Showing 48001 words to 51000 words out of 171073 words

Chapter 17 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7844

tamu". Tayi murmushi suka shiga ciki.

"Shege mutumi na wallahi yarinyar tayi mugun yi, ashe dai ka iya zab'e, ka ganta kuwa?" Hameed ya fad'a bayan su Ibteesam sun shiga cikin gidan.

"Shege!" Zaid ya maimaita yana kallon Hameed, "yi hak'uri ba haka zance ba kyauwun tane ya zaunar dani shiyasa" ya fad'a yana murmushi. "Kyauwun tane ya zautar dakai,? Hameed kana cewa kyauwan tane ya zautar da kai a gaban ido na? Are u mad Hameed,? She's my wife fa ko ka manta ne? Hameed..." K'asa k'arasa yayi sabida nauyin da yaji k'irjin sa yayi masa ga kuma fad'an da yake yi, zaro ido Hameed yayi ganin yadda yanayin sa ya sauya lokaci d'aya hankalin sa ya tashi yace, "I'm sorry Zaid wallahi ban fad'a da wata manufa ba hasali ma ni da wasa nake maka maganar, calm down pls" ya fad'a a rud'e yana kallon Zaid d'in da ya kifa kansa a kan sitiyarin motar yana hakki.

Sosai yake jin zuciyar sa na wani irin tsalle in ya tuno murmushin da ta yiwa Hameed ga kuma yabon kyauwan ta da Hameed yake sai yaji wani dogon abu mai kama da mashi ya soki zuciyar sa, a hankali ya dinga sauke numfashi kana ya d'ago kai idon sa sun koma jajaye ya kunna motar baice komai ba ya fara tafiya. "Kayi hak'uri kaji Zaid ban san zakayi kishi da abinda na fad'a ba". Kusan sub'ucewa sitiyarin motar yayi a hannun sa sabida zallar b'acin rai ya kalli Hameed yace, "baka d'auka zanyi kishi ba kace,? In banyi kishi ba Hameed dariya zanyi,? I'm talking to u dariya zanyi!!" Ya fad'a cikin d'aga murya yana dukan sitiyarin motar cikin wani irin takaici. Kan motar ne ya kwace yazo dukan wata bishiya Hameed yayi saurin dawo dashi dai-dai yana kallon Zaid d'in da tsantsar damuwa a fuskar sa.

Wuci yake yana tuk'a motar shi kam Hameed addu'a kawai yake Allah ya kaisu gida lafiya kar ya kashe su a hanya, suna isowa gate d'in gidan su Zaid Hameed yace, "Tsaya na sauka basai na shiga ciki ba" ya fad'a ba tare da ya kalle shi, ko kallan gefen da yake ma baiyi ba ya danna horn aka bud'e masa ya cilla motar cikin gidan, ya gama parking ya bud'e motar ya fito shima ya fito ya nufi hanyar fita yana murmushi shi kuma yayi cikin gida ransa a mutuk'ar b'ace.

A cikin gidan kuwa yana shiga Anty Amina da take dakon jiran dawowar sa ta shiga d'akin Eman da gudu tace, "Maza ya dawo tashi kije kafin ya kuma fita". Jiki na rawa Eman ta mik'e hijjabin ta har k'asa tace, "Anty ina khamshin kuwa?". "Kina yi mana Eman, maza kije kin san hali? mijin naki" da sauri ta fita ta nufi saman Zaid gaban ta na dukan d'ari-d'ari.

A bud'e k'ofar falon tane hakan ya saka taji dad'i ta shiga da sallama ta mayar da k'ofar ta rufe, cigaba take da takawa har tazo k'ofar d'akin nasa ta kasa kunne ko zata jiyo wani abun, tsittt babu motsin komai kamar babu kowa a d'akin hakan ya bata k'arfin guiwar tura k'ofar d'akin ta shiga, ya fito daga band'aki ita kuma ta shigo d'akin ya kalle ta da mamaki amma sai ya b'oye mamakin sa bai kula ta ba ya zauna a gefen gado tare da d'auko wayar sa, ganin bai mata fad'a ya hantare ta ba taji wani irin sanyi a ranta tayi murmushi ta tako a hankali zuwa inda yake, zare hijjabin ta tayi kayan jikin ta suka bayyana, sanye take da wando three quarter sai riga wacce ko cibiya bata rufe ba kanta babu d'ankwali, "sannu da zuwa Baby na" ta fad'a a shagwa6e tana niyar kai hannun ta jikin sa.

