Showing 84001 words to 87000 words out of 159062 words

Chapter 29 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10381

suna ki rasa wani daraja da kima gwara ki rasa farin cikinki na wani lokaci, dan kuwa Allah yaga zuciyarki yana tare da mai gaskiya..... "Zubewa tayi kan gwiwoyinta tana kuka me tsuma rai, karar shigowan mssge taji a wayarta, tayi saurin dubawa.


_"Ashede kina son Irfan, dan kuwa da kinyi gangancin aurensa a yau, da kin zama tarihi mafi muni a rayuwar irfan, weldon habibty, you did a great job, yours Safwan_
"Tana gama karantawa wani sabon kuka ya b'alle mata, jifa tayi da wayar ta tarwatse bisa tiles. Mugun tsanar Safwan wanda bata tab'a jin irinsa ba yana dada mamaye b'argo da tsokanta.....




"Suna isa d'akin Sadiq Irfan ya wuce ya kwanta, tuni Mamie ta had'a masa ganyen shayi maganin zazzab'i dukda ba wani sha yayi ba, sosai Mamie ta tausaya wa Deejah da Irfan, ta rasa dalili amma can k'asar zuciyanta tanaji akwai wata mak'ark'ashiya, ta d'au alwashin tayasu da addu'a.
"Dan Ruqayya ta bata labarin duk kapan abinda ya faru sanda ta dawo gida, da shike itama Ruqayyan bata jima da shigowa ba.

*Around 5:30pm*
"Sanda Sadiq ya shigo d'akin ya tarar Irfan na bacci, a hankali ya fice ganin call din Nadiya.
"Hello lil sis
"Hello big bro, ya yaIrfan I know he must be having a hard time, we were all worried about him here.
"Sauk'e ajiyan zuciya Sadiq yayi kafin yace" kar ku damu ki fad'awa su Ammah karsu damu Irfan na gidan Mamie, right now ya sami bacci, .., ya d'anja fasali kafin yace" So what's goin on there, how's Deejah?
"Sauk'e ajiyan zuciya Nadiya tayi kafin tace" Deejah ta kulle kanta a d'aki, ta k'i bud'ewa kowa, annnndddd.... sai kuma tayi shiru.
"Cike da firgici Sadiq yace and what???
*" Sauke ajiyan zuciya tayi kafin tace" no nothing, I know Ya Irfan is in good hands zaku kula dashi kaida Mamie, barin fadawa Ammah da Daddy so that they shouldn't worry. Daga haka tayi hanging. Ta bar Sadiq da waya a kunne yana tunanin akwai abinda Nadiya ke b'oye masa.




******************************************




*UNITED KINGDOM*

*England*


_Manchester_


* Garin Manchester babban birni ne a k'asar Englan wanda kusan ko yaushe sanyi ake masu, k'ank'ara ne ke sauka akasarin watanninsu.


