aya ya sake shiga ranta ya kuma burge ta ta dinga jjin kanta on top ganin yadda ake yabon sa ta ko ina.

Godiya suke masa sosai da tun yana amsawa har ya fara k'osawa kafin lokacin tafiyar su Airport yayi, har bakin mota suka raka so suna yi musu fatan sauka lafiya suka shiga motar suka tafi.
*?ASAITAR SO!*

*76_77*

Not edited >?u?




Da la'asar suka sauka a Kano suna fitowa ya kira layin Hameed daman tun a Gombe ya sanar dasu isowar su ai kuwa yana zaune a mota yana jiran su, suka shiga motar suka tafi sannan suka gaisa da Hameed Zaid ya runtse ido tare da fad'in, "I'm so tired" ya fad'a yana goge fuskar sa.

Hameed ya tab'e baki yace, "Rago kawai". Yaji shi amma bai tanka masa ba ya mayar da hankalin sa kan titi, "yauwa Zaid in ka huta yanzu pls kazo muje company wallahi akwai files d'in da suke buk'atar saka hannun ka". Maimakon yayi magana sai yaja dogon tsaki kawai baice masa komai ba.

"Illar ka kenan kai daman ai ana yi maka magana sai kayi banza da mutum, wallahi da gaske nake mutane da yawa sun zo neman ka a jiya bayan ka tafi, harda wata yarinya ma tazo wai tana son ganin immediately na bata number ka" ya fad'a yana kallon Zaid d'in kafin ya mayar da kallon sa kan titin.

Kallon sa yayi yace, "Hameed ka bata number ta? Are you mad? Baka san yarinya ba kawai ka d'auki number na ka bata, what is kind of dis nonsense Hameed?" Ya fad'a a fusace yana kallon sa.

D'age kafad'a yayi yace, "to tace tana so ta ganka ne da gaggawa shiyasa na bata kuyi magana ban san meyasa take neman ka ba". Dogon tsaki yaja bai sake cewa komai ba suka cigaba da tafiya Hameed na y'ar dariya kad'an-kad'an.

Koda suka isa gida Hameed yana parking kowa ya fita daga motar suka shiga ciki shima cikin ya shiga duk da yasan Daddy baya nan, a falo suka tarar da Anty Amina a zaune a kusa da ita suka same su sunaga gaisawa, zama shima yayi a kan kujera yace, "Sannu da gida Anty". Murmushi tayi tace, "Kune da sannu ya hanya?". "Lpy lau, Daddy baya nan?". Tace, "baya nan". Mik'ewa yayi bai sake cewa komai ba ya hau sama Hameed na biye dashi a baya da jakar sa a hannun sa.

Suna ciki suka shiga suka huta tare da cin abinci, Anty Amina tace, "Baby ki d'auki abinci ki kaiwa Zaid sama." Bata musa ba ta mik'e ta had'a abincin ta hau saman nasa, babu kowa sai shi kad'ai a zaune yana ta aikin a laptop kana ganin yadda ya mayar da hankali kasan aikin mai mahimmaci ne, ajjiye abincin tayi a gefe ta koma kusa dashi ta zauna ta kwantar da kanta a kafad'ar sa tana kallon abinda yake yi a laptop d'in, kallon ta yayi tare da shafa fuskar ta ya cigaba da abinda yake yi baice mata komai ba, wayar sace tayi k'ara yayi tsaki ba tare da ya duba ba ya cigaba da aikin sa, aka sake kira nan ma bai kalle ta a na ukun ne ya d'auka ya kurawa wayar ido, bashi da number wanda yake kira hakan ya saka sunan wanda ya kira shi ya fito a truecaller, Hadiza Muhammad shine sunan da ya fito a kan wayar, maimaita sunan yayi yana tunanin ko ya san mai sunan amma bai sani ba sai ya ajjiye wayar ya cigaba da aikin sa.

Kiran da aka kuma yi ne ya saka shi ya d'auka tare da sakawa a speaker daga can b'angaren aka ce, "Assalamu alaikum". Jin muryar mace ya saka ya kalli Ibteesam da itama shi take kallo kafin yace, "Wa'alaiki salam, wake magana?". Tace, "Dan Allah ina magana da Zaid ne?". "Yeah" ya amsa a tak'aice idon sa na kan Ibteesam. "Daman naje office d'in kane jiya baka nan sai MD ya bani number ka". "Okay" ya amsa yana kallon Ibteesam da tayi bala'in had'e rai ta mik'e zata tafi ya rik'o hannun ta tare da dawo da ita ta zauna a cinyar sa, "sunana Hadiza Muhammad za'ayi biki nane end of next month shine nake so dan Allah zan siyi sample takalimi da kuma lace wanda ba'a tab'a bawa kowa ba".

