Showing 30001 words to 33000 words out of 159062 words
Chapter 11 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt
tayi masu treating duk wani wounds dake a jikinsu, sosai suka tausaya masu da jin wnn labari nasu me cike da al'ajabi da tausayawa, Deejah da Ruqayya suna dakin Ruqayya a can tayi wanka Ruqayya ta bata kaya ta kintsa jikinta ta saka.
"Irfan ya dubi Sadiq yace" wato a gaskiya Sadiq samun mutane irinku a wnn zamani nada matukar wuya, thank you very much.
"Murmushi Sadiq yayi kafin yace" haba Irfan ka daina fadin haka pls ai duk wanda ya taimaki wani kansa ya taimaka. Irfan ya danyi murmushi yace hakane, wayan Sadiq ya amsa ya shiga neman layin Ammah, bugu biyu Ammah ta daga da sallama lokacin suna tsaka da zancen komawa station itada Engr. Jin muryan irfan yasa Ammah mikewa tsaye babu shiri tana fa'din" Irfan me ya faru daku daga ina kake kira, ina Deejah.
"Ammah calm down pls, muna nan lafiya muna kan hayanmu ta dawowa gida. Engr ne yayi saurin amsar wayan ka kara a kunnenesa.
"Ashe bakada hankali Irfan, tinda nake da kai baka taba ganin bacin raina ba koh, toh ina mai tabbatar maka karka kuskura kayi abunda zaisa raina ya baci, duk yanda kuke maza ku taho gida.... daga haka Engr ya katse ko sauraren Irfan baiyi ba. Lallai Ran daddynsa ya baci, bai taba jinsa cikin yanayi irin haka ba.
"Sadiq ne ya shigo dakin dauke da abinci yake fadin "friend bismillah fah kai bakaci komai har yanzu ba.
"Girgiza kai kawai Irfan yayi yace" na gode Sadiq hankalin iyayenmu ya tashi, we need to go, daga haka yasa kai ya fito, dole Sadiq ya biyo bayansa.
"A parlor suka tarar haukan Dada ya tashi sosai sai fama ake da ita, ta kankame Deejah tana fadin babu mai rabasu, Deejah kuwa sai kuka take dan sosai Dada ta kankameta numfashima da kyar take.
"Da mugun mamaki Irfan ke kallon lamarin, Mamie ta karaso wajensu da sauri take fadin" yanzu nakecewa Ruqayya ta kiraku, kuzo ku taimaka ku kwace Deejah hannun Dada. Sadiq ya karasa ya soma lallashin Dada yana mata wasa da en dabaru dan ya samu ya kwaci Deejah, wani tokari takai wa Sadiq saida ya kwanta, " kar ka kwace mun 'diyata, kar kazo kusa dani.... tana huci take fadin haka tana hararan Sadiq, nan fah ta shiga ma'kure wuyan Deejah tana fa'din " sun kashe mun diya sun kasheta...... " Ai a tamanin Irfan yayi wata tsalle dukda dingishin da yakeyi bai hanasa capko Deejah ba, suka shiga kokawa da Dada, ciko yakushi duk bai hana Irfan kwacen Deejah ba, Deejah kam bata san sanda ta rungume Irfan ta 'kan'kanmesa cikin jikinta, Ya Salam wani shokin ne kawai ya dirar wa irfan, sun jima a haka, a hankali ya zameta daga jikinsa, ya mata masauki kan kujera,Mamie ta dubi Ruqayya tace maza kawo mata ruwa ta sha, da sauri Ruqayya ta kawo mata cup din ruwa ta mikawa Irfan dake zaune gefenta, hannu Irfan yasa ya kar'ba ya dubi Deejah da har lokacin jikinta na 'bari sabida tsoron ma'kurin Dada data sha, in a soft voice yace" have some water, dago ido tayi tana kallonsa sai ta samu kanta da kasa masa musu, a hankali tasa hannu ta karba ta soma sha, Sadiq kuma tuni yayi ta maza ya shige da Dada 'daki ya kelleta.