Khamshin turaren ne ya bugar masa da kai yayi saurin dafa kansa yana yamutsa fuska, ita kuma ganin bai hana ta ba ya saka ta zauna kusa dashi tana niyar kai hannun ta kafad'ar sa yayi saurin rik'e hannun nata, zubawa hannun ido yayi kamar yana so ya gano wani abun da yake jikin hannun, murd'e shi yayi har sai da ya bada sautin k'asss ta saki k'ara idon ta na cikowa da hawaye.

"Ke kin san waye Zaid kuwa,? Da kin san ni da baki zo a haka kina tunanin wai zaki d'auki hankali na ba, dake da yaron namiji wanda bai haura shekara biyar ba haka kuke a waje na" ya fad'a yana sake murd'e hannun nata idon ta ya fito waje tana niyar sume masa, marin ta yayi ta farfad'o kana ya saka k'afa ya tankad'a ta ta fad'i a k'asa ya dafe kansa dan sosai turaren ya ratsa shi yace, "na baki 10 seconds ki bar min d'aki in ba haka ba...." ai bata jira ba ta mik'e ta fita da sauri hannun ta nayi mata ciwo sosai.

"Washhhh" shima ya furta ya tare da kwanciya a kan gadon ya dafe kansa, wani irin zir zir zir yake ji a jikin sa ko ina na jikin sa ji yake wani abu yana masa yawo kamar tafiyar kiyashi, mik'ewa yayi zaune ya ya bud'e bedside d'in kusa dashi ya d'auki maganin ya b'alla ya d'auki ruwan da yake ajjiye a kusa dashi ya sha, ajiyar zuciya yake saukewa a hankali yana lumshe ido a haka bacci ya d'auke shi.

Bai tashi ba sai shida na yamma ya mik'e dak'yar ya shiga band'aki yayi wanka tare da alwala ya fito, maimakon ya fara shiryawa sai ya zauna gefen gado ya dafe kansa har lokacin yana cikin yanayin da yake jin sa, cizewa yayi ya mik'e ya shirya ya fita daga d'akin ya shiga small cafe d'in sa ya had'a coffee me zafin gaske ya fito ya zauna, sha yake a hankali yana kallo wani wajan daban, _Our wife to be,_ abinda Hameed ya fad'a ne ya fad'o masa rai sai kuwa yayi cilli da cup d'in ya fashe a wajan, tsaki yaja kawai ya mik'e ya koma d'akin ya d'auki wayar sa da makullin mota ya sauka ta waje.

Masallaci ya shiga ya nemi waje ya zauna har aka tayar da sallah aka idar ya d'an zauna jimmm kad'an kafin ya mik'e ya fito, a harabar gidan su suka had'u da Daddy yayi saurin d'auke kansa dan kar ma daddy ya masa magana, "Zaid ina zaka je?" Daddy ya tambaya yana k'okarin shiga ciki, "yanzu zan dawo" ya bashi amsa yana shiga cikin motar dan baya so ya tsayar dashi.

A hankali yake tafiya yana bin hanyar da suka bi d'azu har ya k'araso bus stop, wayar sa ya d'auka ya d'an yi dube-dube kana ya danna kira, har ta katse ba'a d'auka ba ya sake kiran ana biyun aka d'auka tare da sallama,? "Wa'alaiki salam, ku fito ga driver nan ya zo d'aukar ku yana waje" yana gama fad'a mata hakan kawai ya datse kiran ya cigaba da tuk'in sa.