"Wani mutumi na gani wanda ak'alla bazai wuce shekaru 52 a duniya ba, da ganinsa dan Nigeria, yana sanye cikin kayan sanyi, jin dadi zai nuna maka mutumin kaman bai kai yawan shekarunsa ba, yana zaune a wani tapkeken parlor wanda yaji furniture na alfarma, wani hoto ya k'ura ma ido, take ya shiga aikin kuka wanda ya zame masa jiki,
"Wata matace ta fito daga wani lobby, tana sanye da kayan turawa amma gashinta a rufe, ita din tafi kama da mutanen Nigeria, akalla bazata wuce shekaru 27 zuwa da 29 ba, sosai abin yake tab'ata ganin mijinta cikin k'unci, k'arasawa tayi ta karb'i hoton hanunsa, tasa hannu ta share masa hawayensa kafin tace" Haba daddyn Afnan dan Allah ka ringa rage ma kanka wann bak'in cikin. Ta fadi fuska cike da damuwa.
"Hannu yasa ya goge hawayen fuskarsa kafin yace " Bilkisu, I can't help it, bazan tab'a daina tunanin Fateemah ba, na cuceta na cuceta cutan da Allah bazai tab'a yafe mun ba, Kar ki mance nasha fad'a miki, Fateemah tana d'auke da juna biyu na haukatar da ita ta shiga duniya duk akan kud'i, tanada wanda take so aka tilasta mata aurena, na salwantar da rayuwarta da rayuwar abinda ke cikinta, shin kina ganin Allah zai yafe mun wnn babban kuskure da na tafka, wayasani ko ta haife abinda ke cikinta ko bata haife ba, ko tana raye ko ta mutu, duk a sabida abin duniya nayi, gashi a yanzu Allah ya jarabce ni na sami a bin duniya, ina daya daga cikin billoniers amma har yau na kasa jin dadin kudin na kasa samun farin ciki, tunanin Fateemah da abimda ke cikinta ya kasa barina na samu sukuni, Bilkisu banajin zan iya komawa Nigeria, shiyasa a kullum nike baki hak'uri, bazan iya zuwa Niheria ba, ko gawata ce nafi so a binne ni a nan idan naje can Allah ya saka ma Fateemah da abinda ke cikinta... daga haka ya kuma sunkuyawa yana kuka.
"Sosai abun yake damun bilkisu wann shine aikin mijinta, bashida aikin dayafi na kuka da tunanin tsohuwar matarsa da jaririn cikinta, suna a haka yaransu emmata guda biyu suka shigo, Afnan da Aila, suma din sun saba ganin mahaifinsu a haka duka da k'arancin shekarunsu, abin sosai yake damunsu.
"Wann shine Rayuwar gidan Alhj. Musa Abdullah.




*******************************


*Nigeria*
_Abuja_


"Da sassafe ta bud'e k'ofar d'akin ta shiga jawo akwatinta, kana ganin fuskanta zai tabbatar maka bata sami bacci ba sai aikin kuka, a hankali take jan kayan har ta iso k'ofar parlorn.......




QueenSamy ce.
[8/28, 14:10] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


62


*Β©Sameena Aleeyou*


_Queen Samy Novels Forum.....πŸ“–πŸ“š_




"Suna zaune gaba d'aya a dinning yayinda da yawa daga cikinsu ba cin abincin suke ba sai faman juya spoon cikin plate, k'aran footsteps d'inta ne ya sanyasu d'ago ido suna duban wajen.
"Har lokacin hawaye take tana taku a hankali, wani kallon kyama Laila take binta dashi har ta k'araso wajen. Da gudu Nilam ta tafi ta rungumeta tana fad'in" Aunty Dee meyasa kika kulle kanki a d'aki wai da gaske baki son ya Irfan, and why are you with your stuffs are going somewhere?
...." Kasa cewa tayi sai rungume Nilam da tayi tana hawaye. Da kyar ta iya k'arasowa wajen, ta kasa d'ago ido ta kalli kowa cikinsu, tsugunawa tayi idanunta suna kallon k'asa cikin muryan kuka take fad'in"
"Ban cancanci yafiyarku ba, kunmin sutura na yaye maku, kun saka a inuwa na jefaku rana, kun mun gata na tozarta ku,.... hawaye d'aya na bin d'aya suke fita daga idanun Deejah, had'e hannayenta biyu tayi kafin taci gaba da fad'in "Ammah ku yafe mun, dan Allah ku yafe mun hak'ik'a kun cika mutane na k'warai wanda suka san kima da daraja na d'an adam, maciya amana irina bata cancanci zama da mutane irinku ba, you shown me nothing but luv. Abubuwan da kuka min na alkhairi ubangiji ya biyaku da mafificiyar alkhairi,..... "Mikewarta keda wuya tajiyo muryan Laila tana fad'in"
"Umhum, ai kema dai kya fad'a, abinda kikayi wa Irfan Allah ne kawai zai saka masa.... "Deejah bata iya jure sauraren kalaman Laila ba, ta fice da sauri tana ci gaba da kuka me tsuma rai, a guje Nilam Amir da Ayman suka bi bayanta, rik'e trolley d'inta suka shiga yi Nilam na kuka su Amir na faman rok'on Deejah kar ta tafi...
"Tsugunawa tayi ta rungumesu duka uku, da kyar ta iya saita kanta ta soma fad'in" Sweethearts I really have to go, I can't stay here anymore, guys you know I love, and I will surely miss you.....
"Girgiza kai Nilam keyi cikin muryan kuka take fad'in" must you really have to leave, com'on Dee we love you here, pls don't leave us, idan kika tafi waye zai rik'a mana lesson, waye zamu ringa wasan blindfold dashi. Pls don't leave us. Suka had'a baki wajen fad'in haka,
"Share hawayen idonta tayi sanda ta tuna farkon zuwanta gidan a matsayin nannay, tun yaran basu sonta har suka soma sonta gashi yau zata rabu dasu.
"Hannayensu ta rik'e duka, ta k'ak'aro murmushin k'arfin hali ta d'aura saman fuskanta kana tace" Ayman Amir promise me you'll take care of your lil sis kunji yarana, kasa cewa komai sukayi sai kuka da sukeyi.
"Mik'ewa tayi tana share kwalla ta dubesu duka tace" behave my kids, I love you... daga haka tasa kai ta soma sauri dan ysakanin main house da first gate akwai dan tafiya sosai.
"Tana fita ta juyo tana k'are ma gidan kallo abubuwa da dama suka shiga dawo mata, sashen Irfan tabi da kallo daga yanda take tsaye tana hango Window din bedroom dinsa, goge hawayen idonta tayi kafin zuciyarta ya soma bata kwarin gwiwa "You can do this Deejah"


