Showing 18001 words to 21000 words out of 159062 words

Chapter 7 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10400

'kal kana gani kasan hutu ya kamasa wani fresh dashi ga agogon Rollex da ya 'karawa hannun kyau. Hannu tasa ta kar'ba kana ta shiga share hawayenta. Cikin muryan sa me cike da nutsuwa ya soma bata baki" da haka har yayi horn a gate din gidan Alhj Ma'aruf.
"Laila ta juyo tana dubansa wani tsan tsan sonsa ne ke azalzalanta. Murmushi tayi tace na gode yaya Nazif Allah saka da Alkhairi. Murmushi Engr yayi yace no babu komai duk abinda nayi wa Baba Alhaji ban biyasa ba. Ki shiga gida yanzu ki kwanta ki huta snn kar kisa damuwa da tunani wa ranki kinji koh. "Gya'da kanta tayi zuciyanta na mata sanyi, Laila bata shige gida ba har saida taga ficewar motan Engr daga gidan....


"Yana tafe a mota, yana tunanin al'amarin, gaskiya shi ko ka'dan babu batun aure a rayuwarsa a halin yanzu dan macen da yake tsananin 'kauna Fatima ce kuma ya rasata, bayanta sai uwar 'y'yansa Khadija wacce taci albarkacin 'ya'ya, mace 'daya yake jin wani abu game da ita a yanzu, ita 'dinma ko k'dan baijin zai iya aurenta, dan ganinta yake tamkar 'yar da ya haifa ta cikinsa, yafi danganta son da yake mata da son 'ya'yansa. Shi yanzu duk bama wnn ba, baisan ta yaya 'ya'yansa zasu fuskanci lamarin ba idan yazo masu da batun, ya sani they won't understand anything more especially Nadiya.
"Yana gama parking kai tsaye cikin gidan ya nufa sashen su Amma,..... Deejah dasu Amir Aiman Nilam suna Study room suka hango Engr. Gaba daya yaran suka mi'ke suka nufesa. Rungumesu yayi ya shiga 'daga su one by one, Deejah na tsaye ta har'de hannu a 'kirji tana hangosu fuskanta 'dauke da murmushi take kallonsu, sosai Engr da yaransa suke burgeta, tana son taga uba mai damuwa da damuwar 'ya'yansa haka, Engr da yaransa tamkar abokai suke snn idan sunyi ba daidai ba suma sun san sauran... " Nilam tace daddy sannu da zuwa, Engr ya shafi gashinta yace yawwa my precious, Amir da Aiman ma suka masa sannumda zuwa. Kawunansu duka ya dafa yace" what are you guys doing? "Amir yace lesson Deejah take mana a study room, Engr yace good my kids. " 'dago kan da zaiyi yayi ido hu'du da Deejah tana kallonsu tana murmushi. Gabansa ne ya fa'di ya rasa duk sanda yaga Deejah sai ta tuna masa Fatima, wnn dalili ne yasa Engr ke fa'duwan gaba idan yaga Deejah. "Kunya ce ya kama Deejah ganin tayi sakare tana kallonsa har suka 'karaso wajen. Sunne kai tayi ta soma gaishesa, da murmushinsa ya amsa kafin ya dubi yaran yace ayi karatu sosai yarana. Daga haka ya wuce ciki. Deejah ta sau'ke ajiyan zuciya tace" let's continue kids....


"Yana shigs Amma ya samu zaune a parlor ga cazbaha a hannunta tana kallon National Geographic Wild. " ' karasowa yayi suka gaisa kafin tace" Son yaya dai akwai matsala ne. Dan ta gane 'dan nata kaman na cikin damuwa.
"Sau'ke ajiyan zuciya yayi kafin ya fuzar da iska yace Amma I want us to talk....