"Ayya ba'a fad'a miki bana bada sample ba sai a company?". "An fad'a min nima a under companyn ka za'a min kawai dai ina so ya zama sample d'in ya zama naka ne kai ka zana". D'an numfashi ya sauke kad'an kafin yace, "come and meet me tomorrow in my office" ya fad'a yana shafa fuskar Ibteesam ds take a had'e sosai.? "Which time sir?" Ta tambaya. Yace, "by 10am" bai jira mai zatace ba ya kashe wayar tare da ajjiye ta a gefe.

"Precious pls ki saki fuskar ki mana" ya fad'a yana rik'e cheek d'in ta, sake tamke fuska tayi tace, "yanzu mata har waya suke maka ma wai suna son sample?". Murmushi yayi kad'an yace, "gaskiya basu cika kira na ba sai time to time, to meye kike fushi haka?". Hararar sa tayi tace, "to ba sune suke maks iyayi ba suna jin muryar ka free ni wallahi bana so." "Calm down Precious ni bana gane ma wai suna min iyayi cos basa gaba na, matata kuma masoyiya ta mai kuma sunan Mama na Precious ba? ita kad'ai nake gani har na fahinci abinda take yi, just relax my love u are the only one" ya fad'a yana kai mata kiss a wuyan ta.

Turo baki ta sake yi tana kallon gefe ya juyo da fuskar ta ta sake kawar da kai da kai gefe ya sake juyo da ita ga sake kawarw, "Please mana" ya fad'a yana sake dawo da fuskar ta gare shi, "bana so naga kina fushi dani" ya fad'a bayan ya saka idon sa a nata, bakin nata ya d'an ja kad'an yace, "Smile mana haba Baby na, you're my sugarcane fa". Murmushi tayi shima yayi yana lakuce mata hanci tace, "Ga abinci kaci". Yatsine fuska yayi yace, "bana jin yunwa."
"Tun fa breakfast baka sake cin komai ba gashi yanzu har biyar tayi".
"Ni ba wannan abincin nake so naci ba".
"Just tell me wanda kake so yanzu na kawo mata" ta fad'a tana shafa fuskar sa itama.

Baki ya turo gaba cikin shagwa6a kamar mace yace, "ni ke nake so". Zaro ido tayi tace, "ni daman ai taka ce ka fad'i abinda zaka ci na girka maka."
"Nifa ba abinci zanci ba".
"To me zaka ci?".
"Ni ke".
"Da ana cin mutum tabbas zan zauna ka yanki inda kake so a jiki na kaci, stop joking ka fad'i abinda kake so kawai" ta fad'a dan ita kam bata fahimce shi ba.

Shagwa6a sosai yake mata yace, "ana ci mana". Ta rik'e hab'a tare da fad'in, "to ta yaya kenan?".
"Allow me to show you" ya fad'a yana fara binta da kisses a ko ina. "Nidai ka fad'a min ban gane ba". Murmushi yayi yace, "ai nasan baki gane d'in ba shiyasa kike cewa haka, kawo kunnen ki na fad'a miki ta yaya zan samu abinci a wajan ki" ba musu ta mik'a masa kunne ta ya fad'a mata.

"Wayyo Allah" ta fad'a tana kulle fuskar ta da tafukan hannun ta cikin kunya mai tsanani, sake shagwa6ewa yayi yace, "Zan samu?". K'asa ta sake yi da kanta sosai bata ce masa komai ba, "answer me" ya sake fad'a cikin shagwa6a.

"Kai baka jin kunya kai?" Ta fad'a kanta a k'asa, "nidai ba wani kunya kawai ki bani abinda nake so ko nayi kuka yanzu" ya Fad'a harda buga k'afa kamar mace, sai ya bata dariya sosai tayi wuf ta mik'e daga jikin sa tayi hanyar k'ofa tana fad'in, "Shagwa6a tayi maka yawa Daddy ya shagwa6a min kai sosai, zan sha aiki dan wannan shagwa6ar taka kullum gaba take yi". Yunk'urawa yayi zai kamo ta ta kwasa a guje tayi k'asa tana dariya, baiyi Yunk'urin binta ba dan aikin yake so ya gama.

