Showing 1 words to 3000 words out of 159062 words

Chapter 1 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10345

ο»ΏCompiled by Umar Dalha.










πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye*........ 01


_Written by Queen Samy_πŸ‘ΈπŸ»πŸ’„πŸ’‹


*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*America*
_California(Los Angeles)_
2011.


"Gidan yayi shiru banda sautin kukan mutanen dake ciki baka jin komai, wata Dattijiwan matace wacce bazata gaza shekaru 64 ba a duniya ta fito daga wani 'daki hannunta 'dauke da jaririya wacce a'kalla bazata wuce watanni 4 ba.
"Zama tayi tsakiyan yaran dake ta shar'ban kuka cikinsu an rasa me ba ma wani baki, itama wnn Dattijiwa kuka ne sosai ya kufce mata.
"Wasu maza guda biyu ne suka shigo 'daya saurayi ne wanda bazai wuce shekaru 22 ba a duniya, farine sol kyakyyawa yanayinsa zai tabbatar maka shima cikin tashin hankalin yake, mutumin da suka shigo tare dashi yana dafe da kafa'dunsa wanda ko ba'a fa'da maka zaka gane mahaifinsa ne, dan kuwa kammaninsu ya 'baci saidai kawai matashin ya 'dan nun masa 'kuruciya, mutumin bazai gaza shekaru 48 ba, a tare suka shigo cikin parlorn ai kiwa gaba 'daya yaran suka mi'ke suka rungumesu suna kuka.
"Daddy is it true, mummy has gone...... "'Yar budurwan ciki wacce bazata wuce shekaru 12 ba ta fa'di cikin tsananin kuka da tashin hankali, sosai mutumin da ta kira da daddy ya rungumeta kafin yace" Nadiya dukkaninmu 'yan adam ne dukannninmu watarana zamu bar duniya, addu'a shi zamuyi wa mummyn ku Allah yasa ta huta Allah yasa kyawawan ayyukanta su bita.
"Sosai suke kuka, wasu 'yan yara maza guda biyu wanda da gani kasan tagwaye ne baza wuce shekaru biyar ba a duniya suka rungume 'dan matashin cikin suna kuka, 'kan'kamesu yayi yana kuka shima sosai, sun jima a haka ko wanni na kuka kafin daga bisani " Daddy ya 'karasa ya kar'bi 'yar jaririyan dake hannun dattijiwan nan yace" Amma kawota, Amma ta mi'ka masa ita tana gohe hawaye. Kallonta *Engr. Nazif Mumtaz* yake babu ko 'ka'k'kautawa, tausayinta da sonta a lokaci guda yana ratsa 'bargo da tsokansa, sosai ya rungumeta yana sharan hawaye.
"Haka ranan gidan Engr Mumtaz ya wuni cikin tsananin tashin hankali da alhini na mutuwar matarsa kuma uwar 'ya'yansa.


"Zaune yake cikin 'dakinsa ya 'kura wa hoton mahaifiyar sa ido, har lokacin besaka komai a cikinsa ba, ya kasance yana tsananin son mummin sa gashi mutuwa ta masu YANKAN 'KAUNA, Allahu Akbar dukkanin me rai dama mamaci ne, Allah ka bamu 'karshe me kyau ameen.
"Amma ne tayi sallama a 'kofan 'dakin, yayi saurin ajiye hoton gefe gamida gyara zamansa, murmushi Amma tayi na 'karfin hali kafin ta 'karasa shihowa 'dakin, hannayen saurayin nan ta ri'ke cikin nata kafin tace" *Irfaan* you need to be very strong, mu gode wa Allah Khadija ta samu kyakyawan shaida, muna ro'kon Allah yasa kyawawan ayyukanta su bita, snn ka tuna kaine babba cikin yaran nan idan bakayi juriya ka jawosu jiki ba, abun zaiyi affecting dinsu yanda baka tsammani. Addu'a shine gatan mamaci ba yawan kuka da damuwa ba.... " Irfaan ya share hawayen idonsa ya rungumo kakansa yana fa'din " Amma I still couldn't believe that mummy passed away....... kasa 'karasa maganarsa yayi dan kuwa sosai yake kuka, rungumesa Amma tayi tana basa baki ha'di da 'karfafa masa gwiwa.
"Sanda Irfaan ya fito parlor 'kannensa maza twins guda biyu suna zaune da gani kasan sun sha kuka, 'karasawa yayi tsakiyansu ya zauna, ya ri'ko hannayensu, Amir da Aiman suka rungume yayan nasu Irfaan ya shiga shafa gashin kansu ba tarda ya furta komai ba.
"Engr Nazif kuwa ranar bacci tare yayi da 'yar autarsa wacce suke kira da Nilam, koda Amma ta dubasa a 'dakinsa dan kar'bo Nilam, gani tayi ya rungumeta sosai cikin jikinsa dan haka juyawa tayi cike da tausayawa 'dan nata da jikokinta.


