Showing 72001 words to 75000 words out of 159062 words
Chapter 25 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt
masa auren Karime da yayi_ ya runtse runtse idanunsa kafin yaci gaba da addu'a wa Engr Nazif da family dinsa gameda sharrin Karime da zuri'arta....
★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★
*Some weeks later*
"Engr ya dawo daga k'asar Holland, Safwan ya soma aiki gadan gadan da companyn M&M Bulders, snn an saka bikin Deejah da Irfan wata guda kacal me zuwa,
"Shirye shirye ake babu kama kafan yaro, duk yanda Azee da Ahidjo suka so b'ullo wa lamarin Irfan da Deejah abin yaci tura, hankulansu na ci gana da tashi, gaba d'aya sun rasa yanda zasu b'ullo wa lamarin auren suna hanashi aukuwa, kullum sukanhad'u toh kuwa sai sun aikata masha'ansu.
"A b'angaren Nadiya kuwa son Sadiq a kullum kaman k'ara azamata wutarsa ake, tunda sukayi resuming sch kullum saitaje Caf ko bazataci komai ba, sai taje ta gaida Mamie, gaba d'aya duk wani arrogantly nata ta rage, ta soma living simple life, duk wann so da k'auna da take wa Sadiq bata tab'a gigin fad'a masa ba koda da wasa ne, dukda a yanzu ya rage tsanan da yayi mata a baya ,sukan gaisa sosai, sukan jima suna waya, wasu lokutan ya bata shawarwari gameda karatu. Mamie ma sosai suka saba da Nadiya fiye da sabin da sukayi da Deejah.
"A b'angaren Ruqayya kuwa a duniya idan akwai wanda ta tsana toh a bayan Nadiya ce, ko kad'an bata son ganinta musamman da yanzu ta sake sosai da Sadiq, kullum Sadiq cikin tausanta yake yana fad'a mata babu komai tsakaninsa da Nadiya face ya d'auketa tamkar k'anwa.....
"Ammah ta had'a lefe na gani na fad'a, Engr da kansa ya yayi masu visa zuwa k'asar Dubai shi Ammah, Laila, Irfan da Deejah dan zab'an dangin furniture da kuma sauran kayan lefe, wann abu ba k'aramin d'aga hankalin Azee da laila yayi ba.., "Koda suka koma wajen boka abu guda ya k'ara gaya masu, Irfan shine mijin Deejah dukda sai an sami tangard'a a auren, zullumi da tunani babu irin wanda basu shiga ba, Laila dai k'arfin hali take tana tsunduma kanta a hidiman dan kar a d'agota. Azee kam har rama da bak'i saida ta d'anyi kaman wacce ta kwanta cuta.
"Gaba d'aya yaran gidan murna suke musamman dashike bikin fari kenan da zai kasance a gidansu, bama kaman Nilam wacce ta kasance 'yar gaban goshin amarya da ango, kullum tana mak'ale da Deejah, Deejah ta dage zaidai ta tafi da Nilam can gidansu bayan biki.
"A b'angaren Aunty Larai ma ba'a barta a baya ba, dukda yanzu bata orphanage na Abuja tazo maganan shirye shirye, nan Yusra take jin labarin kwatsam sai kuma ta gani a shafukan sada zumunta na yanar gizo.
"Duk wann bidiri Safwan bai tab'a sanin wai Deejarsa ce ta club ake zance zatayi aure ba........
