Showing 72001 words to 75000 words out of 171073 words

Chapter 25 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7816

kallon cikin idon ta.

"Zaid ni kake kira banza?" Ta fad'a cikin mamaki, "to mara hankali kike so na kira ki? Wacece ke in ba banzar ba,? Ko kina da wani sunan ne bayan wannan?" Ya fad'a yana jifan ta da kallon wulaqanci. Cikin muryar ta da tayi rauni tace, "sai nake ji a jiki na akwai ranar da zata zo zaka zo gaba na kana kuka kana na yafe maka, wannan ranar nake jiye maka". Ai a fusace ya mik'e tsaye ya kalle ta tun daga sama har k'asa yace, "Wallahi kinci sa'a da cikin jini na a jikin ki wallahi sai na b'arar dake a wajan nan, ke har kin isa na nemi alfarma a wajan ki har nazo ina kuka for god sake? Oh my god, ke har kina da k'arfin giuwar da zaki ce zan zo na nace ki yafe min,? Wacece ke? Me kike dashi? Me zaki bani,? Da nazo na nemi alfarma a wajan ki gwara nayi addu'a tun kafin ranar Allah ya d'auki raina na mutu kafin lokacin, in kuwa ina raye gwara naje na d'urkusawa bitch,? Do u know bitch? Macen kare ko gwara naje na d'urkusa mata ina kuka nace ta yafe min da dai nace ki yafe min sabida nafi girmama ta a kanki, ki daina wannan banzan tunanin a ranki ranar baza ta tab'a zuwa ba har Allah ya tashi duniya, and before i count 3 ki b'ace min da gani kafin zuciya ta ta kaini ga shak'e miki wuya, kije ki cigaba da had'a plan d'in kashe ni kinji sai muga waye zai nemi yafiyar wani nida ke" ya k'arasa fad'a cikin murya mai amo duk da amsawar da cikin sa yake yi bai hana shi fad'a mata abinda yake ransa ba.

Tunda take a rayuwar ta ba'a tab'a fad'a mata wani abu da ya b'ata mata rai kamar abinda Zaid ya fad'a mata yanzu ba, bata san lokacin da hawaye ya fara sakkowa daga idon ta ta kalle shi tace, "zakayi dana sanin kalaman ka nan ba da dad'ewa ba, kayi tunanin ranar da zaka rok'e ni na yafe maka wanne hukunci zan yanke ni kuma a lokacin?" tana gama fad'ar hakan ta sauka a guje ta nufi b'angaren ta tana kuka sosai.

*******

Abba kuwa daga b'angaren sa direct b'angaren Umma ya nufa yana shiga ya ga Ibteesam d'in a tsaye tana mayar da pillows d'in kujera, "Yauwa Ibteesam" Abba ya fad'a yana shigowa, juyowa tayi ta kalle shi tace, "Na'am Abba". "A'a ya na ganki haka kamar mara lafiya? Meya same ki?" Ya tambaya yana kallon ta, "kaina ne yake min ciwo" ta bashi amsa kanta a k'asa. "Kin sha magani?" Ya tambaya yana kallon ta da kulawa.

"Eh nasha Abba". A lokacin Umma da Jidda suka fito daga d'aki Abba yace, "Ashe Ibteesam bata jin dad'i ban? sani ba?". Jidda ta kalli Umma itama ita take kallo kafin Jidda tace, "Eh ciwon kishi ne yake damun ta Abba" Jidda ta fad'a kai tsaye tana d'an murmushi.

"Ciwon kishi kamar yaya kenan?" Abba ya tambaya da mamaki a fuskar sa, dariya Umma tayi tace, "akwai wani abun ne?". "Yaron nan Zaid ne mukayi waya dashi yanzu yake sanar dani indai ba abincin Ibteesam yau bazai ci komai ba, to gashi kuma nazo itama bata da lafiya."

