Showing 156001 words to 159000 words out of 171073 words

Chapter 53 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7861

yace mata ba, sai ta samu kanta da hawaye tana sake k'ank'ame shi shima haka a haka bacci ya d'auke su dukkan su.

Bata farka ba sai sha d'aya saura na safe tana bud'e ido taga baya nan ta mik'e zaune tare da tab'a jikin ta, babu zazza6i amma har lokacin kanta da nauyi duk da babu ciwo, sakkowa tayi daga kan gadon babu laifi ta yake k'afar tata ta shiga band'aki, wanka tayi ta sake gasa jikin ta tana yi tana tuna kalaman Zaid tana murmushi har ta fito, kaya ta gani a ajjiye a kan bedside ta k'arasa wajan ta tarar da wata k'aramar paper mai kyau a kan kayan, d'aukar paper tayi tana karanta abinda ya rubuta a jiki, _i hope kin tashi lafiya? Ga kaya nan na ajjiye miki ki shirya bana so kisha wahalar zuwa room d'in ki, naje wani waje zan dawo yanzu ina fatan baza kiyi fushi ba, ki kula da kanki kici abinci na ajjiye miki, i love you soo much my sugercaned'?._

Rungume takardar tayi tana murmushi tana jin k'aunar sa na sake shiga jikin ta a haka ta shirya tsaf cikin rigar da ya ajjiye mata ta gyara d'akin duk da bata jin dad'i, falo ta fito nan taga abincin taji baza ta iya k'in ci ba tunda shine yace ta had'a tea tasha kawai bayan ta gama ta kwashe kayan ta daga d'akin na mayar d'akin ta tana jin farin cikin da ita kad'ai tasan adadin sa.

A lokacin ta d'auki wayar ta dai-dai lokacin da kiran Zahra ya shigo ta d'auka tare da sallama, "Amarya wato wayar ma sai anga damar d'auka?" Zahra ta fad'a ciki? tsokana, "ban sani ba" ta bata amsa itama tana murmushi, "muna gidan naki ai sai ki sakko ko kuma muzo mu d'auko ki ne?". Tsaki tayi tace, "Allah ya shirye ki" ta kashe wayar ta fito daga d'akin. A hankali take sakkowa k'asan tana ji kamar iska zata d'auke ta amma haka ta daure har ta k'araso falon suna zaune sai dariya suke yi da alama hira suke mai dad'i, Fateema ce ta fara hango ta ta mik'e tana fad'in, "Waii amarya kinga yadda kika yi kyau kuwa a dare d'aya kawai?". Hakan yaja hankalin sauran duka suka juya suna kallon ta. Banza tayi musu tazo ta zauna tana bin su da kallo da murmushi a fuskar ta tace, "Sannu ku da zuwa y'an mata". "Kan bala'i, wato y'an mata ko? Lallai kin rik'a daga kwana d'aya har an fara kiran mu da y'an mata?"Amina ta fad'a tana rik'e baki.

Dariya tayi mai kyau tace, "to in bance y'an mata ba manyan mata zance? Allah dai ya aurar mun daku". Sai kuwa sukayi mata cahh a ka kowa na fad'ar albarkacin bakin sa cikin raha.

A lokacin Zaid ya shigo yana waya idon sa ya fad'a kanta da take dariya sosai da alama tana cikin nishad'i, cakk ya tsaya yana k'are nata kallo yana murmushin da ba kowa yake ganin sa a fuskar sa ya daina fahimtar abinda ake fad'a masa a wayar sai kawai ya kashe ya had'e hannayen sa yana kallon ta,? duk sunga Zaid d'in itace bata ganshi ba hakan ya saka suka zuba mata ido har ta gama a lokacin suka had'a ido dashi, cak ta tsayar da dariyar sai murmushi ta d'auke idon ta ta mayar kan tv, k'arasawa yayi inda take ya mik'ar da ita tsaye yana kallon ta yace, "Kinyi kyau Precious" ya fad'a yana jan ta jikin sa ya rungume ta tsam a jikin sa.

