Showing 69001 words to 72000 words out of 159062 words
Chapter 24 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt
tanai masa kallon mamaki, me zaiyi da ruwa da towel.
"Sadiq kuwa fuska babu alamun wasa ya dago kai ya d'an dubeta yace" you heard me right, ki kawo mun ruwa da towel.
"A fusace ta fice daga parlorn tana fita kuka ya kufce mata, me ya Sadiq yake nufi, me ya dauketa, me yadauki soyayyansu data jima tana dakonsa, irin kallondata ga yanai ma yarinyar nan ya firgitata... zama tayi dirshan a wajen tana sharen kuka, ta ma mance da batun aikenta da Sadiq yayi.....
"Dawowan Mamie kenan ta tarar da Ruqayya zaune a tsakakr gida tana sharan kuka......
*kuyi hak'uri da wnn dearies idan na sami time da dare will continue..... luv you all*
_Queensamynovels๐_
[8/22, 14:47] Umar Dalha: ๐๐๐๐ *Mallakin Waye*
50
*ยฉSameena Aleeyou*
_Queen Samy Novel Forum.... ๐๐_
"Cike da manaki Mamie ke bin Ruqayya da kallo, ajiye kaya hanunta tayi kafin ta k'arasa ta dafata tana fad'in" Lafiya Ruqayya me ya faru waye ba lafia? Duka lokaci gud Mamie ta jefa mata tambayoyin,
"Kasa amsawa tayi sai wani sabon kukan da ya kufce mata.
Sadiq daya gaji da jiran Ruqayya a fusace ya fito daga parlorn.
"Mamie ta had'e giran sama da k'asafin tace" banson sakarci meke faruwa kinyi shiru, ko wani abin ne ya faru.... daidai nan Mamie ta hangi Sadiq rik'e da labulen parlor yana binsu da kallo.
"A'a Sadiq wai meke faruwa ne. Mamie ta bid'a, cikin sauri Ruqayya ta mik'e ta shiga goge hawayenta.
"Mamie sannu da dawowa ya fadi yana sauke hannun rigarsa da ya nad'e,
"Gajeren tsaki Mamie tayi kafin tace kun soma er fad'an naku ko, kunfi kusa ku kuka sani daga haj tasa kai ta wuce.
"Yakai dubansa ga Ruqayya wacce ta had'e fuska tamau shima babu alamun wasa a fuska a d'aure yace " ina abinda na aikeki?.... "Kiran da Mamie ta kwala wa Ruqayya ne ya katsesu. Cikin sauri Ruqayya ta wuce ta barsa nan tsaye.
"Mamie gani, ta fad'i tana satan kallon Nadiya dake mutsu mutsun tashi.
"Meke faruwa naga Nadiya a nan? Mamie ta tambaya.
"Yaya ne ya shigo da ita tana tangad'i na en maye, Mamie dama kinsan ta ne?
"Shiru Mamie tayi tana nazarin magsnganun Ruqayya kafin tace "ina Sadiq din..... "Kan ta gama rufe baki Sadiq ya shigo da bowl da towel. Mamie ta bisa da kallon "I need an explanation.... "Sadiq ya fada wa Mamie duk abinda ya faru nan Mamie ta gano musabbabin fushin Ruqayya kishin Nadiya take, tai murmushi ta karb'i towel da ruwan ta shiga shafewa Nadiya a jikinta, shi kuwa Sadiq yarrr yaji a jikinsa cikin sauri yabi bayan Ruqayya...
***********************
"Tun daga nesa ya hango motan Laila ns pake alamun shitake jira, gaban Safwan ya fad'i rasss! Yasan bazasu wanye ta dad'i ba muddin ta gansa da budurwa musamman da yanzu take k'ok'arin nema masa aiki a M&M Builders. Juyowa yayi ya kalli Yussy dake faman danna wayarta yace" My Yussy zanyi dropping naki a nan ki shiga adaidaita ki wuce gida da daddare zanje na sameki. "Galala Yusra ta kalle safin tace" Ban gane ka canza mind d'inka ba, inji daga gida ka d'auko ni da kasan baka buk'atana ai dabaka taho dani ba......" Oh pls mana my yussy calm down, don't get the wrong idea, Yakumbo na gani yanzun nan ta shige cikin gidana kinga idan ta ganni da budurwa kuma ai akwai matsal dama ta tak'ura saidai na koma can gidanta, kinga yanzu idan ta ganki zatasa dole na koma, pls mana my yussy you know I love you and I'm dying to be with you... ya k'arashe maganar yana jawo kunkuminta had'i dayi mata kiss cikin salo.
