Showing 3001 words to 6000 words out of 159062 words

Chapter 2 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10404

dan haka ya mallaka masa kampanin mahaifinsa.
"Laila ta gyara zama tace" Hajiya ban fahimci zancen ki ba, wai Alhajin ne ya mallaka ma wani M&M, kan wani dalili.
"Kan dalilin ubansa ne ya masa komai harta shears dinsa ubansa ne ya saya masa,......" Wai hajiya na tambayeki dama M&M *Mallakin waye*
"Tsaki Hajiya Karima tayi kafin tace" a iya sanina mallakin Alhj Mumtaz ne, amintaka dake tsakaninsu da Alhaji ya mallaka masa babban shear a company n da farko sunan companyn Mumtaz Builders 'karshe har ya maida sunan kampanin ta koma M&M Builders wato Ma'aruf and Mumtaz Builders.
"Laila ta sau'ke ajiyan zuciya tace " tab'dijam toh shi wann 'dan nasa me ya dawo yi yanzu Nigeria. Hajiya tace matarsa ta mutu mana, shida uwarsa sun tarkaso sun dawo, dama uwar nasa tun mutuwan mijinta wato ubansa ta koma can American wajen 'danta, sai yanzu ne zai tuna da kampanin ubansa, bayan Alhaji ya gama masa shan wuya, saida company ta ginu, tayi 'kaurin suna a nahiyar Africa baki 'daya, duk yammacin Africa babu kampanin da take shigo da ingantattun kayan gine gine irin M&M Builders, sai yanzu ne zai dawo ya mallaki kampaninsa.
"Laila ta girgiza kai ta furta bazai saku ba Hajiya, M&M *Mallakin mu ne*......
"Dariya Hajiya Karima tayi tace" haba ai duk wanda yasha tuwo da Karime tofah miya ya sha, na jima ina harin wnn Company ta zama mallakinmu nida ke da kuma 'diyarki Aziza. Wnn dalili ne yasa na salwantar da rayuwar Hindatu matar Ma'aruf ta farko, snn na salwantar da rayuwar tilon 'yarsa da jikansa......." Da mugun mamaki Laila kebin hajiya Karima da kallo kafin tace "tilon 'yarsa?? Me Hajiya take nufi?
"Ganin Hajiya ba a hayyacinta take zantuttukan nan ba yasa Laila mi'kewa tsaye tana fa'din Hajiya me kike cewa tilon 'yar Alhaji, kinaso kice ni ba 'yarsa bace ko me? Kinaso kice yaya Faty ce kawai 'diyarsa?..... " Sai snn Hajiya Karima tayi realizing me take cewa, da sauri ta ri'ko hannun Laila tana son zaunar da ita...." Girgiza kai Laila ta soma tana fa'din wllhi sai kin fa'da min komai waye uba na?
"Hajiya Karima ido a 'ke'kashe tace" banso kisan wnn 'boyeyyen sirri yanzu bam amma Allah ya 'kaddari yanzu zaki sani.
"Laila, Alhj Ma'aruf da Alhj Mumtaz sun kasance aminan juna, Alhj Mumtaz ya kasance hamsha'kin 'dan kasuwa wanda tun yana da 'kuruciya Allah ya albarkaci kasuwancinsa, toh a dalilin amintarsu da Alhj ma'aruf yasa shi jawosa cikin kasuwancin, wanda bayan ya bu'de kampaninsa me suna Mumtaz builders daga baya ya maida sunan Companyn M&M Builders wato Mumtaz & Ma'aruf knn, ni kwa na kasance ina zuwa aikatau gidan Alhj Ma'aruf, a lokacin ina 'yar matashiyan budurwa, ita kuwa Hajiya Hindatu ta girme mun sosai babu ma ha'di, sun jima da aure itada mijinta Allah bai basu haihuwa ba, kullum suna sha'awan 'ya'ya musamman idan suka ga 'dan Alhj Mumtaz da Nazif matarsa Hajiya Salma, kullum cikin addu'an Allah ya basu haihuwa suke amma shiru babu haihuwa.
"Watarana Hindatu take cewa 'kawarta Salma itakam tana so mijinta ya sake aure ko Allah zai basu haihuwa. Salma tace kiyi ha'kuri Hindatu, haihuwa lokaci ne da zaran lokaci yayi sai kiga an dace.... tunda na la'be naji wann zance, dukda 'karancin shekaruna a lokacin saida na shiga na fita nayi yanda nayi, Alhaj Ma'aruf ya aureni, Salma matar Alhj Mumtaz ita tayita bawa Hindatu baki lokacin da suka fuskanci nice a matsayin amaryar da akayiwo wa Hindatu.
