Showing 60001 words to 63000 words out of 159062 words

Chapter 21 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10373

sabida abinda yayi, Amma sabida ke da kuma darajan Baba Alhaji na kyalesa, so pls bana so ki sake tono wann maganar ta wuce.... daga haka ya mik'e ya nufi closet dinsa dan daukan takalmi...." Laila kuwa jiki a sanyaye tabi bayansa....


"Ahidjo be tsaya ko ina ba sai guest house din Dad dinsa, har lokacin Azee na cikin maye, da kyar take ture Ahidjo daga jikinta tana fadin ina ya kawota me zai mata, Ahidjo kuwa shedan sai dada angaza sa yake,, nan da nan ya shiga zame kayan jikin Azee, ya shiga romancing dinta, tun tana turesa har tashiga biyesa, be kyaleta ba saida yayi mata kackaca, kafin ya samu sukunin kyaleta, nan bacci ya kuma yin gaba da Azee. (Allah ka rabamu da sharrin son zuciya... Ameen).


**************
"Sadiq da Ruqayya ne zaune gefen Dada suna bata maganin ta Mamie tayi sallama ta shigo, gaba daya suka amsa gamida gaisheta, Mamie ta zauna gefe tana kallon Dada yanda ta damk'e 'yar tsanar dake mak'ale a hannunta, tausayinta ya da'da shigarta, ta amshi maganin hannun Ruqayya ta ci gaba da bata, Sadiq ya mik'e yana fad'in " Little sis come and serve me pls, cikeda zumudi Ruqayya ta mike tabi bayan Sadiq, dan kuwa hidiman Sadiq ko kadan bata gajiya dashi, Mamie ta bisu da kallo fuskanta d'auke da murmushi sosai yaran nata ke burgeta, Fatanta Allah ya nuna mata ranar aurensu, zata fi kowa farinciki.....


"Koda aka tashi daga tutorial Irfan da kansa ya tafi d'auko Dee dinsa, a Amigo suka tsaya yayi masu takeaway, wann rana Deejah ta yarda Irfan masoyinta ne na gaskiya snn ta dau alwashin nuna masa soyayyarta koda kuwa hakan bazai yi dadi ma wasu ba.
"Yana gama parking ya bude mata kofa gamida mika mata ledan, zatayi gardama ya daura dan yatsarsa bisa lips dinsa yace" I don't want to hear anything,.... "godiya tau masa kafin tasa hannu ta karb'a, saida ya taka mata har k'ofan sashensu kafin ya wuce nasa sashen.
"Daidai k'ofa tayi kicib'is dasu Nadiya Nilam Amir da Aiman, gaba d'aya suna k'o'karin k'unshe murmushinsu. Nilam ta k'araso da gudu Deejah ta rungumeta, a kunnen Deejah take rada mata" Deejah wai da gaske ne zaki auri ya Irfan. Deejah tayi saurin d'agowa tana dubansu Nadiya, gaba d'aya suka fashe dariya suka soma fad'in" Yess da gaske ne da gaske ne....." Nan da nan ta daburce ta soma fadin" me kuke fadi, waya gaya maku, ni dai dai..... "Tsalle su Nilam suka shiga yi suna zagaye parlorn yayinda Deejah ta jawo hannun Nadiya suka nufi upstairs.
"Sosai Nadiya ke dariya ganin yanda Deejah duk ta daburce, ke wai meye kika wani razana, bakisan mun sani ba koh...." Harara Deejah ta narkawa Nadiya kafin tace" zaki sani ai solving calculus na nan a gabanki. Nadiya na dariya tace oho dai ai matar yaya ta mana, Deejah ta nufota a guje, nan Nadiya ta fice a guje tana ci gaba da dariya.

