Showing 111001 words to 114000 words out of 171073 words

Chapter 38 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7831

proud to be your husband and i'm so proud to be the first person da ya fara sanin ki a duniya Precious, thanks you precious kin bani abinda yafi komai mahimmaci a rayuwar ki" numfashi ya sauke kafin ya cigaba da fad'in, "Ina sonki da yawa wifey, i love you so much" ya fad'a muryar sa har shaking take ya rungume ta da sauri yana shafa bayan ta dan ji yake in bai saka ta a jikin sa ba a lokacin tabbas akwai matsala babba, zip d'in bayan ta ya sauke ya saka hannun sa a kan fatar ta yana safa soft and smooth skin d'inta yana sama da k'asa da hannun sa a bayan ta yana lumshe ido.

Kalaman sa sunyi bala'in ratsa ta ta ko wanne b'angare ta lumshe ido tana jin yadda yake up and down da hannun sa a bayan ta, tabbas itama tasan tayi sa'a he's super and mr romantic, he's handsome and rich, uwa uba he love her better than komai, tana mafarki irin soyayyar da yake nuna mata amma bata tab'a tunanin zata sami kwatan irin soyayyar da yake mata a duniya ba, wani abu taji yana bin ko wanne b'angare na jikin ta ta bud'e idon ta tana jin sabon yanayin da yake kawo mata ziyara a gangar jikin ta da kuma zuciyar ta da ruyin ta, tsamm ya sake matse ta a jikin sa kamar wani zai kwace masa ita, d'an sassauta rik'o yayi ya d'ago da face d'in ta yayi kissing d'in cheek d'in ta kafin mayar da ita jikin sa yana jin wani irin yanayi a tare dashi sonta na sake bin ko wanne b'angare na jikin sa.

Shi kansa bai tab'a tunanin zai so wata d'iya mace a duniya kamar yadda yake sonta ba, yana jin ta a jikin sa hakan yake haifar sa yake jin rasa ta babbar illa ce ga rayuwar sa gabad'aya.

Motsin da tayi ya saka shi ya sake ta ya koma ya zauna kusa da ita yana me kafa mata idon sa, jin yadda eyeballs d'in sa suke yawo a jikin ta sai ta sake jin new feeling wanda bata san dashi ba kawai ta tsinci kanta a cikin sa, dan daman idon sa na mugun yi mata horo a zuciyar sa nan take zata ji nutsuwa na ratsa ta, kunnen ta ya kama ya rad'a mata wani abu tayi saurin k'asa da kanta tare da fad'in, "am shy" ta fad'a tana kulle fuskar ta.

Zaro ido yayi yana d'age gira yace, "I like it". Murmushi tayi kad'an shi kuma ya kalle ta yace, "oya tell me u enjoyed it or not?". D'ago kai tayi suka had'a ido ta kawar da kai tace, "what?". Gira d'aya ya d'age yace, "Oh u pretend like u forgot ko? Okay lemme repeat it" ya fad'a yana matso da fuskar sa sosai kusa da tata, kafin tace wani abu ta tsice shi yana kissing in and out na bakin ta, sai tayi shiru tare da lumshe ido kawai, a hankali ya dakata ya kalle ta yace, "do u remember or not". K'asa tayi da idon ta cikin shagwa6a tace, "am shy fa" ta fad'a kamar tayi kuka. "U mean u enjoyed it right?". Kulle ido tayi ta bud'e tace, "Akwai ciwo" ta fad'a muryar ta a sanyaye kamar tayi kuka, sai ya sake yin kissing d'in forehead d'inta yace, "I'm Sorry". Wayar sa yaji tana k'ara yaga sunan Daddy ya dafe kai dan sai a lokacin ya tuna yana da magana da Daddy sai ya mik'e tsaye daga kusa da ita yace, "ki kular min da kanki kinji Precious, i love u more than anythings" ya fad'a yana sake kissing d'inta a forehead, har ya wuce ya dawo yaga kwalin 5avile a ajjiye akan mirror ya d'auka ya kalle ta alamun karin bayani, "tun shekaran jiya yake" ta fad'a tana kallon lemon.