A can b'angaren Ibteesam kuwa kallan Jidda tayi da mamaki tace, "Jidda shine fa, a ina ya samu number na to?". "Ina zan sani, kinga tashi mu fita tun kafin ya b'alla mu danni wallahi tsoro yake bani" Jidda ta fad'a tana mik'ewa tare da yafa mayafin ta, Dada da ta fito daga d'aki ta gansu a tsaye tace, "A'a badai tafiya zakuyi ba?." "Tafiya zamuyi Dada" Jidda ta bata amsa tana neman wayar ta, "to ba laifi ku gaida iyayen naku, ungo wannan ku hau mota" ta fad'a tana mik'o musu dubu biyu, karb'a sukayi suka yi mata godiya suka fito.

Motar da aka kawo su d'azu suka gani a fitilolin ta a kunne, "Anty Ibteey ki shiga gaba kawai ni baya zan shiga" kafin tace wani abu Jidda ta k'ara sauri ta bud'e motar ta shiga da sallama,? a ciki ya amsa mata a lokacin Ibteey ta bud'e gaban motar ta shiga ba tare da ta lura da waye a ciki ba, tana juyowa da niyar gaida wanda ya turo suka had'a ido tayi saurin d'auke idon ta shi kuma ya mik'e daga kwancen da yake ya gyara kujerar, "Inda driver d'in ne haka zaki shigo gaba ki zauna kamar matar sa?" Ya fad'a lokacin da ya fara jan motar fuskar nan tasa a had'e.

Shiru tayi bata amsa masa ba dan bata san abinda fad'a ba, juyowar da yayi ya kalle ta ya saka ta d'an turo baki gaba cikin shagwa6a tace, "ai bashi d'in bane" dan har ga Allah takura kanta take zama waje d'aya dashi kawai daurewa take sabida Abba.

Baice komai ba suka cigaba da tafiya babu wanda ya sake magana har suka iso k'ofar gidan su, Jidda ta bud'e murfin motar tace, "Mun gode". "Ki d'auki kaya a boot ki shiga dashi ciki and ki gaida Mama" ya fad'a yana bud'e boot d'in ta cikin motar, zagayawa tayi ta d'auki leda d'aya All???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ah yasa Jafar na wajan ta bashi leda d'aya suka shiga ciki.

Hannu ta saka zata bud'e itama ya mayar da lock d'in motar ya kulle yana bin hannun nata da kallo, jan lallen da yake zane a tafin hannun tane yayi bala'in tafiya da imanin sa bai san lokacin da ya kamo hannun nata ba ya zubawa zanen henna d'in ido ya fito rad'au ga zanen k'ananu, d'an yatsan sa ya saka yana bin zanen hannun nata a hankali cikin d'aukar hankali, "Meye sunan shi?" Ya fad'a yana cigaba da zana yatsan sa akan zanen lallen. So take ta kwace hannun ta amma kamar ya saka mata wani abu na rashin kuzari a jikin ta ya kashe mata jiki, yadda yake bin zanen lallen hannun ta ba k'aramin kashe mata jiki yayi ba har ta lumshe ido bata san tayi ba, "Henna" ta furta can k'asan mak'oshi idon ta har lokacin ya lumshe.

Kiss yayiwa tafin hannun nata khamshin lallen ya bugi hancin sa ya d'an yatsine fuska, d'an kwace hannun ta tayi ba tare da ta kalle shi ba, "dame ake yi?" Ya tambaya yana kallan fuskar ta, kallan sa tayi shima ita yake kallo suka had'a ido ya d'aga mata gira guda d'aya tayi saurin saukar da kanta k'asa tace, "Lalle". "Meye lalle?". "Ban san yaya zance maka ba." "Okay, yayi miki kyau lokacin da Mama na tana nan tana yi a hannun ta." Bata ce komai ba kanta dai yana k'asa ji take kamar ta had'a shi da taga glass d'in motar ya yanka masa wuya, "do u love me?". Kamar daga sama taji tambayar tasa sai gaban ta ya fad'i ta kasa d'agowa ta kalle shi, girgiza masa kai tayi alamun a'a, sake tamke fuskar sa yayi yace, "Shi kike so bani ba ko?". D'aga masa kai tayi alamun eh, sai kuwa ya saka hannu ya doke mata baki, "are not serious, a gabana kike fad'ar hakan?" Ya tambaya cikin fad'a kamar zai dake ta, rik'e bakin ta tayi dan taji zafi ba kad'an ba idon ta ya kawo ruwa hawayen da take ta rik'ewa suka fara zuba, "wait, meyasa bakya sona?". Cikin muryar kuka tace, "Ni ba kaine bana so ba halayyar kace bana so" ta fad'a lokacin kuka ya fara cin k'arfin ta.

