Showing 120001 words to 123000 words out of 159062 words

Chapter 41 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10417

bacci ta soma ji.


"Koda ya fito parlor ya kasa runtswa, banda juyi kan kujera baya komai, meyasa zaiyi haka, me yasa baiyi bincike ba ya yanke hukunci, he was totally stupid, now that the truth came out Allah sa Deejah zata iya yafe masa, he's ever ready ya d'auki duk wani punishing nashi da zatayi amma banda maganan su rabu, he will never ever do that...... "Karan wayarsa ne ya katse masa tunanin da yake, Ammah ce mai kira, jiki babu k'wari ya mik'a hannu ya d'au wayar. Kaman mai bacci haka yake magana
"Ammah tasha jinin jikinta dan gaba d'aya taji yanayinsa wani iri, "Irfan lafiya dai ko, ko har kunyi bacci ne na tasheku dan nasan ku a can dare ne yanzu.
"Dan jimmm yayai kafin ya k'ak'aro murmushi yace" Lafia lou Ammah, ya kowa da kowa.
"Ba don ta yarda dashi ba tace" duk muna lafia, ina Deejah, how's she.
"Tana,... tana lafia.
"Ammah ta d'anyi jimm kafin tace "Irfan are you telling me the truth, me ya sami Khadeejah ka fad'a mun ko har yanzu baka daina mummunar zargin da kake a kanta bane, Ammah ta bid'a (don dama ita kad'ai tasan halin da Deejah da Irfan ke ciki, bayan su Laila da suka shirya abun).
"Girgiza kai yayi kaman tana ganinsa kafin ya soma fad'in" Ammah I can't hide it from you, Deejah is not what I was thinking,... sai kuma ya d'anyi shiru.
"Ammah ta gyara zama sosai kafin tace uhum inajinka me kenan ya faru.
"D'an sosa k'eya yayi kaman tana ganinsa kafin ya soma fad'in" I... I.... cikin kame kame ya fad'awa Ammah duk yanda abun ya kasance har shan maganin da yayi, da kuma irin fushin da Deejah tayi dashi.
"Wani dad'i maras misaltuwa shi ya ziyarci zuciyar Ammah, haka kurum taji ta kasa b'oye farin cikinta, dukda a wani b'angare na zuciyarta taji haushin abunda Irfan yayi.
"Sosai ta masa fad'a ta nuna masa rashin kyautawan sa. "Kaga irin abunda nake fad'a maka koh, Irfan kanada kafiya akan abu, yanzu ga irinta nan, haka kaita wahalar da baiwar Allahn nan kan laifin da bataji ba bata gani ba, ta min daidai ko meye ta maka, maza maza ka dawo min da ita Nigeria ka bata takardan ta na sama mata miji daidai da ita.....
"Mik'ewa yayi a zabure kafin ya soma fad'in" Haba Ammah kema haka zaki ce, Ammah yaushe kika daina sona, ai de kinsan nida Deejah mutu ka raba ne, wllhi mutuwa ce kawai zata rabani da Dee, she's brearh my inspiration my everything....."Ammah kam baki sake take auraren jikan nata yanda duk ya susuce lokaci guda, lallai shakka babu Irfan na tsananin son Deejah.
"Dakatar dashi tayi tana fad'in" Ni yimin shiru d'an soyayyan k'aniya da ba wulak'anta ta kake ba, maza bani Deejahn let me talk to her.... "Kallon k'ofa yayi kaman zullumin wani abin, a hankali yace" Bacci take I promise zan had'aku gobe.
"Ammah ta murmusa kafin tace" fine k'yaleta tayi barcinta, sai goben insha Allah....
"Har zatayi hanging sai kuma ta kira sunan sa ina a serious form kafin taci gaba da fad'in" Take care of Deejah, take good care of her, I know u can do it son Allah maku Albarka ya azurtaku da zuri'a d'ayyiba....."Har cikin ransa yaji dad'in addu'an da Ammahnta masu har baisan sanda murmushi ya subce masa ba, a fili yace" I'll insha Allah Favorite Granny, regads to all I luv you... "Murmushi tayi itama cike da jin dad'i kafin tace I luv you too sweetheart kisses.... daga haka sukayi sallama.
"Wanna dai addu'an da Ammah tayi masu na samu zuri'a d'ayyiba shi yayita yawo a kwanyan Irfan dad'i ya mamaye zuciyarsa da haka bacci mai dad'in gaske yayi awon gaba dashi.....