Matsa shi????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? yayi yaga murfin a b'ule kamar ya kalle ta yace, "shine wanda kika sha a ranar har kika je sama dashi?". D'aga masa kai tayi alamun eh, girgiza kai yayi yace, "time d'in da kika shiga kitchen d'in wa kika gani a ciki?". "Eman" ta bashi amsa a tak'aice, girgiza kai yayi kawai ya fita da kwalin a hannun sa. Yana fitowa yaga Hajiya Batula ta zubawa k'ofar ido shima ya zuba mata ido yana ware mata su, saurin d'auke ido tayi tana raba ido shi kuma ya wuce matan ya hau saman Daddy.

Yana shiga falon ko zama baiyi ba yace, "Daddy wai lafiya naga an cika gidan nan?" Ya fad'a yana zama a kan kujera.

Kallon sa Daddy yayi sai yaga yayi haske sosai fuskar sa har wani shaning take amma ya rame ya kuma tsaho gashin fuskar sa dana kansa ya kuma fitowa, d'auke kai yayi daga kallon sa kafin yace, "Baka san anyi rasuwa a gidan bane?". Yace, "Na sani mana, Eman she passed away to meye kuma zasu zo a cika mana gida?". Tsayar da shan tea d'in Daddy yayi kafin yace, "to ba nan ne gidan mijin taba? Ai a nan za'a yi zaman makokin ta." D'an k'aramin tsaki yaja sannan yace, "i hate this zaman makoki wallahi, pls gobe su koma gidan su suyi a can hayaniya yana damuna" ya fad'a yana yatsine fuska.

"Yanzu ya jikin naka?" Daddy ya tambaya yana kallon sa, "da sauk'i, but Daddy wata magana nake so muyi" ya bashi amsa yana mayar da hankalin sa kansa. Shima hankalin sa ya mayar kansa kafin yace, "ina jinka." Gyara zama yayi kad'an kafin yace, "Daddy zan kai Yayan ka da matar sa k'ara human right sannan zan had'a da court" ya fad'a yana d'ora k'afa kan d'aya.

Da mamaki Daddy ya kalle shi yace, "Ban gane ba?". Ajjiye lemon hannun sa yayi a kan center table yace, "wannan shine lemon da Eman ta zuba mana something a ciki muka sha nida precious by mistake, a yadda na fahimta wanda muka sha nida precious shine wanda iyayen ta suka tsara zamu sha da ita, poison d'in da tasha ta mutu kuma shine wanda aka yi niyar bawa precious" ya k'arasa fad'a yana kallon Daddy.

Daddy yace, "Kai Zaid a ina ka samo wannan labarin kuma?". D'an tab'e baki yayi yace, "Daddy kasan dai bazan maka k'arya ba abinda na fad'a gaskiya precious suka so kashewa Allah ya nuna musu basu isa ba, da kunne na naji suna maganar" ya fad'a yana kallon Daddyn nasa da shima shi yake kallo. Shiru Daddy yayi dan baiso Zaid yasan labarin ba dan shi Amina ta fad'a masa komai da furucin da suka yi a kanta duka tayi recording ta kawo masa yaji dan abinda ya gama saurara kenan Zaid d'in ya shigo.

Kallon Zaid d'in yayi kafin yace, "To tunda Allah ya mayar musu da abin su ba shikenan ba?". Zaro ido yayi yace, "Shikenan? Daddy sunyi attempting d'in kashe min mata, sannan sun bani wani abu nida ita mukayi lossing control har hakan ya kai ga nayi raping d'in precious, i raped her fa Daddy kuma kake cewa shikenan,? Nooo Dad bazan tab'a barin wannnan maganar ba, sabida hakan fa precious take a kwance bata da lafiya nima bani da lafiya kuma na bari impossible" ya fad'a cikin fusata. Anty Amina da ta k'araso wajan lokacin da aka fara maganar tayi murmushi tana mamakin halayyar Zaid yana kallon idon mahaifin sa yana cewa wai yayi mata fyad'e ba kunya babu jin nauyi, shima Daddyn kallon sa kawai yake ya jima da sanin Zaid baya kunyar sa amma bai d'auka rashin kunyar tasa takai haka ba.