"Yau sati guda da rasuwan mummy, hankuka sun soma dawowa jikkunansu, duk da har yanzu Irfaan abin na tare dashi sosai.
"Zaune suke gaba 'dayansu a wasu kujeru mai table a tsakiya wanda daga gani ba sai ance maka na sha'katawa bane dake a farfajiyan gidan, daddy na ri'ke da precious Nilam 'dinsa, Amir da Aiman sunata wasa a can gefe, fruits ne a gabansu wanda aka yayyakan 'kanana kaman friut salat cikin wasu cups masu 'kasa me 'dan tsini, ko wani cup akwai 'dan stick a ciki wanda ake cin friuts 'din dashi.
"Irfaan ne ya fito daga cikin gidan yana sanye cikin armless shirt red da faran three quarter ya 'karaso fuskansa babu yabo babu fallasa ya gaida Amma da Daddy kafin ya zauna a 'daya daga cikin kujerun, Nadiya ta mi'ka masa cup 'daya tace " ya Irfaan have some, ta'be baki yayi yace " no thanks.... kallonsa duka sukayi kafin tace" zai taimaka maka da appetite. Girgiza kai yayi a karo na biyu kafin ya 'karasa ya kar'bi Nilam dake hannun daddy yace " come here Angel. Wasa yake kan yima Nilam tana dariya, shi kansa sosai yake dariya, su daddy da Amma harma da Nadiya saida sukaji da'din sakewan da Irfaan yayi.
"Bayan ya zauna ne Daddy yace" irfaan dama fitowarka muke jira, Irfaan ya 'dago ido yana duban Daddy kafin Dady yaci gaba da fa'din" mun yanke shawarin komawa Nigeria in the next few days, what do you think.
"Shiru kaman nazaice komai ba sai kuma yace" is that really necessary. ?... "Daddy ya ri'ko hannunsa yace Son, hakan ne kawai zai mantar mana da rashi babban da mukayi a nan States, and your siblings ya kamata su san 'kasarsu su san al'adunsu, I think lokaci yayi da zamu koma.
"Shiru Irfaan ya 'danyi kafin ya 'dago ya dubi mahaifin nasa yace" but Daddy what about my sch, na riga na fara university a nan..... " shiru Daddy ya'danyi na wasu lokuta.,.... kafin yace " yeah son hakane,....." Amma ce ta katse su da fa'din" Yes dole mu bar States in a couple of days, na gaji da zaman nan snn mahaifinku ma gwara mu tafi ya samu yayi aure..... ai bata gama rufe baki ba Nadiya ta mi'ke tana masu mugun kallo kafin tace" Amma aure fa kikace, daddy ne zaiyi aure for heaven sake, this is ridiculous. Wllhi daddy bazaiyi aure ba, wato har kin mance mutuwan mummyn mu kina masa magan....." Enough Nadiya, Irfaan ya daka mata tsawa, ma Amma ne ko ma Daddy kike 'daga murya,.... Amma da Daddy kam mamakin kishi irin na Nadiya suke ji, 'karama da ita har tana taya late mother dinta kishi...
" Kuka Nadiya ta fashe dashi ta shige cikin gida a guje, Irfaan na kwala mata kira inaaaa ko saurarensu batayi ba ta shige, Aiman da Amir dake gefe suna wasa ganin Nadiya ta shige a guje tana kuka yasa suma suka fashe da kuka a tunaninsu wani ne zai sake mutuwa, nan suma su Amir da Aiman suka rufa mata baya.
" Engr. Nazif idan akwai abunda yafi tsana tofah shine 'bacin ran 'ya'yansa, musamman da yanzu mahaifiyarsu ta mutu, yayi al'kawarin bazai sa su kuka ba, zai zame masu uwa da uba, zai kasance tare dasu a ko wani irin hali suke ciki... " Da sauri irfaan ya mi'ke yabi bayan 'kannensa..... Daddy yabisu da kallo kafin ya juyo yana kallon Amma yace" pls Amma you need to be more understanding with what they are going through, you shouldn't have talk that way. Ki tunafa they just lost their mother, be kamata kimin maganar aure yanzu ba, especially at their presence.
"Kallon mamaki Amma tabisa dashi kafin tace" dole mu koma Nigeria, bazan iya tsayuwa inaji ina gani 'dabi'un turawan yamma yayi tasiri a zukatan jikoki na ba,..... daga haka Amma ta mi'ke ta shige cikin gida.