Kallon ta yake da mamaki daga d'an buge mata baki sai wannan uban kukan kamar wanda ya dake ta, sai kuwa ta sake bashi haushi yace, "wacce halayyar tawa? Ina da halayya ne mara kyau?". "Look at you? Kalli kanka ji wani zane kamar musulmi ba, sam baka amfani da kayan mu na hausawa sai dai na turawa." Zaro ido yayi waje cike da dubin mamakin ta yace, "Ohhh dan nace ina son ki har kin samu bakin da zaki fad'a min wannan maganar,?". "Son da kake min d'in ya saka na fad'a dan nasan zaka iya canjawa tunda har kana so na d'in." "Damn it, who told you son da nake miki har ya kai ki tsaya a gaba na kina fad'a min wannan maganar,? Kin manta waye ni ne?" Ya fad'a da d'an daga murya.

"Another bad behavior, komai fad'a, shouting, kuma a haka kake cewa kana so na kana yi min fad'a,? Ba dole nafi son Khalid ba tunda shi baya yi min fad'a duk abinda nake so shi yake yi kummm...." d'au ya d'auke ta da mari mai zafin gaske yace, "Khalid again? Kunne k'ashi ne dake ne wai,? Sau nawa zan miki warning akan sa? Yau shine har da fad'ar sunan sa a gaba na a kuma cikin ido na,? Ohhh god kin san ya nake ji?" Ya fad'a yana d'an dafe kansa cikin fad'a.

Dafe take da kuncin ta tana kuka sosai tana jin sa yana fad'an sa, "get out for car" ya fad'a yana wuci, "another one shine duka, a haka zan soka kana duka na,? Bazan tab'a son mutum mai irin halayyar ka ba". "I said get out!" Ya fad'a da d'an k'arfi yana nuna mata k'ofa, "Sorry" ta fad'a cikin kuka ya d'ago ido suka had'a ido a lokacin da hawaye suke gangarowa a idon ta, ta d'auke kai ta bud'e murfin motar ta fita ta shige gida da sauri ko waiwayen sa bata yi ba.

Da k'arfi ya finciki motar har yana tayar da k'ura ya bar unguwar zuciyar sa nayi masa wani irin k'una kamar ana tafasa ta haka yake ji.



*Dan Allah kada a fitar min da littafi.*=?O?


*?ASAITAR SO!*

*33_34*



Ibteesam kuwa haka ta shiga cikin gida fuskar ta a had'e ko ta babban falo bata bi ba sabida takaicin da take tare dashi, a falo ta tarar dasu Umma a zaune sun saka kayan a gaba suna ta kallo, kayan ciye-ciye ne da yawan gaske sai turaru ka masu kyau da tsada.

"Umma ni ya zanyi da lamarin mutumin nan ne? Anya zan iya abinda Abba ya saka ni?" Ta fad'a tana zama a kusa da Umma, "me kuma ya had'a ku yau?". "Tsinannen fad'a masa Umma har da mari fa" ta fad'a kamar zatayi kuka.

"Jidda tace min yace wai ku daina hawa keke napep?". "Eh Umma kiji sai kace wani miji na sai kafa min doka yake, wallahi bai isa ba ba aure na yake ba bazai takura min ba, darajar alqawarin Abba kawai yake ci na raga masa yau." Umma ta d'an yi murmushi tace, "Hak'uri dai zakiyi ki sauke alqawarin da kika d'aukawa Abban naku." "Sabida hakan kawai na k'yale shi yau ai, da anyi abu yace shi sona yake to haka ake so?" Ta fad'a tana jan tsaki.

