Showing 150001 words to 153000 words out of 171073 words

Chapter 51 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7843

aure a tsakanin ku amma jikin ki dani kad'ai ya kamata ki had'a da nawa a yanzu, Na lura kina sane kike duk abinda bana so sabida ki b'ata min rai na sake kwanciya a asibiti." Girgiza masa kai take alamun a'a tana hawaye kafin yace, "To naji a ajjiye batun Khalipha, duba comments d'in hoton kiga me ake cewa". Ba musu ta shiga dubawa nan tayi karo da masu yabon surar ta da kyauwun ta kamar hauka har da mai cewa ta bashi sha'awa.

Kafin tayi magana yace, "munyi dake babu rawa kika je kina rawa akayi posting a media, munyi dake babu saka kaya fitted kika je kika saka, burin ki ya cika an yabi kyauwun ki da surar ki a media dan na lura abinda kike so kenan, congratulations maza sun gani sun kuma yaba kin kuma b'ata min rai hankalin ki ya kwanta" ya fad'a cikin fad'a kana jin yadda yake maganar kasan ransa a b'ace yake sosai.

"Wallahi ban san za'ayi posting a media ba ban kuma san rigar ta kama ni ba, Zahra ce ta tura komai ni kawai sai riga na gani ban kuma gwada ba sai d'azun da nasan tayi min haka da da wuri za'a canjo ta, I'm sorry please" ta k'arasa fad'a murya a sanyaye.

A fusace yace, "Amma ai kin san yanzu abu kad'an ake jira ayi posting a media ko?". "Kayi hak'uri."

Banza yayi mata tare da kawar da kansa, "kayi hak'uri dan Allah" ta sake fad'a. "Naji zanyi hak'uri amma ya zanyi da posting d'in nan da maza suke ta yabon ki har yanzu?". Sanin babu abinda zata ce masa ya saka ta sake cewa, "I'm sorry". Ajiyar zuciya kawai yayi baice mata komai ba dan sosai abin yake tab'a masa zuciya.

Jin ta kuma fashewa da kuka ya saka shi cewa, "Is okay ya wuce, but kar na sake ganin hoton ki a social media koda wasa". Jin hakan ya saka tace, "insha Allah baza'a sake ba wannan d'in ma bani ce nayi ba". Shafa kanta yayi yace, "yau zaki tare a gidan Zaid ko?". Turo baki tayi tace, "meyasa kayi min wayo ka gudu?". Kyakykyawan murmushi yayi mata yace, "Nasan kece weakness point na Zaid shiyasa na gudu ban yadda na sake ganin ki ba."
"Amma meyasa ka gudu ka bar gida Daddy duk ya damu?".
"Inda ya damu bazai hana ni abinda nayi niya ba."
"Amma meyasa ka kashe wayar ka?".
"Ban kashe waya ba kawai nayi blocking dukkan layukan kune".
Tace, "yanzu amma ka gama fushin ko?". Kumatun ta ya ja yace, "na gama yau zan koma gida ma, za'a kawo min amarya ba dole na koma gida ba."

"Ka yafe musu amma ko?" Ta tambaya tana kallon sa, shiru yayi kad'an kafin yace, "uhum na yafe musu babu abinda zan yi musu,gari yayi haske muje ki kwanta" ya fad'a yana mikewa tsaye itama ya mik'ar da ita, k'okarin bud'e zip d'in rigar ta yake yi yana fad'in, "ki cire kyafi jin dad'in baccin". Juyawa tayi da sauri tace, "A'a ni bana jin bacci ma mu tafi kawai." Zaro ido yayi yace, "k'arfe shida fa madam, babu inda zani nikam sai anjima" ya fad'a cikin muryar sa mai dad'in saurara duk da fuskar babu walwala, Dole haka ta hak'ura itama ta zauna kafin bacci ya d'auke ta shima haka.