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.........
[8/19, 06:25] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye*

🌹13


*and this chapter is for you my Fans...... I luv you guyz like crazy πŸ˜ƒπŸ˜œ*


"Amma ta gyara zama tana duban Engr kafin tace ina saurarenka Nazif.
"Amma Baba Alhaji ne bashida lafiya, yana National hospital unconscious.... "Amma ta zaro ido tana karanto innalillahi wa inna'ilaihirra ji'un, Nazif me ya samesa? Engr ya share duskansa da tafukan hannayensa kafin yace" he's having a heart attack, yana intensive care yanzu haka. Amma ta mi'ke tana fa'din muje ka kaini na gansa...." riko hanunta Engr yayi yace" calm down Amma, Drs basu bari a gansa sai ko zuwa gobe, kar ki damu Amma Allah zai basa lafiya, muyi masa addu'a. Zama tayi jiki a sanyaye tana tunanin me ya samesa har ya sami jeart attack..... " Muryan Engr ne ya 'katse ta sanda yake fa'din" Ya kirani ba da jimawa ba, yace yana nemana urgently...... toh isana na tarar da wann al'amari. Bayan mun kaisa asibiti Hajiya ke fa'da mun ga maganar da zaimun...." Amma ta tsaida idonta akansa kana tace" me yake son fa'da maka Nazif.
"Hajiya tace mun wai kan maganar auren Laila ne, wai tunda ta gama idda he wants me to marry her......" Gaban Amma ne yayi mugun fa'duwa da jin zancen wanda ita kanta bata san musabbabin wnn fa'duwan gaba ba. Bata ce komai ba sai kallon Engr da take yi...." Muryansa ne ya 'kara katseta....." Amma I don't know what to do, I'm completely lost. Hannayensa Amma ta ri'ko kana tace" I do understand you Son, this is not easy for you. Ka kwantar da hankalinka mu ci gaba da addu'a Allah shi mana za'bi madi khairi, snn what's important now shine lafiyan Baba Alhaji. Sun jimamsuna tattaunawa da Amma kafin ya mi'ke ya nufi sashensa...


"Kusan kullum sai Engr yaje duba Alhj ma'aruf haka kuma duk sanda yaje toh sai ya ha'du da Laila, Laila kullum burinsa ta da'da shige masa, tun yana avoiding 'dinta har ya soma sakin jiki da ita. Haka Hajiya da Aziza sun sake sosai da Engr. Aziza kuwa burinta bai wuce uwarta ta auri Engr ba itama ta samu ta mallaki Irfaan.
"Amma ma sau kusan uku tana zuwa duba Alhj Ma'aruf, yanda Hajiya Karima take mata kirki harsu Laila da Aziza take jin da'di sosai, ko babu komai ita yafi mata idan Nazif ya auri Laila, gata 'yar aminin babansa gashi kuma ta yaba da hankalinta snn hankalinsu zai zo 'daya tinda dukansu sun ta'ba aure.....