"Kuka sosai su Nilam keyi, rarrashin duniyan nan Laila da Ammah sunyi amma sunk'i yin shiru. Nadiya da takaici ya dameta tsawa ta daka masu" You Kids should shut that your trap, let her go where ever she wants, she doesn't love any of you, she don't care about you and yet kun bud'e ugly mouths d'inku kuna mana kuka, let me hear you crying again, wllhi sai na zane yaro,... daga haka ta mik'e ta nufi stairs tana cusa earpiece a kunnenta...

"Ammah kam mik'ewa tayi ta nufi sashen ma'aikata dan ganawa da Hajja.


"Laila ce ta jawosu tana rarrashinsu, "Com'on kids, let her be, tace bazata iya zama damu ba, bazata iya auren yayanku ba, ku kyaleta tayi tafiyarta, besides you have your love ones here with you, we all love you here....." Nilam ce ta fizge jikinta tana kuka sosai take fad'in" No I don't love you, ni Deeee nake so, she's second mum, taci gaba da kuka tana ambato Engr. Dadddddy,... daddy....daddy!!!




"Ahidjo ne ya gama parking a kofar gidansu Sadiq, da sallama ya shiga, Mamie na zaune a parlor ta amsa masa da sakin fuska, sosai suka gaisa da Mamie kafin ya tambayi su Sadiq, " Mamie tace Sadiq dai ya tafi Office Irfan kuma yana can d'akin Sadiq maza ka duba sa. Cikeda rusunawa kaman mutumin arziki Ahidjo ya amsa gamida mikewa ya nufi d'akin Sadiq.


"Saida Ahidjo ya razana da ganin Irfan, kaikace yafi wata yana jinya ramar kwana d'aya. Can k'asan zuciyarsa ya d'anji tausayin irfan, a hankali ya k'arasa gamida dafa kafd'unsa yace" guy how you feeling.
"Irfan ya dago yana dubansa ba tareda yace komai ba.
"Sauke ajiyan zuciya Ahidjo yayi kafin ya zauna gefen Irfan sunfi minti uku a haka, sanin kansa ne ko zasu kwana a haka Irfan bazaice masa komai ba.
"Ahidjo yayi gyaran murya kafin ya soma fad'in" Bro kayi hak'uri ita rayuwa ta gaji haka, ba komai bane da kake so zaka samu, kayi imani da k'addara alkhairinsa da sharrinsa, Allah yana tare da masu hak'uri, what you are goin through isn't easy na sani, I feel bad Irfan, you are my friend and also my bro duk abinda ya sameka tamkar ni ya sama, kayi hak'uri Irfan......" "Daga masa hannu yayi alamun yayi shiru, dan kuwa baisan dalili ba amma kalaman Ahidjo tamkar wuta yakeji ana k'ara zuba masa.
"Mik'ewa yayi daga darduman da yake zaune akai yace" ina su Ashraf?
"Ahidjo yace" sun tafi, flight din safe sukabi, munyita k'ok'arin contacting wayoyinku kaida Sadiq basu shiga, so sai sukace kawai I should tell you sun wuce.
"Gyad'a kansa kawai yayi kafin yasakai ya fice daga d'akin.... "Ahidjo yabisa da kallo gamida tab'e baki.