Basu farka ba sai tara na safe shine ya fara tashi yayi wanka ya shirya ya had'a komai nasa da yazo dasu sannan ya fita, bai jima sosai na ya dawo a lokacin ta fito daga band'aki tana zaune, "amaryar Zaid" ya fad'a yana k'arasowa inda take, murmushi tayi ya mik'a mata yace, "oya take it ki saka". Ba musu ta karb'a ta bud'e doguwar riga ce harda undies ta kalle shi yana zaune yana kallon ta, mik'ewa tayi zata koma band'aki ta shirya taji yace, "wallahi kika shiga band'aki sai na sake miki wanka zamu bar nan". Jin ya rantse ya saka ta tsaya cakk ta kasa juyowa, sai ta fara mai dara tana fad'in, "ni wallahi bazan iya shiryawa kana nan ba". Sake gyara zama yayi yace, "meye bak'o? Meye ban gani ba? Meye ban sani ba Precious?".? Mak'ale Kafad'a tayi tace, "nidai A'a." "Okay mu kwana a nan" ya fad'a yana d'auko wayar sa.

Ganin kamar hankalin sa na kan wayar ya saka ta fara shiryawa tana kallon sa kawai taga ya d'ago ido ya kalle ta sai kuwa ta firgita tayi baya kamar zata fad'i, kasa d'auke idon sa yayi daga kanta ya lumshe ido ya bud'e daman khamshin turaren da yake jikin ta ya kashe masa jiki ga kuma a yanayin da ya ganta, saurin kawar da kansa yayi yana lumshe ido ita kuma ta gama shiryawa ledar kayan da ya kawo mata ta cusa rigar a ciki da saurar kayan suka fito.

Har suka je gidan Mummy yanayin sa ba dai-dai yake ba tana lura da hakan ta kuma yi mamaki itama dan bata d'auka zata kwana ta tashi tare dashi bai mata komai ba lallai dole ta sake amince da son ta yake ba sha'awar ta ba, "Baby lafiya dai na ganka ka canja?" Ta tambaya tana kallon sa, kallon ta yayi da idon sa da suka koma wani iri yace, "Kece Precious" ya fad'a yana kallon idanun ta.

"Me nayi kuma?". Kallon ta kawao yake baice mata komai ba kafin yace, "Kin san mene ki tausayawa mijin ki kice musu a kawo ki gidan ki da wuri kinji?". Sai ta biye masa tace, "to zan fad'a." Yace, "baza ki iya ba muje na fad'awa Mummyn" ya fad'a yana k'okarin bud'e k'ofar.? Da sauri ta dakatar dashi da fad'in, "Zan iya fad'a ka barni na fad'a mata basai kaje ba." Yasan k'arya take ba iyawa zatayi ba amma ya k'yale ta ta fita daga motar dan yana so yaje compony kuma yaje wajan Daddy.

Company ya fara nufa ya gama abinda zaiyi ma Hameed bai shigo ba ya fito ya nufi gida, ba ta gate d'in gidan Daddy ya shiga ba ta gate d'in gidan sa ya shiga yayi parking yana kallon gidan, shi kansa gidan ya burge shi tun daga waje yasha fenti sai d'aukar ido yake yi, fitowa yayi daga motar ya shiga cikin gidan ta k'ofar baya ya shiga wani madaidaicin falo mai kyau wanda aka zuba masa kujeru da kayan kallo sai khamshi yake yi, k'arewa falon yake kafin ya bud'e wata k'ofar ya sai gashi a wani falon babba wanda steps suke a falon, yana shigowa falon suka had'a ido da Mummy da Mama Asma'u, d'an murmushi kad'an yayi yana k'arasowa inda suke, "Zaid! Yaushe rabon da na ganka?" Mama Asma'u ta fad'a tana rik'e baki.

"Ina kwana" ya fad'a yana kallon su dukka, suka amsa kafin Mummy tace, "kwana biyu ka b'uya ko ganin ka ba'a yi sai jiya wai akace min kaje wajan partyn baby amma ko ka shigo". "Ina sauri ne" ya bata amsa yana sake kallon gidan yace, "Mummy an gama komai?". "An gama mana Zaid, babu abinda ba'a saka ba kaje ka duba." Bai musu ba ya hau saman yana sake k'arewa ko ina kallo na gidan, saman ma falo biyu ne kamar na farko da bedroom hud'u haka ya gama zagayen sa sannan ya sakko ya fita.

