Showing 57001 words to 60000 words out of 159062 words

Chapter 20 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10407

iya mayar masa da magana.


"Laila kuwa ta sami karb'uwa sosai wajen Ahalin Engr Nazif, kowa ya saki jiki sosai da ita, hakan yasa ta k'ara samun matsayi sosai wajen Engr dukda har rana me kaman ta yau bai tab'a jin sonta ba amma kula da iyalansa da takeyi sai ya bata matsayi sosai a zuciyarsa.

"Toh wai yanzu me kike so na miki ne Yussy, kinsan dae bazan ta'ba yarda wann cikin nawa bane, besides bani kadai bane nake fita dake, bayan alkawarin da kika min bazakina kula kowa ba, ance maki bansan kina bin wasu mazan bane..... " Ahidjo wllhi kai kadai ne nake yarda ka kusance ni babu condom kaga kuwa definitely this pregnant is yours.
"Gajeren tsaki Ahidjo yayi kafin yace yanzu me kike so nayi kinsan dae ban isa kai wa iyayena wnn labari ba. "Yussy ta juya idanunta dan kuwa tarkonta ya kafu ya kama Ahidjo nan tace" Toh that's why called you, yanzu hundred thousand kawai zaka tura min account dina naje a cire cikin, Ahidjo ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace Ok ok fine naji zan tura maki, and make sure an cire cikin nan kinji.
"Tayi wani k'asaitaccen murmushi kafin tace toh sai naji alart........
"Wani tsalle Yussy tayi" kai yauwa yanzu kuma saura Safwan shima haka zan kirasa ne kanna masa k'arya na tsesa...... " Ta kwanta bisa gadonta iPhone 7 dinta na gefe ta shiga kallon irin kayan more rayuwa da yanzu take dasu ba kaman da da take orphanage ba, kai lallae rayuwa ya mata dadi... haka ta ringa kiran samarukanta tana tara kudi......


"Deee pls mana wnn punishment din ya isa haka I need see you, wnn rules naki yayi yawa ko dan kinga am dying for you ne.... ya k'areshe maganar cikin sigan shagwab'a yana mai juyi cikin kujeransa na office...... "Daidai lokacin da Sadiq ya turo kofan office din ya shigo.
"Daga d'aya b'angaren Deejah cike da jin kunya tace" Kai ya Irfan sch ne fa ya b'oye ni......" No karma kice sch, ever since dana furta ina sonki kika shiga wasan b'uya dani, ko a gida na daina ganinki.
"'Dan murmushi kawai ba tare da tace komai ba ..,. Irfan kuwa ko ajikinsa yaci gaba da gaya mata kalaman soyayya hardai saida yaga kaman Sadiq ya gaji da jira kafin ya kashe wayar.


"Mr lover anya zaka bari ta k'arasa sch din kuwa kafin ayi auren,.... "Kai haba Sadiq ta k'arasa sch fah kace like you don't know she's just starting, ai na gama k'ok'ari ta k'arasa aji d'aya sauran bayan aure taci gaba, yanzu ma daba don hankalin Daddy yana wajen sauk'e tsohon chairman din nan ba da tuni na masa maganar.
"Sadiq ya murmusa kana yace" kaga sabon shigan soyayya, Irfan kuwa lumshe idonsa yayi ya kwanta cikin kujera me juyi snn yace "whatever..... " dariya sosai Sadiq yayi kafin yace "toh mijin Deejah yanzu dai ka tashi mu tafi conference hall kasan daddy baison muna attending meeting late......


"Ai kuwa hall ya cika su kadai ake jira, Suna shiga da kadan Engr ya shigo, Shear holders da staff gaba daya an hadu, nan akayi meeting kan sauke tsohon chairman bisa samunsa da akayi da shigo da kaya na bogi, wnn nasara kuwa ya samu ne ta dalilin Sadiq da Irfan, Engr sosai yaji dadin yanda suke aiki bisa gaskiya da amana a wnn company, take aka k'ara masu matsayi a M&M Builders, kama daga masu hannun jari harma da ma'aikata na companyn sunji dad'i dan kuwa suna jin dadin aiki sosai da Irfan da Sadiq.