"Washe gari bai fita ba saida ya tabbata taci abinci tasha magani, dukda bata kulasa bata masa magana bata amsa sa, dukda tsananin son kasancewa da yake da ita dole ya d'anyi nesa da ita gudun kar yayi provoking nata ta sake rikice masa, hakan yake binta tamkar k'wai a hannun yaro,
"Yana gama bata abinci ya mik'e gamida pecking goshinta yace" My Dee I'm off to work, pls takecare of your self kinji baby, and if you need anything just give me a call I'll be right here kinji. "Ko kallonsa batayi ba balle ta amsa sa, yasan bazata amsan ba dan haka salin alin ya mik'e ya d'au briefcase d'insa ya fice, yana ficewa ta raka sa da harara gamida ja d'an gajeren tsaki, jibi yanda ya wani canza lokaci guda, wata zuciya tace bake yake so ba jikin ki yake so, take ta kuma jin wani haushin Irfan ya tokare mata mak'oshi, tunowar da tayi da plan d'in datake ka shiryawa yasata sakin wani murmushi gamida kunna tv.


*Nigeria*




"Kanbuuuu wai wacce shegiyar zaka aura Safwan, danma rainin hankali baka tashi fad'a min ba sai yanzu mekenan kake nufi....."Tsaki Safwan ya buga gamida fad'in" Just shut up Laila, how dare you scold me that way, ke uwata ce da zaki sakani gaba kina min yelling aka, wait a moment me kike nufi kar nayi aure kenan na k'are rayuwata a kwartanci, aurena bayana nufin k'arshen alak'armu kenan ba kaman yanda aurenki bai hanamu kasancewa tare ba. Snn da kike cewa wata 'yar shegiyar zan aura wann shegiyar ne dai wacce sirrinki yake tafin hannunta, kar ki mance I'm doing this for both of us, ni ke da kuma 'yarmu Azeeza, Yusra is so desperate I'm pretty sure idan ban aureta zata iyayin komai, yarinya d'aya nake so duk fad'in duniyar nan ke kanki kin sani Deejah is d luv of my life, dole ne yasani auren Yusra ba don naso ba, ki gode ma Allah don taimakon ki nayi kuma wllhi ba saboda ke nayi ba saboda Azeeza ne, if not because Azee dana bari asirinki ya tonu tunda kika kasa saka mijinki ya amince ya turani Manchester ya tura d'ansa. Duk wani shirin samun kud'in da nayi ya rushe, you ruined everything Laila.....
"Goge zufan da ya keto mata a goshi tayi kafin tace" Safwan that's is enough, kaima kasan nayi maka hallaci, maganan tafiya kuma wllhi bani bace wann shegen d'an iskan mijin Nadiyan ne ya tak'ura saidai antura Irfan, kasan yanda Engr ya yarda dashi ya d'auki komai ya basa ya amince dashi, amma kar ka damu akwai wasu ways muda muke shirin *Mallakn* gaba d'aya company d'in, Hajiya tace mu d'an bata lokaci she's planning something for us. "Tabe baki yayi kafin yace idan kin sami chance kizo ki sameni wann maganar bata waya bace akwai abubuwa da yawa da ya kamata muyi discussing. Bai jira cewarta ba ya katse wayar gamida jifa da ita. Abun duniya duk ya damesa gashi bai samu chance din da yake son samu na tafiya k'asar Manchester ba don da ya sayar da M&M Builders ga maganan auren Yussy da idan ya tuna yakeji kaman ya kurma ihu, ga Deejah ta kufce masa har abada bayan duk sharrin da ya mata da alama it doesn't worked out. Tsaki ya kuma yi a karo na biyu gamida kwanciya cikin kujera.