"Har wajajen k'arfe shida na yamma babu Azee babu labarinta, Laila ta kira wayanta yafi abunda yafi baya shiga, koda ta tambayi Zulai sai ce mata tayi makaranta ta tafi gashi da motan Laila ta fice. I zuwa yanzu hankalin mutanen gidan ya tashi, musamman Laila, Engr Ammah da kuma Deejah,
"Engr ya tusa Deejah da Nadiya a gaba da tambaya ko yau sunje sch, Deejah tace " Eh tutorial mukayi Daddy amma ni kadai naje Nadiya da Azeeza basu je ba, Nadee tace haka ne, nan hankalin Engr da Laila ya kuma tashi, aka kira Hajiya ko tana can shiru bataje can ba,
"Cikin sauri Engr ya tura Nadiya kiran Irfan suka nufi station yayinda su Ammah dasu Hajja keta faman bawa Laila baki, dan kuwa zama dirshen tayi a k'asa tana kuka......




πŸ‘ΈπŸ»QueenSamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„......
[8/22, 14:44] Umar Dalha: πŸŒ˜πŸŒ˜πŸŒ”πŸŒ” *Mallakin Waye*


44


*Na Sameena Aliyu*


_β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘ To All the readers I love you Oceans and Galaxiesβ˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†_




"A hankali ta soma bud'e idonta da suka mata nauyi tana me dafe kanta gamida jijjuya kan nata, ta yunk'ura zata tashi saiji tayi zafi sosai ta k'asanta, kasa d'aga koda k'afa guda tayi balle tayi tunanin tashi,... Take komai ya soma dawo mata kwanyanta, Jarrr ubancan wato Ahidjo fyad'e ya mata, wani wawan ihu ta sake wanda yasa Ahidjo fitowa daga bathroom babu shiri, ganinsa sindir da tayi gabanta yasata sake runtse idanunta tana ihu tana bige bige, ..... "Da sauri ya zuri towel ya d'aure k'ugunsa kafin ya k'araso yanda Azee ke kwance, rungumeta yayi sosai cikin jikinsa yana fad'in" Calm down baby, calm down take it easy......" Bangaje sa tayi kafin ta soma fad'in" dama wann shine k'udirinka akaina, dama kayi niyayyan ka rabani da abinda na jima ina tattalinsa wa masoyina ne, ka cuce ni I was stupid da na biyeka daka ce zaka taimaka min Irfan yasoni, dama wann shine taimakon, na tabbata koda ace Irfan zaiso ni bazai tab'a sona yanzu ba,..... "Ahidjo yayi saurin saka bakinsa cikin nata, da k'arfin gaske Azee ta turesa ta shiga goge bakinta, tana watsa masa mugun kallo take fa'din" ka cuceni ka cuceni mugu kawai azzallumi....." Sosai Ahidjo ya rungumeta cikin jikinsa kafin ya soma fad'din" ki saurareni kiji me zance, da kike ta cewa I raped you wayace maki fyad'e na maki, cikin sauk'i kika bani had'in kai mukayi komai...... "Cike da masifa take fad'in " Sabida ka bani kayan maye nasha hankalina ya gushe shiyasa na biyeka ai......" Enough!!!! Ya daka mata tsawan da saida ya firgita ta kafin yaci gaba da fad'in" Ke mahaukaciyar ina ce, did I force you to drink it, ai bani na na tilasta maki sha ba in the first place, kuma da kika sha am pretty sure yanzu kinji canji a jikin ki,....." yayi wata murmushin k'eta kafin yaci gaba da fa'din " Ke barin fad'a maki yanda muka fara ki bari mu ci gaba, idan kika k'i kin san zan sanarwa Irfan komai snn zai da'da tsanar da ya maki akan nada, and babu wanda zai yarda fyad'e na maki tunda ke kika kawo kanki....so just corporate baby and get what you want, idan kika amince mun kin samu Irfan an gama. Daga haka yayi ficewarsa zuwa parlor ya barta nan cikin k'unci
"Dafe kanta tayi ta shiga kuka me tsuma rai, tabbas abinda Ahidjo ya fad'i gaskiya ne, idan ya fada kowa ma a gidan zai tsaneta harta momynta balle Irfan da dama ya washeta, biyewa Ahidjo shine kad'ai mafita a gareta. Da wnn tunani ta yunk'ura zata tashi taji zafi, haka ta rarrafa ta shige bathroom dinsa ta kintsa kanta.....