Ta hanyar da zaka shiga gidan Daddy ya shiga suka had'u da Daddy a compound d'in gidan yana waya da alama fita ma zaiyi, sai da ya bari ya gama wayar sannan yace, "Daddy." Jin muryar gudan jinin sa tilon d'an da yafi so sama da komai a duniya ya saka shi ya juyo yana fad'in, "Zaid." "Yes Daddy, an tashi lafiya." Maimakon ya amsa sai ya kama hannun sa suka koma cikin gidan ta saman Zaid d'in, sai da ya zaunar dashi a kan kujera sannan yace, "Zaid ina ka shiga hankali na ya tashi ina ta neman ka?".

"Daddy ina chilla hotel naso na bar k'asar babu passport a hannu na". "Amma shine ka kashe wayar ka babu wanda yake samun ka?". Zaid ya bashi da amsa da fad'in, "Bana son a karya min zuciya na kasa abinda nayi niya shiyasa."

Daddy yace, "Kar ka sake irin haka Zaid koda wasa". Shafa kai yayi sannan yace, "Tohm kayi hak'uri". "Yanzu ka yafe musu?" Daddy ya gefa masa tambayar yana kallon sa. D'aga kai yayi alamun eh, Daddy ya kalle shi da mamaki sosai yace, "Me kayi musu?". Ya kalli mahaifin nasa yace, "Daddy inda nayi wani abun ai nasan zaka ji." Daddy yayi murmushi yace, "Zaid ina jin a kaf duniyar nan babu wanda ya san halayyar ka kamar ni, bana so ka fara yi min k'arya daga nan dan nasan babu ta yadda za'ayi ka yafe musu ba tare da wani abun a k'asa ba, so tell me me kayi musu?".

"Wallahi Daddy banyi musu komai ba, bayan bari na nan da kwana biyu nayi mafarki da Mama na a cikin yanayi mai kyau ta k'ara haske tayi kib'a, shine take sanar dani na fasa duk abinda nake kudirin yi na barwa Allah shine ya k'addara hakan kuma na yafe musu, haka da na sake kwanciya a daren na sake mafarki da ita tana sake fad'a min the same abinda tace haka a na uku ma, shiyasa na hak'ura amma Daddy zan jima banje inda suke ba har sai na wuce sabida indai zan gansu yanzu zan dinga tunawa ne kuma tunawa ta yana nufin kasa yafe musu ne" ya k'arasa fad'a a sanyaye sosai.

Murmushi Daddy yayi yace, "Allah yayi maka albarka Zaid". Shima murmushin yayi yace, "Amin Daddy". "Yau zaka tare da matar ka gashi anyi min kiran gaggawa daga Abuja zan tafi yanzu". Zaid yace, "Daddy ya kamata ka ajjiye aikin nan haka babu abinda kake nema a duniya kuma yanzu, wannan wahalar da suke baka tayi yawa wata k'ila ma suce wata k'asar zaka je". Murmushi yayi sosai ya shafa kan Zaid yace, "To za'a duba maganar ka Zaid" ya fad'a yana mik'ewa shima ya mik'e ya raka Daddyn har k'asa ya shiga mota suka tafi Airport shi kuma ya dawo cikin gida.

Yana gidan har dare zuwa lokacin kaf kayan sa ya saka an kwashe an bayar dana bayarwa an mayar da wasu wancan gidan an jera a d'akin da yake nasa an saka key an kulle, yana zaune a gidan har akayi magariba nan yaji motoci na shigowa da alama an kawo amaryar, murmushi yayi ya mik'e ya fito velconcy yana kallon su yana shan tea abin sa hankali a kwance, a lokacin Yayar Anty Amina ta fito da ita daga mota tana rik'e da hannun ta, sanye take cikin milk din lifaya tayi mata kyau sosai duk da kanta a rufe yake, murmushi yayi sosai har haqoran sa suka bayyana kafin ya koma ciki.

