Showing 105001 words to 108000 words out of 159062 words
Chapter 36 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt
Turkey keda Sanata, shine yanzu bari su lik'awa d'anki.
"Burauban can salatin gauro, cewar Ammi, mik'ewa tayi gamida d'aukan mayafi ta dubi k'awarta tace" tashi zama bata same mu ba,...
"Haj Farida ta mik'e fuska fall murna take fad'in ina muka nufa. Ko amsa Ammi bata iya yi ba sai saukowa daga bene data soma, tun daga k'ofa take doka kirawa driver ya fito da mota.
"Haj Farida ta dubi Delu tace" Maza tashi mu tafi kece shaida, su Delu jiki na rawa an sami shigewa ta mik'e tabi bayan Hajiya Farida.....
"Basu zarce ko ina ba sai gidan Engr Nazif Mumtaz, tun daga waje Ammi da Haj Farida ke doka ruwan bala'i da masifa,.. "Laila na tsaka da faman gyaran d'akin mijinta taji hayaniya yak'ici yak'i cinyewa, tuni ta lek'o ta window dan gane ma idonta abinda ke faruwa aikuwa babu shiri ta nufo downstairs.
"Ammah da Hajja na parlor sukaji hayaniyar suma suka fito...
"Deejah da Nadiya dake kulle d'aki ana masu gyaran jiki tuni suma suka nufo waje...
"Huci kawai Ammi take yi tana karka'da k'wank'wanso haj Farida na tayata.
"Ammah baki na rawa tace "Lafiya haj Jamila... meke faruwa. "Laila taiyi saurin cewa mu shiga daga ciki mana...." Haj Farida ta katseta ta hanyar dakartawa da hannu kafin tace" ba zama mukazo yi ba, kayan d'anmu muka zo ansa mun fasa auren...."Daidai lokacin da Deejah da Nadiya suka iso wajen......"Idon Deejah ya sauk'a kan Delu, a fili ta furta Deluu... "Gaba d'aya suka juyo suna dubanta, Ammi ta watsa mata harara kafin tace" wann shine tabbacin ba k'arya Delu ta mana ba, kunsan juna tuntuni, d'ana yafi k'arfin auren shegiya maras asali balle tushe....." Maganganun Ammi ya girgiza zukatansu, Babu kaman Deejah wacce Jiri ke shirin kada ita, a zuciyarta ta maimaita kalman _"Shegiya maras tushe balle asali, shin itace shegiyar???_....
"Haj Farida taci gaba da fad'in" mun riga munsan komai, ashe ita ba 'yar gidan nan bane, farko ai d'ankune me sonta, shine kuka hanasa aurensa kuka lanjab'a wa namu d'an....." Laila kaman ta zuba ruwa a k'asa tasha dan farin ciki, wani kallon k'yama ta soma bin Deejah dashi... "Ammah cike da b'acin rai ta dakawa haj Farida tsawa" Ke maras kunya maras tarbiya, kar ku sake kuyi tunanin zaku shigo har cikin gidan nan ku muzanta wani...." karan da Deejah ta sakene ya dakatar da Ammah, tuni Deejah ta fad'i sumammiya, Nadiya tayi saurin rik'ota cikeda tashin hankali, Ammah ta dawo kan Deejah tana ambaton sunanta, tuni Hajja da Nadiya sun tallafe Deejah sun shige da ita cikin gida....
"Su Ammi kuwa basu fasa rashin mutuncin da suke kan zubawa ba, Laila ta yab'e baki ta dubesu tace "kunmin daidai dan ko nice bazan bar d'ana ya aureta ba..." Haj Farida ta watsa mata harara kafin tace" ba gulma muka ce ki mana ba, kaya zaku bamu....
"Laila da kanta tayi directing nasu har yanda kayan suke suka shiga jawo akwtuna....
"Hannun Deejah rik'e cikin na Ammah sanda ta farfad'o take fad'in" Ammah dan Allah ku kira min Aunty Larai, ku kira mun Aunty Larai.... daga haka ta kuma rufe ido lupp... Hankali tashe Ammah ta shiga neman layin Larai... kan kace me Aunty Larai ta iso gidan cikin tsananin tashin hankali.