"Tsohon chairman kuwa ya kira tsohuwar kilakinsa wacce tayi k'aryan k'aninta ne wato Hajiya Karima suka shiga jajanta lamarin, sosai Hajiya ta cizi yatsa ji take kaman ta kashe Nazif da d'ansa ta huta, da ba don tilon d'iyarta da tilon jikarta sun k'wallafa rai akansu ba da tuni ta kar Nazif da Irfan ta huta, amma idan sunsan wata basu san wata ba, da Karime suke zancen, duk wandata yaci tuwo da Karime to kuwa babu ko shakka miya ya sha.... Ta juya ta galla wa Alhj Ma'aruf harara kana ta dungure shi a goshi tace" Bak'in mahassadi duk kai ka jaza min wnn da yanzu M&M ya zama *Mallaki Na*. Hawayen takaici ne kawai ke sauk'a daga idon Alhj Ma'aruf....


"Yau ta kama Saturday ita kad'ai take kan shirin sch dashike suna da tutorials kasancewar jarabawa na farkon zango na k'aratowa, babu yanda batayi su Nadee su shirya ba sun'ki dan haka ita kad'ai ta shirya ta sauk'o k'asa, dawowarsa kenan daga jogging sukayi kicib'is......




_πŸ‘ΈπŸ»QueenSameeπŸ˜πŸ’„πŸ‘„_
[8/22, 14:40] Umar Dalha: πŸŒ˜πŸŒ˜πŸŒ”πŸŒ” *Mallakin Waye*


42


*Na Sameena Aliyu*


"Kallonta yake babu ko kyafta ido tai masa kyau sosai dukda ba wani makeup ne face dinta ba, riga da skirt ne na leshi a jikinta sai hijabin da bai k'arasa gwiwa ba,
"Ganin irin kallon da Irfan ke mata yasat saurin sunne kai da kyar ta lalumo kalamai ta iya gaidashi, ya amsa sanda yake cire headphones din dake mak'ale kunnensa.
"Where are you heading to Gorgeous?
"Idonta na kallon k'asa ta amsa da "School" a takaice
"Toh ai yau Saturday driver din naku baya zuwa da safe ko kin mance ne.
"Dama taxi zan shiga.
"Wai class ne kike dashi, ya tambaya cikeda kulawa.
"Eh tutorial ne zanje.
"Agogon wayansa ya duba kafin yace" let me get dressed sai na kaiki. Daga haka ya wuce sashensa, sai snn Deejah tabisa da kallo komai nasa abun burgewa ne harta tafiyarsa, a hankali ta sauk'e ajiyan zuciya.