"Yau ta kama d'aurin auren Ahidjo da Yesmin buduri iya buduri anyishi, amarya dai harda had'a shisha night, ba zallan shisha aka sha a wajen ba kayan maye aka dinga bugawa, harta lokacin da aka kai Yesmin gidanta layi take alamun a buge take,


"Har wajajen k'arfen goma yana tare da Azee suna watsewar su, Azee ta dubesa tana shafa hab'arsa tace" Hidjo guy amaryafa tana jiranka ya kamata ka tashi ka tafi, wani tsaki Ahidjonya buga kafin yace" dan Allah ki daina tuno min da wann ashawon, amarya ko saura......"Azee ta kwashe da dariya kafin tace " isn't that what you deserve hum? Haba nawan don't be ridiculous ai shege sai shegiya, daidai da kai kenan...." Harara ya narka mata gamida tsalle akanta ya danneta gamida cuikwiyeta ta ko ina...."Dariya Azee keyi tana fad'in" Easy honeyboo tana masa nuni da cikinta take fad'in kar kayi wa abokinka asaran d'ansa.
"Dariya Ahidjo yayi gamida mik'ewa yana fad'in wani pankon cikin naki, ke ni ban yarda da ka'daicewar mijinki da masoyiyar sa Deejah ba, nasan mutumi na yana can yana cin amarci ke kina zaune a nan da pankon cikin k'aryarki gwara ma tun wuri kisan halin da suke ciki......Jikin Azee yayi sanyi kuma gaskiyar Ahidjo ne lallai tayi wautan barin Deejah tabi Irfan tuni hankalin Azee ya tashi nan ta lalub'o waya ta soma neman layin Irfan amma sai taji baya shiga.
"Ahidjo ya gama d'aura belt d'insa yana had'e buttons din rigarsa yake satan kallon Azee yanda damuwa ya nuna a fuskarta, murmushin mugunta yayi a ransa kafin yace a cikin ransa" _ba ni kad'ai zanji bak'in cikin rasa Deejah ba kema ki d'and'ani naki bak'in cikin na rashin Irfan_... Daga nan kiss ya manna mata a goshi kafin yace "toh baby girl sai kinji daga haka ya fice Azee kuwa ko zarafin amsa sa bata samu ba ta fad'a duniyar tunanin mijinta.






"Tun yana mota Ammi take masa waya tana balablesa da masifa wai Yesmin ta mata waya tana kuka har yanzu baije ba ya barta ita kad'ai, 'dan gajeren tsaki Ahidjo yayinkafin yace" Ammi am on my way there na tsaya saya mata abinci ne, "Toh dama maza maza kaje kar ka bari na sake maka waya, daga hakanta katse wayar.
"Gajeren tsaki yayi anfili ya furta "Bitch".




"Tun daga gate k'aran sauti ya cika masa kunne, bai gama shan mamaki ba saida ya bud'e k'ofar parlor nan ya hangi amaryarsa daga ita sai pant da brazier sai tik'an rawa take kaman Allah ne ya aikota tana yi tana kora kwalban Totallin......






Sameena ceπŸ‘ŒπŸΎ


πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*



86


*©Sameena Aleeyou....✍🏽*


_Queen Samy Novels Forum....πŸ“–πŸ“š_




"Kallon ikon Allah Ahidjo ya tsaya yi, shi ko a film bai tab'a jin labarin amarya irin wann amaryar tasa ba, wani haushi da takaici ya tokare masa mak'oshi, d'if ya kashe socket d'in fuska a tamke kaman bai tab'a dariya ba.
"Yesmin kuwa sai lokacin tayi noticing Ahidjo ya shigo, karairaya ta soma gamida k'arasawa kusa dashi tana k'ok'arin kwantowa jikinsa take fad'in" Awww honey when did come in, banji shigowar ka ba I was busy celebrating...."Dakatar da ita yayi alamun kar ta kwanta masa a jiki kafin ya soma fad'in" Are you mad, are you insane, are you stupid, are you daft hum,... uban wa yace maki ki k'ure min kid'a a gida ko ce maki akayi nan club ne huh??? Mugun kallo ya kuma watsa mata kafin yace" this should the first and the last warning wllhi kika yin abu makamancin haka nida ke ne, idiot kawai, ya k'areshe maganar yana hayewa stirs..