Su Zahra sai aka fara kallon-kallo ana kunshe dariya cikin burgewa, Zahra ta zaro waya tana musu video cikin burgewa, d'ago ta yayi daga jikin sa yayi mata kiss a kuncin ta yace, "Kinci abincin?". Kai ta d'aga masa alamun eh yace, "Really?". Sai ta shagwa6e tace, "Nasha tea kawai". Girgiza kai yayi yace, "Tea bazai rik'e ki ba."
"Kai kaci ne?".
"A'a banci ba."
"Meyasa?".
"In kika ci kamar naci ne."
"Nidai A'a".
"Ni kuma eh" ya fad'a yana bata kiss a lips d'in ta.

Fateema da taga abin fa zai wuce kansu sai tayi gyaran murya da dole ya saka hi ya juya ya kalle su, girgiza kai yake har lokacin yana rik'e ita cikin mamaki yace, "mutanen Gombe yaushe kuka shigo?". Suka kalli juna Zahra tace, "Tun kafin ka shigo muke a nan?". Da mamaki yace, "Really?". Zahra tace, "Of course". Ya kalli Ibteesam yace, "Wai haka precious?". Ta d'aga masa kai alamun eh.

"Damn it! Banfa gansu ba in ba yanzu ba" ya fad'a sabon murmushi shinfid'e a kyakykyawar fuskar sa, ya juya ya kalli Ibteesam yace, "Ta tabbata in kina waje bana ganin kowa sai ke" ya fad'a yana lakuce mata hanci. Zahra da ta cika da mamakin cousin d'in nata ganin yadda yake magana da murmushi kamar bashi ba bata san sanda tace, "Yaya Zaid yau kaine da murmushi haka da magana?".

Fad'ar hakan da tayi sai ya sake saka shi murmushin da bai shirya ba shi kansa yasan yau ta daban ce cikin rayuwar sa shima ya sani, bai amsa ba yace, "Zo muje kiga wani abu" ya fad'a yana jan Ibteesam zuwa waje. Ibteesam ta juyo ta kalle su ta d'aga musu gira d'aya ta fita, sai kuwa suka kwashe da dariya Fateema tace, "Allah ya roke ka muma ka aurar damu, ke anya bazan cewa Hajiya kaka ayi bikin nan ba? Kinji yadda suka saka min shauk'in son yin aure?". Zahra tace, "bake kad'ai ba Faty kalle su fa kamar a india sai soyayya ake zubawa har bai kula damu ba, wai yau Yaya Zaid ne yake murmushi haka." Aysha tace, "Ke ba dole ba Allah kad'ai yasan abinda ya kwasa dan daman tasha gyara" sai kuwa suka sake fashewa da dariya.

Kwalla musu kiran da suka ji tana yi ne ya saka su suka fita a guje suka tarar da ita a gaban wata mota fara karrr sai k'yali take sai tsalle take tana murna shi kuma yana kallon ta yana ta murmushi kamar soko, "Sisters kunga mota ta" ta fad'a musu tana nuna musu motar da hannu tana rungume Fateema.

Sai suka sake gigicewa Zahra ta fad'a jikin ta da k'arfin gaske har taso fad'uwa tana fad'in, "Congratulations sister". K'arasowa wajan yayi ya d'aure fuska yace, "Are u mad Zahra? Kin kika yar da ita fa?". Zahra bata kula shi ba sai zuzuta motar da suke yi suka amshi key d'in suna zaga gidan.

Sai da suka gama murnar sannan suka koma ciki suka same su a zaune a kan kujera har lokacin Ibteesam farin ciki take ta rasa abinda zatace masa, ajjiye mata key d'in sukayi suka tattara suka koma part d'in Anty Amina da zumud'in suje su fad'a mata, "thanks you so much Baby, har na rasa me zance maka" ta fad'a tana kallon sa sai kuma ga hawaye sharr a idon ta.

"Ya rabbi, pretty meye na kukan kuma?" Ya fad'a a rud'e yana kallon idon ta da yake fitar da ruwa, "kukan farin cikin nake Baby" ta fad'a tana sake tsiyayar da hawayen, kissing d'in lips dinta ta fara gently har sai da yaga hawayen ya tsaya sannan ya zare bakin sa yace, "Ko kukan farin ciki ne bana so na ganshi a fuskar ki, kin wuce komai a waje na ina kwatanta kyautar da kika yi min ne nima nayi miki amma badan ta kai waccan ba, ki daina kuka kinji komai na Zaid naki ne, ganin kukan ki yana tayar min da hankali over sai naji kamar bani da amfani indai har zan barki kiyi kuka."