"Duk wnn abinda ya faru a idon Ammah dake zaune balcony dinta ya faru, ta kasa daina murmushin da take, kai itakam Allah yasa Irfan da Deejah son juna suke da saitafi kowa farin ciki, Hajja ne ta shigo ganida ajiyewa Ammah fresh juice na abarba a gabanta, har zata juya Ammah tace, Hajja nikam na tambayeki mana.
"Hajja ta rusuna kafin tace toh Hajiya ina jinki Allah sa na sani.
"Ammah ta kurb'i drink din kafin tace" nasan yanda Deejah ta daukeki tamkar uwa bata b'oye maki komai, inaso naji ko tanada wani saurayi da takeso.
"Hajja ta sauke ajiyan zuciya kafin tace" Hajiya gaskiya Khadeejah bata tab'a min labarin wani saurayi ba, hasalima ban tab'a jin tana zancen ba.
"Ammah ta kad'a kai kafin tace" toh Irfan fah baki ganin akwai wani abu a tsakaninsu.
"A zabure Hajja ta d'ago kai kafin tace" Hajiya ina 'Karamin Alhaji _sunan da take kiran Irfan_ ina Khadeejah..........."Kar ki damu Hajja ki fad'a mun idan kin sani, dukanmu mutane ne babu wanda yafi wani wajen Allah sai wanda yafisa tsoronsa, Hajja tun dawowar mu Nigeria kike muke tare da ke kike mana aiki, a halin yanzu mun zama kaman 'yan uwa, Khadeejah yarinyar arziki ce wacce irinta nake ma jikana Irfan fatan samu, yau da ace Irfan da Deejah zasu kasance ma'aurata da sai na fi kowa farin ciki, dan haka ki fad'a min idan akwai abinda kika sani tsakaninsu.
"Hajja ta gyara zamanta kafin ta soma fad'in" Hajia tunda kin buk'aci ki sani zan fad'a maki duka ita Khadjian bata son kowa ya sani, dan ita ta hana k'aramin Alhaji ya fad'a maku a cewar ta bata san yaya zaku karb'i abin ba, watak'ila bazaku aminta ba dubaga matsayinta a gidan nan da kuma matsayin K'aramin Alhaji, wanda hakan na iya jawo k'arshen zamanta a gidan nan, musamman da yanzu ta sami gurbin karatu, toh Hajiya kinji dalilin Khadija na b'oye wnn al'amari.
"Ammah gaba d'aya ta kasa b'oye farin cikinta,..... "Suna a haka gogan yayi sallama ya shigo nan Hajja suka gaisa da Irfan kafin ta fice,
"Yanayin dayaga Ammah ya tabbatar masa tana cikin farin ciki, dabadon kar Gorgeous dinsa tayi latti ba daya tsaya zolayan Ammah ko ta samo wani bazauri ne.
"Ammah ta lura da yanda yake ta sauri tayi saurin cewa" yaya dai mijin saurin me kake ne da bazaka tsaya mu gaisa da kyau ba.
"Irfan ya k'araso ya manna mata peck a goshi kafin yace" Granny am in a hurry Deee zatayi latti zan dropping nata sch ne.
"Ammah ta murmusa kafin tace" dukda baka fad'a min I already found out, Irfan nafi kowa farin ciki Allah ya sanya Alkhairi.
"Cikin rashin gane ina Ammah ta dosa Irfan ya soma girgiza kai yana d'aga gira kana yace" sorry Granny don't get you.
"Murmushi ta kuma yi kafin tace "idan ka dawo zamuy7 magana, daga haka ta shige bathroom, ta bar shi na sak'esak'en me Ammah ke nufi. " 'dan 'daga kafa'darshi yayi gamida d'aga gira sam kafin ya fice,


"Da kansa ya bud'ewa Deejah front seat ta shige ya maida marfin ya rufe, kafin ya k'arasa driver seat ya bude.
"Engr Nazif dake tsaye windown d'akinsa a idonsa komai ya faru, duk k'arfin hali da dakekken zuciya irin na Engr saida yaji mugun fad'uwan gaba ganin yanda Irfan ya bud'ewa Deejah k'ofar mota yana mai rirtata, da kyar ya iya k'arasawa gefen gado yanda Laila ke kwance ya zauna zuciyarsa na tafarfarsa wanda shi kansa besan dalili ba.
"Zulai baki sake take kallon Deejah da Irfan ganin abin tayi tamkar a film, a sittin tayi sashen Aunty kai tsaye d'akin Azee ta wuce ta shiga dokawa, Azee na kwance kan makeken gadonta kamar a mafarki ta jiyo bugun da Zulai keyi, da masifa ta nufo k'ofar d'akin ta bude, yanayin dataga Zulai yasata yin biris tana kallonta,
"Ke lafia meye na ganki haka....... cewan Azeee, "Zulai na haki ta kwashe komai ta fadawa Aziza,........"Wani irin Duuummm! Azee taji, hijabi ta wawura ta suri car key din Laila har tana bangaje Zulai ta fice tayi waje a guje, nan ta hangi bayan motan Irfan na ficewa, saurisauri ta shige motar Laila ta fice.