"Muna zaune a haka shekaru suka 'danja, Hindatu ta ri'keni tamkar 'kanwa bata nuna min komai, nima de shiru babu haihuwa har abin ya soma damuna, ana haka kwatsam Hindatu ta sami ciki, aikuwa zo kiga murna wajen Hindatu da Ma'aruf harma da aminansu guda biyu suna taya su, nan fah hankalina ya tashi sosai, na shiga na fita amma Allah ya 'kaddara sai Hindatu ta haihu, cikinta wata tara kuwa ta haifo 'diyarta kyakkyawa. Nan kulawan Ma'aruf ya koma kanta kwacaukam dama yana tsananin sonta bare ta haihu, nan fa na koma tamkar saniyan ware a cikin gidan, shiru shiru ban samu ciki ba, har diyar Hindatu Fatima ta soma girma yarinya me shiga ran jama'a, mussaman Ma'aruf Fatima ta shiga ransa sosai dan sunan mahaifiyar sa taci.
"Ana haka naji 'kishin 'kishin Hindatu nada wani ciki gashi ni shiru, aifa nan nace banci ta zama harta 'kasashen 'ketere sai na tsallaka dan nemo magani, a wnn yawo nawa nayi yo cikinki, babu maganin da bansa wa Hindatu ta mutu ba ita da binda ke cikinta amma shiru, wata rana da daddare na shiga har 'dakinta na mur'kusheta da pillow har ta mutu ita da jaririn cikinta da baifi na wata biyu ba.
"Kuka wajen Alhj Ma'aruf ba'a magana, babu yanda Salma batayi abata Fatima 'diyar aminiyanta ba amma fir na'ki, nace kaji kini bini banza haka nayita falfala mata rashin kunya dole ta ha'kura shima Alhj ma'aruf nason kasancewa da Fatima dan tana debe masa keyawan uwarta. Bayan na haifeki ne kuka taso Fatima a matsayin yarki, koda Fatima ta girma takai aure aka mata aure, nan fa na soma tuanain watarana dukiyan Alhj Ma'aruf zai zama mallakinta ita ka'dai idan tana raye, a lokacin sunso juna ita da Nazif 'dan Alhj Mumtaz da Hajiya Salma, amma fir naki bari suyi aure, dan kuwa sai abinda nace, hana Nazif auren Fatima danayi ba 'karamin tashin hankali ya shiga ba, tindaga wnn lokaci yayi tafiyarsa can 'kasar America yaci gaba da karatunsa, bayan tadiyansa na tilasta aka aurawa Fatima wanda bata so, dan kuwa Nazif shine masoyinta.
"Koda Nazif yaji Fatima tayi aure nan yace bazai dawo Nigeria ba, har ya sami wata wacce suka ha'du a makaranta ya aureta suka hayayyafa.
"Toh Fatima ta jima bata haihu ba, har kema kika kai aure, sanda naga Fatima ta samu ciki na tabbata watarana dukiyan Ma'aruf zai zama mallakinta da abinda ke cikinta toh tunda ga nan na mata asiri ta haukace ta shiga uwa duniya, wanda daga baya nace maku ta mutu, muka ha'da baki da mijinta bayan na cika masa aljihu da makudan kudi mukace ma Alhj Ma'aruf mutuwa tayi ita da abunda ke cikinta, har rana me kaman tayau bamusan yanda ta dosa ba, ko ta haifi abunda ke cikinta oho mata, ko bata sai Allah, amma boka ya tabbatar mani bata sake dawowa cikin rayuwata ba.
"Hajiya Karima ta ri'ko hannayen Laila tace" Laila duk wnn abubuwan danayi nayisu ne dan inganta rayuwarki dana 'diyarki Aziza. Kinga yanzu ko Ma'aruf ya mutu dukiya de namu ne mu ka'dai, ni da ke da kuma 'diyaki Aziza, snn ni nayi sanadiyan mutuwan Alhj Mumtaz duk dan wnn Company da ya tsolen ido ya dawo mallakin mu. Bayan na gama sa ran Nazif da uwarsa Salma bazasu dawoba kwatsam sai su dawo rayuwata. Bazai ta'ba sakuwa ba. Dole musan abinyi. Dole mu kashe mijinki ki auri Nazif.....
"A zabure Laila ta mi'ke tana duban Hajiya kafin tace" A kashe mijina kuma hajiya, tsaki hajiya tayi tace" yo se me? Ke barin fa'da maki Nazif yafi wnn mijin naki komai da kika sani, a sanin da na masa da kyakyawan saurayi ne wanke hannu ka ta'ba, balle yanzu da Amurka ta da'da goge fatarsa.
"Murmushi Laila ta soma kafin tace" Kai Hajiya baki da 'dan'danin imani, aiko tundp a baya tun inda 'kuruciyata idan nagansa yazo wajen yaya Fati wani haushi nake ji, dan bana mance kamanninsa, kuma har yanzu ina sonsa. Ta ru gume Hajiya tana fa'din shawarinki yayi Hajiya.