Yace, "Zaid ka daina wannan maganar y'an uwan nawa zaka kai human right? Kuma naga sun aikata abu kuma ya koma kansu ba shikenan ba." Wani murmushi yayi mai nuni da tsantsar takaici yace, "Haba Dad, kashe ta fa suka so suyi". Daddy yace, "Amma basu kashe ta d'in bako?". Zaid yace, "wai Daddy kafi son sune akan precious?". Kallon sa yayi ya kalli Anty Amina da take tsaye ya sake dawo da kallon sa ga Zaid d'in yace, "dukka ina son su Zaid". Jingina yayi akan kujera yace, "amma kafi son su a kanta, dan in badan haka ba baza kace na k'yale su kar na kai k'ara ba, Daddy ina da power da zan iya sakawa a kulle min su bama a cell ba a prison kuma life in prison but bana so nayi ne kaita masifa akan meyasa nayi shiyasa zanbi komai a tsari, in kuma ka haka billahi zan saka thugs su koya musu hankali". Daddy ya rik'e hab'a kawai yana kallon sa shi yana murna Zaid ya shiru ashe halin yana nan yace, "Zaid nine nake masifa?" Ya fad'a yana zaro ido.

Ta kasan ido ya kalle shi kafin yace, "i mean kai ta fad'a" ya fad'a yana yatsine fuska, Daddy yace, "Shikenan Zaid naji, amma ka bari gobe ayi sadakar uku kaga rasuwa akayi musu in yaso sai ka kai k'arar amma kana da evidence ko?". D'an jimm yayi alamun tunani kafin yace, "Wannan lemon baza'a rasa fingerprint d'in wanda ya zuba abin a ciki ba, sannan chemical d'in yana cikin drink d'in." Daddu yace, "i know all dis but kana da evidence akan iyayen ne suka saka ta ta zuba ba on her own tayi ba?". Shiru yayi yana tunani tabbas maganar Daddy gaskiya bashi da wannan hujjar da zaice sune, Daddy ya katse shi ganin yayi nasara a kan sa da fad'in, "Kaga babu kai babu kai k'ara kenan" ya fad'a yana kallon sa.

"Cctv cameras" ya fad'a yana kallon Daddy, shiru Daddy shima yayi kafin yace, "Zaid ka bar maganar kai k'arar na fad'a maka tunda Allah ya kare ku ba shikenan ba?". Kallon Daddyn yayi a kaikaicee kafin yace, "ohhh Daddy na k'yale su shikenan sun cutar da banza sun saka I'm raped my precious? Daddy why zan k'yale su bayan sune silar rashin lafiyar ta?" Ya fad'a yana kallon Daddyn.

Daddy ya dafe kai shi kam bai san yadda zaiyi da rigimar Zaid ba yace, "shikenan naji yanzu ka bari ayi sadakar bakwai bama uku ba in yaso da kaina zan saka a bincika cameras d'in gidan sai a baka evidence d'in da kace kaji sai ka kai human right d'in, but not now pls son" Daddy ya fad'a alamun rok'o.? Ajiyar zuciya yayi yace, "naji Daddy, amma in nan gaba ka hana ni d'aukar matakin wallahi zan yi duk abinda naga ya dace dan babu yadda za'ayi a tab'a precious a zauna lafiya,? and kaja musu kunne wallahi wani abu ya samu matata hmmmm" ya saki wani murmushi mai nuni da tsantsar mugun ta a tare dashi.