"Hankali kwance yake driving jifa jifa yana hirawa Dee dinsa, dukda sunne sunnen kan da Deejah keyi, Irfan ya d'an rage speed kafin yace" Dee all this kunya kuyan nan naki zan cire maki su soon, aurenmu da two days ma zamu tafi honeymoon so ki zab'i wani k'asa kike so.
"Ta d'anyi far da idanunta kafin tace "Kai ya Irfan ko saka ranar auren fah ba'ayi ba,.
"Irfan ya murmusa kafin yace" soon za'a saka ai, danni bazan iya wann b'oye b'oyen naki ba, ya d'an rank'wafo da kansa saitin kunnenta kafin ya rage murya yace" Am eager to be with you Gorgeous, bazan iya k'ara 1year ba tareda ke ba.
"Tafukan hannunta tasaka ta rufe fuskanta tana murmushi, murmushin shima yayi sanda ya maida hankali bisa titi.

"Daidai kwanan Nile University Ahidjo ya hango motar Irfan na shiga makarantar, nan shima ya karya hancin motarsa yabi bayan Irfan daidai lokacin da Azee ma ke biye dasu.


"Har k'ofar lecture hall Irfan yayi parking da kansa wnn karan ma ya sauk'o ya bud'e wa Gorgeous dinsa k'ofa, fuskan nan nasa dauke da murmushi yana sanye cikin red shirt da black chinos wanda ya fito da farar fatarsa da asalin kyaunsa, hannu yasa ya rik'o jakar Deejah yana k'ok'arin karb'a,.... "Deejah ta d'an turo baki a shagwab'e tace" kai ya Irfan what's this...... "Da sauri cikin kwaikwayan muryarta yace" zan rik'e wa Gorgeous jakarta ne, mak'e kafad'a tayi kafin tace" kagafa mutane na kallonmu....." Shima mak'e kafad'ar yayi kafin yace" I don't care kowa ma yasan I love my Gorgeous and I can do everything for her, be ko jira cewanta ba ya karb'e jakar yace oya muje na raka ki k'ofan hall din......" Jama'a kuwa gaba d'aya idonsu kan Irfan da Deejah, daga masu cewa Woow sun dace, sai mau cewa inama sune suke jerawa da Irfan ya rik'e masu jakka, lallai Deejah sarauniya ce. Hamida course mate dinsu ce ta k'araso tana kashe wa Deejah ido wai sun dace, Hamida ta gaida Irfan kafin ya mik'awa Deejah jakarta saida suka k'ara shan soyayyarsu kafin ya wuce, Deejah da Hameeda suka wuce hall, Hamida na faman yaba kyau da had'uwa irin na Irfan.
"Azee da Ahidjo fah..... "Azee dai ji tayi tamkar ta kashe Deejah ta huta, Ahidjo kuwa sha'awan Deejah k'aruwa masa yake bayan ko wani second musamman da yanzu ya sake yin tozali da ita, yana hankalce da irin kallon da Azee ke masu dan gefenta yayi parking. ?.........
"Ganin Azee ta fincike mota ta fice a guje yasa Ahidjo saurin bun bayanta.....




"Gudu Azee keyi tamkar zata tashi sama, Ahidjo ma nan ya k'ara speed yana binta a guje, Azee bata tsaya ko ina ba sai wajen wani ruwa ta yunk'ura zata fad'a Ahidjo yayi saurin rik'ota...... Ta kuwa shiga tirjewa tana fad'in ka kyaleni na mutu, bazan iya rayuwa ba tareda Irfan ba, na gaji da soyayyan wanda besan inayi ba..... kuka me k'arfi ya kufce mata, nan Ahidjo ya rungumeta cikin jikinsa ya soma rarrashinta, saida tayi me isarta kafin ta d'ago cikeda mamaki tana kallon Ahidjo..... "Da sauri ta matsa baya kafin tace" Malam lafia? Wanene k? Meye had'inka dani?
"Ahidjo yayi k'asaitececcen murmushi kafin yace" Nine Ahidjo kabeer Babban Abokin Irfan Mumtaz wanda kike dying akansa, idan kin bani had'in kai nine solution na matsalarki snn kece solution na matsalata......" Cikeda mamaki Azee ke kallon Ahidjo".........