_Toohh fah, yaya kenan zata kaya readers? Shin kuna ganin Safwan zai bari ayi auren nan, shin Azee ta hak'ura da Irfan kenan, shin Ahidjo ya janye k'udirinsa akan Deejah kenan. Toh wai ina kuka baro Yussy shin zata rufa wa Aminiyarta asiri har ta cimma burinta na auren Irfan..... Shin yaya zata kaya tsakanin Ruqayya, Nadiya da kuma Sadiq........ Wai yaya batun fita da baba Alhaji k'asar waje , shin Hajiya Karime zata bari hakan ta kasance???_
_Toh ku biyo Queen Samy dan jin ci gaban wann rikiceccen al'amari zata kaya_👌🏽
_👸🏻QueenSamy.......😍💄👄_
[8/28, 14:08] Umar Dalha: 🌗🌗🌗🌗 *Mallakin Waye*
53
*©Sameena Aleeyou*
_Queen Samy Novels Forum...... 📖📚_
"Gaba d'aya Irfan sai wani shisshigewa jikin Deejah yake yanai mata salon soyayyarsa, wanda duk wani mahaluk'i dake wajen saida suka burgesa, koda Mc ya bak'aci amarya da ango su fito suyi rawa dan nuna farin cikinsu, Deejah kam kasa tashi tayi, Irfan babu ko kunya ya kamo hannunta duk tabi ta daburce, a hankali ya tallafo k'ugunta suna rawa a hankali wanda zamu iya cewa motsa jikinsu kawai suke, jin yanda jikinta ya soma rawa a kunnenta Irfan yake rad'a mata, "just calm down baby I love you dukda daurewa kawai yake amma yana tsananin buk'atan babynsa...., kaji Mc ya soma fad'in"Wooow so fascinating, this Groom really luvs his beautiful bride, nan su Ashraf mutan US suka nufosu abinda sukafi so kenan Ahidjo ma ba son yaso ba ya taso amma ji yake kaman ya shak'a Irfan ya huta, lik'i suka yi masu babu k'kautawa suna tayasu rawan k'arshe hannun abokinsu suka rik'e aka saka masu music d'in da suka fi so suna tik'a rawa tamkar su ke rera wak'ar, Deejah kuwa a haka ta sulale ta koma mazauninta, duk gaba d'aya sai kunya take faman ji yanda irfan keta wani riritata..... tana zama taji muryan Nadiya a kunnenta tana fad'in" Ohhh gaskiya wnn angon daga gani babu d'aga k'afa Deee zakiyi bayani mudai babu ruwanmu, ta k'areshe maganar tana k'unshe dariya. "Harara Deejah ta narka mata ba tarera ta iya furta koda kalma guda ba, dan gaba d'aya ji tayi jikinta yayi sanyi kaman wani abu na shirin faruwa da ita, ta hangi fuskan Irfan farincikinsa a bayyane yake, annuri ne tsantsan ke tashi a fuskan nasa, a hankali ta sauk'e ajiyan zuciya gamida runtse ido jin yanda k'irjinta ya soma lugude haka kawai...
"Daga yanda suke tsaye sun gama ganin komai Safwan ya jawo hannun Yussy suka nufo waje, fizge hannunta tayi kafin tace" wllhi bazan tafi ba ban nuna wa Deejah b'acin raina na rashin gayyata ta da batayi ba, kaidai idan zaka tafi bisimillah go ahead,.... " Gajeren tsaki Safwan yayi kafin yace" that's enough am not in the mood... just don't provoke me Yusra. Deejah will never ever get married, she need to stop that dreaming of hers. Ya k'areshe maganar yana mai shafe namar goshinsa.
"Harara Yussy ta galla masa kafin tace" tace kan me zata fasa aurenta, sabida har yanzu kana sonta ko? ...... "Shiru Safwan yayi bai iya amsa ta ba, "Yusra ta kuma tunzura..... "Ka fad'a mun Safwan har yanzu son Deejah kake ko, Deejah will never love you back, you'll never ever win her heart, ta sami wanda take so, ka dubi yanayin mijin Deejah ka dubeka babu had'i wutsiyar rak'umi ya riga da yayi nesa da k'asa, Mijin Deejah yafika da komai da komai..... "Ji kake Tasssssss!!!! Safwan ya kifa mata mari, dafe k'uncinta tayi tanai masa mugun kallo gaba d'anyansu sai huci suke, jawota yayi daf da jikinta ya matse ta sosai kafin ya soma fad'in" be careful witj what you're sayin right now, so kike kiji daga bakina "Noo I don't love Deejah anymore, right now am fighting for my niece to achieve her dream. Fad'a zanyi wa 'yar yaya na ta sami farin cikinta Irfan, but not for my self... did you get thaaaaat!!! Ya karashe maganar cikin daga murya.