*4 years later*
*********************************


*Cibiyan goya marayu*
_Gidan marayu_....


"A hankali take takun sa'daf sa'daf har ta samu tafice daga 'kofan, ta juyo tana kallon ta gefenta tace" Yusrah wllhi yaukam da wuri zamu dawo kafin Anty Larai ta capke mu. Yusra tayi dariya maras sauti tace" kai *Deejah* da'dina dake akwai tsoro, harara Deejah ta galla mata tace muje yana can 'kasa yana jiranmu. A tare suka nufi yanda yayi parkin motarsa.
"'Kwankwaswa sukayi ta glass din motan, aiko da sauri ya bude masu yana mayaudariyan murmushi yace" Deejah gayu bismillah, yamutsa fuska Deejah tayi tace " kaga Safwan banson irin wnn kashe idon naka ni na fa'da maka ni ba 'yar iska bace. Tsaki yusra tayi tace Deejah dan Allah ki shiga mu tafi kadin 'yan sa idon Anty Larai su ganmu. Harara Deejah ta galla mata kafin ta shige gaban motan.
"Safwan kuwa dariya yayi yace a ransa kaji Deejah dai da wani maganar rainin hankali, tana aikin rawa a club tana ce mani ita ba 'yar iska ba, ko 'yar meye ita oho..... " daidai nan sukayi parking a 'kofar " Amazing Club.....


πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹..........
[8/18, 20:23] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye*


_Written by QueenSamy_......πŸ“


"Safwan na gama parking ya fito da sauri ya bu'ewa Deejah, harda wani na'de hannunsa ta baya guda daya ya 'dan sunkuya kafin yace" here we are gwanar rawa... "Murmushi kawai Deejah tayi kadin ta sako 'kafarta ta soma fitowa, takalmin 'kafar high hill ne sosai ba'ki me 'dan farin duwatsu, tana sanye cikin ash din top ta 'daura black boyfriend jacket a sama, wandon jikin red ne sai veil red data 'daura a kanta. Deejah budurwa ce 'yar kimanin shekaru 19 ba fara bace snn bata layin ba'kake, ba wani kyau sosai take dashi ba amma ba'a kirata maras kyau ba, tana da kyaunta daidai misali, hakan nan gashin kanta me tsanti da tsaho ne, kyaun jikinta shi yafi komai 'daukan hankalin da yawan mazan da sukayi tozali da ita, Allah ya mata diri irin na wacce zaka gani kace lallai wann ta cika mace. Deejah gwanar son rawa ce wnn dalili yasa tayi 'kaurin suna a Amazing Club, takan je tayi rawa akan Stage mutanen da suke club din susha kallo yayinda da yawa suke mata 'barin ku'di, da yawan maza suna son kawo 'ko'kon baransu wa Deejah amma babu fuska, dan haka nan take da azaban masifa, bata barin kota kwana balle tayi tsami, wnn dalili shi ya ceceta daga idon maza 'yan bariki ma'abota zuwa club. Safwan ne ka'dai Deejah take kulawa shima 'din dan babu yanda ta iya dashine, ko fa'da ta nemo Sadwan ke tare mata, tun tana hantaransa har 'karshe suka koma tamakr abokai.