Daddy yace, "Shikenan naji zanyi amma kaima ka k'yale su a yanzu kuma kayi musu gaisuwa kaga yarinya suka rasa". Tab'e baki yayi yace, "Lokacin tane yayi Daddy ni babu wani gaisuwa da zan musu infact office ma zanje yanzu" ya fad'a yana mik'ewa tsaye. Har ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya kalli Daddy yace, "Daddy who is Amina?". Daddy ya kalle shi yace, "Lafiya?". Yace, "no i want to know". Kallon Anty Amina Daddy yayi yace, "She's your step mum and your mother in law" ya fad'a yana nuna Anty Amina. Kallon ta yayi na wasu seconds kafin ya kad'a kai ya fita daga falon.

Bayan fitar Anty Amina ta zauna ta kalli Daddy tace, "wato shi Zaid bai san wani abu k'arya ba haka bai san wani abu kunya ba" ta fad'a tana murmushi.? Shima Daddy murmushi yayi yace, "Bai san su ba ko kad'an kina gani yana kallon idona yana cemin wai he raped her, ni fa na d'auka yayi hankali ashe halin yana nan". D'an murmushi tayi tace, "Amma sai nake ganin ka k'yale shi ya kaisu k'arar dan sun kullace shi a yanzu sosai". Daddy yace, "Amina kamar baki san halin Zaid ba? Yanzu na barshi nace yayi abinda yake so ai sai ya jawo min a abin kunya a duniya, kamata ace d'ana ya kai y'an uwana da nake ciki d'aya dasu k'ara ai kinga babu dad'in ji ma, ni da Allah zan barsu Amina bazan iya kai ko d'aya daga cikin su k'ara ba haka kuma bazan bari ya kai ba gashi tun ba'a je ko ina ba Allah ya fara nuna musu ishara". Ajiyar zuciya tayi tace, "Haka ne, amma da hukuma su shiga maganar gaskiya." Girgiza kai yayi yace, "bazan bari hakan ta faru ba Amina, ko hukuma ta shiga maganar baza su fasa abinda suka yi niya ba, hukuma zata bani kariya ne? Allah kad'ai ni dashi na barsu kuma nasan zai min maganin su cikin ruwan sanyi tunda ni ban nufi kowa da sharri ba." Anty Amina tace, "Haka ne, amma zaman Ibteesam a gidan nan a yanzu akwai hatsari gaskiya sun sha alwashi a kanta shiyasa nace zance ta koma gidan Umman ta ko gidan mahaifin ta kafin a gama zaman makokin." Daddy yace, "Haba Amina kamar ba ke ba? Har sun firgita ki akan y'ar magana kad'an, kar ki bani mana akan haka ki k'yale Ibteesam a nan zaman ta a nan shima yana da amfani sosai ma" ya Fad'a yana kallon ta.

"To shikenan Allah ya kare mu daga duk me nufin mu da sharri". Daddy ya amsa da amin ta tashi ta fito shima Daddy ya sakko ya koma cikin y'an zaman makokin.

Zaid har ya shiga mota ya tuna da wayar Ibteesam a aljihun sa sai ya fito ya sakee komawa fuskar nan a had'e mutane sai gulmar sa ake amma babu wanda ya ishe shi ko kallo, ta falon ya sake ratsawa ya wuce ya sake wuce na Any Amina kafin ya k'araso d'akin, handle ya bud'e ya shiga suna tare da Maman ta a lokacin, ajjiye wayar yayi akan mudubi kawai ya juya ya fita daga d'akin.

Washe gari akayi sadakar uku aka watse dan Zaid yacewa masu zama an gama zaman makoki kowa ya tafi haka su Yaya Babba suka tafi da mugun nufi a ransu a kan Zaid da Ibteesam.

Bayan kwana biyu


Ibteesam taji sauk'i sosai kamar ba ita ba sai dai ta rame kuma tak'i bari su had'u da Zaid koda wasa, hakan ya dame shi sosai amma aiki da yayi masa yawa a office dole yake hak'ura.