"Laila da ta gama jin komai ta karaso gamida janye Yusra daga jikin Safwan..... "Kallonta yussy tayi tsaf ta ganeta karuwan Safwan ne kuma matan Ogan sa na Company snn mahaifin Irfan. Fizge hannunta tayi daga rik'on da laila tayi mata. Murmushi Laila ta sakar mata kafin tace" Yusra ki bani hankalinki a nan keda Safwan idan kina so kiyi kud'i fine zakiyi shi yanzun nan if you cooperate, zamuyi wani aiki tare dan na riga naji kalaman ku"Deejah was once a club member.!!!!! Ta k'areshe maganar tana wani murmushin k'eta.
"Sauk'e ajiyan zuciya Safwan yayi, dan kuwa ya shirya a wargaza wnn aure da Deejah ke k'ok'arin yi, har yau har gobe bazai daina sonta ba, snn farin cikin 'yarsa Azeeza shine farin cikinsa, muddin Azee zata samu Irfan tofah babu abunda bazaiyi ba dan ta samu koda hakan na nufin shi ya rasa nasa farin cikin.
"Motan Laila suka shige su duka ukun suka zuge glass yanda babu mai noticing nasu suka shiga tattauna ya da al'amarin zai kasance,
"Suna gama tattaunawa Yussy ta kanne ido tana kallon Laila kafin tace" Banda wuce gona da iri, ku min alk'awari iyaka abinda kuka fad'i zakuyi ma Deejah banda k'ari, dan Deejah aminiyata ce kuma ina sonta har gobe dan tana d'aya daga cikin mutane masu muhimmaci a rayuwata.
"Laila ta murmusa kafin tace" idandai wann ne bakida matsala, you have my word, just count on me. "Gyada kai Yussy tayi kafin tace inaso naji alart first thing in the morning if not zan b'ata komai, murmushi Laila ta kuma kafin tace bakida wann matsalan as far as I'll get rid of that witch kin gane... Juya idanu kawai Yussy tayi ta kalli Safwan tace bani wasu mintoci ina zuwa snn ta fice...... "Nan ta bar Safwan da Laila suka soma watsewar su dan basu raina had'uwa, koda na minti guda ne sai sun rage lokaci.... "Wa'yazubillah.
"Sanda Yussy ta shiga hall d'in an buk'aci amarya da k'awaye su fito su nuna nasu farin cikin, dan haka kai tsaye cikinsu ta nufa, ta sauk'o da gashin attach dinta ya rufe mata Sideview nata dan bata so wanda suka santa su ganeta.
"Kai tsaye wajen k'awarta Deejah amarya ta k'arasa yanda aketa faman rawa ana having fun.
"Kunnen Deejah ta k'arasa a hankali take rad'a mata "Congratulations my dearest aminiya,........ "Gaban Deejah ne yayi mugun fad'uwa "Yusra ta fad'i a zuciyarta, d'ago kai tqyi suna kallon juna, Yussy ta sakar mata murmushi kafin taci gaba da fad'in" You did a great catch, you choose the most handsome guy on earth, Ohh dear partner in Crimes, don't tell me kin k'i gayyata na ne dan kar na ruining maki happy life da kike ciki, am I right??, perhaps am quite sure husband to be dinki baisan true color dinki ba. But don't worry am not here to ruin your event, anyway nazo ne na tayaki murna though baki gayyace ni, but remember this friend *" Be careful with the people around you,watch your steps, my advice to you* daga haka Yussy ta kutsa tana neman hanyan ficewa..... "Irfan dai ya lura da yanda yanayin Deejah ya sauya sosai tunda wnn yarinya ta nufota, yaga alamun tanai mata magana snn baiga fuskan ta sosai ba dukda yaso gane kamannin yarinyar, ganin abun na neman damunsa yasa sa watsar da tunanin guje ma rushewar farin cikinsa.
"Ahidjo kuwa sauri sauri yabi bayan Yussy a sace saidai kan ya iso yanda suke ya hangi Laila Safwan da Yussy sun fice daga wajen, murmushi yayi yana shafa sajensa kafin ya furta "Something is goin on.