Yana shiga ya had'u da Hameed da ledoji a hannun sa manya yace, "Ango amarya tazo banga ka shirya ba" ya fad'a yana zama a akan kujera, "to ina ruwan ka? Meye wannan?" Ya fad'a yana nuna ledar. "Abinda ango zai shigarwa da amaryar sane nasan ba sanin hakan kayi ba tunda ba zuwa kake ba shiyasa na siyo maka, kullum kana gida kamar mace". Girgiza kai Zaid yayi yace, "Thanks you friend". Hameed yayi murmushi yace, "lallai Zaid yau kaine da gode min?".

Sai kuma yaja tsaki yana cigaba da shan tea d'in sa, "ka tashi ka shriya mana ango ana i'sha na raka ka sai na wuce". Da sauri ya kalle shi yace, "Ka raka ni ina?". Hameed yace, "Gidan amarya mana." Zaid yace, "Bana buk'ata nagode ni kad'ai zanje, Wizzy ma sunyi sun gama". Dariya Hameed yayi dan daman tsokanar sa yake yasan bazai bari ba.

A gida yayi i'sha sukayi shida Hameed kafin Zaid ya shiga ciki domin shiryawa, tsayawa yayi yana kallon kayan kafin yace, "Hameed meye wannan?". Hameed da yake jiran kiran daman ya shigo yana fad'in, "kayan ka mana." Da mamaki ya kalle shi ya d'auki babbar rigar da ya ajjiye masa yace, "u mean wannan katuwar rigar ni zan saka kamar wani Daddy,? Dan fa kace nayi d'inki ne ya saka na baka go ahead a kai amma shine zaka min wannan d'inkin kamar wanda Daddy zai saka?".

Dariya sosai Hameed yake hakan ya sake kular da Zaid yace, "ina maka magana kana dariya?". "I'm sorry, to kai banda abin ka ka tab'a ganin ango ya shiga gidan amaryar sa babu babbar riga? Ai haka zaka daure Zaid yau dai d'aya ka saka daka shiga fa zaka cire shikenan."

"Hameed gaskiya i can't wearing dis, ai sai na fad'i" ya fad'a yana sake d'aga babbar rigar da yake ganin kamar buhu zai saka, Hameed yace, "Wallahi zaka iya gwada ka gani" yana fad'a ya fita ya bar masa d'akin shi kuma ya fara saka na cikin, sai da ya gama sannan ya kwala Hameed d'in kira yazo ya saka mishi babar rigar yana masa dariya ganin yadda ya rasa yadda zaiyi, gyara masa Hameed yayi ya d'auki hular ya saka masa yana kallon sa da murmushi a fuskar sa yace, "Kai ango ka ganka kuwa? Wallahi baka tab'a kyau kamar na yau ba".

Wajan mirror ya nufa yana kallon kansa shikam baiga kyauwun ba sai ma zafi da ya fara ji, a haka dai aka gama shirin aka fito, lokacin gidan tsitt babu kowa da alama tunda dare yayi tara har ta wuce suka sakko k'asa ta falo Hameed na bayan sa da ledojin a hannun sa, Anty Amina ce ta fito da hijjabi a jikin ta nan ta kula dasu tayi kamar bata gansu ba tana niyar wucewa taji yana fad'ar, "Hameed wallahi i can't zafi nake ji ni cirewa zanyi" ya fad'a yana k'okarin cirewa. Da sauri ya dakatar dashi yana fad'in, "Haba kaifa ango ne dan Allah ka kar ka cire." Zaiyi magana ya kula da Anty Amina da ta d'auki ruwa a fridge, "Anty ban ganki ba na sakko zanzo naga mutane sunyi yawa, ina wuni" ya fad'a yana kallon ta ita kuwa duk kunyar sa take ji.

"Lafiya lau Zaid, ka dawo lafiya?" Ta amsa masa ba tare da ta kalle shi ba, "lafiya lau ya taro?" Ya fad'a yana sab'a babar riga, "Alhamdulillah" ta fad'a tana niyar wuce a nan yace, "Hameed nifa sai na cire a bar nan." Hameed yace, "Anty ki saka baki dan Allah kar ya cire."