"Yusrah na taka mata baya Safwan na gefenta suka shigo cikin club din, nan fah waje ya kacame da ihu da shewa da pito, fa'di suke ga Deejah ga Deejah, wasu kuma na fa'din the Great DD wato Deejah Dancer, tana isowa kuwa ta shiga'daga masu hannu nan ta haye kan stage gamida cire jacket din jikinta tayi jifa dashi, nan fah aka kuma saka shewa, wa'kan da take tsananin so aka saka mata nan ta soma rawa kama babu 'kashi cikin jikinta. Nana aka soma tururuwan zuba mata ku'di Yusra na tarawa.
"'Karfe 11:30pm daidai Deejah ta sau'ko daga kan stage ta jawo Yusra suka ke'be tace" Yusee we need to leave this place right now, Yusee ta 'dan ha'da rai tace kai Deejah daren fah da saura, Deejah taja tsaki a hankali kafin tace" Yusee kindai san yanzu dole Anty Larai ta saka mana ido sabida gulman mu da ake kai mata ya soma yawa, kinga dai kallon malaman addini take min, yanzu idan ta gane ni 'yar rawa a Club ne, me kike tunanin zai biyo baya.
"Yusee tayi murmushi tace" toh Deejah mu daina wnn sana'a mana, am pretty sure ku'din da kika tara yanzu zai isheki ki soma karatun jami'anki. "Deejah ta sau'ke ajiyan zuciya kafin tace" wllhi Yusee inaso nayi university yanda baki tsammani, snn inaso watarana na rin'ka taimakawa Orphanage foundation, ina tausayin wa'enda suka tashi babu iyaye iri na, rawan da nakeyi a club yana 'daya daga cikin burina na tara ku'di dan taimakawa marayun da suke Orphanage, ba zallan wnn ba kinsan rawa hubby na ne.
"Yusee ta saka hijabinta kafin ta mi'kawa Deejah nata tace oya saka mu tafi, Deejah ta kar'ba ta saka gamida cire dogon takalmin 'kafarta kafin suka fito can gefen titi.
"Safwan na zaune na jiransu cikin club ashe su tuni sun fice. Ta glass yake hango su suna 'ko'karin taran mashi. Ai a sittin Safwan ya mi'ke ya fito ya nufesu. Kallon mamaki ya bisu dashi kafin yace da 'dan mashin din "malam jeka abinka.
"Deejah ta 'dan hararesa kafin tace" kaga Safwan yanzu gari yayi shiru idan ka kaimu za'a iya ganinmu. Murmushi Safwan yayi kafin yace" Deejah bazan iya barinku ku tafi ku ka'dai cikin daren nan ba, duk da nasan kun saba wuce haka a waje, but this is very risk, is dangerous, someone might harm you, bai jira cewansu ba ya 'karasa ya kawo motarsa har gabansu yace oya ku shige mu tafi.
"Babu musu suka shige, a cikin mota Safwan yake cewa" Deejah meyasa baku so asan kuna wnn sana'a?
"Wata uwar harara Deejah ta watsa masa kafin tace" malam kaga this is non of your business, idan zaka kaimu muje, idan bazaka kaimu ba, fine ai dama ba saka mukayi dole ba...." murmushi ya kuma yi kafin yace" Allah huci zuciyarki, ni da zaki bi shawarata ma da kin bari na turo maganar auren..... " bai gama rufe baki ba Deejah ta dakatar dashi" Au me? Kaga Safwan ni bance maka aure zanyi yanzu ba, karatu nake shirin farawa, kuma da kaga bamu so asan muna zuwa club a Foundation 'dinmu sabida kar a mana aure ne, anaji za'a ha'damu aure da koma waye, idan har kana so ala'karmu ta ci gaba toh kaja bakinka kayi shiru, idan lokaci yayi naga zan iya aurenka fine...." Da mamaki Safwan ke kallonta bata ta'ba kawo masa magana makamanciyar wnn ba, wani da'di ne ya ziyarci zuciyarsa, shikuwa ko yaushene yana iya jiran Deejah muddin zata yarda ta auresa.


"A can hefen layinsu yayi parking kafin suka fice, cikin san'da suka shigo Orphanage ta 'kofan baya, dan dama har spire key na 'kofar garesu. Suna shigowa suka samu kowa yayi bacci, kai tsaye 'dakinsu suka wuce, suna shiga suka soma shirin bacci... " motsin da sukaji ne yasasu saurin rufe idanuwansu kaman masu bacci.
"Anty Larai ce ta shigo ta tarar suna bacci, a hankali ta rufe 'kofar tayi ficewarta, tana fita suka bu'de ido ha'di da yin dariya.