"Knocking Daddy keyi a 'kofar 'dakin Nadiya amma fir ta'ki bu'dewa, " Pls sweetheart, let us talk....cikin kuka take fa'din" no just go away, I don't wanna see you, you going to marry another woman, aren't you?.
"Daddy ya fuzar da iska yace" Sweetheart, let me in first, let's talk about this..... juyawan da Daddy zeyi yaga Amir da Aiman suna shar'ban kuka, da sauri ya 'karasa wajensu ya tsuguna ya rungumosu yana fa'din" what's wrong boys....." cikin kuka suke fadin" Adda Nadiya told us you're going to abandon us, you'll have a new family in Nigeria......." Dafe kansa Daddy yayi a hankali ya furta" Lord of mercy" rungumesu yayi yace" that will never happen boys, I love you ultimately, I will never abandon you. Oya come here , ya manna masu kiss a gashinsu, kafin ya mi'ke yana ri'ke dasu suka soma sau'kowa daga stirs.......


πŸ‘ΈπŸ»QueenSamyNovelsπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.......
[8/18, 20:21] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye* 02


_Written by QueenSamy_........πŸ“


"Haka Nadiya taki bu'de 'kofan nan har dare, gaba 'daya hankulansu yatashi, da 'kyar da magiya ta bu'de wa mahaifinta, lallashinta ya shiga yi kaman wata 'karamar yarinya ita kuwa sai basar da dad din nata take, wnn mummunan 'dabi'a na western people sosai yayi tasiri a rayuwan gidan Engr. Nazif Mumtaz,
"Daddy promise me you'll not remarry. Nadiya tace cike da shagwa'ba, rungumota Daddy yayi yace" my dear stop thinking silly ok, for now kula da rayuwarku shine a gabana ba batun aure ba, your grandma wasa take kawai, ba sabida aure take so mu koma Nigeria ba, you see sweetheart, akwai Company din late daddy na a Nigeria *M&M Builders*, so ever since your grandpa pass away amininsa shi yake running company din, I think lokaci yayi da zan koma na kar'bi companyn dad dina na ci gaba da kula dashi, what do you think.
"Shiru Nadiya ta 'danyi kafin tace" what about your job here in the States. Hannayenta daddy ya ri'ke yace "I'll resign darling.
"But daddy are you sure we gonna have a better life there, I mean our sch and so on........" Cike da 'kosawa da tambayoyin Nadiya 'karama da ita sai yawan magana, daddy yayi gyaran murya yace" of course honey that will be even much better. I promise you that.
"But daddy what about our friends here in the States, am sure we gonna miss them.... ta 'karashe maganar tana turo baki.
"Daddy yace" sweedy pls stop making this so difficult okay, you'll have a chance to say good bye to them okay... now let's go and have dinner ok.
"A tare suka sau'ko downstairs daddy na ri'ke da hannunta, he's so friendly to his kids.... "Amma tabisu da kallo kawai tana mamakin yanda gaba 'daya 'dabi'un turawa yayi tasiri a rayuwan gidan 'danta.
"Da murmushi Daddy yace" kids tomorrow you'll visit all your friends, and say goodbye to them ok.... Amir da aiman suka soma murna suna fa'din" yeeeey we leaving to Nigeria. Ta'be baki Nadiya tayi ba tare da tace komai ba.
