Showing 75001 words to 78000 words out of 159062 words

Chapter 26 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10397

juna kafin yace Alright sai munyi waya..
Sadiq ma nan yayi waya ya sanar da mamie jikin Deejah da sauki gashi nan dawowa da Ruqayya. Nan sukayi sallama da Irfan shima ya wuce.
"Su Ammah na fitowa itada Nadiya rik'e da Deejah, ji yayi kaman yaje ya sungumeta ko ya rungumeta cikin k'irjinsa, da sauri ya k'araso ya bud'e masu mota suka shige nan shima ya shihe driber seat sai faman juyowa yake yana mata sannu...kai tsaye suka nufo gida,
"Irfan sai faman rirtata yake, baby ko na d'aukeki ne? Bata iya ce masa komai sai girgiza kai kawai, parlorn Ammah ta zauna da kansa ya shiga kitchen had'o mata shayi, babu yanda su Ammah dasu Nadiya basuyi ba ya bari suyi d'awainiyar Deejah fir yak'i da kansa ya had'o tea din. Ammah ta tan'e baki gamida yin murmushi, tace baban soyayya ba d'aki ta wuce bayan tayi ma Deejah Allah k'ara sauk'i
, "ya zauna gefenta yace oya seat up ki shanye wnn yea din,.... zatayi gardama taga babu alamun wasa a fuskansa.
"Babu musu ta karb'a ta soma sha, ....."Laila ce ta shigo fuskanta cike da damuwa kaman gaske, kai tsaye wajen Deejah ta nufa ta soma mata sannu
"Oh my dear you must be nervous, but dole kici abinci, ai hidiman biki ya gaji haka, tasa hannu ta karb'i cup din daga hannun Irfan, ta shiga bata a baki. Ta kalli Irfan cike da kulawa tace" Son I know you must be exhausted, you need some rest, kaje ka kwanta I'll look after her for you kaji son, ta k'areshe maganar cikin sigan yaudara.
"Babu yanda Irfan ya iya dole ya amince da batun Laila, yana bata matsayi sabida yanda take kula dasu baki d'aya.
"Kallon Deejah yayi wanda itama shi take kallo kafin yace" baby make sure you take all your prescriptions okay, I love you, ya hura mata kiss kan tafin hannunsa,
"Ba Azee dake lab'e kan staircase tana kallonsu ba harta Laila dake zaune gabansu kaman hoto saida abun ya tab'ata, tabd'ijam wani irin so Irfan keyi wa Deejah, ganin dai zata rasa mind dinta yasata saurin composing kanta ta maida hankali wajen kula da Deejah, Azee kuwa sulalewa tayi a wajen tana maysan k'walla dan kuwa tasan Irfan bazai tab'a sonta ba, babu shakka zuciyan Irfan *Mallakin Deejah ne*......






πŸ‘ΈπŸ»QueenSamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„.......
[8/28, 14:08] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