Tana sauka Anty Amina tace, "Baby Mumnyn ki tace in kun dawo na tura mata ke can, ki koma ki tambaye shi sai ku tafi". Da to ta amsa ta shiga d'aki ta d'auki wayar ta ta tura masa messy bata jira taga reply ba suka shirya aka fara tsayawa a gidan Umma aka sauke? Jidda aka gaisa kafin su tafi gidan Mummy.

Bai sakko ba sai dare ya samu Daddy a falo ya zauna kusa dashi tare da fad'in, "Daddy ban san ka dawo ba ai, ya gida?" Ya fad'a yana kallon sa, "lafiya lau Zaid kun dawo lafiya?". "Lafiya kau Daddy." Daddy yace, "mahaifin ta ya kira ni d'azu yana ta min godiya ka kai musu kaya da yawa can Gomben, naji dad'in abinda kayi sosai Zaid ashe dai ka fara hankali". Ai da sauri ya d'ago ya kalli mahaifin nasa yace, "Daddy da bani da hankali kenan?". Daddy yace, "Haba ni na isa nacewa Abdallah bashi da hankali? Kana dashi amma na yanzu yafi yawa."

"Suna da kirki sosai Daddy bakaga yadda suka nuna min kulawa ba" ya fad'a yana kallon Daddyn nasa, murmushi yayi sosai yace, "Masha Allah haka nake so naji daman ai Zaid, yanzu an tsayar da bikin ku nan da sati biyu zaku tare daman abinda bai rage a part d'in naka ba fenti za'a sake kuma na saka an fara". Kwanciya yayi kad'an a kan kujera yace, "to Daddy. "

Daddy yace, "Sai batun lefe kuma da zaka yi mata, a nan zaka siyi kayan ko a wata k'asar?". Zaid yace, "oh ready na gama da wannan issue d'in nayi order komai saura kad'an suzo." Daddy yace, "amma baka fad'a min ba? Nawa ka kashe?". Kallon mahaifin nasa yayi kafin ya mik'e zaune sosai yace, "Daddy tunda na tashi komai kaine kake min wannan nayi da kaina na baka hutu".

Murmushi Daddy yayi yace, "hakkin ka ai yana wuya na Zaida har gobe dan haka ka fad'a min nawa ne zai ishe ka har a gama bikin nan." "Daddy ina da kud'i a hannu na nima sosai basai ka bani ba". "Abdallah nawa zan baka?" Ya sake tambaya alamun babu wasa kenan. Zaid yace, "shikenan Daddy zanyi lissafi sai na fad'a maka." Daddy yace, "ko kaifa, sai batun kayan da za'a zuba a gidan naku."

"Shima zan san abinda za'ayi" Zaid ya fad'a yana mik'ewa tsaye, Daddy ya kalle shi yace, "ina zaka je kuma?". Waya ya mayar aljihu yace, "Zanje gidan Mummy ne." Kallon sa Daddy yake tun daga sama har k'asa sannan yace, "A haka zaka je gidan Mummy?". Kallon kansa yayi kana yace, "me nayi?".

"Wai ka manta yanzu Mummy sirikar kace? Mijin ta kuma shine mahaifin matar ka shine zaka je musu da k'ananun kaya?". Yatsine fuska yayi yace, "Ni wancan takura min sukeyi Daddy bana son su." Daddy yace, "Ai kam indai zaka je gidan mahaifin ta ko inda ta taso dole ka saka manyan kaya sabida girmamawa, ka koma yanzu ka canja sai kaje." Ya bud'e baki zaiyi magana Daddy ya riga shi da fad'in, "kaje kayi abinda nace." Bashi da ta cewa dole ya koma sama badan yaso ba ya canja kayan kota falon bai biyo ba ya fita.