"Yau ta kama birthday 'din nilam, hidima suk kan yi a gidan bayan celebrating da akayi da yamma a farfajiyan gidan, da dare ki'da suka 'kure a parlor sai cashewa suke su Deejah kuwa abun nema ya samu.
"A gajiye ya dawo gidan, da kusan wuni yayi a side, wani construction da company dinsu keyi, kuma shike supervising wajen. Da 'kyar ya gama parking motarsa a farfajiyan gidan drivern Engr ya 'karasa da motar parking lot.
"Jin hayaniya ya gauraye cikin gidan yasa sa jan tsaki a hankali, shifa wnn hayaniyan ya damesa he's not used to it at all. Side 'dinsa ya wuce ya sakar ma kansa shower, yana fitowa ya shirya cikin 'kanan kaya. Fridge ya wuce ya 'dauko farm fresh ya soma sipping, wani irin bacci yake ji, dan gaba 'daya he's exhausted, hayaniyansu ya hana shi ko shiga balle ya sanar wa Amma ya dawo. Koda ya jawo laptop dinsa da niyyan duba mails dinsa ma kasawa yayi, tsaban baccin da yake ji. Ya 'dan kishingida kan gadonsa gamida lumshe ido..... amma me hayaniyan su ya hana sa samun peace. Gajeren tsaki yayi ya jawo pillow ya danne kunnuwansa dashi, still bai daina ji ba. A kasalce ya jawo landline din dake gefen bedside dinsa ya shiga dialing lamabar parlorn gidan....
"Deejah ta saka kayan Miss Pizza sai rawa take suna mata dariya, harta Nadiya ma abun ya bata dariya dukansu sun sata gaba suna dariya, Amir da Aiman kuma sai zagayeta suke suna fa'din we want pizza we want pizza..... Sautin wayan ta jiyo ta cire abunda ta saka a kanta tana dariya ta 'karasa wajen wayan gamida 'dagawa duk a tunaninta Amma ce...." Daga 'daya 'bangaren murya a kasalce taji yace" Can you turn down the music.
"Yi tayi kaman bataji ba tace" Hello.... hello... wanene.....
"Tsaki irfaan ya buga, a hasale ya kuma cewa" What's wrong with you hum? Am trying to get some sleep here... I said turn down your dammn music or I'll come over there and turn it down myself.......
"Har ga Allah da kyar Deejah take fahimtar turancinsa dan kuwa asalin slangs english yake yi..... jin tayi shiru ta kasa fa'din komai yasa yin tsaki gamida ajiye wayan, sarai ya gane voice 'dinta, toh me yarinyar nan take nufi, tana ji yana magana tayi banza dashi. Mi'kewa yayi ya zura slippers dinsa ya nufi sashensu...


"Deejah da sauri ta 'karaso tana fa'din" ya Irfaan yace mu kashe ki'dan, ta 'karasa ta kashe... Nadiya ta taso ta kunna tana fa'din" why kede bakiji da kyau ba, ya Irfaan ma yasan we having some fun here, yanzu dancing competition za'ayi. Gaba 'daya yaran suka ce yesss, Nadiya ta ci gaba da fa'din " nida Amir we're team, Nilam with Aiman.... Nilam ta turo baki tace nidai da Deejah zanyi...
"Nadiya tasha mur tace" this is family dancing competition...... " Nilam ta 'bata fuska tace pls Adda Nadiya ki barta muyi tare, remember this is my day, pls don't ruin it for me.
"Saida nadiya da galla wa Deejah harara kafin tace" Ok lil sis just because you insist, you guys should go first, Amir and Aiman team dinsu daya. I will be the judge.
"Hannun Deejah Nilam ta ri'ko suka fiti tsakiyan parlorn. Nadiya ta 'kirga three kadin suka soma rawan..
" A 'kofa ya tsaya yana kallonsu, hannunsa har'de a 'kirjinsa yake kallonsu. Nadiya ce ta hangosa gani tayi yasha mur sosai, babu alamun wasa a tattare da shi... cikin san'da ta 'karasa ta kashe ki'dan tayi saurin hayewa upstirs..., hakan yasa gaba 'daya suka kalli 'kofa.... "Deejah sosai taji kunya ganinta da yayi tana rawa, Nilam kuwa wajensa ta nufa tana fa'din" ya Irfaan pls kar ka hana mu. Murmushi yayi don yana tsananin son Nilam hadi da tausayinta dan ta tashi babu uwa. Hannayenta ya ri'ke yace" no Angel I didn't say you should turn off the music, I only said you should turn it down. You see Angel, I just came back from work, and I'm terribly exhausted, so I need to get some sleep. Go ahead and enjoy..... murmushi tayi tace I luv you ya Irfaan. Shafa kanta yayi yace and I luv you too angel. Harara ya galla wa Deejah daidai nan Amma ta sau'ko daga stirs...
"Irfaan yaushe ka dawo, shigowa ciki yayi ya gaida Amma kafin yace bai jima da shigowa ba. Amma tace sannu mai gidan, nasan baka saba aikin wuya haka ba, kar ka damu you'll soon get use to it. Irfaan ya 'dan murmusa ba tarda yace komai ba, ya mike yana fa'din barin kwanta Amma. Amma tace abinci fah. Girgiza kai yayi yace na 'koshi Amma,
"Um um Irfaan, I can't allow you to go bed with an empty stomach.... Da sauri ta kalli Deejah dake 'ko'karin tattara parlorn tace" Deejah maza ha'da masa abinci ki kai masa sashensa pls... Gaban Deejah ne yayi mugun fa'duwa jin ita zata kai wa Irfaan abinci...


πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.....
[8/19, 06:25] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye*


🌹14


"Tafi minti biyar tana tsaye 'kofan parlorn Irfaan, tunani take wllhi ya mata rainin hankali ba 'kyalesa zatayi ba, hannu tasa tayi nkckn shiru ba'a amsa ba, ta kuma yi a karo na biyu nan ma shiru, gajeren tsaki tayi ta shiga doka sallama. Shiru babu alamun za'a amsa ta. A fusace ta juya da niyan komawa, ko me ta tuna oho, sai dawowa tayi ta mur'da handle 'din 'kofar nan ta jita bu'de,...
"Tana shiga parlorn sanyi ac ne ya fara ratsa tsoka da 'bargon jikinta. TV ne keta faman aiki tashan Ball da alama yake kallo.... kallo tabi parlorn dashi ya burgeta sosai tsarin parlorn komai white and blue ne, snn ko ina tas tas baka ce 'dan adam na rayuwa a wajen ba sabida yanda wajen yake very need, ga wani 'kamshi dake tashi... kai wnn dagani 'danngayun 'karshene ta fa'di a zuciyanta. Tana ri'ke da tray 'din tana 'kare wa parlorn kallo kwatsam idonta ya sau'ka kan Irfaan can gefen staircase yana "press up" exercise..... " Da mugun mamaki Deejah ke binsa da kallo, lalle wann ya cika 'dan renin hankali, wato ashema yana jinta taketa faman doka sallama da 'kon'kosa 'kofa yayi banza da ita. Tsaki tayi ta nufi kan center table dinsa ta dangwala tray 'din akai. A fusace ta nufi 'kofa zata fita Irfaan yayi wuf yasha gabanta.
"Kallon kallon suka shiga yiwa juna, 'kwarjininsa yasata saurin kauda kai gefe. Fuska a murtu'ke yace" wa kike ma tsaki?
"Galala Deejah ta kallesa kafin ta ta'be baki ta kauda kai gefe tace" wa ka gani a wajen.
"Da mugun mamaki Irfaan ke binta da kallo, lallai ma yarinyar nan akwaita da raini batasan duk gidan nan shine babba ba, snn bataga irin girman da 'kannensa ke basa bane take 'ko'karin rainasa..... " Muryanta ne ya katse sa" ni ka bani hanya na wuce pls, ta fa'di tana ri'ke kunkumi....
"Gajeren murmushi yayi dan abun nata ya soma basa dariya, kafin yace" Idan an'ki fah what can you do hum? Are you going to beat me up or what, ke wai wa ma ya baki izinin shigowa nan in the first place.
"Bakinsa kawai Deejah ke kallo yanda furta kalamai kaman baison yi, daga gani dole yake maganan nan ba don yaso ba. Tayi murmushi a ranta tace aiko ka ha'du da Deejah duk miskilancinka da sannu zaka daina.
"Young Master may I... ta 'karashe tana wani juya ido tana masa nuni da 'kafa da idanunta...
"Nanata sunan yayi a fili "Young Master" murmushi ya kuma yi kafin yace a ransa I'll clear your doubt yarinya, watoma nime young master.... " Matsowa yayi da fuskansa daf nata, Deejah a razane ta shiga matsawa baya har ta isa jikin garu. Irfaan ya kuma Matsowa daf da ita suna iya jiyo sautin fitan numfashin juna...." Deejah ta razana sosai, runtse idanu tayi ta shiga bawa Irfaan ha'kuri....." Sassauta murya yayi yace" mema kikace sunana? " bu'de idanunta tayi ta sau'kesu tsaf kan kyakyawan fuskansa... ta soma girgiza kai tana fa'din" um um na manta wllhi.