**************************
*Police Station Wuse 2, Abuja*


"Suna zaune shida Engr a reception bayan Engr yayi filing case d'in b'atan Azeeza, har no motan Laila data fita dashu da time din da suke expecting ta fita Engr ya fad'i....
"'Dan gajeren tsaki Irfan yayi sanda wayarsa ta soma k'ara kafin ya matsa gefe yana amsa wayan, Sadiq ne ya kirasa bayan sun gama waya da Sadiq Deejah ta kirasa ta soma tambayarsa ko an samu Azee, " So you also believed that she was lost, babu wani b'atan da tayi kawai dai yawonta ta tafi, ya fadi cikeda b'acin rai,
"Haba ya Irfan don't talk like that, ina zataje ta zauna har dare, da gaske b'ata tayi, wait a minute...... "idan kace haka kenan muma lokacin da muka b'ata yawonmu muka tafi.? "A hasale ya soma fadin karma ki hada b'atanmu da nata, two different things ne, ke da kanki kikace ba ki ganta a sch ba, toh ina taje inba yawo ba. " Deejah ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace" dukda haka dai idan mutum ya fita tofah sai Allah ya dawo dashi lafiya, mudai muyi addu'an Allah sa tana cikin k'oshin lafiya,..... " Gajeren tsaki ya kuma yi kafin yace" bari ku gani babu b'atan da tayi, am quite sure zata dawo da kanta, ... Zatayi magana ya canza zancen zuwa na soyayya na suka b'uge da hiran soyayyar su har ya d'an sami sauk'in haushin da yakeji.....
" Yana gama wayan ya dawo yanda Engr yake, sauro duk sun soma cizonsa abunka da ajeboter take jikin ta soma canza launi, "Daddy pls mu koma gida haka tinda munyi filing complaint besides yarinyar nan fah yawonta kawai ta fita tunda kowa ya sani ba sch taje ba,...." Ya isa haka Irfan Engr ya daka masa tsawa, kafin yaci gaba da fad'in" bana son irin haka yarinya ta b'ata kuma kana cewa yawonta ta tafi, zuwa anjima securities na Nile din zasu kawo CCTV information mu gani idan ta tafi sch, munddin taje makarantar kuwa zasu fito mana da 'yar mu dan k'ara zan shigar dasu.
"Irfan dai baice komai ba, Amma zuciyar sa ta ci gaba da ayyana masa Azee yawonta kawai ta tafi, gaba d'aya ji yayai ta k'ara sane masa.


_8:39pm_
"Daidai lokacin da securities na Nile University suka kawo CCTV information nan aka soma playin, Engr da sauran officers din suka maida hankalinsu kan video din yayinda Irfan ya koma gefe yana ci gaba da danna wayarsa.
"K'arara motar Laila da Azee a ciki aka nuno ta shige cikin Nile.... jim ka'dan aka nuno ficewarta daga makarantar......" Engr ya sauk'e ajiyan zuciya, tabbas Aziza ta fita daga makarantar toh ina ta nufa? Wnn shine babu wanda yasan amasar. Engr yayi godiya sosai wa securities din Nile yanda sukayi cooperating kafin suka wuce.


"K'arfe 9:00pm daidai Engr da Irfan suka bar station din kan idan an sami wani labari gameda Azee zasu kira Engr. Sosai Engr yayi masu godiya bayan ya cikasu da arziki.
"Ran Irfan idan yayi dubu ya b'acu kan wnn k'azamar yarinyar aka fito dashi da daren nan, dabadon Daddy yake tu'kawa ba da tuni ya fincike motar, haka ya rink'a sak'e sak'e a zuciyarsa har suka isa gida.
"Suna isa Laila ta fito a guje tana tambayansu, Ammah da Deejah dasu Hajja suka rufo mata baya, "Dan takaici Irfan kam wucewa yayi sashensa ba tareda yako tsaya ba.