"Sunyi jigum jigum a parlor Aunty Larai ta shigo da sallama, cikin tashin hankali ta soma tambayan lafiya babu wanda ya iya amsata cikinsu... jin muryar Aunty Larai a parlor yasa Deejah fitowa, da sauri Aunty Larai ta k'araso wajen Deejah, zata rungumeta Deejah tayi saurin dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu kafin ta soma fad'in" Asalina nakeso ki fad'a mun....."Gaban Aunty Larai yayi mugun fad'i, tunda suke da d'iyarta Deejah bata tab'a mata tambaya makamanciyar haka ba, "Aunty Larai tad'an sha mur kafin tace" wane irin tambaya kike mun Khadeejah, wani asalinki ne baki sani ba, na sha fad'a maki a zaizayan k'asa aka tsinceki......" Da sauri Ta katseta ta hanyar dakatarwa da hannu kafin tace" Aunty ki fad'a mun wacece ni, su waye mahaifana, shin da gaske a bola aka tsince ni banida mahaifa, shin da gaske ni shegiya ce maras asali....."Da sauri Aunty Larai ta toshe bakinta hawaye na bin k'uncinsu su duka biyu harma da sauran mutanen parlor su Ammah Nadiya da Hajja, idan ka d'auke Laila wacce ke binsu da kallon k'ask'anci....."Aunty Larai taci gaba da fad'in" Ke ba shegiya bace Deejah, kinada mahaifanki..." Cikin tsawan da batayi zaton zai fito mata ba ta furta" then where are they, ina suke ina kika tsince ni?..... Aunty Larai ta rik'e hannayenta suka zauna bisa carpet kafin ta soma fad'in" Deejah 'yata, na jima ina b'oye maki wann dad'dd'iyar sirri sabida tsananin sonki da nikeyi, amma yanzu lokaci yayi da zan sanar dake.
"Shekarun baya da suka shud'e, watarana na fito daga Orphanage na fito wajen sana'ata kenan, na hangi wata mahaukaciya tana nak'uda, na tausaya mata sosai, nan na k'arasa na taimaka mata har Allah ya sauk'eta lafiya, ni nasa hannu na d'auke ki sandan kika fad'o duniya, lokaci guda Allah ya jefa mun k'aunarki cikin raina, nayi saurin nad'eki cikin zani na nufi Orphanage dan banyi nisa ba dama, nan na mik'aki hannu abokan aikina na sanar dasu komai, snn na buk'aci su taimaka min mu koma wajen mahaukaciyar nan mu taimaka mata, hakan kuwa akayi, saidai kash.. sanda muka wajen bamu tarar da mahaukaciyar nan ba ta tafi....."kuka ya kuma kufcewa Aunty Larai, Deejah wacce hawayene kawai na tausayin kanta da rayuwarta ke bin k'uncinta, ta kasa komai sai hawaye, sai yanzu take tuna mafarkanta da wata mahaukaciya, ashe ita 'YAR MAHAUKACIYA CE kenan da gaske batada uba, tunda mahaukaciya kowa na iya tsareta yayi alfasha da ita...."mikewa tayi kaman zararriya ta shige d'aki a guje ta maida k'ofa ta rufe, durk'ushewa tayi wajen ta shiga rusa kuka mai tsuma zuciya........
"Babu yanda basuyi ba Deejah ta bud'e k'ofa tak'i bud'ewa, Aunty Larai kuwa kuka take sosai tareda danasanin fad'a mata wann sirri, su Ammah kuwa tausayi da al'ajabi ne ya cika zuciyoyinsu, sai snn Ammah ta tuna da batun masu d'aukan kaya, Laila tayi caraf tace" wllhi Ammah kar kiga irin hak'urin da na basu amma fir sunk'i yarda dole suka kwashi kayansu dan naji suna cewa zasu had'a da hukuma idan ba'a basu ba..." Ammah ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace" Shikenn yamafi sauk'i dan wann ko anyi auren babu kwanciyar hankali, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, ai dama ba sonsa yarinyar keyi ba, su suka tak'ura sai an basa, tunda haka suka zab'a shikenn, Allah ya bata wanda yafisa..." A fili Laila ta amsa da ameen a zuciyarta kuwa cewa tayi _Ba ameen ba, itada aure har abada_..."(kuji makirci irin na Laila).