"Take Safwan ya jshe jikin Yusra da kalamansa da kuma salon soyayyarsa. A haka ya sami kan Yusra ta fice neman adaidaita. Saida ya kintsa kansa jikin madubin motar kafin ya k'arasa wajen Laila bariki๐ .
"Wani kallon sha biyu saura kwata Laila ta masa kfin tace" 'Dan cutie wai ina ka tsaya for goodness sake ka barni ina jiranka for almost an hour, kasan dai I hate to be waiting.
"Bude mata marfin mota yayi yana k'ok'arin tura kai jikin wuyarta yake furta" Haba giwar mata, daga zuwa babu wani kalamai masu dad'i sai k'orafi, kinsan halin Yakumbo yanzu haka ma daga wajenta nike ta kafe saidai na rik'a kwana a gidanta shiyasa na tsaya bata baki kinsan abinki da tsofi.. ya manna mata kiss a wuya yace I miss you cikin sark'ewan murya.
"Murmushi Laila tayi jin Safwan na k'ok'arin afka mata cikin mota yasata saurin turesa kafin tace" wait d'an cutie ko ka mance a waje muke..... Ya mik'e yana kashe mata ido d'aya yace" So ko kina tunanin d'an tsohonki kar ya ganmu ne, "Murmushin k'asaita tayi kafin tace " kasha kuruminka baya k'asa ma tun jiya ya tafi Holland.
"Safwan ya zaro ido waje yana murmushi yace kice yau apzamu kashe dare,.. murmushi kawai Laila tayi kafin tace" dama nan nayi niyyan zuwa amma dole naje gidan Hajiya yanzu dan akwai wani issue da zamuyi discussing nida ita very urgent. Zuwa nayi mu tafi dan kaima maganar ta shafeka. Shafa fuskarta Safwan yay kafin yace barin shigar da motata ciki sai ki bamu ride. Murmushi Laila tayi tana wani jshe masa ido guda. Yana fitowa ya shige front seat suka zuge glass dan kr agansu dashike glass din motar mai duhu ne.
******************************
"Bayan sun gama ganin gidan kai tsaye wani *Shawarma Spot* suka nufa, yana gama parking ya jiyo ya kalli Deejah data langab'e kanta jikin seat yace" my bride to be akwai problem ne? Girgiza mai kai tayi alamun a'a kafin tace" is getting late ya Irfan ya kamata by now muna gida kar hankalin Ammah ya tashi, kuma kaga su Nadiya might get worried tunda a sch muka rabu dasu though nace wa Mamie ta fad'a masu kazo ka d'auke ni.
"Murmushi Irfan yayi zurfin tunani da hankalin Deejah na burke sa yana d'aya daga cikin abinda yasa ya k'ara sonta da bata daraja na musamman cikin zuciyarsa. "Ya d'an turo baki yana kwaikwayon maganarta yace" so probably kinga Ammah tasan kina tareda Husband to be dinki definitely, so nothing to worry about, sauko muje..... "Girgiza kai kawai tayi tana dad'a turo baki tace" am tired fahhh Master bazan iya sauk'a ba,
"Toh fad'i fillings din da kike so, beaf or chicken. Ya fadi yana bude safe din cikin motarsa.
"A hankali tace duk wanda kake so nima shi nake so.
" 'dagowa Irfan yayi yana kallonta sosai ta burgesa, murmushi ya kuma yi kana ya fice, mintuna kadan ya dawo hannunsa rik'e da ledoji suka wuce gida direct.