"Irfaan ne ya shigo babu ko sallama sai cewa da yayi " Hi everyone, daddy yace" Son let's have dinner. Irfaan ya 'dan yamutsa fuska yace" daddy I don't feel like eating, just go ahead. Amma tabisa da kallo kafin tace" irfaan zo ka zauna kaci ko ka'dan ne, kallonta Irfaan yayi da manyan idanunsa harda wani juyasu kafin ywce" Okay granny just because you insist..... " ya zauna a 'daya daga cikin kujerun yana duban Nadiya, Spoon 'din gabanta ya 'dauka kafin yace" hey are you still mad, baki a tureta 'dago ido tana dubansa..... "Daddy yayi karaf yace" Son eat up, is your favorite, murmushi Irfaan yayi ya soma cakalan abincin kaman me tausayinsa,
"So when are you guys leaving? Irfaan ya tambaya, daddy yace in a couple of days, Son be careful while you're here alone okay....
"Irfaan ya gya'da kansa yace" you really don't have to worry about that daddy, am not a spoiled child, kai da mummy raised me well, may she rest in peace, duka suka amsa da ameen.
"Daddy yace" duk da haka Son, you really need to be very careful, kaga yanzu ka soma karatu just level 2 kake, snn kace har masters zakayi kafin ka dawo Nigeria, so kaga dole na damu.
"Irfaan ya juyo ya kalli Amma yace" Amma you see daddy is treating me like a kid again, ko zamu zauna dake a nan States ne.
"Ta'be baki Amma tayi tace" Allah tsareni da ci gaba da zama a nan, yara duk baku san al'adunku ba kun ri'ke _al'adun wasu_ kuna koyi dasu, kaima da zaran ka gama sch zaka dawo Nigeria.
"Murmushi kawai irfaan yayi yace a ransa _me zai kaini Nigeria for goodness sake, I rather stay here all alone da na koma Nigeria_..... "Tattaunawa suka ci gaba dayi har zuwa lokacin da suka gama cin dinner.


"Nadiya ta dubi Amma tace" Amma zamu tafi da Nannyn Nilam Nigeria knn, Amma ta narka mata harara tace" akan me taje taci gaba da koya mata 'dabi'un wasu, I'll find her another Nanny a Nigeria. Nadiya tayi kicikicin da fuska tace pls Amma kinga mun yarda zamu koma Nigeria, pls do this for us, mu tafi da Patricia taci gaba da kula da Nilam, itace tasan Nilam tasan abunda take so da wanda bata so, pls Amma don't say no, I beg of you.... ta 'karaso ta haye jikin Amma tana ro'konta.
"Dole ba don Amma taso ba tace" alright fine, naji zamu tafi da Patricia amma da zaran Nilam ta soma wayo zamu sama mata nanny musulma a Nigeria wacce zata koya mata da'bi'u masu kyau. Nadiya ta 'dan turo baki ba tareda ta kuma cewa komai ba. Daddy ma yayi na'am da shawarin Nadiya, dan kuwa Nilam bata yarda da kowa sai Patricia snn idan akwai abunda ya fi tsana tofah shine kukan Precious 'dinsa....
"Kwana biyar suka 'kara a Los Angeles kafin suka 'daga zuwa gida Nigeria.....




*Nigeria*
_Abuja ( LifeCamp)_........


"Unguwar LifeCamp dake birnin tarayya Abuja, unguwace wanda gidajen dake ciki ka'dai ya isa ya tabbatar maka da cewa gidajen masu hanu da shuni ne, ko wani gida yana jere cikin tsari da kyau, akasarin ginannukan gidajen bene ne.
"Gidan Engr.Nazif Mumtaz yana 'daya daga cikin jerin gwanon gidajen nan, tsayuwa fa'din irin tsaruwan da gidan yayi 'bata lokaci ne, dan kuwa komai na gidan me kyau ne abin birgewa gwanin sha'awa. Kyaun gidan yasa Nadiya taji da'din dawowa Nigeria, dan kuwa ita yarinya ce me bala'in son kyale'kyale.