"Suna fitowa da kaya basu zarce ko inaba sai gidan Hajiya Farida, Yesmin na zaune parlor taga ana shigowa da kaya mommy na directing nasu, da mamaki take bin kayan da mommy da kallo, baki sake tace mommy wad'an nan kayan fa, mommy ta mata alama da ido kan ta tattara kwalaban totalin din dake center table, da sauri ta tattara ta watsa bayan kujera, tana ganin Ammi tayi saurin k'arasawa ta rusuna tana k'k'arin gaisheta, Ammi fuska fal fari'a ta d'agota gamida rungumeta tace" Tashi tashi my inlaw,..." kaman a mafaeki haka Yesmin taji, wai Ammi ta kirata her inlaw, wayyo Allahn ta dadi kasheta, shikenan da gaske zata zama *Mallakin* Ahidjo,... "
"Yesmin da ita aka karb'i kayan lefenta, Ammi tace zata turo Ahidjo zance, Yesmin da mahaifiyarta ranan tamkar sallahn su haka suke ji dan farin ciki, burin su ya kusa cika.....
"Ko kad'an Engr baiji dad'in abinda ya faru ba, koda ya d'aga waya ya kira Senator Dad din Ahidjo sai ce masa yayi, shikenan shi babu abinda zai iyayi, idan matarsa ta yanke hukunci shikenan ya zauna, ran Engr ya kuma b'aci, ace namiji ya koma sakare bashida Say a gidansa sai abinda macce tace" girgiza kai yayi gamida fuzar da isa ya shiga tunanin ina mafita....
"Ahidjo ya galla wa Ammi wata harara kafin yace" Why Ammi, Why kin kuwa san abinda kikayi, sarai kinsan irin wahalan dana nasha kafin na samu amincewar Deejah, and now you ruined everything, kuma ma wai kina ce min Yesmin zan aura, yarinyar da babu partyn da bata zuwa a Malaysia Bushiya ma ake ce mata karewar iskancinta......" Ammi ta daka masa tsawa da fad'in" Yin min shiru sakare kawai, sabida ta shanyeka ko, ka fad'a mun me Yesmin ta rasa da zaka k'ita, Allah yasa itace uwar karuwan Abuja saika aureta, idan yaso idan an aura maka ita, ka kashe kanka...."Da mamaki Ahidjo ke kallon Amminsa, tun tasowarsa bai tab'a cewa yana son abu bai samu support dinta ba sai wnn karan...." mikewa yayi yana huci kafin yace" Ammi I swear you must pay for this...
"Harara Ammi ta watsa masa kafin tace" duk abu da zakayi kayi amma kam inaji ina gani bazan barka ka auri shegiya ba.....
"Saida ta bari gari yayi shiru sosai ta mike ta dau paper da biro tayi rubutu, a hankali ta fito daga d'akinta ta nufo downstairs, daidai kan center table ta ajiye note din da tayi, tana share hawayen idanunta ta nufi k'ofa a hankali, haka da sand'a ta bud'e karamin k'ofa ta fice, saida ta k'arewa Gidan kallo, kafin ta furta... " ku yafe mun but I really have to do this, bana da sauran feature a rayuwata, gwara nayi nesa daku dan tun zuwana nake saka ku a damuwa, share hawayenta ta kuma yi kafin ta soma tafiya...
"Wani irin razana yayi wanda yasa sa farkawa babu shiri, a fili ya furta Dee, da sauri ya dau wayarsa ya duba pass 12, shabiyi ta wuce, dafe kansa yayi wanda ya shiga sara masa, zuciyarsa ta gaza kwanciya, yana son sanin halin da Deejah ke ciki, lambar Nadiya ya shiga dialing, ,...
"Saida ta razana da ganin wayar yayan nata at this hours, tana d'agawa taji muryansa cike da tashin hankali, da sauri ya soma fad'in" Nadee ina Dee take..."Nadiya tayi d'an mika kafin tace" wllhi yaya you scared me, tana 'dakinta, ta k'i budewa kowa d'akin, so yake ya tambayi me aka mata amma kuma gani yake bashida wann lokacin, cikin sauri yace" Oya jeki dubo mun ita...