"Yana gama parking saida suka sha soyayyarsu kafin ya mik'a mata laidanta har kofan sashensu ya rakata kafin yace bari ya wuce ya dan freshing up kafin ya shigo gaida Ammah,
"Har ta soma tafiya tajiyo sautin muryansa a hankali daidai saitin kunnenta yana fad'in" baby ko zamuje ki min wankan ne..... Zaro ido waje tayi tana kallon sa gamida jefa masa hararan wasa...., shi kuwa Irfan dariya yayi dan tayi abinda dama yakeso tayi juya idanunta, kantayi magana ya furta" I love you baby, daga haka ya wuce yana murmushi. Kallo ta bisa dashi har ya b'ace mata sonshi da k'aunarshi na d'awainiya da ita.
"Ammah na zaune a parlor tana kallon program din *The Dr's* Deejah tayi sallama ta shigo.... "Ammah sannu da gida, ta fadi sanda take k'arasa shigowa, Ammah ta amsa da yauwa sannu Khaddejatu, ina sauran 'yan uwan naki.
"Turus Deejah tayi jin tambayan da Ammah tayi mata, dan ita ta nata tunani su Nadiya sun tsufa a gida........
_Queensamynovels.....๐_
[8/28, 14:07] Umar Dalha: ๐๐๐๐ *Mallakin Waye*
51
*ยฉSameena Aleeyou*
_Queen Samy Novel Forum...... ๐๐_
*Wannan page d'in naki ne Mrs Haidar Waziri Allah ya bar k'auna... it's indeed a blessing having someone like you as a friend, May The Almighty bless you and your entire family ๐*
_Masu k'orafin ci gaban *Zubaidah* kuyi hak'uri yana nan tafe da zaran na idda mallakin waye insha Allah, lot's of luff guyz๐_
"Ammah su Nadiya basu dawo ba ta tambaya fuska cike da mamaki.
"Ah a, ince daga makaranta kike? Ammah ta jefo mata tambayar... "Eh na baro sch tun d'azu ya Irfan ya d'auko ni na d'auka by now suna gida.
"Gajeren tsaki Ammah tayi kafin tace" duk kun kama kun kashe wayoyinku, na kira wayoyinsu baya shiga har naki na kira bai shiga, shi Irfan din meyasa be d'aukoku gaba d'aya ba, inama kukaje da tsakar yamman nan, wato dan kunga daddynku baya gari bari ku tsira yawo ko......"Tunda Ammah ta soma fad'a idon Deejah ke kallon k'asa, da kyar ta iya furta "Kiyi hak'uri Ammah.....l muryanta na sark'ewa, "Maza kira min yayan naku Ammah ta katseta.
"Da sauri Deejah ta fice kiran Irfan.....
"Duk ta gama rud'ewa ganin ran Ammah sosai ya b'aci gaba d'aya bata tab'a mata fad'a irin haka ba, dan haka ko tunanin sallama batayi a kofan d'akin Irfan ba, kai tsaye ta danna kanta cikin d'aki....
"Yana tsaye gaban *closet* dinsa towel ne kawai d'aure a K'ugunsa yana shafe gashin kansa da shampoo alamun wanka zai shiga.... turo k'ofan da tayi yayi daidai da juyowarsa aikuwa nan sukayi ido hud'u...... "'kara ta sake gamida rufe fuskanta da tafukan hannayenta, jikinta ya soma rawa.
"Irfan kuwa abin sosai ya basa dariya ganin ta tsaya cak ta k'ank'ame idanunta ta kasa koda motsawa daga yanda take.
"Baby lafiya, ya tambaya yana k'arasowa gabanta..... "Still idanunta a rufe muryanta cike da tsoro take fad'in" Emm.... emm kayi hak'uri Master it was unintentional, I shouldn't have bang into your room, dama Ammah ce ta kazo..... Tana gama fad'in haka ta juya da sauri, juyawan da zatayi kuwa ta bige kanta jikin k'ofa.... "Irfan kuwa baisan sanda yayi kanta yana fad'in baby...... "Ai kuwa nan ta fad'o cikin k'irjinsa, Kallon juna suka shiga yi na d'an dak'ik'ai da sauri Deejah ta soma kiciniyan mik'ewa, cikin sauri shima ya saita kansa kana yace" hope dai bakiji ciwo ba, d'aga masa kai kawai tayi tasa kai zata fita sai jiyo muryansa tayi yana fad'in" be careful baby, am coming right away. Jallabiya kawai ya zura yabi bayan Deejah.