"Sosai lamarin yabawa Deejah tsoro, haka kawai taji mahaukaciyar ta shiga ranta, haka nan dukda zafin makura datasha bata so aka raba ysakaninsu ba. Jikinta duk ya mace sabida shauki.
"Har waje su Mamie da Ruqayya suka raka su yayinda Sadiq yaja su zuwa gida......
"Safwan ne zaune gaban Yakumbo mahaifiyarsa nasiha take masa gameda da duniya," Safwan kaga ku biyu rak Allah ya bani daga kai sainmarigayi yayanka, gashi shima yau baya nan saura kai kadai, Safwan ina so kabi duniya a sannu sann idan ka tashi aure ka auri matar kirki, abu na gaba bance karka rinka zuwa duba Aziza ba 'yarka ce tinda 'yar wanka ne, amma ko kadan bana so kana alaka da wadann mutane dan basu da mutunci basu san mutunci ba.
"Ta'be baki Safwan yayi ya mike yana fadin, Yakumbo Aziza dai jikarki ne kuma yar yaya nane dan haka babu yanda za'ace mu rabu da ita ni kinga fita na ma can na nufa..... baki sake Yakumbo ke bin Safwan da kallo har ya fice tama rasa kalma guda a bakinta balle ta masa magana.
"Tunda suka karyo kwanan LifeCamp zuciyan Sadiq ta kuma jaddada masa anya Irfan ba 'dan Engr Nazif Mumtaz bane President na M&M Builders, wata zuciya tace ka dakata dai kaga yanda kuka nufa, da wnn tunani har suka iso makeken gate din gidan Engr Nazif Mumtaz.
"Sadiw ya dubi Irfan yace" dama kai dan gidan nan ne, murmushi Irfan yayi yace kasan Dad dina ne sanda ake hangame masu first gate.
"Nasansa jiya jiya yayi employing dina a company dinsa, mutumi mai mutunci da sanin darajan dan adam, murmishi kawai Irfan yayi ba tareda yace komai ba, Deejah kuwa cewa tayi a ranta tabbas kayi gaskiya Sadiq, Engr akwai sanin darajan 'dan Adam daidai lokacin da second gate ta gama zugewa ta bude dan da sensor na jikin mota take amfani.......
_Kuyi hakuri da mistake da ya faru a page 21, instead sai nayi numbering dinshi page 20, my mind was somewhere elseπ you guys should bear with me pls. Labarin bai canza ba daidai yake tafiyaππΌ_
πΈπ»Queen Samyπππ...........
[8/19, 06:25] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
23
"Sallaman su a kofar parlorn yayi daidai da jan hankalin illahirin mutanen dake parlorn, Irfan ne ya soma sako kafarsa da niyyan shigowa, Cikin tsantsan 'bacin rai wanda ya rufe idon Engr ko kula da yanayin Irfan beyi ba ya mike ya nufe sa, baiyi wata wata ba ya sau'ke wa Irfan lafiyayyar mari ji kake tasss 'karan marin da Engr yayiwa Irfan.
"Ba Irfan kawai ba harta su Ammah da Nadiya dake zaune cikin parlorn saida sukaji shock da wnn al'amari, Deejah da Sadiq dake 'ko'karin shigowa ai tuni suka kafe 'kafarsu ta kasa 'karasawa ciki.
"Da mugun mamaki Irfan ya dago yana duban mahaifin nasa sanda yake dafe da 'kuncinsa, abune da bai ta'ba shiga tsakaninsa da yaransa ba, lallai ran maza ya 'baci.
"Rai 'bace Ammah ta taso tana fa'din" meyasa zaka maresa Nazif, baka ganin yanayinsa ne, ka bari muji ta bakinsa.
"Engr na huci yake fadin" me zamuji me zaice mana, bansan rashin hankalin Irfan har yakai haka ba, au wato zamanka a turai har yakai ka dauki budurwa sukutum ka gudu da ita....." Ya isa haka! Ammah ta fadi cikin kakkausar murya hannu tasa ta ei'ko Irfan wanda har lokacin yake nan kaman mutum mutumi, je just couldn't believe it wai daddy ne ya maresa yau.