55


*Β©Sameena Aleeyou*


_Queen Samy Novels Forum.....πŸ“–πŸ“š_


"Tunda ta kwanta ta kasa samun nitsetsen barci sakamakon wasu irin sararan mafarkai marassa kyau da take tayi, mik'ewa tayi da k'yar ta shige bathroom ta d'auro alwala tazo ta tada sallah.
"Tana nan zaune bisa sallaya wayanta ya soma ruri, wanda haka ya sauk'ar mata da mummunar fad'uwan gaba, da kyar ta iya k'arasawa jikin socket ta shiga kallon screen d'in wayar, ganin bak'uwar lamba ce yasata kuma jin wani fad'uwan gaban wanda ita kanta batasan dalilinsa ba.
"Har saida wayar ya yanke bata sami courage na d'auka ba, nan aka kuma kiranta, da k'yar ta iya sa hannu ta cire daga jikin chargi kafin ta k'ara a kunnuwanta had'e da sallama.
"Daga d'aya b'angaren aka bushe da dariya kafin yaci gaba da fad'in"
"Congratulations my dearest one, So kin zata zaki guje min a cikin garin nan kije kiyi aure, kin zata zan daina sonki ne har abada ko kuma kin zata zaki iya b'ace mun ne Deejah??
"Cikin k'unan rai Deejah ta soma fad'in" what do you want from me Safwan, me kake so a wajena, meyasa kake kirana....."Saurin k'atseta yayi da fad'in" Ke nake so Deejah, ke kanki kinsan da haka, ever since I met you my dream is to be with you, how dear now zaki juya mun baya, after all that I've done to you is that how repay me Deejah, com'on fad'a mun me kike nufi da kika gudu kika barni, kin mance duk irin taimaka ma rayuwarki da tsare rayuwarki da nayi a can baya.
"Cikin kuka take fad'in" Safwan banci amanarka ba hasalima ban tab'a furta ina sonka ba, dan Allah na rok'i arzikinka ka fita hanyata pls, kar ka rusa mun farin cikin da nake ciki......"Dariya Safwan ya kwashe dashi kafin yace" Deejah yaushe kika yi sanyi haka, yaushe kika soma bada hak'uri wa mutane, tabbas lallai kina son wann miji naki da kike shirin aura, "amma dai inaga Familyn Nazif Mumtaz basu wacece d'ansu ke shirin aura ba, kokuma nace shi angon naki baisan wacece ke ba....
"A zabure Deejah ta mik'e daga yanda take zaune ta nemi kukan da take ta rasa, cikin sark'ewar murya take fad'in" Me ka isa ka min you juck, let me make this clear to you wllhi baka isa ka rabani da farin ciki na Irfan ba, da kake cewa basu sannni ba, k'warai sun san ko ni wacece tinda sunsan daga Orphanage nake daga gidan marayu nake sunsan labarin yanda iyayena suka salwanta, and still they accepted me the way I'm, so am quite sure there's nothing you can do to make them reject me....... "Woow! Bravo my dear, ashedai har yanzu bakin naki na nan, toh barikiji na gaya maki, ni nan Safwan inada abinda zaisa su tsaneki su tsani saninki da sukayi har abada, ba Irfan kawai ba duk wani masoyin Irfan sai ya tsaneki...... "Ki duba whatsapp dinki kiga pictures da videos din na tura maki, am quite sure zaki kirani ki nemi solution if not am gonna revealed it to the world. Daga haka ya katse kiran ya barta a tsaye tamkar gunki.....
"Jiri na neman kada ita sanda ta shiga whatsapp dinta taga Vidieos na rawan da tayi a club wanima maza sun sakata a tsakiya, ga kayan jikinta duka babu kyaun gani, ga pictures dinta marassa kyaun gani duka na club ne..... "Runtse idonta tayi ta soma karanto "Innalillahi wa inna'ilaihirraji un tana mai sulalewa a k'asa...."Me Safwan yake nufi da ita, me zai faru idan ahalin gidan nan suka ga wann pics da videos, wani irin kallo Irfan zai mata... "Tunaninta ya katse sanda ta tuna Irfan yasha fad'a mata babu abinda ya tsana a duniya kaman mace me zuwa club mace maras kamun kai, shin idan yaga wnn abu wani irin kallo zai mata...."Kuka ya kuma kufce mata da sauri ta shiga dialing numbern Safwan tana mai girgiza kai tana fad'in" No that can't be, bazai yuwu ba.......
"Da dariya ya d'aga wayan kafin yace" I knw you must call back, now kin yarda inada abinda zanyi ruining life d'inki...."Cikin kuka take fad'in"Safwan videos da pics din daka turo tsohuwar Deejah ce ba Deejahn yanzu ba, I've changed already, dan Allah kar ka ruining mun life din da nike ciki a yanzu I beg of you pls....."Cikin d'aga murya Safwan ya katseta da fad'in" Just shut up Deejah, did you think you I can let you go, kina tunanin zan daina sonki ne, well if you think that I'll leave for someone else then you're mistaken. I prove you wrong, bazan tab'a barinki ma wani ba Deejah, you are mine we are meant for each other besides we bothe suite each other mun dace da juna. Ina mai baki shawara idan baki so su san wnn hali naki just called up tje wedding just cancel your wedding with Irfan if not your precious life is inndanger, zannk'ara da abinda bakima yi ba na kuma sanar dasu har yanzu muna had'uwa a club....."Enough of this you juck, how could you blackmail me Safwan, if you truly loved me kaman yanda kake fad'a then let me be with the love of my life Irfan, let me with the family I love the most,... "Ta d'an sassauta murya kafin taci gaba da fa'din" Dan Allah Safwan karka min haka kar ka rabani da mutanen da nake jinsu kaman 'yan uwana na jini, kar ka rabani da mutanen da suka nuna mun tsan tsan so da k'auna......"Safwan ya katseta da fad'in" And if you don't want that to happen then ki fasa auren Irfan, ki janye batun auren Irfan ni kuma na miki alk'awarin babu wanda zaisan wancan abu da kikayi a baya, ki yarda dani Deejah na maki alk'awarin samun farin ciki maras misaltuwa farin cikin da kike mafarkin samu zan tanada maki su a gidana... "Shawara ya rage naki Deejah kinada zab'i guda biyu" Is either ki fasa auren Irfan asirinki ya rufu ko kuma ki amince da aurensa asirinki ya banka'du... daga haka Safwan ya kashe wayar yana murmushin mugunta.