Da yamma yana saman sa yana aiki a system hankalin sa gabad'aya ya karkata ga aikin yaji an bud'e k'ofar an shigo duk a tunanin sa Hameed ne hakan ya saka bai d'ago ba har aka zauna, jin ba'ayi masa magana ba sai ajjiye tray da akayi ya saka ya d'ago kai suka had'a ido da Ibteesam da take kallon sa, murmushi ya saki mai kyau yana kallon ta kafin ya ture system d'in gaban sa yace, "Kin wahalar dani da yawa precious" ya fad'a yana mik'o mata hannu alamun tazo.

Nok'e Kafad'a tayi fuskar ta a had'e ba tare da tace komai ba, rausayar da kai yayi yace, "Wai me nayi miki haka precious?". Nan na shiru bata ce komai ba sai sake had'e fuska da tayi kamar hadari, mik'ewa tsaye tayi tace, "Mama tace na kawo maka tea shiyasa ma ka ganni da babu abinda zai kawo ni inda kake" ta fad'a tana niyar tafiya ya rik'o hannun ta, mik'ewa tsaye shima yayi jikin sa duk yayi sanyi dan bai san laifin da yayi mata ba yace, "Precious laifin me nayi miki? Ko dai duk akan abinda ya faru ne har yanzu bai wuce ba?".

"Ya za'ayi ya wuce, in a wajan ma ya wuce ni a waje na bazai b'ata wucewa ba dan ka raba ni da abinda zan kawa miji na wanda zan aura in ka sake ni dan ina so ka sani ni bazan zauna dakai ba domin bana sonka!" Ta fad'a cikin masifa ba tare da ta juyo ba, runtse ido yayi yana cize baki tare da matse hannun ta har sai da tayi k'ara, shi bawai bata son sa da tace shine abinda ya tab'a shi ba maganar auren wani shine yayi bala'in tasiri a cikin zuciyar sa har yake jin bugun ta, "Precious wai me kike so nayi miki ne ki soni?" Ya fad'a kamar yayi kuka yana kallon ta.

Juyowa tayi a fusace tace, "ka sake ni shine zan soka so na har abada, amma bara kaji yau ba gobe ba zanje na samu Daddy a raba auren nan bana son zama da kai a matsayin miji na Khalid nake so". A fusace ya d'aga hannu zai mare ta sai kuma ya dunkule hannu ya naushi iska fuskar sa ta canja kala lokaci d'aya ya fara wani irin wuci kamar zaki, magana yake so yayi amma bakin sa rawa yake sai nuna ta kawai da yake yi hankalin sa yayi bala'in tashi, numfashi ya fara saukewa a hankali kafin yace, "Precious kin san abinda kike fad'a kuwa?". Hararar sa tayi tace, "na sani kuma ko yanzu zan kuma maimaitawa, bana sonka bazan zauna dakai ba dole ka sake ni na auri wanda nake so" ta fad'a cikin fad'a.

Sakin hannun ta yayi ya fad'a kan kujera sharaf ya dafe kansa da duka hannayen sa zuciyar sa na bugawa a guje kamar kunna ta akayi, duk da a.c dake falon amma zafi yake ji yana ratsa ko wanne b'angare na jikin sa take ya fara gumi ya b'alle ma6allan rigar, d'agowa yayi ya kalle ta da jajayen idon sa yace, "Ko baza ki soni ba precious ki amince ki zauna dani nayi miki alqawarin zan baki dukka abinda kike so zan kuma nisanci duk abinda bakya so, amma ki daina min zancen wani in muna tare bana so ina jin zafi a zuciya ta, ina ji kamar na mutu sabida azabar da nake ji pls" ya fad'a muryar sa na wani irin rawa wacce ta bayyanar da zallan raunin da yake tare da muryar tasa.

"Bazan zauna dakai ba domi baka girmama min mahaifiya ko wacce shara ka kaso sai kazo ka zuba a kanta me ta tare maka a duniya,? Bana sonka kamar yadda baka son mahaifiya ta bana jin kuma zan soka koda nan gaba kuma dole ka sake ni" ta fad'a tana tsaye a akan sa kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login