"Jar ubancannn!!!! Haka Yesmin ta furta a zuciyarta, kaji wann k'aramin d'an iskan zai nemi raina mata hankali, ita yake kira stupid insane lallai kuwa zata koya masa hankali, ko cemasa akayi bata san duk wani movement nasa bane a garin nan, murmushi tayi gamida kora kwalban totallyn dinta kafin ta bi bayansa.


"Yana tsaye d'aki yana cire agogon hannunsa yaji an banko k'ofa kaman z'a b'alla, full of surprised yake binta da kallo, yama rasa me zaice. Bai ankara ba saiji yayi ta shak'o kwalan rigarsa tana watsa masa harara take fad'in" Ahidjo Sani Na Allah, kai kayi kad'an wallhi kaci mutunci na, am quite sure kanada labarin wacece Yesmin Anka, kasan inada kunne inada ido a ko ina a cikin Abuja, nasan duk wani iskancin da kake yi a garin nan, idan kaji ana mai 'yammata mai samaruka mai 'yan daudu toh Shakka babu Yesmin Anka ce, tai wani murmushi kafin taci gaba da fad'in " Ko kana so yanzu haka ma na fad'a maka daga yanda ka fito ne, wajen karuwar ka Azeeza ko....."Yanzu kam lamarin Yesmin ya soma bawa Ahidjo mamaki, wani murmushi ta kuma yi ganin tarkonta ya kamasa kafin taci gaba da fad'in" But don't worry honeyboo your secret is safe with me, but only in one condition, condition dina kuwa ba komai bane illa ka yi min biyayya, just do as I say, idan ka sab'a kuwa tayi wani murmushi tana tangad'i tana juya ido irin na 'yan maye kafin tace " Your best friend Irfan will learn everything, and when I said everything I mean yeah everything. Just obey my rules buddy..... tana kaiwa nan ta shiga kissing d'insa kaman wata tsohuwar mayya, tun Ahidjo yana tureta har yaji dai abin nata ba nak'are bane, hankad'asa tayi ya fad'a kan gado kaman wata zakanya haka ta shiga fincikan botiran rigarsa tana yi tana lashesa kamar mayya. Shikam Ahidjo ya kasa katab'us don tsoronta yake ji gani yake kaman had'awa da bakinsa zatayi ta cinue fatar sabida yanda take sunbatar sa. Kan ya ankara sai ganin Yesmin yayi tayi tsirara d'an panta da bra din ta cire, ashe dama bra d'in ne ya d'an rik'e nonuwan nata da duk sun zube tamkar wacce ta shayar da mutum goma abin dai babu kyaun gani balle ya birge balle ya baka sha'awa, tuni Ahidjo ya runtse idanunsa don baison ganin jikinta ko kad'an, shi harga Allah ma k'yama ta basa.... salon da yaji Yesmin na masa ba kad'an ya firgitasa ba kai shi duk iskancinsa wann yarinya taci uwarsa,... A wann dare dai Ahidjo yaji jiki wajen Yesmin dan kuwa tabbas fyad'e ta masa, da k'yar ya k'waci kansa dukda haka Yesmin bata daina sudz'e jikinsa tana tura masa jikinta kaman wata mayya, ai a sittin ya samu ya arce daga d'akin don dole yaje yayi jinya shakka babu yau sai yasha maganin gajjiya...