Murmushi take sosai yace, "wannan murmushin naki shi kad'ai ya ishe ni basai kince komai ba". Dariya tayi kad'an tana kwance a k'irjin sa yace, "wayyo Mama, Mummy, Umma na, kizo zan mutu, ka bari please da zafi" ya k'arasa fad'a cikin zolaya da tsokana kamar ba Zaid ba sai kuwa ta cusa kanta a k'irjin sa tana kukan shagwa6a, y'ar dariya yayi kad'an yace, "I love you precious". "I love you more Baby." "Me kike so?".
"Kai".
"Oh ready ni naki ne, wani abu wanda kike so a duniya zaki fad'a min."
"Farin ciki kuma ka bani."
"Nop precious just tell me."
"Nifa babu."
"Akwai baza ki fad'a bane amma zan gano da kaina, kuma in na gano zan baki shi insha Allah."
"Nifa kasancewa da kai yafi min komai a rayuwa ta Baby"

"Muje mu gaida su Daddy?" Ya fad'a mata a kunne, d'aga masa kai tayi alamun eh, yace, "zaki iya zuwa?". Tace, "Zan iya mana." Yace, "kar fa su gane abinda Zaid yayi miki dan naga......" bakin ta tayi saurin rufewa da hannun ta tana cusa kanta a k'irjin sa. Dariya yayi mai kyau kafin ya mik'e ya hau sama ya d'auko mata mayafi ya yafa mata ya rik'e hannun ta suka fita.


*?ASAITAR SO!*

*87_88*

Not edited >?'?




Suna fita taga ya nufi sabuwar motar ta sai ta tsaya tana kallon sa tace, "ba gida zamu shiga ba?."? Juyowa yayi ya kalle ta yace, "nan zamu je." "Amma shine sai mun shiga mota?". Dawowa yayi ya rik'o ta ya bud'e gaban motar ya saka ta ya zagaya ya shiga sannan yace, "Kin san ba lafiya ce dake ba har yanzu tafiyar ki ba normal take ba bana so kisha wahala" ya fad'a lokacin da ya kunna motar ya danna horn mai gadi ya bud'e suka fita daga gate d'in gidan, kwana kawai yayi sai gasu a gate d'in gidan Daddy kasancewar na Zaid ya shiga bayan gidan na Daddy kuma yana kan titi, horn ya danna mai gadi ya lek'o ganin fuskar Zaid d'in ta gaban motar ya saka shi komawa tare da wangale masa gate ya danna motar cikin gidan.

Sai da ya dai-daita parking d'in sannan ya fito ya zagaya ya fito da ita yana rik'e da hannun ta suka shiga cikin gidan, Daddy da bai jima da dawowa daga Abuja ba yana zaune a falo yana danna laptop da alama aiki yake yaji sallamar Zaid, d'agowa yayi ya kalle shi ta cikin medical glass d'in idon sa sai kuwa ya saki fuska farin cikin sa ta bayyana lokaci d'aya yace, "Zaid kune tafe?". Sai da ya zauna sannan yace, "Eh Daddy".

A kan carpet ta zauna sab'anin shi da ya d'are ka?kujera ganin ta zauna a k'asa sai shima ya sauka yana kallon ta, girgiza kai kawai Daddy yayi yana murmushin farin ciki ganin haske ya shigo cikin rayuwar d'an sa lokaci d'aya, "Daddy barka da rana" ta fad'a kanta na k'asa shima ya maimaita abinda tace, Daddy ya amsa da fad'in, "Lafiya lau, kun tashi lafiya?". "Lafiya lau Daddy, ina Anty?" Zaid ya fad'a yana d'an kallan gefen sa.

"Ganin nan" ta fad'a tana shigowa falon da murmushi a fuskar ta ta k'araso ta zauna, "Mama barka da Rana" Ibteesam ta fad'a tana kallon ta ya sake maimaita abinda Ibteesam d'in tace, sai da Anty Amina tayi murmushi sannan tace, "barkan ku Amarya da Ango, kun tashi lafiya?". "Lafiya lau" Ibteesam ta amsa.