"Kasa zama Irfan yayi dan kuwa tuni fuskansa tayi jazur zuciyansa na tafarfasa, shi ba zafin marin bane ya damesa, no zargin da daddy ke masa ne, me yake nufi kenan, yana nufin shi din 'dan iska ne ko me. Rai 'bace Irfan ya juya ya fice daga parlorn gaba daya..... Kallo daya yayi wa Deejah ya dauke kansa zai wuce, itakam kasa kallonsa tayi, Sadiq ya soma binsa yana kiransa ko saurarensa beyi ba, sashemsa ya shige ya kulle kansa.
"Ammah ta riko hannun Deejah suka shige parlorn yayinda Sadiq ya take masu baya, Ko kadan Deejah ta kasa daga ido ta kalli Engr bata sani ba amma kullum girmansa a idonta karuwa yake, saidai yau abunda yayiwa Irfan sosai ya ta'ba zuciyarta.
"Sadiq! Engr ya kira sunan Sadiq yana mai kallonsa cike da mamaki, Sadiq ya 'karaso yana mai rusunawa yake gaida Engr. Nan Sadiq ya kwashe komai ya fa'da masu, nan fah Engr ya dada harzu'ka yana fa'din" banda rashin hankali irin na Irfan yanzu da wani abun ya samesu fa, snn ya kama ya dauki yarinya ya tafi da ita tayi kwanan daji fisabilillahi......Deejah kam tune ta sulele ta gudu daki dan kuwa kirjinta barazanr tarwatsewa take sabida bugawa da take da sauri da sauri dama har yanzu zuciyanta bata daina tunanin mahaukaciyar nan datayi ba, snn sai yanzu mafarkinta da takeyi da wata mahaukaciya ya dawo mata kwanyanta.
" Nan fah Sadiq ya shiga bawa Engr baki yana nuna masa faruwan hakan mu'kaddari ne daga Allah.
"Daga karshe Engr da Ammah sukayi godiya wa Sadiq kafin ya mike da niyyan tafiya, Amma tace a'a baka tafi haka nan ba baka sha ko ruwa ba... ta juya ko zataga daya daga cikin ma'aikata idonta ya sauka kan Nadiya dake bin Sadiq da wani asirteccen kallo dan kuwa sarai ta ganesa. Ehen yawwa Nadiya kawo masa abin ta'bawa Ammah tace tana mai kallon Nadiya, sai sann idon Sadiq ya sauka kan Nadiya for sure ya ganeta, maras kunyan yarinyar nan sunan da zuciyansa ta lakabawa Nadiya.
"A'a wllhi ba komai yanzu zan tafi ma ai, Sadiq yace yana dan shafa kansa. Engr yace no Sadiq ka zauna ka huta ka dan taba wani abu bazan ji dadi kazo har gidana ka tafi hakan nan ba, feel at home kaji.
"Babu yanda Sadiq ya iya dan kuwa Ogan nasa ya gama dauresa dole ya zauna ba don yaso ba, Ammah da Engr mikewa sukayi suka nufi garden din dake cikin gidan dan tattaunawa..
"Yatsina fuska Nadiya tayi sanda taga Sadiq ya daure fuska tamau kamar bai ta'ba dariya ba, Zama tayi ta mike fararen sawayenta ta saka earpiece a kunnenta ta shiga kwalawa Zulai kira... babu shiri Zulai ta bayyana a gabanta, a dakile ta kalli zulai kafin tace ki serving wnn, ta fadi tana mai nuni da Sadiq...
"Kutt, kaman ya mi'ke ya kai mata naushi haka yaji dan takaici, daba don kar ya fice Engr ya gansa ba da tuni yayi tafiyarsa.
"Cikeda ladabi zulai ta amsa kafin ta wuce kitchen dan aiwatar da umarnin Nadiya.