"Zatayi magana yace" just go straight banson complain and don't hang the phone oya jeki ina jinki...." mikewa tayi tana ture turen baki kafin ta zura slippers dinta ta bud'e k'ofa ta nufi d'akin Deejah....
"Ido Nadiya ta ware cike da mamaki sanda taga d'akin a bud'e, da sauri ta k'arasa ta shiga kiran sunanta tana buga k'ofan toilet... "K'irjin Irfan yaci gaba da dukan uku uku yana me sauraren Nadiya dake kiran sunan Deejah...cike da tashin hankali ya furta whare is she Nadiya....
"Girgiza kai Nadiya ta soma tamkar yana ganinta kafin tace" bata d'akin, am afraid she's gone. ?....
"WHAT???? ya furta da k'arfi kafin ya diro daga saman gadon, yana tambayarta ina ta tafi, what's going on there? Ya karashe maganar yana zura jallabiya.
"Nadiya da gaba daya ta zama lost, ta soma fadin, I don't know yaya.... da sauri Irfan yace Okay gani nan zuwa keep searching the house, daga haka ya katse wayar yayi saurin zaran car key....
"Azee dake kwance dakinta dan kwana biyun nan ta kasa gane kansa, sai ganin sa tayi ya nufi downstairs, a razane ta karasa gabansa tana tambayarsa " My one ina zaka at this hours lafiya... " Ko kallo bata ishe sa ba yasa kai ya fice......
QueenSamy ce...ππ½
[8/28, 14:14] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
74
*Β©Sameena Aleeyou....βπ½*
_Queen Samy Novels Forum.....ππ_
"Gudu yake bisa kwalta kaman me shirin barin gari, bai damu da yanayin da gari yayi na shiru ba kasancewar dare ya soma ja, 'kirjinsa na ci gaba da barazanar tarwatsewa, shi kadai yake sumbatu tamkar zararre, "No no Dee, I can't loose you, I just can't, wata zuciya ta soma tambayar sa kodai ta fasa auren Ahidjo ne, if not meyasa kurum zata bar gidan, toh wai ma kan wani dalili zata tafi.... "lokaci guda ya sake dialing numbern Nadiya izuwa lokacin gaba d'aya ahalin gidan sun tashi suna kan neman ta suna jimami, Engr tuni yayi waya ya sanar da hukuma masu patrol......
"Tafiya take tana hawaye, kalman na kuma yawo a kwanyanta da dodon kunnuwanta _She's a Barster shegiya ce ita, bata da uba_ wani sabon hawaye ya shiga wanke mata fuska.....
"Wasu samaruka ne guda biyu zaune can k'asa da layin daga gani kasan 'yan zauna gari banza ne, d'aya ya tab'a d'aya yana nuna masa Deejah wacce bata san da mutane ba, hasken streetlights ya haske ta fes suna kallonta, da sauri suka mik'e suna washe baki suka soma binta.
"Gabanta ne yayai mugun fad'i jin kaman ana biyota, nan ta soma sauri gashi yanda suke babu mutane sosai a wajen... "Cikin muryoyinsu na 'yan shaye shaye suka soma fad'in" 'Yan mata tsaya mana, tsaya mu baki makwanci munsan irinku bakuda shimfid'a.... sosai ta soma gudu gudu nan taji suma sun soma, karanto duk addu'an da yazo bakinta take tana me ci gaba da kuka...."Kaman daga sama ta hango hasken wutan mota ya haske su....nan ta soma addu'an Allah yasa me motan nan ya taimaketa....
"Cikeda tashin hankali ko parking me kyau baiyi ba ya diro daga motan lokacin samarukan sun cimmata sun soma k'ok'arin d'aukanta, ihu take tana neman taimako kan kace me sun toshe mata hanci da powder, luu ta fad'i sumammiya nan d'ayan yayi saurin azata a kafad'a....
" A guje ya k'araso wajen yana fad'in" let go off her, let her go...wani wawan naushi Irfan ya sake ma guda d'ayan saida ya fad'i sumamme tuni ya saki Deejah ta fad'i k'asa, aiko d'ayan na ganin haka yayi saurin janye d'an uwansa yana k'ok'arin guduwa...