Nasiha Daddy yayi musu sosai akan zamantakewar aure da kuma yanayin rayuwa, sosai nasihar ta shiga jikin su especially Zaid da yasan wani abun da Daddy ya fad'a da biyu ya fad'a, bayan ya gama Anty Amina ma tayi musu tata suka yi musu addu'a da fatan zaman lafiya me d'orewa.

Daddy yace, "Zaid gobe zamu Cyprus nida Antyn ka zamu d'an jima kad'an dan i think zamu d'auki 2weeks haka wani aiki ne ya taso a can". Langwa6ar da kai yayi yace, "Daddy meyasa kake son wahalar da kanka for god sake? Me kake so wanda baka dashi,? Please ka ajjiye aikin nan ka huta haka." Murmushi yayi yace, "To Malam Zaid zan duba na gani". Zaid yace, "haka kake cewa kawai Daddy but baka son hutun ne i think." Daddy ya kalle shi da kyau sai yaga yayi masa haske yayi kyau sosai kamar ba Zaid ba ga murmushin dake fuskar sa ya k'ara masa kwarjini daman kuma manyan kaya ya saka, "Abdallahn Daddy murmushi yak'i barin fuskar ka, any gist?".

Sai da ya sake yin murmushin sosai ya d'ago ido maimaikon ya kalli Daddyn sai ya kalli Ibteesam kafin ya kalli Daddyn yace, " Daddy it's special day for me, i think it's the best day in my whole life." Daddy ya girgiza kai cikin farin ciki sosai yace, "Masha Allah." Daddy ya sake cewa, "Ko zaka raka ni wani waje?". Sai kuwa ya d'aure fuska yace, "Daddy kasan ango babu inda yake zuwa a irin wannan ranar ko?" Ya fad'a a shagwa6e kamar yana magana da Ibteesam.

Murmushi Daddy yayi yace, "I know, but dubiya zamu je yanzu kuma zamu dawo kaga gobe bana nan." Turo baki yayi kamar yaron goye yace, "To Daddy ka tambaye ta." Daddy ya juyar da kallon sa Ibteesam yace, "Daughter a ara min shi muje mu dawo but in kin yadda". Ibteesam kunyar duniya ta ishe ta ta kifa kanta cinyar Mama tana sake b'oye fuskar ta, "ki amsa" Zaid ya fad'a yana kallon ta cikin burgewa dan sometimes kunya na burge shi. Dak'yar ta iya cewa, "to Daddy". Daddy ya mik'e yana dariya yace, "thanks you Daughter, tashi kai kuma muje". Mik'ewa shima yayi yace, "Daddy i can't drive".

Daddy baice komai ba ya fita shima yabi bayan sa, sai da taji fitar su ta d'ago kai sai kuwa suka had'a ido da Mama sai ta mayar da kanta cikin kunya mai tsananin gaske dariya ta bata sai tace, "amaryar Zaid". Ai kuwa kamar me haka ta sake jefa Ibteesam cikin kunya sosai tana so tace ya siya mota amma ta kasa sai dak'yar tayi k'arfin halin cewa, "Mama ya siya min mota". Tace, "Su Zahra sun fad'a min kafin su tafi, sun shigo suna ta murna nima na taya murna sosai, Allah ya sanya albarka Ibteesam." Ta amsa da amin kafin Mama ta fara mata nasiha irin ta uwa da y'a akan zamantakewar aure da kuma nusar da ita akan hak'uri akan komai, sosai taji dad'in nasihar ta kuma shiga jikin ta sosai.

Mama ta d'ora da cewa, "na san yanayin sabbin amare yanzu za'a fara yi miki tallan magungunan mata, to ki kula kar ki d'orawa kanki wannan shaye-shayen na banza dana wofi ki rik'e duk abinda Mummyn ki ta fad'a miki natural abubuwa zaki dinga amfani dasu wanda kike dasu a cikin gidan ki zaki had'a kuma da kanki, especially ma irin na matsin nan da yawan su suna jawo viginal infection sabida wani ba'a san dame aka had'a shi ba amma mu mata neman farantawa miji bama bincike akan abinda zamuyi amfani dashi sai kawai mu siya, to kiyi hankali ki san abinda kike yi kar ki rufe idon ki ki cuci kanki".