"Jiri ne ya soma d'iban Deejah, tabbas kalaman Yussy sunyi mugun d'aga mata hankali, me Yusra take nufi, patner in crimes, yeah quite alright ta sani zuwa rawa a club babban haramun ne, sab'awa ubangiji ne, amma ko ada lokacin tana zuwa club rawa kawai take bata tab'a bin wani namiji ba balle shaye shayen kayan maye, me Yussy take nufi tayi hankali da mutanen da take tareda su Anya ba wani abin take shirin k'ulla mata ba, if Irfan finds out she was once a dancer in a club ta sani he'll definitely hate her, dan kuwa yasha fad'a mata the wotse abinda ya tsana a rayuwarsa toh fa mace maras kamun kai nee,.
"Sosai Jiri ke d'iban Deejah sai faman kama goshinta take tana yunk'urin fad'uwa, cikin sauri Irfan ya k'arasa ai kuwa nan ta fad'i cikin jikinsa, nan hankulan mutane yayi kansu. Kiran sunan ta yake yana jijjiga ta amma inaaa tamakar macecciya haka ta koma, cikin d'aga murya ya d'agi yana duban jama'an wajen yanda sukayi caaa in a shock suna kallonsu ya soma fad'in" Get a car, Sadiq just do something, ya ci gaba da jijjjiga Deejah yana ambaton sunanta.... 'Kaman zararre ya fice yabi bayan Sadiq da Deejah a hannunsa, su nadiya dadai sauran relatives nasu gaba daya suka bi bayansu hankali tashe.....
👸🏻Queensamy😍💄👄............
[8/28, 14:08] Umar Dalha: 🌗🌗🌗🌗 *Mallakin Waye*
54
*©Sameena Aleeyou*
_Queen Samy Novels Forum......📖📚_
"Nazif lafia dai ko na ganka haka, you don't seem normal, kaman wani abu na damun ka, cewan Ammah dake k'ok'arn zama gefen Engr.
"Sauk'e ajiyan zuciya Engr yayi kafin yace" Ammah baki kwanta ba,
"Kai kawai ta gyad'a kana tace" Ai bazan iya kwanciya ba har sai naga dawowan yaran nan gida.
"Murmushi Engr yayi kafin yace Amman Irfan kuma Ammah na.
"Zama tayi tana me murmusawa kafin tace" ina saurarenka meke damunka.
"Shiru kaman mai nazari sai kuma ya shafi gashin kansa ya soma fad'in" Ammah, akan Deejah ne, gaba d'aya d'abi'un ta yana mun shige dana Fateemah, ina ganin fuskan Fateemah a fuskanta, yanayinta yana mun tamkar Fateemah,...... "Shiru yayi kaman wanda ya tuna wani abin.
"Cikeda tausayin d'an nata Ammah ta matso dap dashi hannayensa ta rik'e cikin nata, a hankali ta soma fad'in" Nazif har yaushe zaka cire son Fateemah a ranka, har yaushe zaka fuskanci rayuwa yanda tazo maka, Fateemah ta tafi she's gone forever. Koda ace Fateemah tana raye bazata zama *Mallakin Ka* ba, ta riga tayi aure da waninka balle ma bata raye." Soyayyan da Irfan keyiwa Deejah da kuma soyayyan da gaba d'aya ahalin gidan nan suke mata shiyasa kake ganinta tamkar Fateemah. Ammah ta kuma rik'e hannun Engr sosai kafin tace" Son, you need to let go of your past, ka mance da Fateemah har abada a duk sanda ka tunota kayi mata addu'a, snn kayi k'ok'ari yakice tunanin ta a zuciyarka, Allah yana tare da kai bazaka tab'e ba da yardansa,
"Murmushi Engr yayi yana mai sunbatan hannayen Ammahn sa, hak'ik'a Ammah jigo ce babba a rayuwarsa, yayi godiyawa Allah da ya bar masa uwarsa har yau a raye, wacce ta kasance garkuwa ma rayuwar sa......."Suna a haka wayar Engr ta soma ruri, Nadiya ce me kira.