"Dafe kanta tayi ta zube a wajen zuciyarta na barazanar tarwastewa, ta nemi addu'a ma ta rasa, wani irin tausayin kanta ne ya kamata, Allah sarki rashin iyaye babban ciwo ne, yau da tanada nata iyayen ta tabbata da makamancin haka bai faru da ita, tana tsananin son Irfan fiye da yanda take sin kanta, bata jin zata iya rayuwa da wani mahaluk'i bayan Irfan, ta tuna irin kalan soyayyan da yake nuna mata, ta tuna yanda ya yarda ya amince da ita koda basu san tak'amemmen iyayenta ba, ta tuna yanda familyn Irfan suka d'auke ta, shin idan suka ga wann mummunan hotuna da videos me zasu kalleta dashi, "Zuciyarta ya shiga raya mata zasu tsaneki yanda baki tsammani, babu kaman Irfan sai ya tsaneki fiye da mutuwa, shin kin tuna wani rana sanda kuka d'auko Ahidjo da Yusra a club, kin tuna yanda Irfan yayi reacting, wata d'iya mace ma kenan balle ace matan da yake shirin aure itace cikin irin wnn yanayi yaya kike ganin lamarin zai kasance...."Da sauri ta shiga toshe kunnuwanta tana girgiza kai ta soma gamida tak'urewa jikin gado tana rawan d'ari dan kuwa zazzafan zazzab'i ne ya sauk'ar mata. Sai yanzu take d'an danasani maras iyaka gameda rayuwar zuwa club da tayi, dama haka ne kar mutum ya raina aikin sab'o komin k'ank'ancinsa sanadiyan k'arami yakan iya zama babba, ko wani sharri Safwan ya lak'a mata babu wanda bazai yarda ba muddin suka ga wann video, Allah sarki rayuwa kenn mutum baya wuce kaddaransa a rayuwa... Runste idanunta tayi hawaye masu zafi suna bin k'uncinta, yayinda kyakkyawan fuskan abun k'aunarta Irfan ke mata gizo.....Baccinnda bata samu har wayewar.