Kallon ta Umma tayi tace, "Eh amma ai zata iya dan dai d'an simple things ai bazai gagare ta ba". Turo baki gaba tayi bata san lokacin da tace, "Ina matar tasa ba sai tayi masa ba komai sai ni" ta fad'a ba tare xa tasan a fili tayi maganar ba, "matar sama bata da lafiya ai Ibteesam" Abba ya bata amsa yana kallon ta da mamaki dan sai yanzu ya gane maganar Jidda, saurin kallon Abba tayi ta kalli Jidda taga tana dariya sai ta d'an diririce tace, "Toh" abinda ta iya furtawa kenan tayi kitchen da sauri.

Murmushi Abba yayi ya fita daga falon Umma ta shiga? d'aki.

Rasa me zata dafa tayi sai kawai ta had'a chicken pasta da dan pepe soup, kasancewar Umma bata rabo da zob'o ta dafa ta had'a ta saka k'ank'ara ta had'a komai yadda ya dace sannan ta fito ta shiga d'akin Umma, suna zaune ita da Jidda tana taya Umma tsifa ta shigo da sallama ta mak'ale a jikin k'ofa tace, "Umma na gama." "To sannu da aiki, bara na kira Abban naku naki ya za'ayi dashi" ta fad'a tana d'auko waya ta kira Abba tana sanar dashi an gama, Ibteesam ta kalla? tace, "Yace ki kai masa part d'in sa zaije gidan ya duba shi yanzu sai ya tafi dashi". Da to ta amsa ta fice daga d'akin.

Bayan Abba yayi azahar aka saka masa abincin a mota ya tafi dashi, bayan ya shiga cikin gidan Daddy yake cewa, "Da kanka ka kawo abinciin? Kai amma Zaid ya wahalar da kai" ya fad'a yana murmushi.? "To ya za'ayi ai babu komai, da driver zanyi maka waya a tura sai na tuna yanayin da ake ciki a gidan ba kowa ya kamata a dinga bawa abinda Zaid zaici ba, ita kuma Ibteesam d'in bata jin dad'i da ita zan saka ta kawo". Girgiza kai Daddy yayi cike da gamsuwa yace, "Me ya same ta?". "Ciwon kai ta tashi dashi yau." "Allah ya k'ara lafiya, mun gode Allah ya saka da alkhairi. " Murmushi kawai Abba yayi kafin yace, "Amin, a gurguje abu akan auren sa da yake kan Ibteesam, sai nake gani ya kamata a sanar dashi a yanzu kodan yanayin ciwon sa." Daddy ya gyara zama yace, "in aka fad'a masa yanzu kenan ya samu abinda yake so cikin k'asaita, ni nafi so ya wahala ya san zafin neman abu ya rasa yasan cewa ba komai iko da k'asaita da fad'a suke bayarwa ba, shiyasa zanzo takanas na fad'awa Maryam d'in ta daina raga masa a kan komai ko marin ta yayi ta rama". Abba ya zaro ido waje yace, "ta rama fa kace?". "Eh ta rama in yayi sau d'aya yaga ta rama bazai sake yunk'urin dukan ta ba, amma indai zai mare ta ta tsaya tana kallon sa gobe ma zai kuma, za'a fad'a masa amma ba yanzu ba." Girgiza kai Abba yayi yace, "ai ko ba aure tsakanin su akwai tazarar shekaru da dama a tsakanin su ba'a ce in ya mare ta ta rama ba" Abba ya fad'a da murmushi yana mik'ewa tsaye dan sauri yake.
Daddy yace, "Hmm baka san halin Zaid bane wallahi da baka ce haka." "Duk da hakan dai baza ayi hakan ba gaskiya, yanzu zan tafi duka abinda yake akwai mayi waya". Daddy yace, "Shikenan Allah ya taimaka" Daga haka dai saukayi sallama Abba ya tafi.

Daddy da kansa ya d'auki abincin ya kai masa saman sa ya same shi a zaune sai wuci yake kamar zaki, kallon sa Daddy yake kafin yace, "Zaid lafiya?". Kallon Daddy yayi yace, "Waccan matar taka ce ta b'ata min rai, abincin precious ne?" Ya fad'a yana kallon abinda yake hannun Daddy.

"Eh shine, gashi nan kaci, Abban ta yazo yana sauri ya tafi dan da kansa ya kawo maka abincin" Daddy ya fad'a yana ajjiye masa. Baice komai ba? ya bud'e abincin ya tashi ya? d'auko plate da spoon ya fara ci Daddy kuma ya sauka.