"Washe gari da safe, Deejah tayi wankanta ta fito cikin shiri dan dama tana 'daukan ajin yara a makarantar su dake cikin Orphanage, kai tsaye wajen karywa ta nufa, Anty larai na zuba wa yara breakfast Deejah ta 'karaso, haba nan fa yaran suka soma Anty Deejah Anty Deejah, nan Deejah ta soma wasa wa yaran nan kaman yanda ta saba, Deejah akwai farin jini wajen yara da manya dake rayuwa a Orphanage, wnn dalili ne yasa wasu suke hassada da ita.
"Deejah ta kar'bi abincin daga hanun Anty Larai ta ci gana da rabawa yaran, bayan ta gama ne tace dasu" Ok kids kowa ya wuce aji ina nan zuwa, banda makara duk wanda ya makara zan masa bulala, tana fa'da tana masu alamau da hannu fuskanta dauke da murmushi. Da gudu yaran suka nufi wajen wanke hannu suka wanke kafin suka doshi ajijiwansu.
"Anty Larai ta dubi Deejah tace" Deejah dama akwai maganar da nakeso muyi, Deejah ta dawo da hankalinta gareta tace na'am Anty. Anty larai ta dubeta tace" Deejah maganganu akanki da Yusra a Foundation din nan ya soma yawa, labari ya riske cewa kuma yawon dare...." Da mamaki Deejah ke kallon Anty larai kafin tace" Haba Anty, meyasa zaki rin'ka 'daukan zantukan mutane akanmu, kawai de hassada suke yi damu, ta juya tana watsawa Tani dake can gefe harara kafin taci gana da fa'din "Anty fa'da mun wacce munafukar ne ta kawo maki wnn labarin 'kanzon kuregen, yanzu taga yanda koyawa muafuki hankali, kawai dan sunga kinaso na shine bari a nemi hanyar rabamu, ta 'karsa gaban Tani tana girgiza taci gaba da fa'din" wllhi duk munafuncin munafiki duk sa idon basa ide nan gani nan bari, haka zai ganmu da Anty Larai ya barmu...." Tani cikin 'kuluwa ta mi'ke tana fa'din" ke da wa kike. " Dake nake good for nothing hypocrite.... nan fah fa'da ya soma tashi tsakanin Tani da Deejah, a fusace Anty Larai ta 'karaso tana masu fa'da, Yusra kuwa hayaniyar da taji yasata saurin fitowa cikin uniform dinta da alama makaranta zata dan ita bata gama sakandare ba,
"Sosai Anty Larai ta masu fa'da, Tani rai 'bace ta bar wajen, Yusra sulum sulum zata wuce Anty Larai tace" zo nan yusra, Yusra ta zaro ido tace na'am Anty, kinjini sarai, Anty larai ta bata amsa, Anty zanyi lattin sch.... kallon da Anty larai ta watsa mata yasata saurin 'karasowa.
"Ku fa'da mun gaskiya kuna fita da daddare kokuwa, 'kwalla ne ya ciko idin Deejah, ganin haka yasa jikin Anty Larai yin sanyi, dan kuwa tana tsananin son Deejah, wani sa'in daughter ma take kiranta, wasu nannys a wajen ma Deejhn Larai suke kiranta. Da sauri Anty larai ta 'karasa ta ri'ko hannun Deejah ta dubi yusra tayi mata alama da hannu kan ta tafi. Yusr hamdala tayi a ranta kadin ta fice.
"Hannu Anty larai tasa ta soma sharewa Deejah hawayenta kafin tace" Deejah, you're like a daughter to me, bana son abunda zai sameki, tun tasowarki kimsan da haka, duk fa'din gidan nan babu yarinyar da nake so irinki, kowa ya maki shaida da hali na gari, ba yara ba ba manya ba, ina tsorin kar ki 'bata rayuwarki. Dole na damu da jin zance da yake tashi a gidan nan, yau idan labarin nan ya isa ga gwamnati kinsan hukumcin aure za'a maku da kowaye, so banaso haka ta faru dake daughter, da inada halin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login