"Isowarsu yayi daidai da shigowan Mamie da Nadiya, da mamaki suke kallonsu gaba d'aya, yanayin Nadiya tayi sanyi sosai tamkar ba ita ba, Sadiq ne ya shigo da murmushinsa ya nufi yanda Irfan ke tsaye ya gaida Ammah kafin suka fice farfajiyan gidan shida Irfan.
"Ammah tayi wa Mamie sannu da zuwa Nadiya ta sha jinin jikinta sosai ganin irin kallon da Irfan yayi mata, tasan yau sai ya kusa b'allata a gidan nan, da sauri taja hannun Deejah suka nufi backdoor.
"Mamie bata fad'awa Ammah asalin abinda ya faru da Nadiya ba, saidai tace mata ita ta tafi da Nadiya gidanta bayan an tashi a sch. Ammah ta d'an nuna rashin jin dad'inta dan kuwa at least ko waya ita Nadiyan zatayi ta sanar zata gidan Mamie, Mamie tayi apologizing unbehalf of Nadiya.. ...
"Suna tsaye a backdoor tana narrating abinda ya faru wa Deejah, Deejah ma tana bata labarin fad'an da Ammah tayi suka jiyo muryan Ammah na doka masu kira. Cikin sauri suka k'araso sai snn Deejah ta sami zarafin gaida Mamie Nadiya kuma ta gaida Ammah.
"And where is Azeeza? Ammah ta tambaya tana dubansu, Deejah ta kalli Nadiya, Nadiya ta kalli Deejah..... "Ba magana ake maku ba! Ammah ta kuma daka masu tsawa.
"Nadiya ce tayi saurin cewa Ammah wllhi a sch muka rabu da ita tace Aunty ta kirata a waya bansan ko gidan Hajiya ta wuce ba
"Ammah ta gyad'a kai kafin ta ciro waya ta shiga neman layin Laila, bugu biyu Laila ta d'aga cikeda ladabin munafunci. Ammah ta tambayeta ko Azeeza na gidan Hajiya tareda ita.... cikin inina Laila ta amsa da Eh.... eh Ammah gata muna tare a nan wani abu ne? "Ammah tace" a'a no ba komai next time dai idan zata wuce can gidan sai ta fad'a kar hankula ya tashi.
"Laila ta amsa da toh Ammah zan mata fad'a, kiyi hak'uri.
"Ammah tana gama waya Deejah da Nadiya suka kalli juna, haka kurum sukaji basu yarda cewa Azee gidan Hajiya ta wuce ba, sosai Mamie da Ammah suka masu nasiha a matsayinsu na emmata kafin suka haye sama suka bar Mamie da Ammah na hira akasarin hiran gameda jinyar Dada ne, Ammah tace insha Allah zanzo na dubata ban tab'a zuwa ba. Mamie tayi murmushi tace" haba dai ai babu komai, Jibi ma za'a wuce da ita can garinmu Daura wajen mai magani zata kwana biyu a can.
"Ammah tace dama ku en Daura ne, Mamie ta amsa da eh Ammah daga can muke.
"Allah sarki toh kuwa ai daga jiha guda muke dan muma asalinmu 'yan Katsina ne, "Mamie tace Allah sarki ashe abin duk abu guda ne..... suka suka b'arke da hira sosai..
"Har saida su Mamie sukayi sallahn Magrib kafin suka wuce...
"Nadiya da Deejah kuwa sun k'ule a d'aki suna hiransu, akasarin hiran Nadiya keyiwa Deejah gameda abinda takeji akan Sadiq, I zuwa yanzu kam ta gama yarda sonshi take with all her heart.
********************************
"Wani pills Ahidjo ya ciro cikin drawers ya mik'a wa Azee yace "oya shanye.... "Kallonsa take cike da mamaki kafin ta yamuysa fuska tana mai girgiza kai tace ban gane ba?
"Mayaudarin murmushi yayi kafin yace" bazaki gane ba sai kin farka kin ganki da ciki nan ne zaki gane idan Irfan yak'i aurenki.