D'akin Amina Daddy ya nufa ya same ta zaune ta dafe kai alamun wacce taci kuka ta k'oshi, "Amina lafiya?" Daddy ya fad'a yana shigowa d'akin.?

"Babu komai" ta bashi amsa ba tare da ta kalle shi ba dan shima tasan haushin ta yake ji, "Daman tambayar ki zanyi" Daddy ya fad'a yana zama nesa da ita. Kallon sa tayi ta d'an yi murmushi tace, "Meyasa na zubawa Zaid poison ko? Meyasa nake so na kashe Zaid,? Me yayi min,? Nida waye muke so muga mu? kashe shi, wannan sune tambayoyin ka ko?" Ta fad'a tana kallon sa ido cikin ido babu alamu tsoro ko nadama a tare da ita.



*Kar a fitar min da littafi dan Allah. *

*?ASAITAR SO!*

*45_46*

Not edited>??


Mamaki ya hana Daddy magana sai zuba mata ido kawai da yayi yana kallon ta har ta kai k'arshen maganar ta kafin yace, "Abinda zan tambaya kenan fad'a min ina jin ki" ya fad'a fuskar sa tamke yana kallon ta.

"Eh tabbas nice na bawa Zaid guda amma bada niyar kashe shi nayi hakan ba, sai dan......" saurin d'aga mata hannu yayi tare da fad'in, "Sai dan me? Nace sai dan me Amina!? Ni kike kallon idona kike fad'a min ke kika zubawa gudan jini na abinda nafi so a duniya guba kuma kike cemin ba dan ya mutu ba,? To dan ya samu lafiya kika bashi Amina?" Ya k'arasa maganar cikin fad'a da d'aga murya wacce tunda suke tare dashi bai tab'a yi mata ba.

Ta tsorata da yanayin sa sosai ta zaro ido waje ta girgiza masa kai tace, Wallahi Allah ban bawa Zaid guba dan ya mutu ba ka yadda dani ka tsaya nayi maka bayani". A fusace ya Mik'e tsaye yana jifan ta da kallon kask'anci yace, "Bayanin me zaki yi min Amina? Bayanin ta yadda kika d'auki hankali na kika zuba masa poison a ruwa shi zaki fad'a min,? Ban tab'a yin dana sanin zama dake ba sai yau, ban tab'a jin haushin ki a raina ba sai yau, ban tab'a jin na tsani wata halitta ba sai ke, ban san bakya sona ba sai yau Amina, duk me sona yaso Zaid shi kad'ai ne wanda na mallaka a duniya sai wanda yake cikin ki, bani da uwa bani da uba na rasa matata ta farko Zaid kad'ai nake kalla a duk duniya naji dad'i a raina, shi kika bawa guba kuma kike kallon ido na kike cemin badan ya mutu kika bashi ba, kika zama silar kwanciyar sa a asibiti yaron nan jiya da daddare baiyi bacci ba sabida azabar da kika saka shi a ciki, me ya tare miki a gidan nan Aminaaaaa,! Shi da ko sabgar ki baya shiga me yayi miki?" Ya fad'a muryar sa tayi rauni a lokacin.

Ta rud'e sosai tsoro ya kamata dan gani take zai iya dukan ta a lokacin, jikin ta ya hau rawa ta fara ja baya tana dana sanin fad'ar abinda ta fad'a masa tace, "Ka tsaya ka saurare ni dan Allah, ban tab'a kwana da nufin kashe Zaid ba hasalima...." bai san lokacin da d'auke ta da mari me zafi ba, dana shi baya so yaji tana cewa bata yi niyar kashe Zaid ba, "in zaki fad'a min gaskiyar dalilin ki na so ki kashe min d'a ki fad'a min, amma kika sake cewa bakiyi niyar kashe shi ba zan saka a kulle ki, ina da power da zan kulle ki koda ba'a k'asar nan bane balle a cikin Nigeria kuma wallahi babu wanda ya isa ya fito dake" ya fad'a yana nuna ta da yatsa idanun sa sun koma ja sabida b'acin rai.