Ita kam ta rasa irin Zaid a rayuwar ta y'ar kunyar nan ma ta sirikai babu a tare dashi hakan ya saka ta dake tace, "Ka barshi mana Zaid". Girgiza kai yayi yace, "Zai kashe ni ne in barshi". Dak'yar aka samu ya bar babbar rigar nan ita Anty daman burin ta bai wuce ta bar wajan ba suna fita ta bar wajan da saurin gaske da nauyin Zaid d'in take ji yau.

Suna zuwa k'ofar da zata kaisu wancan part d'in ya tsayar da Hameed dole ya tsaya yana ta dariya tare da tsokanar sa ya juya ya fita daga gidan shi kuma ya shiga cikin gidan cikin takun izza da k'asaita.
*?ASAITAR SO!*

*83_86*

Not edited >?'?




Babu kowa a falon sai yana bud'ewa ya lumshe ido yana shak'ar khamshin da yake falon gashi ya had'e da sanyin a.c sai abin ya bada kala sosai, a hankali yake taka falon ya lek'a d'akin k'asa da kitchen da kuma d'aya falon ya tabbatar babu kowa sannan ya kulle ya hau saman, shima falon shiru babu hakan ya saka shi nufar d'ayan, nan ma shiru babu motsin kowa sai sautin a.c y bud'e d'akin da yasan yafi girma dan nan ne natan.

Da sallama ya tura ya shiga ya hango ta zaune a gefen gado kanta a lullub'e da liyafar da take jikin ta, had'e hannayen sa yayi a k'irji yana kallon ta farin ciki yana sake ratsa shi, daga zaunen taji alamun kallon ta yake yi sai ta sake k'asa da kanta tana murmushi, k'arasowa cikin d'akin yayi da sallama ta amsa a hankali, kusa da ita ya zauna yana lek'a fuskar ta itama tana saka hannu tana rik'e liyafar a fuskar ta sosai.

Murmushi yayi mai sautin kafin ya kamo hannayen ta ya rik'e yana kallon zanen henna da yayi maroon a hannun ta, yatsa d'aya ya saka yana bin zanen henna a hankali dan sosai abun yana burge shi in ya ganshi a hannun ta, kamar tafiyar tsutsa haka yake yi mata a hannun nata duk wani zane sai yabi da yatsan sa ya sake bi, lumshe ido tayi tsigar ta tana tashi tana so ta kwace hannun ta amma bata so ya fahimta ta sai ta k'yale shi ya cigaba da abinda yake yi.

Hannun sa d'aya yana rik'e da hannun ta ya saka d'ayan ya d'aga liyafar da ta kulle fuskar ta, farar fuskar ta ta bayyana wacce ta k'ara haske da kuma shek'i ga wani kwarjini na musamman da yake shinfid'e a fuskar tata duk da fuskar ta a chunkushe take amma tayi kyau over, rik'e fuskar tata yayi yana shafa cheek d'in ta da thumb d'in shi yana kallon fuskar ta da idon ta yake k'asa.

Mik'ewa tsaye yayi ya cire babbar rigar da take damun sa ya ajjiye sannan ya kama kafad'un ta ya mik'ar da ita tsaye ya d'auki babbar rigar da ledar da ya shigo da ita da hannu d'aya hannu d'aya ya rik'e hannun ta suka fita daga d'akin, falon da yake nasa suka k'arasa ya ajjiye babbar rigar da ledar ya bud'e master bedroom d'in sannan ya d'auki kayan yana rik'e da hannun ta suka shiga cikin d'akin, duk da kanta a sunkuye yake hakan bai hana ta k'arewa d'akin kallo ba ganin duk yadda ake yabon nata da zuzuta shi nasa yafi nata fiye da tunanin mutum dan shi girman sa ma abin kallo ne.

"Preciousss!" Ya furta cikin wata irin murya mai amo wacce ta fita a hankali cikin sauti mai kawo nutsuwa da kwantar da hankali da kuma k'ara cilla zuciya cikin kogon shauk'i da yanayi mai wahalar fassarawa, lumshe idanu tayi tana jin yadda sunan ya bi ko wanne sashi na jikin ta ta kasa furta komai, "Muyi sallah ko?" Ya fad'a har lokacin yana rik'e da hannun ta yana kallon ta, d'aga masa kai tayi alamun eh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login