Showing 99001 words to 102000 words out of 159062 words
Chapter 34 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt
"Sadiq na cikin dube duben documents na sababbin contracts da Engr yayi signing wanda za'a yi su kwananan yaga wata takarda na business Ventures da zasuyi da wata compnay a England(Manchester) na shigo da kayan gini na zamani kan billions of Pounds, abin da ya d'aure masa kai shine Sunan wanda ya gani, sunan Safwan ya gani. Girgiza kai ya soma kafin yace " no never I won't allow that jerk, am pretty sure he's capable of destroying this company, bazan bari hakan ta kasance ba, I've bad feelings about him. Tattara takardun yayi ya saka su cikin wani file. Burinsa Engr ya dawo daga Singapore suyi maganan....
"Rabon Safwan da gidan Yakumbo ya mance, yau tana zaune tana k'ulla aya taji sallaman Safwan, k'in amsa masa tayi taci gaba da abunda take. Gajeren tsaki yayi kafin ya k'arasa shigowa ya nemi waje ya zauna. Yakumbo mun sameku lafia? Kaman babu hallita a wajen hakan Yakumbo ta masa, sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yasa hannu a aljihu ya ciro bunch d'in 'yan d'ari biyar wato dubu hamsin ya ajiye a gabanta ya mike yana k'ok'arin tafiya.
"Yakumbo ta goge hawayen da suka zubo mata kafin tace" dawo ka d'auki kud'inka bana so, Safwan ya juyo yana watsa mata mugun kallo kafin yace" wai ke Yakumbo shikenan komai nayi banyi daidai ba, idan wai don bana zuwa ne, kinsan yanayin anguwan naku na talakwa sai ya b'ata mun mota, inafa k'ok'ari...... "Rai b'ace ta mik'e hadi da watsa masa mari maiji da lafiya tana huci tana rik'e k'irjinta tqce " Ka tafi Safwan kar ka sake dubani har na koma ga uban gijina ka gani ko bazan iya sauran rayuwar da ya rage mun ba. Kaje gaka ga duniya ta isheka riga da wando. Ko mai kama da kai na kuma gani a lungun nan sai nayi k'aran ka. Daga haka ta wuce k'uryar d'aki ta barsa nan tsaye.
"Tab'e baki yayi gamida d'aga kafad'u irin ko ajikinsa kafin ya soma tafiya..
"Safwan na fita gidan Hajiya Karime ya wuce dan sanr da ita details na abinda ake ciki.
"Hajiya Karime sai faman washe baki take sanda Safwan ya ciro photocopy na wasu documents ya mik'a mata. Tsuke baki tayi kafin tace" Yo ni me na sani a nan, bayani zakamin dalla dalla.
"Safwan yayi murmushi dan kuwa cutansu Hajiya Karima bazai masa wuya ba, gyara zama yayi kafin ya soma fad'in" Wann takarda da kika gani na k'ulla kasuwanci ne tsakanin Company M&M builders da wata Company a k'asar England, mai Kampanin 'dan Nigeria ne, zasu shigo da kayan ginin da ba'a jima da fito dasu a duniya ba zuwa nan gida Nigeria, toh shine company guda biyu suka had'e. Snn sunana Mr President yayi signing akai, ma'a ni zan wakilci kasuwancin.
"Wann kuma kud'ad'e ne kimanin biliyan d'ari biyu zamu b'atar dasu, da zaran sun b'ace companyn zata sami kariyan arziki wanda a turance ake kira _Bankrupt_ kinga daga nan zasu saka company a kasuwa dole dan bazasu iya ci gaba da running nata ba, daga nan mu kuma sai mu saya kinga companyn ta zama *Mallakin mu*
"Ga mamakin Safwan tsalle yaga Karime ta tashi ta buga harda rawa, kafin tace" amma baka tab'a zuwa mun da zance mai dad'i irinta yau ba, Kai Safwan ka cika d'an halak, Allah dai ya biyaka... "Murmushi Safwan yayi a ransa kuwa cewa yayi _Ai bazaki san ni d'an halak bane sai M&M ta zama mallakina_..