"Ki lallab'a ku rabu lafiya dai ko daina masa rashin kunyar nan taki shine zaku zauna lafiya dashi" Umma ta fad'a ba tare da ta kalle ta ba, "Umma ni mamaki kuke bani keda Abba wallahi, kamar an canja ku in kuna cewa nayi abinda yake so, kun manta wai babu komai tsakani na dashi ne? Ba d'an uwa na bane ba kowa nawa ba amma kuka amince na saki jiki dashi haka" ta fad'a tana kallan yanayin Umman. Murmushi Umma tayi mai sauti tace, "Ibteesam kenan, amincewar da mukayi dake ya saka muka amince ku zama abokai dashi, yadda da tarbiyyar ki ya saka hakan ba wani abun ba" ta fad'a mata tana d'an bud'e ledar da take gaban ta.

Bata ce komai ba kawai ta mik'e ta shiga d'aki.

Umma ma kwashe kayan tayi ta ajjiye gefe kasancewar ba ita ke da girki ba tasan Abba zai shigo ya musu sai da safe in ya shigo zata nuna masa.

Bayan Abba ya shigo Umma ta kwaso kayan ta ajjiye a gaban sa ya kalle ta ya kalli kayan yace, "Shopping kika je ne?". Y'ar dariya tayi tace, "Shopping ba tare da ka sani ba,? D'azu da na aiki Jidda da Ibteesam gidan Dada suka had'u da mutumin nata har sun shiga napep ya saka suka fito, na tak'aice maka labarin dai shi ya kaisu ya koma ya d'auko su ya kuma hana su hawa napep ya kuma bawa Jidda kayan ta shigo dasu."

"Tohh har sun fara shiri haka?" Abba ya fad'a yana hard'e hannayen sa a k'irjin sa, "To ina na sani ta dai dawo ido yayi ja alamun sun yi fad'a". Murmushi Abba kawai yayi yace, "Kuyi amfani da kayan kawai, ma k'arasa maganar gobe sai da safen ku" ya fad'a yana ficewa daga falon nata.

Zaid tunda ya isa gida ya kunna sigarin sa yana zuk'a cikin b'acin rai, _Ba kaine bana so ba halayyar kace bana so,_ kalaman ta suka fad'o masa a rai ya cillar da sigarin ya murza ta da takalimi yana lumshe ido, numfashi ya furzar ya kama k'ugu yana kallan sama da hadari ya fara had'owa gari ya fara yin bak'i aka fara walk'iya sama-sama, "ni zata kalla tace ina da bad behavior,? Who is she?" Ya fad'a yana kaiwa iska naushi cikin takaici, k'arar wayar sace ta katse mata hanzari ya juya k'wayar idon sa ya kalli wayar ganin sunan Daddy ya saka ya d'auke idon sa ba tare da ya d'aga kiran ba, kiran ne ya sake shigowa hakan ya saka ya d'auka a fusace ya kara a kunne ba tare da ya ce komai ba, "Zaid sauko k'asa yanzu ina jiran ka" yana gama fad'ar hakan ya katse kiran bai jira yaji mai zaice masa ba.

D'an k'aramin tsaki yaja? gabad'aya yau ranar ransa a b'ace yake, Hameed ya b'ata masa rai da farko na biyu Eman na uku ita kanta Ibteesam d'in, fitowa yayi daga varander ya nufi k'asan a guje, a babban falon ya tarar dasu a zaune an saka Eman a gaba da d'aurarran hannu ana ta jera mata sannu, bai san lokacin da yaja tsaki ba wanda ya jawo hankalin mutanen falon ya kalli Daddy yace, "Daddy gani" ya fad'a hannun sa a hard'e a k'irji yana kallan gefe d'aya, "Zaid me ka aikata haka?" Daddy ya tambaye shi yana kallon sa, "me kuma nayi?" Ya fad'a yana kama k'ugu da hannayen sa duka biyun yana kallan Daddy.

"Au kana so kace baka sani bama kenan?" Daddy ya fad'a yana kallan sa, "Dad in na sani kasan bazan tambaya ba" ya fad'a cikin k'osawa da maganar gabad'aya, "Kalli hannun Eman" ya fad'a yana nuna masa inda Eman take, kallan wajan da aka nuna masa yayi ya dawo da kallan sa ga Dad yace, "Na gani akwai wani abu ne?". Gabad'aya kowa na falon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login