*M&M (Mumtaz and Ma'aruf) Builders Of Company*


"Alhaj Ma'aruf ya kalli Daddy yace " gwara da Allah yasa ka dawo dan dama ni gaji da ri'kon wnn mu'kami, dan shekaru sunja, nima ina bu'katan hutawa. Daddy yayi murmushi ya kalli Alhj Ma'aruf aminin mahaifinsa kafin yace" Baba na gode da 'dawainiyan dakayita min da dukiyata Allah ne kawai zai biyaka.
"Girgiza kai Alhj Ma'aruf yayi yace" Nazif idan akwai wanda yafi cancanta ya mi'ka godiyansa to nine, dan kuwa mahaifinka Mumtaz ya gama min komai a rayuwa. Ya shiga bu'de files yana ciro takardu ya mi'ka masa kafin yace" an jima zamu kira meeting gaba 'daya staff su hallara, the New President of M&M Builders is here.
" Daddy ya girgiza kai yace" A'a Baba you'll remain the president, ni zan ri'ke mu'kamin Chairman, Alhj Ma'aruf ya girgiza kai yace" Nazif kai zaka zama president, besides kaine me highest shears a M&M builders, ni zan yi retire ne daga rana me kamar ta yau, kai zaka ci gaba da juya mun dukiyata.....
"Haka aka kira meeting a babban conference hall dinsu tareda Shear holders da kuma staff dinsu, aka gabatar da new President of Mumtaz Builders, .... "Daddy ya gabatar da kansa hadi da gaisawa da illahirin mutanen....






"Hajiya Karima ta cika tayi fam dajin irin batun da mijin nata yazo mata dashi, ita fah zama dashi take dan ta mallaki M&M Builders amma bacin haka me zaisa taci gaba da zama da wann tsohon wanda tasan nan bada jimawa ba zai zama gawa. "Mikewa tayi taci gaba da safa da marwa a cikin 'dakinta, a hankali ta furta tabb inaa bazata ta'ba sakuwa ba, dole na san yanda zanyi na kar'ba wa tilon 'yata Companynta.......


πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹......
[8/18, 20:21] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye* 03


_Written by QueenSamy_........πŸ“


"Laila ce keta doka Sallama a 'kofa amma ko ka'dan Hajiya Karima bataji ba, sosai hankalinta ya tafi ga tunanin da take, da mugun mamaki Laila ke bin mahaifiyar tata da kallo har ta 'karasa shigowa cikin 'dakin.
"Hajiya! Shiru hajiya karima bata amsa ba, Laila tayi gajeren tsaki ta shiga buga kujeran da Hajiya ke kai tace" Hajiyaaa! Wnn karan da 'dan 'karfi sai snn Hajiya Karima ta 'dago tana duban Laila tace" Ke kuma yaushe kika zo...." Laila ta jakanta bisa sofa tana zame mayafin kanta take fa'din, nafi minti biyar a nan ina sallama baki jini ba, Hajiya tunanin me kike ne haka.
"Hajiya Karima ta sau'ke ajiyan zuciya kafin tace ke kuma daga ina?
"Laila tace na sau'ke Aziza gidan 'kawarta shine na 'karaso,. Hajiya wai meke damunki ne, kinsan fa likita ya hanaki yawan damuwa.
"Galala Hajiya Karima ta kalli Laila kafin tace" tunanin 'dan isakan tsohon nan nake.
"Da mugun mamaki Laila ke kallonta kafin tace" waye kuma 'dan iskan tsoho?
"Tsaki Hajiya ta buga kafin tace Alhj Ma'aruf........
"Kan ubancan! Hakan Laila tace a fili. Ido cikin ido take duban mahaifiyar tata kafun tace wai dama Alhaji ne 'dan iskan tsohon, mahaifi na.
"Tsaki Hajiya ta buga a karo na biyu kafin tace" yo meye idan ba 'dan iska ba, har nice zai dubi tsaban ido na yace ya cire hannunsa a M&M Builders, wai 'dan Late Alhj Mumtaz ya dawo daga States

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login