"Laila na kitchen tana had'a abincin mijinta yau zai dawo daga Singapore taji wayanta na ringing duk a zatonta Engr dinta ne ke kira, da murnan ta ta d'auka nan kuma taji akasin haka, Muryar mace taji.
"Daga d'aya b'angaren aka ce" Hajiya Laila uwar munafukai kin yini lafia?..
"Gabanta ne ya fad'i dan kuwa sarai ta gane muryan Yusra. Tsayawa tayi da gauraya miya kafin tace " Me kuma kike nema wajena, thought na gama dake,
"Yussy ta kwashe da dariya kafin tace" kun tura min kud'i amma ba wann bane kawai nike buk'ata.
"Laila taja tsuka kafin tace" Ke k'aramar 'yar iska karki sake kirana babu wani kud'in da zan turi maki.
"Yussy ta kuma fashewa da dariya kafin tace" Kar ki katse kiran dan kuwa katse kiran na daidai da yin gagarumin nadama agareki.Ki gaya wa d'an iskan kwartonki Safwan kar yayi gigin cewa bazai aureni ba,.
"Laila tayi tsuka kafin tace" Yoni ina ruwana idan yace baya sonki, mi nawa a ciki.
"Yussy tayi dariya kafin tace" bazan zauna babu aure ba, kun raba k'awata da wanda take so kun lik'a masa shegiyar 'yarki wacce ba'a sameta ta hanyar aure ba...... "Jikin Laila ya soma b'ari zufa ya soma karyo mata. Cikin in.. ina take fad'in" Eye na'am mi kike cewa.
"Yussy tayi dariya tace" na tabbata kinji abinda nace snn kinsan zan iya tona asirinku, idan kinaso wann sirri naku yaci gaba da rufuwa toh kiyi abinda nace" Ki fad'awa Safwan dole ya aureni snn dole ki daina bibiyan mijina bayan ya aureni. Yunk'urin kasheni na daidai da tonuwar asirinku dan kuwa ina connection da manyan area boys 'yan iskan da suka ci uwarku a iskanci cikin garin nan. Dan haka idan kunne yaji jiki ya tsira.....
"Bata san sanda ludayi ya fad'i daga hannunta ba, tuni cikinta ya soma kukan zawo, lamban Safwan ta shiga bugawa cikin tsananin tashin hankali.....
Queensamy ce ππ½..........
[8/28, 14:13] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
70
*Β©Sameena Aleeyou..........βπ½*
_Queen Samy Novels Forum....ππ_
"Ta kiran wayan Safwan yafi abinda yafi bai d'aga ba, k'irjinta kuwa an runtuma dutse haka take jinsa, shiganta toilet kuwa yafi a k'irga dan tsaban firgici da razana, anya bazata kira su Over suje su gama da Yussy ba, ta had'e ta gumi zaune kan gado har miya ta k'one bata sani ba.
*Lebanon* _(Berute)_.......
"Wani balarabe ne wanda a ak'alla bazai gaza shekaru 60 a duniya ba ke zaune kan wata kujera na alfarma, daga ganin fuskansa zaka gane na cikin tsananin tashin hankali,
"Wani matashin balarabe ne ya shigo gamida rusuna masa kafin ya mik'a masa wasu takardu, cikin harshen larabci suka so a magana, yanda matashin yaci gaba da fad'in" Abbu wad'an nan sune takardun da mukayi bincike akai, *Khadeejah* a United States Los Angeles ta zauna shekarun baya tun bayan barinta Lebanon, tayi aure snn har ta haifi yara, mutumin data aura d'an Africa ne.... "Dattijon ya mik'e da murnan sa harda hawaye ya rungume matashin kafin yace" _Shukran As'ad shukhran laka,_ na gode As'ad, yanzu zanga tilon 'yata zan ganta harda 'ya'yanta..... "Hawayen da ya gani suna bin fuskan As'ad ya tabbatar masa akwai matsala, cikeda damuwa yake tambayan As'ad meke faruwa.
"As'ad ya share hawayen da suka zubo masa kafin yace" _Abbu lak'ad mata Khadeeja_ "Abbu Khadeejah ta rasu....