*England, Manchester*




"Yau kwana hud'u kenan ta warke ba kaman da ba, wajen ya rage mata ciwo, yanzu babu abinda ke gabanta illa ta aiwatar da abinda take tunani shine mafita a gareta.
"Shi kuwa Irfan a kullum kwad'ayin kara kasancewa da ita ne ke azalzaln sa, yana tsananin buk'atar matarsa, baik'i ya kasance da ita koda yaushe ba, duk dare kuwa idan ya kwanta sai yayi mafarkin yana saduwa da ita, gashi k'wak'waran magana bata masa, idan ya matsata da magiya tashi take ta bar masa wajen ko ta saka masa kuka, kukan ta kuwa yafi komai d'aga masa hankali, dole yake nesa da ita ba don yaso ba, idan ka gansa sai ka tausaya masa duk ya rame yayi bak'i ya fita hayyacin sa, harta Alhj Abdullah saida ya tambayesa meke damunsa, kawai saidai yace canjin yanayi ne.


"Tunda suka shiga meetin d'in Alhj Abdullah yake nazarin Irfan gaba d'aya he's not with them bai tare dasu he must be somewhere far away, jikinsa yana basa Irfan is going throug a difficult time shakka babu wani babban lamari na damunsa, tausayinsa ya cika zuciyar Alhj Abdullah dan shima yakan shiga yanayi irin haka mussaman idan ya tuno tsohuwar matarsa.
"Haka kurum yaji zuciyarsa ta yanke, Deejah ta fad'o masa a rai, tabbas ya mance yau bai rufeta ta waje ba, anything might be possible tunda tasha fad'a masa ita zata tafi Nigeria, da sauri ya soma girgiza kai shi kad'ai kaman wani tab'bb'e yana fad'in" No...no..no that can't be, kaman wanda aka zabura sai gani sukayi ya mik'e ana tsaka da meeting, excusing kansa yayi gamida ficewa cikin sauri. Sauran participant d'in zasuyi magana Alhj Abdullah ya girgiza masu kai alaman a'a kafin yace" let the meeting continue... "Zuciyarsa na tunanin halin da Irfan ke ciki har aka k'arashe meeting d'in shima bai wani fahimce komai ba.








"Bai ko tsaya kiran mai taxi d'insa ba, boss stop ya wuce kai tsaye ya shige, daidai street din Hilton Hotel aka sauk'esa, gudu gudu sauri sauri haka yake tafiyan, addu'a kawai yake cikinn zuciyar sa Allah yasa lafiya, receptionist tana masa welcome sir, ko amsa ta bai tsaya yi ba ya shige lift, nan ya dann floor dinsu cikin sauri hannunsa har b'ari yake, ga k'irjinsa dake duka tara tara, gani yake kaman lift d'in ma bai aiki hankalinsa duk ya gaza kwanciya, yana isowa floor din ya wani fice a guje daga cikin lift d'in ya nufi room d'in su......"Cak yaja ya tsaya yana kallon abin mamaki, a bu'de ya tarar da k'ofar, girgiza kai ya soma yana ja da baya yake fad'in" No... no,..no it can't be, no this is not possible.... A guje ya shige cikin d'akin yana fad'in" Deee... Deejah!!! Deee whre are you, bata bedroom bata bathroom, kaman wani zararre hakanya fito a guje yana sunbatu shi kad'ai...."No Deejah you can't do this to me, you can't leave me, I can't possibly do without, I need to find you where ever you are.


"Ba receptionists kawai ba harta masu kai komo a reception din saida suka razana da ganin yanda yanda Irfan ya fito daga lift a guje... "Kai tsaye wajen receptionists d'in ya nufo cike da masifa da d'aga murya yake fad'in" Where is she?? I said where is she...."wann ya kalli wannan wancan ya kalli wancan haka suke kallon juna don basu fahimce me yake nufi ba,...."D'aya receptionist namijin ne yace" Excuse me sir, but we don't get you, who are talking about....." A zuciye Irfan yayi kansa gamida shak'o wuyarsa yana fad'in" How dare you, just tell me where my wife is, I search every where tje bedroom, the bathroom but she isn't there.... just tell

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login