"Engr yana dagawa daga d'aya b'angaren Nadiya ta soma fad'in "Daddy it's Deejah, she fainted a while ago a wajen event....."Innalillahi wa inna'ilahirrajun Engr ke fadi, ya mike tsaye yana tambayan Nadiya me ya faru wani asibiti, suke,..... "Ammah ma mikewa tayi tana kallon Engr cikeda firgici.
"Engr na gama waya da Nadiya ya sanar wa Ammah halin da ake ciki, salati Ammah ta shiga yi babu shiri ta fice zuwa sashenta dan dauko mayafi, Engr da kansa yayi driving nasu zuwa hospital din.
"Irfan na zaune a gefenta tana jingine da pillow hannunta na hangu mak'ale da drip ruwa yake bata a cup tana kurb'a da kyar. Yayinda Ahidjo, Sadiq, Nadiya da Ruqayya ke tsaye gefe duk suna mata sannu.... "Su Ammah da Engrne sukayi sallama suka shigo, kai tsaye wajen gadon suka nufa sunai ma Deejah sannu suna tambayan me ya faru, Irfan ne ya soma masu bayani"
"Dr yace there's nothing to worry about, she's been stressed up da hidiman biki and bata son cin abinci yunwa ne yasa ta sume.
"Ammah ta karasa ta dafata tanai mata sannu, nan sauran jama'an dake cikin d'akin suka soma gaida Engr da Ammah. "Engr ya matsa kusanta yanai mata sannu" Gaba d'aya sai kunya ya lullub'e Deejah, sai faman sunne kai take.
"Engr ya dubi su Nadiya yace" ina Aunty naku??
"Cikin sauri Azee ta soma fad'in" daddy dama zata biya gidan amarya tace zasu kai kaya itadasu Aunty Salma.
"Gyada kawai yayi dan kuwa abun Laila ya soma damunsa, aiko da biki ake ta sanar dashi idan zata wani wajen, ganin halin da ake ciki yasa sa kau da tunanin, daga haka su Sadiq Ahidjo dasu Nady da Azee suka fice zuwa reception
"Engr ya dubi Irfan yace" Son" daga yau a dakatar da sauran Events din da ba'ayi ba, idan Allah ya kaimu ranr daurin auren kawai sai a daura auren. "Ammah tace hakan yayi lafiya ai yafi komai.
"Kai kawai Irfan ya gyada kafin yace" toh daddy.
"Ina Dr din I want to speak with him. Cewar Engr, kan ya gama rufe baki Dr ya shigo lokacin drip dinma saura kadan.
"Bayan sun gaisa da Engr, nan suka soma tattauna lamarin, Dr yace babu komai stress ne kawai da yunwa, drip na karewa za'a discharging nata basai ta kwana ba. A tare Dr da Engr suka fice suna magana.
"Azee tana fita ta shiga neman layin Laila, nan ta shafa mata komai abinda ake ciki, wata shewa Laila ta kwashe dashi ta dubi Safwan dake gefenta ta kashe masa ido guda, nan tace wa Azee ta kwantar da hankalinta komai zai zama normal, Irfan ya kusa zama *Mallakin ta* daga haka tayi hanging up. Azee kuwa rik'e wayar a hannu tayi tana nazarin kalaman momynta Laila.
"Drip na k'arewa aka sallamesu.
"Suna tsaye a haraban asibitin su uku kafin su Ammah su fito da Deejah, Irfan ya kalli Sadiq da Ahidjo yace, Friends na gode sosai da kulawarku a gareni.
"Murmushi sukayi kafin Sadiq yace" come on guy babu godiya ai, you are indeed our bro from another mum right Ahidjo??? Ya k'areshe maganar yana duban Ahidjo. Ahidjo ya gyada kansa kana yace "Sure haka ne Sadiq. Hannu Ahidjo ya mik'a masu kafin yace barinje na duba su Ashraf, daga can zan wuce gida, ya dubi Irfan yace "Friend Allah k'ara sauk'i a gaida madam sosai. Murmushi Irfan yayi suka danyi hugging