_Toh masu karatu yaya kuke ganin wann kwamacala zata kasance?? Ku biyo Semee dan jin wann daddan labari me cike da darussa_


_πŸ‘ΈπŸ»QueenSamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„_
[8/22, 14:42] Umar Dalha: πŸŒ”πŸŒ”πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye*


43


*Na Sameena Aliyu*


"Zama sukayi dan gefe da ruwan har lokacin Azee bata daina mamakin Ahidjo ba, hannu ya saka a lajihunsa ya ciro Emzolin maganin muran yara, mik'a mata yayi bayan ya kurb'a....." Da mugun mamaki Azee ke kallonsa kafin tace" what's this ce maka akayi ina shaye shaye.... "Mayaudarin murmushi Ahidjo yayi kafin yace" Easy baby, nima ba shaye shaye nake ba, wnn da kika gani shine maganin damuwan duniya, bet me kina sha zaki nemi damuwarki ki rasa. Ya k'arashe maganar yana wani kashe idanunsa.
"Azee dai sai kallon kwalban kawai take ta kasa tab'uk'a komai...." Ahidjo ya kuma murmusawa kafin yace" Ni da Ke muna fuskanta matsala guda son maso wani wanda hausawa suke cema k'oshin wahala, so why not bazamu ji dad'i ba meyasa zamu bari damuwa yayi mana lahani bayan wa'inda muke damuwar a dalilinsu basu san munayi ba.
"Kalaman Ahidjo tabbas sun tafi da Azee batasan sanda ta kar'bi kwalban hannun Ahidjo ba tana d'aga kai kuwa ta kwankwad'e tass sai kwalba kawai ta ajiye.
"Ahidjo ya shek'e da dariya kafin yace" ko kefa keda damuwa sedai kiga anayi....." K'wayoyo masu k'arfi Ahidjo ya tara cikin maganin nan dan haka sosai ya k'ara wa maganin k'arfi.... "Kan kace me Azee ta soma ganin jiwa, luuuu ta fad'a jikin Ahidjo, shikuwa gogan ya fashe da dariya kafin ya d'auketa ya jefata cikin motarsa, har wani tsalle yake yana fadin "wuuuhhh yau akwai morewa daga haka ya finciki motar suka bar wajen.....


"Hajiya ta cika tayi fam bayan ta gama waya da Laila ta fada mata sallaman Ashiru da akayi daga M&M Builders, banda tsaki babu abinda takeyi tana fama tsine wa mijinta Alhj M'aruf.
"A b'angaren Laila ma ta cika tayi fammm tana zaune bakin gado har Engr ya fito daga bathroom tana nan zaune, ko kallo bata ishesa ba ya k'arasa shirinsa. A fusace ta mik'e ta nufosa tana faman huci....." Na maka magana kayi banza dani ka fad'a mun me Kawu na yayi ka sallamesa daga Company.?
"Engr ya kalle ta a kaikaice ba tareda yace komai ba ya k'arasa saka agogon hannunsa. Gani dai ficewa zaiyi ba tareda ya tanka ta ba yasata saurin shan gabansa, nan da nan ta soma k'ak'alo kukan munafunci " Haba my Engr ina maka magana kayi banza dani, what have I done to deserve this,
"Girgiza kai yayi kafin ya zauna bakin gado, gefensa ya nuna mata yace" zo ki zauna, babu musu ta k'arasa ta zauna, Kallonta yake da kyawawan idanunsa, gaba d'aya sai ji tayi ta kasa jure kallonsa dan kuwa k'warjinin sa ya cika d'akin gaba d'aya. "Sauk'e ajiyan zuciya Engr yayi kafin yace" When did you become like this, yaushe kika soma min tsawa Laila, bansanki da rashin kunya ba so pls kar ki koya yanzu,....." Cike da shagwab'a tace" My Engr Kawu na fa ka kora, then how do you expect me to react...... "Engr ya rik'o hannayenta cikin nasa kafin yace" You should have let me explain first before you judge me. He was caught red handed da almandahana da cucuwa tareda shigo da kaya na bogi kan kud'i masu tsadan gaske, and doka ne na kampanin duk wanda aka kamasa da cucuwa a bakin aikinsa, yaja ma kampanin asara me yawan gaske coz mutane 'yan kwangila da dama sun dawo mana da kayayyakin mu bayan da suka soma amfani dasu suka gane kayan bogi ne. I should have send him to jell

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login