"Cikinsu babi me cewa kowa cikanka haka suke zaune a parlorn, banda sanyin ac da karar tv dake tashi a hankali bakajin komai sai kamshin gidan 'yan gayu dake wanzuwa cikin makeken parlorn.
"Zulai ta jere gaban Sadiq da kayan makulashe da tande tande da kuma shaye shaye... ko kalla Sadiq beyi ba balle yayi tunanin ci ko sha, jiran lokacin da ya diba yake ya cika ya tashi ya cika ma rigarsa iska.
"Wayansa ne tayi ringing take kyakyawan fuskansa ta cika da annuri ganin 'kanwarsa ce kuma sahibarsa me kira.
"Hello my little ya akayi ne, kinji shiru ko, kar ki damu na kusa dawowa.... yayi wata smile da zan iya kira killing smiling kafin yace I luv you..... Nadiya da earpiece ke manne kunnenta ashe gaba daya hankalinta naga Sadiqπ, yatsina fuska ta danyi tace ko ma waye wann zai gwada yanga oho. Haka kawai ta tsinci kanta da jin haushin wayan da yayi, a fusace ta mike ta tsaya a gabansa.
"Ko kallo bata isheshi ba balle ya tankata." Malam kaci abinda aka kawo maka ka tashi ka tafi pls dan nasan abunda ka zauna ci kenan, coz your presence irritates me.
"Sai snn Sadiq ya dago ido yana watsa mata mugun kallo cikeda tsana kafin yace" and who ordered anything da zakice naci abinda ya zaunar dani. Mind you karki nemi raina min hankali, karamar yarinya dake sai rashin kunya... ya girgiza kai kafin yace tir da hali irin naki, daga haka ya mike yasa kai ya fice daga parlorn... kallo ta bisa dashi gamida jan tsaki tana maijin haushin kanta meyasa ta masa shiru ya gaggaya mata maganganu yana yaron babanta. Rai bace ta nufi stirs.....
"Aziza ce zaune saman mota a parking lot ta fa'da kogin tunanin abin kaunarta da baisan tana existing ba wato Irfan, har Safwan ya gama parking motarsa a gefe Aziza bata sani ba, murmushi yayi ya karaso yanda take yana fa'din "Azee baby, tsalle tayi ta diro daga saman mota sanda ta jiyo muryansa taga ya nufo yanda take, da gudu ta tafi ta rungumesa tana fa'din" oyoyo Uncle Safff, hannunta ya riko suka nufi cikin gidan yana fadin" tunanin me kike ke kadai a waje.
"Juya ido ta waniyi kafin tace" Uncle Safff am in love..... Dariya Safwan yayi yace iyye ashe daughter na ta girma, who is the lucky guy.... Tayi wani murmushi tana juya ido kafin ta soma masa hiran Irfan...
"Hajiya nifa gani nake kamar aikin bokan nan bayayi ki duba ki gani har yanzu shiru, yace Engr da kansa zai nemeni gashi babu labari, anya kuwa bazamu canza boka ba, Laila ta fadi haka cike da damuwa.
"Dariya Hajiya Karima tayi kafin tace" kai dadina dake bakida ha'kuri kamar zawo, yo ba shekaran jiya jiya aka soma aikin ba, ki jira ki gani harta uwarsa sai mun basa izini ya gaisheta balle 'ya'yansa dasuke hanasa aure.
"Laila ta sau'ke ajiyan zuciya tace hakane Hajiya ai na yarda dake.... daidai nan Safwan da Aziza sukayi sallama suka shigo.....
πΈπ»Queen Samyπππ.......