"Sulewa Abbu ya tashiyi a k'asa sabida tsananin tashin hankalin da ya shiga, kallon As'ad yake kafin yace" ka fad'a mun gaskiya As'ad..... kuka ya kubcewa dattijo Abbu, Rungume hoton ta yayi tun tana yarinya kaman zai maida hoton cikinsa yana fad'in Ya _sageeraty ya Bintee ya habibty_... Sunbatu ya rink'ayi yana fad'in" _La'kad zalama nafsee_ na zalunci kaina zalunci mafi muni, na zalunceki keda mahaifiyarki Khadeejaty, gashi kema kinbi hanyar databi... "Dago kai yayi yana kallon As'ad kafin yace "Ina suka koma ina zan samu jikokina na gansu.
"As'ad cike da tausayawa yace" A yanda nayi binkice mutumin Africa ta aura sai dai bansan wacce k'asa bace a Africa kuma bayan mutuwanta ya tattari 'ya'yansa sun koma can k'asarsu...
"Abbu ya share hawayen idanunsa yana shafa hoton da hannunsa yake fad'in" As'ad idan ta kama ka zagaya k'asashen Africa dan nemo zuri'an da d'iyata ta bari inaso kayi shi, inaso a samomun 'ya'yanta don a yanzu su kad'aine farin ciki na.
"As'ad ya gyada kai cike da rusunawa yace " An gama Abbu, Intercom ya ciro a aljihunsa yace ma guard su fara processing visa na k'asashen Africa one by one... (Ni kuwa Samy nace kaga masuyi da gaske, idan bakayi bani waje π).....
*Nigeria* _(Abuja)_
"Cikeda tashin hankali ta kuma dialing lamban Safwan, jin ya d'aga yasata sauk'e ajiyan zuciya, kan yayi magana ta soma fad'in" Safwan lafiyanka kuwa...
"Cikin ko in kula yace" ban gane ba meke faruwa, Laila ta kwararo masa duk bayanin da Yussy ta mata.
"Safwan ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace" wann yarinya akwai shu'uma dukda na bata kud'i sama da one million bazai kashe bakinta ba.
"Laila ta goge zufan da ya keto mata dukda sanyin AC dake ratsa d'akin tace" Nidai Safwan kawai ka amince ka aureta kar ta tarwatsa mana jin dad'in rayuwar da muke ciki.
"Safwan ya fuzar da iska kafin yace" Let me handle this, zan sameta, karma kisa ma ranki damuwa, duniya yanzu muka soma cinta da tsinke.
"Laila dai har lokacin a razane take, da k'yar ta iya furta toh shikenan sai naji feedback daga gareka, barin tashi na shirya My Engr na hanya...
"Kwalliya Laila tayi sosai cikin wani tsadadden leshi wanda a ido kawai kasan yaji kud'i, duk wann kwalliya datayi ogan nata baice tayi kyau ba, wann abu na damun Laila yanda koda wasa Engr bai tab'a furta mata kalman so ba, ita kam ta lura kaman mata basu gabansa. (NI kuwa Samy nace kece dai Laila baki sani ba, Zuciyan Engr ba *Mallakin ki bane Mallakin Fateemah ce*).
"Washe garin dawowan Engr daga Singapore Sadiq ya tattaro documents d'in yazo har gida dan su gana. Kaman daga sama ya hango Nadee tsaye wajen Ostrich tana basu abinci, murmushi yayi a ranshi yake raya yanda Nadiya ke son jimina, a hankali ya k'arasa yanda take.
"Zuciyarta ne ya raya mata Sadiq na wajen, da sauri ta juyo nan kuwa zarginta ya tabbata, ido hud'u sukayi da juna, da sauri ta had'e rai zata tafi yayi saurin shan gabanta yana binta da kallon k'auna yake furta" Kar ki tafi ki bar zuciyan data aminya da k'aunarki, Nadee laifi me na maki kike punishing d'ina the most hardful way, ware hannayensa yayi ganin bazata masa magana ba yasa sa cewa "Alright fine idan so kike na durk'usa kan gwiwoyina na baki hak'uri na fad'a maki ina tsananin k'aunarki fine sai nayi.... "Ni bance ka durk'usa mi....... Kan tayi shiru ta gansa gwiwoyinsa k'asa yana fad'in" Nadiya Nazif Mumtaz I love you since from tje very time I set my eyes on you, pls accept my proposal.