"Suna zaune parlorn Engr sai faman lallashin Laila yake, I zuwa yanzu harta su Nadiya sun shiga damuwa, suna a haka sai jin Sallama sukayi...." Ahidjo ne ya shigo Azee na biye dashi,
"A tamanin Laila ta isa ta rungume Azee dukansu biyun suka fashe da kuka, Ahidjo ya k'arasa can gefen Daddy ya soma gaishesa, da mamaki Engr yace" Ahidjo ina ka samo ta??
"Ahidjo kansa na k'asa uwa mutumin arziki ya soma sharo k'arya yana juyewa.
"Daddy I found her can wajen gari, amrobbers sunyu mata robbery, sun kwace motarta and all, I was shocked lokacin datace min ita 'yarka ce, sai nace mata nima kai baba na ne, so that's why I brought her here, bayan na kaita asibiti anyi treating nata, ....
"Illahirin mutanen parlorn godiya suka shiga yiwa Ahidjo babu kaman Laila da Engr. Ahidjo ya saci kallon Azee dake kwance cinyar Laila ya kashe mata ido d'aya, nan ta mayar masa da martanin alamun yayi k'o'kari. Daga haka ya mike yana fadin" babu komai daddy barin duba Irfan.
"Azee ta kuma shigewa jikin Laila tana cije cijen leb'e sabida azaban ciwon da Ahidjo yaji mata.
"Police ne sukayi wa Engr waya cewa an sami motan a so so place, yanzu haka suna nan zuwa.
"Engr ya kuma masu godiya gamida fada masu an samu yarinyar.




πŸ‘ΈπŸ»QueenSamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„...........
[8/22, 14:45] Umar Dalha: πŸŒ”πŸŒ”πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye*


45


*Na Sameena Aliyi*


"Kallon mamaki Irfan yabi Ahidjo dashi kafin yace" itama club d'in kenan ka ha'du da ita kuka gama watsewarku a can snn ka d'auko ta ka kawo ta gida kuka shera k'aryanku, Am I right? Ya k'arashe maganar yana mai kallon Ahidjo da witsiyar ido...."
"Haba Irfan "what the heck are you talking about, why on earth could make me lie to you, ka tuna fa we've been friends for long time kai our friendship has gone beyond ordinary friendship tinda mun zama kaman 'yan uwa you're my brother from another mother, wllhi Irfan this is whole truth, I found her wajen gari, and she's been robbed.......burki Ahidjo yayi da maganar tasa kafin yace" wait a second, why do you even care, meyasa kake tambaya kodai sonta kake???....." wani mugun harara Irfan ya watsa masa kafin yace" Watch your mouth guy, ko na rasa macen so ai bazan so that thing ba, kai I've never seen a disgusting being kaman ta ba tunda nake a rayuwata, the next time da ka sake hadani da yarinyar nan you gonna be sorry, ...
"Murmushi Ahidjo yayi kafin yace" naga dai tafi yarinyar da kake nema asali da kyau......" Bai gama rufe baki ba Irfan ya kaimai naushi sai a bakinsa...." huci yake kaman rud'en dake tafasa bisa murhu...." Dukda jini dake bin bakin Ahidjo bai hana Irfan sha'ko wuyansa ba, yana huci yake fad'in" Didn't I warn you idiot,......" Securities ne suka nufo su a guje da shike a farfajiyan gidan suke tsaye jikin motar Ahidjo, take Ahidjo ya fizge wuyan rigarsa yana fad'in" Let go of me, Irfan ya kalli securities din yace su koma bakin aikinsu ba fad'a suke ba norms ne πŸ˜‚, babu musu suka koma.
"Ahidjo yasa hannu yana d'an goge jinin kafin ya d'ago yana duban Irfan yace" You need someone to tell you the truth Irfan, kar ka bari soyayya ya rufe maka ido, how on earth zaka soma soyayya da mere girl irin Deejah yarinyar da baka san asalinta ba for goodness sake, all you know about her is that daga Orphanage take, you don't know her real family who knows ko street girl kake nema, you and she are from different world Irfan, ka dubi girman family dinku, ka dubi arziki irin na mahaifinka, you're his eldest son you suppose to marry from responsible family, wanda za'ayi recognizing nasu, duk mutanen da za'a gayyata daga k'asashen duniya ka rasa wacce yarinya zaka kawo of all people duk matan da suke dying akan ka turawa larabawa kai har koreansa kanada masu sonka sai wann street girl din... haba ..... haba Irfan don't be a disgrace to your Family..........."ENOUGH OF THIS Ahidjo!!!!! Ya ishe ka haka, What is your stress da abun da ya kasance zab'i na, don't make me hate you for the rest of your life, Duk abubuwan da ka lissafo akan Deejah haka na ganta kuma nake sonta, it doesn't matter her status in life, what matters here is that I loves her..... I love her with all of my heart and nothing will change that love that I feel for her, snn duk emmatan da kake k'irgowa basu gaba na, ni ita na gani kuma nake so, fatana burina ta zamto mata *Mallaki Na*..... "So idan kana so relationship din mu ya dore kar ka kuma fad'in nasty things about her or else......" ya dan ja birki kafin yace " Ahidjo just leave pls, ka tafi dan Allah befor I hate you.
"Kad'a kai Ahidjo yayi kafin yace" Irfan bazan tab'a gajjiya da fad'a maka gaskiya ba..... don't make a wrong decision, choose wisely......● daga haka ya bud'e motar sa ya wuce●●●●●●●● Duk wnn abun da akayi Ahidjo yayi dialing wayan Azee ta gama sauraren komai.....
"Har ya fice daga gidan Irfan be dena bin motarsa da kallon mamaki ba, ikon Allah banda d'aurawa kai damuwa ina ruwansa da matar da ya za'ba, gajeren tsaki yayi gamida girgiza kai kafin ya wuce sashen Ammah.....β˜…