Sai ta rasa me zatace kawai sai ta fashe da kuka ta takure a jikin bango kamar ba mai ciki ba, a fusace ya finciko ta da k'arfin gaske yaji abu ya fad'o a k'afar sa ya kalli k'afar tasa ya kalli daga inda abun ya fad'o ya dawo da kallon sa ga fuskar Amina da ta sake rud'ewa, sunkuya yayi ya d'auki d'an curin pillown da ya fad'o daga cikin ta ya kalle ta cikin mamaki, tashin hankali, ala'ajabi, b'acin rai, takaici yace, "Amina mai zan gani haka,? Daman yaudara ta kike ba ciki ne dake ba? Nace daman yaudara ta kike ba ciki ne dake ba!?" Ya fad'a cikin sauti mai amo wanda ya saka ra sake gigicewa ta d'aga masa kai alamun eh ba tare da ta sani ba.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" shine abinda ya iya furtawa ya jingina da wardrobe d'in ta ya zuba mata ido kawai cikin rashin sanin me zaice, me kuma zaiyi mata, "wannan dalilin ya saka ki tunda cikiin ki ya kai watan da zai bayyana kike gudu na bakya kwana a inda nake,? Na gane shiyasa duk wani abu da zai had'a ni dake kike nisantar kanki dashi, sai kice min cikin ya saka bakya so na rab'e ki ashe k'arya kike, Amina wanne hukunci zan miki na wuce?". Kuka take so yi sosai cikin kunya da nadamar abinda ta aikata tace, "ka kashe ni in zaka iya, amma ina so ka tsaya ka saurari abinda zan fad'a maka koda baza ka yi amfani dashi ba". "Kina da sauran abinda zaki fad'a min ne har yanzu,? To ina jinki sanar dani nima wanne shiri ake na kashe ni,? Fad'a min ina jin ki" ya fad'a yana takowa inda take ita kuma tana yin baya.

"Dan Allah ka saurare ni kaji abinda zan fad'a maka". Shak'e ta yayi a jikin bango yace, "baki da sauran abinda zaki fad'a min Amina, yau nayi dana sanin kasancewa dake a rayuwa ta, Zaid yasha fad'a min yana ganin rashin gaskiya a tare dake amma nace ba haka bane har nayi masa fad'a ashe maganar sa gaskiya ce, kin cuce ni kin kuma cuci kanki" yana gama fad'ar hakan ya cillar da ita a kan gado ya fita daga d'akin da saurin gaske.

Yana fitowa daga d'akin yaci karo da Yaya Babba da matar sa a falo da alama shi suke jira, bashi da k'arfin giuwar da zai musu magana hakan ya saka shi d'auke kansa kamar bai gansu ba ya fara taka steps d'in saman sa, "Lallai Abubakar yau ni ka gani ka d'auke kai" Yaya Babba ya fad'a yana kallon sa da mamaki.

Numfashi Daddy ya fesar ya tsaya daga niyar hawa saman da yake yi yace, "Kayi hak'uri." "To daman zancen tafiya saudia ne ya kawo ni, yaushe ne tafiyar ne naji shiru kuma na riga na fad'awa abokai zanyi tafiya kar naji kunya." Ya fad'a yana kallon Daddy da shima shi yake kallo cikin mamaki.

"Amma kasan jiya Zaid a asibiti ya kwana ko? Ko kuma zuwan ka Saudia yafi lafiyar d'an dana haifa ne,? Dan Allah ka k'yale ni tun kafin na fad'a maka magana mara dad'i" daga haka ya hau saman ya barshi baki bud'e yana kallon sa har ya b'acewa ganin sa.

Yaya Babba da ya daskare a wajan ya juya ya kalli matar sa cikin mamaki yace, "Kalli abinda yaron nan yayi min fa." Tab'e baki tayi ta bud'e hannayen ta tace, "Wata ran ma dukan ka zaiyi indai baza ka tashi tsaye ba, ka duba wulaqancin da yayi mana yanzu". K'wafa Yaya Babba yayai yace, "kira min Eman d'in mu gama da ita mu tafi."