Tayi mata fad'a sosai ta kuma shiga jikin ta sosai ma kuwa.

Sun jima tare har bayan la'asar tana wajan ta har lokacin kuma basu dawo ba, Anty Amina ta bata abincin su tace ta koma can ta zauna ta jira shi.

Sai biyar? sannan suka dawo fuskar nan a had'e haka ya shiga falon Anty Amina yana baza ido ko zai ganta, "Anty tana ina?" Shine abinda ya fara tambaya, "ta koma can ai Zaid" ta? bashi amsa baice komai ba ya fita.

Anty Amina tace, "sannun ku da zuwa, kun jima." Zama yayi yace, "Gidan Yaya Babba fa muka je dashi". Anty Amina tace, "Allah sarki." Daddy yace, "Baki ga yadda ya dinga kuka yana neman yafiyar Zaid ban d'auka Zaid zai yafe ba amma wallahi sai yayi min bazata yace ya yafe musu amma bai b'oye musu ba ya sanar dasu bazai tab'a daina ganin su da abin ba". Ajiyar zuciya Anty Amina tace, "ni kam har ga Allah naso a hukunta tasu kodan masu hali irin nasu, kayi hak'uri gaskiya nake fad'a kar kaji haushi na, tunda kuma ya yafe Allah ya yafe mana baki d'aya. " Murmushi Daddy yayi yace, "Amin" daga haka suka cigaba da hira akan tafiyar da zasuyi.

Zaid kuwa a kitchen ya sami Ibteesam tana kunna kettle zata d'ora ruwan zafi, k'arewa bayan ta kallo yake ganin ta canja shiga zuwa street gown ta atampa wacce ta fito mata da duk wani shape na jikin ta, a hankali ya k'araso ya rugume ta ta baya tare da d'ora kansa a kafad'un ta yana shak'ar khamshin ta, "wayyo Allah na!" Ta furta a firgice dan ya bata tsoro ganin shine ya saka tayi ajiyar zuciya tace, "ka tsorata ni". Sake rik'e ta yayi gam a jikin sa yace, "Kin d'auka wani ne daban?".

"A'a nasan ma ai babu mai shigowa naji tsoro ne kawai, sannu da zuwa" ta fad'a har lokacin yana jikin ta, "sorry na jima ko? Daddy ne ya saka mu yawo". Murmushi tayi tace, "meye na hak'uri?". Hannun sa ya saka a cikin ta ya shafa yace, "cikin ki babu komai kinci abinci kuwa?" Ya fad'a yana juyo da ita yana kallon fuskarr ta, "nasha tea dai bana jin dad'in baki nane har yanzu" ta fad'a masa a shagwa6e.

"Ohh sorry precious, but ya kamata kici wani abun daurewa zakiyi" ya fad'a yana rik'e fuskar ta yana mata magana, kai ta d'aga masa kawai ya jawo hannun ta zuwa ga abincin da ya gani a ajjiye, zuba mata yayi ya zauna kusa da ita yana bata a baki a hankali baya cewa komai har ta d'anci da dama kafin tace, "Kaima kaci".? Yace, "Ni kin san daman ban cika cin abinci ba." "Aikam kaci" ta fad'a tana karb'ar plate d'in ta fara bashi kamar yadda yayi mata.

Sai da suka gama cin abinci sannan ya kwantar da ita a cinyar sa tare da zame d'ankwalin kanta yana shafa kanta yace, "Precious ki fad'a min abinda kike so". Tace, "nifa na fad'a maka babu komai." Murmushi yayi sosai yace, "kin san mena tuna?". Girgiza masa kai tayi alamun a'a yace, "ranar da muka fara had'uwa dake mana". Dariya itama tayi tace, "u know what, wallahi a lokacin ban d'auka kai bahaushe bane ba ganin yanayin ka kamar bana hausawa ba da kuma yanayin kayan jikin ka, infact na d'auka kai arne ne". Sunkuyawa yayi ya mata kiss a forehead sannan yace, "amma fa a lokacin nan kinyi ganganci dan badan ke bace ba ko hmmmm" ya fad'a yana d'an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login