"Murmushi Azee tayi ta karb'i pills d'in ta jefa a baki ta had'iya da ruwa kafin tace" toh ai kaine baka min bayani ba, shiyasa nake ji da kai kasan kan hark'a, mayaudarin murmushi ya kuma yi kafin ya kuma jawota cikin jikinsa yanai mata wasu salo yace" sweet girl yanzu haka zaki tafi ki barni, kinsan zanyi kewarki anya ma kuwa zan iya kwana ba tareda ke ba.
"Turesa Azee tayi tana me ci gaba da gyara zip d'in rigarta tace" baka ganin dare ya soma yi ne, za'a nemeni a gida, a kunnan ac ka rufe ko ina gaba d'aya ban gane dare yayi ba, com on ka tashi kayi dropping dina gidan Hajiya pls ni yau canma kawai zan kwana........ "Kan ta gama rufe baki wayarta ya soma ringing kunnawanta kenan... ganin Momynta ne me kira yasa gabanta mugun fad'uwa tasan tayita kiranta bai shiga. Da k'yar ta saita kanta kafin ta d'aga wayar.
"Hello momy........
"Dan ubanki gidan uban wa kikaje kika zauna har iwar haka da baki koma gida ba, Laila ta katseta da fad'in haka.
"Azee murya na shaking take fad'in" momy fah gidan Hajiya naje......."Hajiyar uwaki, munafuka gani nan a gidan Hajiya ina kika shiga. Toh dama duk yanda kike kiyi maza kizo gidan Hajiya ki sameni daga haka ta katse wayan.
"Ai kuwa cikinmsauri ta shiga tattara komatsanta ta cusa cikin jaka, Ahidjo ya jawo side drower ya ciro bandir d'in 'yan dubu dubu wato hundred thousand ya saka mata cikin jakar yace muje nayi dropping naki baby.
"Sai kallon mamaki Azee take binsa dashi lallai Ahidjo d'an masu maik'o ne, ai kuwa ta samu wajen samun kud'i, cikin sauri suka wuce mota shima Amminsa tai masa waya tana son ganinsa,.
"Safwan ya kuma jawo Laila cikin jikinsa snn yace" giwar mata ki kwantar da hankalinki nasan Niece d'ita is a good girl, she'll take good care of her self, she will soon arrive here safely, yanzu yaya batun namu zaki bini mu tafi ko dan kinsan I can't afford to miss you to night..... ya k'areshe maganar yana kashe mata ido guda.
"'Dan turesa Laila tayi kafin tace" haba dai Safwan ai yanzu kam 'yarka ta b'ata mana plan d'inmu dole na jirata ta iso nan snn ni na koma gida na kwana, idan yaso gobe sai ka dawo da Azee can gida kaga babu wanda zai zarge mu.... ni kuma nai maka alk'awarin samun farin cikin kasancewa dani.
"Murmushi Safwan yayi ya shafi wuyanta zuwa k'irjinta yana wani kashe mata ido guda kafin yace" dui yanda kika ce sarauniyar mata. Murmusawa Laila tayi kafin tace" kadaiji abinda Hajiya ta fad'a maka aiki sosai zaka mana a company din nan bamu so gane ka, har sai ka samu shiga sosai wajen Engr.
"Ki kwantar da hankalinki idan dai wnn anyi an gama Engr Nazif sai ya yarda dani fiye da yanda ya yarda da d'ansa Irfan. Zanyita cin dunduniyarsu har sai M&M Bulders ya zama *Mallakin mu*.
"Dariya suka fashe dashi gaba d'aya uwa babu kwab'a.... _Allah ka tsarkake mana zukatanmu ka kiyashemu aikata danasani.....Ameeen!_
"Sosai Laila tayi fad'awa Azee kan abinda tayi harsaida Hajiya tasa baki,
"Alhaji Ma'aruf dake kwance kan gadonsa kallonsu yake hawayen takaici na gangaro masa _Allah sarki rayuwa, wann shine barewa bazatayi gudu 'yarta tayi rarrafe ba, wnn shine illan zina takanbi zuriya gaba d'aya, tun daga kan kakar har jikan abu guda suka tashi a kai, kaico