"Hannu tasa tana rufe bakinta fuskanta full of surprise bata tab'a zaton watarana namijin da take so zai mata haka ba, da sauri ta soma fad'in "big bro pls ka tashi, pls... "Murmushi Sadiq yayi kafin yace" No Princess bazan tashi ba sai kin amsa min you love me...... "Fitowan Engr daga sashensa ne yasa Sadiq mik'ewa cike da kunya, Nadiya ma kunyar taji.
"Engr dayagama ganin komai babu wanda yakaisa farin ciki, kasancewar Sadiq surkinsa hakan ba k'aramin dad'i zai masa ba.
"Sadiq yayi saurin k'arasawa yanda Engr yake... "A'a Sadiq ka iso, cewan Engr. Rusunawa Sadiq yayi kafin yace " Eh daddy, Nadiya ta k'araso sai faman sunne kai take tana twisting 'yan yastun hannunta tace" Daddy sannu da fitowa, da murmushi Engr ya shafi kanta yace" Yauwa sweetheart, maza kice ma Ammah na fita, na shiga na samu tana sallah, gyad'a kanta tayi cikeda ladabi tace"A dawo lafia daddy.
"Daddy dama kan maganar wad'ancan documents d'inne, Engr ya dubi agogon hannu sa kafin ya d'ago ya dubi Sadiq yace" Accountant ka rik'e takardun a hannunka kawai, inada meeting yanzu da FCT minister, idan yaso zan nemeka sai muyi maganar. Sadiq ya gyada kai cike da rusunawa yace okay daddy barin dubo Cimon din, kai tsaye Sadiq ya wuce kiran Cimon ya fito da mota....
"Safwan ya dubi yussy yace " Haba Yusra ina kike tunanin zan kwasheki na kaiki, ko mun auri juna hankalinmu bazai tab'a kwanciya da juna ba, sabida kowa zai ringa tunanin d'an uwansa yana ha'intarsa, dama kin nemi wanine kika aura, ni kuma na maki alk'awarin komai na bikin zanyi, kama daga kayan d'aki zuwa shagulgulan biki.
"Taunar cwingum dinta taci gaba da yi kafin ta tuntsure da dariya, galala ta kalli Safwan kafin tace" Waye ya soma sakani a wann hanyar idan ba kai ba, ai babu wanda ya dace na aura sai kai, fasik'i ai sai fasik'a, bama wann ba, wa kake tunanin zai aureni a garin nan, kaima kasan bazan samu mijin aure ba bayan kai, tunda tare muka fara sai mu k'arasa ko yaya kace patner.
"Fuzar da iskan bakinsa yayi gamida cire hulan kansa kafin yace" Wai ma yaya akayi kikasan sirrina ne Yusra.
"Dariya tayi harda shewa kafin tace" ashe ba bariki kakeyi dani ba, a wallet dinta naga DNA test da aka maka da Azeeza tun tana 'yar shekara biyu. Kai Safwan wllhi rufin asirinka kenan ka aurni ko kuga b'aranbarama.
"Zata bud'e marfin mota yayi saurin rik'o hannunta yace" Shikenan naji zan nemeki duk abinda ake ciki, but pls don't exposed my little secret kinji.
"Murmushi Yussy tayi tana kanne ido kafin tace karka damu your secret is safe with me, sai najika. Hura masa iska tayi a fuska kafin ta fice.
"Safwan ya dake starryn mota yana furta" Ohh shitss, yanzu yaya zanyi da wann jarabebbiyar yarinyar. Kasa nemo solution da yayi yasa sa kunna mota ya soma tafiya.
***********************************
"Kullum Ahidjo sai yaje Caf ya samesu, Deejah kuwa tana ganinsa take tafiya, a yau Ahidjo yayi abinda ya bata mamaki wanda har take tunanin k'ila da gaske ya canza, wasu mazane suka tasamma cin zarafin wata yarinya, Ahidjo ya masu dukan tsiya yayi saving yarinyar.