"Ni ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kasan ba son shiga cikin gidan nake ba gwara na kira ta a waya" ta fad'a tana fito da waya tare da kiran wayar Eman, ba jimawa Eman d'in ta fito ta gaishe su suka amsa Yaya Babba ya kalli gida gabad'aya yaga babu kowa kafin yace, "karb'i akwai bayanin komai a ciki" ya fad'a yana mik'o mata leda. Ba musu ta karb'a daga nan suka fita daga falon ko wanne da mugun nufin sa a zuciyar sa.

Fitar su babu jimawa Mummy da Zahra suka shigo cikin falon suna sallama amma shiru babu kowa, zama sukayi Mummy ta kalli Zahra tace, "Kira wayar Zaid d'in muji" ta fad'a tana mik'a mata wayar ta, gab da wayar zata katse ya d'auka tare da fad'in, "Mummy". "Na'am Zaid nazo gidan naku amma banga kowa ba kana ina?". "Ina sama, steps d'in da yake kusa da dining zaki biyo". Kashe wayar tayi ta kalli Zahra tace, "Wai mu hau saman sa, ma hau saman gidan mutane bayan basu san da zuwan mu ba?".

Zahra tace, "To mu daman ba dubiya muka zo ba, mu hau kawai wajan nasa" ta fad'a tana mik'ewa tsaye, mik'ewa itama tayi suka bi hanyar da ya fad'a musu suka fara hawa saman nasa.

Da sallama suka tura k'ofar falon suka shiga, amsawa yayi yana daga zaune yace, "Welcome Mummy". Sai da ta zauna kana tace, "Ina mutanen gidan ne naji gidan naku shiru?". D'an mik'ewa yayi daga kashingid'e d'in da yake yace, "Ban sani ba."

"To ya jikin naka?" Ta fad'a tana kallon sa, sai da yayi ajiyar zuciya kana yace, "da sauk'i." "Babu abinda yake maka ciwo yanzu,? Tun d'azu naso zuwa to da Abban su Zahra zamu zo na zauna zaman jiran sa ya kira yace min sun shiga meeting." "Eh babu" ya fad'a kamar zaiyi kuka.

"Yah Zaid wannan abinci haka, gaskiya zanci daman yunwa nake ji" Zahra ta fad'a bayan ta bud'e abincin dake gaban sa, da hannu yayi mata alama da zaki iya ci ya mayar da hankalin sa kan wayar sa, "Mummy fa?" Ya fad'a bayan ya d'ago yana kallon Mummy. Girgiza kai Mummy tayi alamun ta k'oshi, Zahra da ta fara cin abincin ta kalle shi tace, "Kai gaskiya abincin yayi dad'i sosai, Mummy kici kiji". Murmushi yayi kad'an jin an yabi abincin Ibteesam yace, "Mummy precious ce tayi fa kici" ya fad'a yana mayar da hankalin sa kan wayar sa.

"Sirika ta?" Ta tambaya tana kallon sa, d'aga mata kai yayi alamun eh, "lallai Zaid an girma, yaushe to zaka kawo min ita mu gaisa kafin na bar Kano?". "In naji sauk'i" ya bata amsa a hankali. Murmushi tayi tace, "Allah ya bada lafiya, ina nan ina jiran ta".

**********

"Anty Ibteey! Kizo ga Khalid yazo" Jidda take fad'a da d'an k'arfi tana jijjiga Ibteesam da take bacci, bud'e idon ta tayi ta kalli Jidda taja dogon tsaki tace, "Jidda wai ban hana ki tashi na in ina bacci bane ba?". Jidda tace, "Allah ya baki hak'uri, Khalid ne daman yazo yana falon Abba yana jiran ki" tana gama fad'a mata hakan tayi hanyar fita daga d'akin. "Khalid kuma? To me zan masa?" Ta fad'a tana bin Jidda da kallo, "ina na sani?" Jidda ta bata amsa lokacin da take ficewa daga d'akin.

"Mtswwwww to ni uban me zan masa zai zo ya saka a tashe ni ina bacci na mai dad'i" ta fad'a tana sakkowa daga kan gadon ta shiga band'aki, fuska ta wanke tayi alwala ta fito ta zari hijjabi ta fita daga d'akin, falon Abban ta nufa da sallama ta hango shi a zaune yana tab'a waya yana gano ta ya ajjiye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login