"Azee na gama jin wayan nan wani ihu ta kurma gamida zubewa k'asa ko zafin ciwon dake jikinta bataji ba, nan kuwa jini ya shiga bin k'afafunta...... "Shigowar Laila kenan a rud'e taga jini na bin k'afafun Azee burki tayi sabida abinda idanunta ya gane mata k'rjinta na faman lugude...... _Toh fa wata sabuwa inji en chachaπŸ˜‚_

"Ammah na zaune saman darduma ta idda shafa'i da wuturi yayinda Deejah keta faman jera mata kayan guga cikin wardrobe Irfan ya shigo da sallama, Deejah ce kawai ta amsa sallaman dan Ammah na tasbihi lokacin......" Sak'o suka aikawa junan su ta idanu kafin ya k'arasa ya soma tayata jeran kayan..... "Dan marairaice fuska tayi alamun ya daina tana mai masa nuni da Ammah dake lazimi.
"Satan kallon Ammah yayi dashike can gefe dasu take kafin ya matso kusa da Deejah sosai cikin sigan rad'a yake fad'in" Why? Bakiso Ammah ta gano ki ne, kina son mata kwacen miji......" Deejah ta turo baki saida ta saci kallon Ammah ta tabbatar hankalinta baya wajensu kafin tace a hankali" pls mana ya Irfan Ammah might hear us, ni dai babu ruwana....." Yanda tayi maganan sosai ta bawa irfan dariya, yana k'ok'arin maida dariyan Ammah ta mik'e tana k'ok'arin linke darduma.... da sauri Deejah ta k'arasa ta karb'a tana fad'in, Ammah barin linke maki.
"Ammah na murmushi tace"Khadeejah baki gajjiya,..... "Ammah takai dubanta ga Irfan wanda take kan masa magana amma inaa hankalinsa na kan Deejah duk wani movement nata yana kallo gashi sanye take cikin doguwar rigar atamoa wanda ya zauna d'aram a jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login