"Sallama yayi wa Mamie snn ya fito ya nufi wajen motar sa. Ahidjo ne ya k'araso kana yace " let me drive you Irfan. "Girgiza kai kawai yayi kafin yace" don't mind zan iya. Daga haka ya shige cikin motarsa ya bar Ahidjo nan tsaye.
"Kallo Ahidjo yabi motar dashi har ya b'ace masa kafin yace" Tooh fahh miskilanci sai abinda ya k'aru kenan. Murmushin mugunta yayi kafin ya shige cikin motarsa yabi bayan Irfan.....






"Kai tsaye gida ya wuce, yana gama parking ya fito, sashen Ammah yabi da kallo kaman zai shiga sai kuma ya fasa ya wuce nasa sashen ya maida k'ofa ya kulle....
"Gaba d'aya basusan ya dawo ba har saida Ahidjo ya shiga ya sanar ma Ammah, Ammah godiya ta ringa yima Ahidjo tana fad'in" Sannu Ahidjo sannunku da k'ok'ari kaida Sadiq babu abinda zamuce maku sai Allah ya saka maku da alkhairi kuda family dinku, Ahidjo yana rusunawa yake fad'in ai babu komai Ammah muda Irfan ai mun zama d'aya we will always be there for him insha Allah.....


"Tana isowa k'ofan gate d'in orphanage taji wani sabon hawaye, jiki a mace ta k'arasa shiga.. su delu ana bakin pampo tana shigowa suka kwashe da dariya harda rangad'a gud'a suna tafe hannu. Wani zafi taji zuciyarta na mata sanda tajiyo habaicin dasuke jifarta dashi.


"Kwanan biyu yana d'aki ko lek'owa beyi ba banda coffee da tea baya shan komai, kullum yana cikin Design room dinsa yana zane ko yana kallon hoton mummynsa aikin kenan harta wayoyinsa ma kashesu yayi. Ranar kwana na uku Engr yayi da gaske yasa sa bud'e k'ofa, fuskan Engr babu walwala yace dashi yana son ganinsa a parlorn sa, ko kulawa ya lallashe shi baiyi ba ya juya, duk da ganin irin raman da yayi.


"Misalin k'arfe 8:00pm Engr Nazif Mumtaz zaune a parlorn sa, gefensa Lailace ke zaune, can d'aya kujeran Ammah ce ke zaune, "Can k'asan mak'oshinsa yayi sallaman kafin ya shigo yana sanye cikin red shir mai guntun hannu da dark blue din wandon jeans, fuskarsa babu yabo babu fallasa, k'arara kake iya ganin raman da yayi. Gefen k'afan Engr ya zauna Ammah ta bisa da kallon mamaki dan kuwa ya aske gashin kansa saura kad'an yayi lowcut sai ya fito tamkar bature askin tayi masa kyau sosai gamida d'an raman da yayi.
"Cikin muryasa me dad'in saurare ya gaida su, Engr ya dubesa da kyau kana yace" Irfan nasan halin da kake ciki, na sani you're having a hard time, but that doesn't mean you can quit your relationship with your parents, ko meye ya sameka you need to be strong, kai na miji ne Irfan soon zaka uba kaima kayi naka family din, but har yaushe zaka bari tunanin mace ya maidaka haka son, baka zuwa office, baka fitowa, ka yanke alak'arka da kowa, muma nan da ka gani abin ya tab'a mana zuciya ya shafe mu ma, amma babu yanda muka iya da k'addaran ubangiji. Irfan kai musulmi ne, kuma yanadaga cikin cikan imanin mutun musulmi yayi imani da k'addara alkhairinsa da sharrinsa, I supposed you know that, Son pls kar ka bari shedan yayi leading naka to a wrong path. Kayi hak'uri innallah ma'assabirin.