"Murtu'ke fuska ya kumayi yace" au bazaki fa'da ba koh, kinsan Allah ko ki fa'da or I'll still a kiss from you..." Ai a zabure ta bu'de idanun baki na 'bari tace" sunanka "Master" dan tasan ka'dan daga aikin wanda ya tashi cikin turawa, yanzu saiya mata kiss a wajensa ba komai bane...
"Irfaan yayi murmushi yace" ba young master ba... Girgiza kai tayi da sauri tace" a'a Master ne.
"Ya kuma yin murmushi yace" good" daga haka ya matsa gefe... da sauri Deejah har tana buge 'kafa jikin flower vase ta wuce... Irfaan yabita da kallo har ta fice, murmushi yayi ya furta Deejah a hankali, sunan mum dinsa kenn. Zama yayi bisa kujera yana tuno yanda take fari da idanunta da 'dan bakinta sunfi komai tafiya dashi a tattare da Deejah. 'Karan da wayansa tayi ne ya dawo dashi daga duniyan tunanin da ya tafi.." wani irin farin ciki yake ji maras misaltuwa, yana daga wayan daga daya 'bangaren aka ce" Dude Nigeria ya 'boyeka.
"Murmushi irfaan yayi yace" Aheedjo ka bari kawai, na dawo na tararr da aiki, daddy yayi employing dina a company dinsu, am always busy wllhi.
"Aheedjo yayi dariya yace" good, kaga yanzu zaka zama committed, daddy ya min daidai, miskilancika zai ragu yanzu. Anyway ya na jika in a good mood duk da nasan baka son Nigeria.
"Irfaan ya kuma yin murmishi yace" is it that obvious.
"Eh mana guy, wllhi kana 'daukan wayan naji muryanka full of joy. Am pretty sure you having a good time there.
"Irfaan ya kuma yin murmushi yana tuno fuskan Deejah yace" kasan no place like home, inajin da'din Nigeria, though akwai wata yarinya da take annoying 'dina.....
"Dariyan da Ahidjo ya kwashe dashi ne yasa Irfaan jan fasali. Ahidjo yaci gaba da fa'din, who is that lucky girl, da har tayi catching attention dinka Irfaan,.....
"Kaga malam enough pls. Ni ba sonta nake ba, on the contrary I found her annoying. Kai kasan am not womanizer, da zan nemi mata da nayi tun a US yanda classic babes suke,. They're always annoying and disgusting.
"Toh guy nide addu'a na Allah nuna min wacce zatayi winning heart dinka Irfaan.
"Gajeren tsaki irfaan yayi yace" lets change the subject Dude. Yanzu nake ganin anyi releasing Prison break season 5 episode 1.
"Eh wllhi, an saka ma jiya a Los Angeles cinema, muna tare da mutanenka su Fabulous.
"Irfaan yayi murmushi yace" am dammn missing you guys and Los Angeles.
"Murmishi Ahidjo yayi yace" wllhi guy ka bari kawai tunda ka tafi Los Angeles ta bar da'di, anyway na kira na fa'da maka zamu dawo Nigeria muma ina a couple of days..." Mikewa Zaune Irfaan yayi yace" like serious.
"Yes dude, am tired of States, nima ina son dawowa country na, besides tunda ka tafi wllhi 'kasar ta zama very bored,.
"This is glad to hear, oh friend you have no idea how happy I'm, at last zan kara kasancewa da aboki na.
"Ahidjo yayi murmushi yace same here friend..... haka dai suka ci gaba da piransu har sukayi sallama....


"Ahidjo Kaita, shi kaidaine abokin Irfaan a rayuwarsa, Ahidjo dan Nigeria ne da suke zama da iyayensa a United States, wani ziwa hutu Niheria dasu irfaan sukayi Nigeria suka hadu dasu Ahidjo a jirgi zasu hutu US su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login