"Cikin sauri Irfan ya shiga jijjigata yana kiran sunanta inaa bata amsawa, nan ya shiga fadin" you'll be fine Dee, no you can't leave me, Dee I still do luv you, I luv you......shiru yayi sanda ,ya lura da k'ofofin hancinta yanda suka bud'a mata powder, d'aukarta yayi tamkar baby ya saka bayan mota, kafin ya bud'e driver seat ya soma driving, tadiya kad'an sai ya juya yaga halin da take ciki, tunani yashiga yi, " Shin waima meye yasata gudawa wann karan, toh shima Ahidjon ta fasa aurensa ne, kasa nemo amsar tambayansa yayi dan haka gaba d'aya ya maida hankalinsa ga tuk'i..
"Gaba d'aya da mugun mamaki suke kallon Irfan sanda ya bud'e marfin mota ya fito da Deejah d'auke a hannunsa kaman baby, Azeeza na gefen laila sunyi famm kaman zasu fashe, wato kan wann shegiya karuwan ya fice yana b'arin jiki, cewan Azee cikin ranta,..."Laila kuwa kallon anya kina amfani da magungunanki tayiwa Azeeza.
"Su Ammah dasu Hajja suka k'arasa, suka hau tambayar Irfan lafiya ina ya samota, Engr na da sauri ya fito jin hayaniya yanda yake amsa intercom da Chief of Defense Staff,
"Irfan bai ajjiyeta ko inaba sai kan doguwar kujerar parlorn Ammah, ya dubi Nadiya yace kawo bargo a rufa mata she's having fever, da sauri Nadiya tayi yanda yace.
"Engr ya k'araso yana tambayan me ya faru a ina aka sameta, sai snn Irfan ya mik'e har lokacin idanunsa suna kan Deejah kafin ya dawo da dubansa ga ahalin mutanen dake wajen ya fad'a masu duk abinda ya faru..." Bud'an bakin Azee sai cewa tayi, Kaima dai my one ai da baka kula ka d'aukota ba, tunda rayuwar da ta zab'a wa kanta kenan........." Wani mugun kallon da Irfan ya watsa mata yasata had'iye maganarta.
"Irfan ya k'arashe fad'a masu komai, kafin yace" but Daddy Ammah meke faruwa ne har ta fice a daren nan wanda ba don Allah ya tsare ba da bumusan me zaije yazo ba,..
"Gaba d'aya hamdala sukayi idan ka dauke Azee da uwarta Laila...
"Kan kace me Laila tayi caraf ta soma fad'in" Uhm wai dan iyaln gidan Senator sunzo sun amshe kayan lefensu sumce d'asu ya fasa aurenta dan asalinta ya bayyana wann shi ne yasata yanke shawarin guduwa, shegiya ce ita batada asali uwarta mahaukaciya ce a bola ta haifeta....."Enough Laila, Engr ya daka mata tsawa kafin yaci gaba da fad'in" da girmanki da hankalinki zakina fad'in munan kalamai kan 'yar uwarki musulma, Deejah tanada iyaye, mune iyayenta mune danginta, kar na kuma jin koda wasa kin fad'i abu makaman ciyar haka akanta, ranki zaiyi mugun b'aci, daga haka Engr ya fice daga parlorn dan ransa yakai mak'ira wajen b'aci. Nadiya kuwa dad'i taji har ranta yanda Daddy ya sille Laila, dama ta sane mata daga ita har 'yarta.
"Irfan kuwa har ransa yaji zafin munan kalaman da laila ta fad'i gameda Deejah, meyasa iyayen Ahidjo zasu muzanta ta, batayi Deserving haka ba girgiza kai yayi kafin ya dubi Ammah dake shafe ruwa a fuska yace" Ammah you need to take good care of her... ya k'arashe maganar yana duba agogon hannunsa, gyd'a kai kawai Ammah tayi ba tareda ta furta komai ba, dan yau itama taga rashin hankalin Laila a fili
"Kofa ya nufa kafin yace zan dawo da safe insha Allah... da sauri Azee tabi bayansa tana fad'in saida safe mommy, ko iya amsata Laila batayi ba dan