"Sosai kalaman Engr suka tab'a ran Irfan, take yaji jikinsa yayi weak sosai, a hankali ya soma fad'in" Daddy nasan ban kyauta ba, kuyi hak'uri pls ku yafe mun, insha Allah bazan sake abu makamancin haka ba.
"Laila na murmushin makirci take fad'in" haba Son, what you're going through isn't easy, we understand you,.. "Ammah ta matso kusa dashi gamida rik'e hannayensa tace " We all love you prince, murmushi yayi gamida kwantar da fuskansa kan hannayen Ammah yace " thank you world best grandma.


"Muryan Engr ya dawo da hankulansu yanda yake fad'in" Irfan akwai abinda yayi saura da ban fad'a maka ba, bansan yaya zaka d'auka al'amarin ba, but I've already made my decision as your father, bansan ko inada wann matsayin a gareka ba, though na sani kai yaro ne mai biyayya ever since you were a kid...
"Dago kai Irfan yayi yana kallon Engr yayinda ya samu kansa da mummunar fad'uwan gaba, da kyar ya iya furta, daddy mene decision dinka da har kake tunanin sanar dani, daddy you're my father you have every right a kaina. I would continue being that obedient child, insha Allah , what was it dad....


"Kaman a mafarki ya jiyo muryan Engr yana fad'in" Irfan na aura maka Azeeza a ranar da Deejah ta fasa aurenka, yanzu haka kai mijin Azeeza ne tana can gidanka Aso Drive ta tare, ka shirya ka koma gidanka da fatan kaima zaka min biyayya kaman yanda ta mun........." Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" kalman da yaji bakinsa na kan nanata masa kenan, meke shirin faruwa dashi, shin daddy yasan consequences din dazasu biyo baya, tunani ma ya soma wacece *Azeeza* zuciyarsa ta shiga basa amsa, itace dai wnn yarinyar da kafi tsana a duniya, kai shi kwata kwata zai iya k'irga iya maganan da ya tab'a had'asa da ita, she's worse than anything ya tsaneta like hell, and yet ta zama matar shi, kai no this can't be possible he must get rid of her, he can't stand been her husband. Shi a halin yanzu yama tsane duk wata mace balle wata wai Azeeza. Wani sabon tsanar Deejah yake ji a b'angare guda na zuciyarsa, duk ita ta jefasa a wnn fitina, dama baisanta ba a iya rayuwarsa, da duk haka bata faru ba....
"Daya bayan d'aya yabi mutanen parlorn da kallo, Laila dai kasa kallonsa tayi sai lugude da k'irjinta keyi, tasan baza'a kwashe da Irfan lafiya ba... to her greatest surprised, kai dukansu uku ma sunji mamakin reaction din irfan, kallon Engr yayi yana murmushin yak'e wanda hausawa kan cema kafi kuka ciwo yace" Toh daddy Allah yasa hakan shine alkhairi, daga haka ya mik'e yasa kai ya fice, ko minti guda bai k'araba. Gaba d'aya suka bisa da kallo, cikin sauri Ammah ta mik'e tabi bayansa dan tasan kawai dai sabida ganin girman mahaifinsa ya amince amma ba har ransa bane, snn tasan Irfan idan baiso abu ba toh komai na iya faruwa, ba abun mamaki bane su shafa suji ya bar k'asan, wnn kadanne ga aikin Irfan dan haka da sauri tabi bayansa. Dan dama ita ko kad'an bataso wnn had'i da akayi ba.


"Kallon Ammah yayi sanda ya jiyo shigowarta yana tsaye a lobby abubuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login