A can gidan Mummy kuwa sun baje a falo kasancewar dare ne suna ta hirar Gombe? har da Abba da ya fito a lokacin, "Ai mutanen Gombe sunji dad'in abinda Zaid yayi musu sosai suna ta godiya" Abba ya fad'a yana kallon Ibteesam. Mummy tace, "Ai ya kyauta wallahi nima naji dad'i balle su." Sallama akayi tare da turo k'ofar aka shigo hakan ya saka suka mayar da hankalin su ga wanda yake shigowar, Zaid ne ya had'e cikin army green d'in shadda an mata d'inki mai gajeren hannu tsayin rigar iya guiwa, yayi kyau sosai duk da bai saka hula ba amma kayan sun amshe shi sosai, "Mutanen Gombe sannu da zuwa" Mummy ta fad'a da murmushi tana kallon sa cikin farin ciki. K'arasawa yayi cikin falon suka gaisa da Abba kafin Abban ya sake masa godiya shidai kawai sai dai yayi murmushi.

Abba bai jima ba ya mik'e daman fita zaiyi ya fita sannan Mummy ta kalli Zaid tace, "Baba na ya naga har an had'e fuska? Badai haka kaje Gombe kana d'aure musu fuska ba ko?" Ta fad'a cikin wasa tana kallon sa, kallon ta yayi yace, "Mummy nifa ba wajan ki nazo ba" ya fad'a murya a k'asa yana kallon ta. Rik'e baki Mummy tayi tace, "to mara kunya wajan wa kazo?". Idon sa ya mayar kan Ibteesam da take nunawa Sultana assignment yace, "gata nan a zaune."

"Me zakayi mata?" Mummy ta tamabya tana kallon sa, da mamaki yace, "Mummy me zan mata fa kika ce? Kin manta wacece d'ina ne?". "Ban manta ba amma yanzu kai da ita sai dai kallo dan magana ta daina had'a ku inda ba a waya ba sai kun tare kuma." Gyara zama yayi sosai ya kalli Mummy yace, "yaushe wannan ayar ta sauka kuma ban sani ba? Dan dai nasan babu ita a cikin alkur'ani". Duk dakiyar da Mumny taso tayi da ya bata dariya tace, "Ba aya bace ba kuma hadisi bane, wannan umarni na ne". Tab'e baki yayi yace, "for what reason?". Mummy tace, "kai bana son tambaya abinda bace shi za'ayi."

"Okay, daman tambayar ta nazo zanyi ina mota tazo ta same ni, good night Mummy, Zahra and twins" ya fad'a yana fita daga falon. Murmushi Mummy tayi mai kyau bayan ya fita tace, "bar assignment d'in nan Baby jeki ki dawo". Ta amsa da to ta yafa mayafi ta ta nufi motar tasa, gaban motar ta bud'e sai taga baya nan daga bayan motar taji ance, "gani nan". K'ofar gefen ta ta bud'e ta shiga tace, "da driver kake ne?". Girgiza mata kai kawai yayi dan tana shigowa kamshin turaren ta ya saukar masa da kasala sosai, "gani" ta fad'a tana kallon sa. Bai magana ba sai zuba mata ido da yayi ko kiftawa bayayi? ita kuma idon sa ya zamar mata kamar dafin da yame canja mata yanayin jikin ta yanzu zata tsinci kanta a yanayin da bata yi zaton zuwan sa a lokacin ba, "ka daina kallo ka" ta fad'a a shagwa6e.

Bai d'auke idon sa a kanta ba yace, "meyasa?".
"Ina jin wani iri in kana min irin wannan kallon."
"Nima ina jin wani iri in kina min wannan maganar."
"Uhum uhum nidai bana so ka daina" ta fad'a har da buga k'afa. Lumshe ido yayi ya bud'e lokaci d'aya yaji in baiji ta a jikin sa ba zai iya shid'ewa sai kuwa ya jawo ta kamar wanda aka jonawa wani abun ya k'ank'ame ta tare da zare d'ankwalin kanta yana shafa kitson kanta.

Sun d'auki mintina a kalla biyar a haka kafin ya sassauta rik'on da yayi mata ya fara zagayawa da d'an yatsan sa a fuskar sa yace, "size d'in takalimin ki zaki bani" ya fad'a ba tare da ya daina abinda yake mata ba, idon ta a lumshe tana kwance a k'irjin sa tace, "size 38". "Kina using da hill shoes ne?". Ta d'aga masa kai alamun eh, "oh ready nasan na undies d'in ki no need ki fad'a min". Kallon sa tayi tace, "Kamar ya ka sani?".
"An fad'a miki ina tare dake ne kawai ba tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login