[8/19, 06:25] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
24
"Yana nan har kusan 'karfe 5:pm a sashensa, zaune yake cikin lallausan sofa da ya 'karawa parlorn kyau da annuri, yana sanye cikin 'bakar riga maras hannu gaban rigan an rubuta _Armany_ wandon jikinsa kuwa three quater ne me ruwan toka, kallon tashan ball yake amma da alama hankalinsa gaba daya baya wajen. "Sai yanzu yake da'da jin tsanar mata a ransa, tsakaninsu da mutane babu komai sai sharri, bacin haka meyasa daddy zai masa mummunan zargi gameda Deejah, for goodness sake har ya gama zamansa a States bai ta'ba bin mace ba saida ya dawo nan, why on earth zaiyi haka a rayuwansa, tun tasowarsa tun yana 'karami daddynsa bai ta'ba 'daura koda 'dan yatsa a jikinsa da sunan duka ba sai gashi yau har marinsa yayi, and the most annoying thing din shine akan mace ya maresa. Hiss yayi gamida mikewa ya nufi yanda yake motsa jiki a cikin sashen nasa, ya jima akan keken motsa jikin har yanzu fuskan Deejah yake gani akanta daddy ya maresa har yake zarginsa. Tsaki ya kuma ganin bazai bar tunanin ba yasa sa daukan car key ya nufo waje...
"Deejah Nilam Amir da kuma Aiman ne zaune a farfajiyan gidan suna wasa kaman yanda suka saba mussaman dashike jiya sunyi missing dinta, ita kuwa hankalinta gaba daya naga sashen Irfan ko Allah zaisa ta gansa, dan ta 'kagu tasan halin da yake ciki.
"Aiko yana fitowa sukayi ido hu'du, yayi matukar yin kyau shigar ya kar'besa tamkar balarabe zalla babu surki haka ya fito. Kallo daya ya mata ya dauke kansa ko takan 'kannensa dake wajen bebi ba ya nufi parking lot.
"Nilam ce ta fara hangosa ta tafi da gudu ta rungumesa nan su Amir da Aiman ma suka mara mata baya.
"Ko kadan Irfan bai wani sake da 'kannen nasa kaman yanda ya saba ba, fuska a daure ya hamasu karasowa yanda yake, wann al'amari ne da basu ta'ba gani ba, dukda yayan nasu miskili ne amma ko ka'dan baya hantaran 'kannensa snn yana jansu a jiki yana tsananin sonsu, dan haka gaba daya sai suka sha jinin jikinsu harta Nilam 'yar gaban goshin nasa. Ita kanta Deejah saida abun ya mata wani iri dan bata ta'ba ganin yayi hakan wa 'kannensa ba.
"Ammah dake zaune kan resting chair a balcony sosai abin ya bata mamaki lallai ran Irfan ya 'baci, amma fushinsa bai kamata ya shafi 'kannensa ba.
"Cikin tsanaki yake tu'kin motar 'kirar _Camryy Anaconda_, bai tsaya ko ina ba sai Amigo, koda ya shiga zama yayi ya kasa ordering komai, kaman daga sama Ahidjo ya hangosa shima shigowansa kenan.
"Tun daga nesa Ahidjo yake fa'din" what a coincidence!
"Kallonsa kawai irfan yayi gamida yin kasalcecciyan murmushi wanda take dabi'ansa ne, Ahidjo ya saba da miskilancin Irfan tu a US dan haka baiji komai ba da ya masa haka.
"Guy what's up, Irfan ya fa'di sanda Ahidjo ke zama seat next to him. "Kallonsa Ahidjo yayi yana murmushi kafin yace" you will never change Irfan, will you?, na dauka Nigeria zai canza ka ashe nothing has changed. Kai na tunama ashe fada mukeyi da kai, I was waiting for you jiya zaka zo ka dauke ni, babu kai babu labarinka and your phone baya shiga, bakaga wuyan danasha ba, kai yesterday was awful..
"Har yanzu Irfan bai ce masa komai ba sai wasa da car keys dinsa da yakeyi, Ahidjo ya kura masa ido sai yanzu ya kalli alamun ciwo a jikin Irfan.
"Guy me ya same ka haka, why are you wounded.
"Au sai yanzu zaka tambayeni bayan ka gama zubannaka, Alright fine now that you asked zan fada maka, wadan nan ciwo daka gani is all because of you, zaro ido Ahidjo yayi kafin yace " ni kuma, ban gane ba Irfan pls spell it out.
"Kaman bazaice komai ba sai kuma ya labarta wa Ahidjo yanda lamarin