"Wann dalili yasa yau ta d'an sauraresa.
"Deejah wllhi zanyi komai idan zaki soni, ya fadi fuska cike da damuwa... "girgiza kai tayi kafin tace" No ni babu shirin soyayya yanzu a rayuwata.
"Ahidjo ya kuma yin fuskar tausayi kafin yace" idan akan Irfan ne, *Mallakin wata* ne a yanzu, shi yanacan yayi aurensa yanajin dad'insa da matarsa, ya barki a nan har yanzu kina dakon soyayyarsa.
"Har ranta taji zadin kiran Irfan *Mallakin wata* da yayi, a fili murmushi tayi kafin tace" Irfan bashi yak'ini ba hasalima ni nak'isa, mikewa tayi ta dau jakarta kafin tace" ban shirya yin wata magana ayanzu ba.... "Kaman daga sama ta tsinkayo muryar Ahidjo yana fad'in" Deejah idan kikaji na mutu to babu shakka kece sanadi, da sauri ta juyo tana dubansa, kan tayi magana sai gani tayi ya suri car keys dinsa yana gohe hawayen fuskarsa yace" Na tafi, zan tafi na kashe kaina sabida soyayyarki..... "Da sauri ta shiga kiran sunan sa inaa bai tsaya ba kai tsaye mota ya shige ya fita aguje.....
"Dafe kanta tayi tana salati... "Oh ni Deejah shikenan ban iya komai ba sai hurting mutane, what if ya kashe kansa, runtse idanunta tayi hawaye masu zafi suna zubo mata, wann wani irin jarabawa take fuskanta a rayuwa... Take zuciyarta ta soma jero mata addu'o'i.....
*Katsina* _Daura_....
"Malam ya gama jero duk addu'o'in da zaiyi, ya mikz'awa Hajja Umma ruwan maganin na addu'o'i yace insha Allahu wann idan an shafe mata fuskarta dashi shikenan, ayoyin Alqura'ani ne na karya sihiri da duk wani asiri, duk randa tayi ido hud'u da wanda ta sani la shakka hankalinta zai dawo....
"Hajja tayi godiya sosai wa malam ta karb'i maganin hannu bibbiyi.....
"Kwana biyu da faruwan wann al'amari Hajja Umma ta sahwarci Mamie kan a koma da Dada gida wala'allah watarana zatayi tozali da wanda ta sani..... Hakan kuwa akayi, Mamie da Sadiq harma da Ruqayya sukazo tafiya da Dada, yanda Hajja Umma ta tada hankali saidai a saka auren Ruqayya da Sadiq, tunda mahaifan Ruqayya suka rasu ta d'au alwashin had'asu aure da Sadiq.
"Da k'yar Sadiq ya shawo kan Hajja Umma kan idan yayi magana da uban gidansa sai a saka ranan. Da wann zance Hajja Umma ta hak'ura.
Queensamy ceππ½
[8/28, 14:13] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
71
*Β©Sameena Aleeyou.....βπ½*
_Queen Samy Novels Forum......ππ_
*National Hospital Abuja*......
"Ammi hankali a tashe ta kuma neman layin Dad din Ahidjo har lokacin idonta na kafe kan Ahidjo wanda yaji ciwo sosai sakamakon hatsarin mota da ya tapka.
"Secretary din Dad ne ya d'au wayan dan lokacin Dad na cikin meeting, Cike da masifa Ammi take fad'in" If don't want your self to get fired ka bashi waya muyi magana, banza sha sha kawai. "Cike da rusunawa secretary din ya soma bawa Ammi hak'uri, dan yasan Ammi idan ta fad'i magana toh fa ta zauna, dan Senator ba k'aramin tsoronta yake ba.
"Hankalin Dad a tashe ya bar meeting d'in ya nufo asibiti..... tun daga nesa da ya hango Ahidjo hankalinsa ya tashi, Jamila what happened to Champ me ya samesa.
"Ammi rai a murtuk'e tace yo ni