"Duk bai wani sami ishesshen barci ba, hankalinsa na kanta, ya k'agu gari ya waye yaga yaya ta kwana, gashi through out the night neman wayarta yake daga farko yaga line busy daga baya yaji wayar gaba d'aya a kashe, ya danganta hakan da rashin wadaceccen network, .
"Tsaf ya shirya cikin Royal blue Jampa ya saka hula zanna bukar dark blue, woow zokaga yanda shigar ya karb'esa musamman dashike ba gwanin saka manyan kaya bane, turaren Vasece ya feshe jikinsa dashi ga agogo mai tsadan gaske da ya d'aura a hannunsa, kai masha Allah, sosai Irfan yayi kyau kana ganinsa ba sai ance maka ga ango ba, kai tsaye sashen Engr ya wuce dan gaishesa nan ya sami Laila na serving Engr break fast.
"Da sallama ya shigo yayinda suka amsa gaba d'aya fuskokinsu d'auke da murmushi suna daga dinning area. "Son k'araso mana Engr ya fad'i yana mai alama da hannu.
"Karasowa yayi ya zaune gefen kujeran Engr kadin yace" Daddy ina kwana, Engr ya amsa masa da sakin fuska kafin ya gaida Laila, itama faram faram kaman kullum ta amsa masa sai zolayansa take shikam Irfan murmushinsa mai class kawai yake yai.
"My dear I know you haven't eaten your break... let me serve you cewar Laila dake k'ok'arin bud'e warmers.
"Dan murmushi Irfan yayi kafin yace" No Aunty barin lek'a Deejah am ok though, daga haka ya mik'e, muryan Engr ya jiyo yana fad'in" Irfan yau mutanen Katsina zasu iso, nayi bucking masu flight, inaga by 12noon zasu iso, so sai ka sanar da drivers suje su dauko su a airport idan time din yayi, ni yanzu Office zan wuce I hope kaima zaka lek'o dan akwai wani desing na nake so kayi observing kafin a soma ginawa..... ."Da sauri Laila ta katse Engr da fad'in" Haba dai Daddy ai yau ranar Irfan ce, bai kamata yaje Office ba har sai nan da sati uku kafin nan ya gama cin angoncinsa.... "Engr na murmushi ya dubi Irfan dake faman sosa k'eya kana yace" wai hakane Son, hutun bai maka yawa ba... "'Dan murmushi Irfan yayi kafin yace" hakane daddy huyun baiyi yawa, I was even planning to go for Honeymoon, Engr ya kuma yin murmushi gamida fad'in" come here son ya bud'e masa hannunsa alamun runguma, nan irfan ya karasa yayi hugging mahaifin nasa, Allah yayi maka albarka Irfan cewar Engr, Laila dake ta faman murmushin yak'e da sauri tace ameen. Shima Irfan din da ameen ya amsa kafin yace thank you daddy, thank you for always been there for me, I love you, murmushi Engr ya kuma kafin yace" anything for you son, I love you too, when you finish deciding wani country kuke son zuwa Honeymoon you should let me know ok, sai na maku arranging komai. Godiya Irfan ya kuma yi wa Engr. Laila tana tayasa godiya kamar mutuniyar arziki. Mikewa Engr yayi ya nufi stirs
"Irfan ya juyo da dubansa ga Laila kafin yace" Aunty I forgot to ask you, jiya kuwa baby tasha maganin?
"Nan da nan Laila ta saka fuskan tausayi kafin tace" uhm Irfan bansan meke damun bride to be d'inkan nan ba, babu yanda banyi ba ta fad'a mun idan akwai abinda ke damunta amma tak'i, I don't know ko har yanzu bata sake dani bane, amma kai nasan zata iya fad'a maka tunda you are about to be her husband bazata b'oye maka komai ba.
"Kallon mamaki Irfan keyiwa Laila kafin yace" meke damunta Aunty...
"Laila ta dan saka fuskan tausayi kafin tace" my point exactly, nayi nayi ta fada mun tak'i watak'ila kai zata fad'a maka..... "Cikin sauri ya mik'e ba tareda ya gama jin me Laila ke fad'i ba ya fice.




"Babu yanda Hajja batayi ba Deejah ta saka wani abu a cikinta amma tak'i, Deejah ta kalli Hajja da idanunta da suka rine kafin tace"Hajja dan Allah kosu Ammah sun neme ni kice ban tashi ba.
"Hajja ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace" Ammah dai ta tashi amma su Nadiya kam basu tashi ba, su nilam kuma sun tafi sch duk da anyi yak'i dasu kafin suka tafi, wai yau bazasu ba ana biki a gidan su.
"Sauk'e ajiyan zuciya Deejah tayi kafin tace" Irfan fah? Kinga itowarsa.... "Girgiza kai Hajja tayi alamun a'a kafin tace" Khadeejatu wai meke damunki....."Knocking din da akayi a k'ofa ne ya katse su........




πŸ‘ΈπŸ»QueensamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„.........
[8/28, 14:09] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


56


*Β©Sameena Aleeyou*


_Queen Samy Novels Forum.....πŸ“–πŸ“š_




"Hajja ce ta k'arasa ta bud'e k'ofan, gaisawa suka somayi da Irfan, Deejah kuwa gabanta ne yayi mummunar faduwa jin muryan Irfan runtse idanunta tayi da k'arfin gaske.
"Hajja ta tashi kuwa? Ya tambaya cikeda kulawa.
"Kwarjinin Irfan ya hana Hajja tayi masa k'aryan bata tashi ba, cikin sauri ta gyada kanta kana tace"eee ta tashi k'aramin Alhaji.
"Gyada kai kawai yayi dan kuwa miskilin ba kasafai ya faye magana, duk cikin ma'aikatan gidan da Hajja kawai yake magana.
"Taci abinci? Ya kuma jefo ma Hajja tambaya. "Girgiza kai Hajja tayi kafin tace "bata ci komai tun tashinta.
"Ok kawo mun breakfast din,.. daga haka Hajja ta wuce tana fad'in "toh K'aramin Alhaji.


"Kwance ya ganta kan gadon ta tak'ure waje guda, da sallama ya shigo cikin muryansa mai dad'in saurare, kallo d'aya ya mata ya gane akwai abinda ke damunta, Deejah kam gaba d'aya kasa d'ago ido tayi ta dubesa.
"Hajja ce ta shigo da kayan kalaci ta ajiye gefen kan rug, daga haka ta fice.


"Tsare ta yayi da idanu yana zaune kan stool hannayensa had'e bisa hab'arsa, har lokacin ta kasa d'ago ido ta dubesa. Murmushin sa nan mai tsada wanda yake yi da gefen bakinsa shi ya d'anyi kafin yace" oya taso kiyi breakfast bai jira cewanta ba ya shiga zuba abinci a plate.
"Sai snn Deejah ta sami zarafin kallon Irfan" bai tab'a mata kyau irin ta yau ba, da yasan yanda manyan kaya suke masa kyau daya lak'anci saka su, yanda yake zuba abincin a plate ya burgeta kallonsa take cikeda so da k'auna, a lokaci guda taci bak'in cikinta ya yaye kallon Irfan ya yaye mata damuwarta, "Ohh she can't do without him.
"Dago kyawawan idanunsa yayi yaga ta kafesa da ido tana murmushi. "Murmushin shima yayi wanda hakan yasata jin kunya, tayi sauri rufe fuskanta da tafukan hannayenta,
"Tasowa yayi ya dawo kusa da ita, a hankali yasa hannunsa ya bud'e fuskanta kana yace" baby meke damunki, what's wrong with you pls.
"Murmushin k'arfin hali Deejah tayi kana tace" babu komai master, "a zahiri bata san me zata soma ce masa ba.
"Are you sure babu komai, you know I hate it when you're hidden something from me. Idan akwai abinda ke damunki just tell me, don't hesitate to tell me, remember we're one now, you'll soon be my Wife. Kwanan zaki zama matata kuma Sirri na.
"Murmushin ta kuma yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login