Showing 12001 words to 15000 words out of 159062 words

Chapter 5 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10402

yace thank you Princess. Su Nadiya sai faman dariya suke, Nilam ta mi'ko masa drawing din, kowa ta zana shi da sunansa a 'kasa, kar'ba yayi yana murmushi yace " what's this Angek, Nilam tace it's a welcome gift I hope you'll like it.... kallon drawing din yayi yana mirmushi yace" woow this is fascinating, of course I love it, family over everything. Gaba daya suka dariya. Amir yace and where is our mum, you didn't draw her..... gaba 'daya jikin Amma harma Irfaan da Nadiya yayi sanyi. Nilam ta 'dan kalli Amir tace" because mum is in heaven right now, Deejah tace mun na ri'ka mata addu'a kullum, tace idan nayi sallah na ri'ka cewa _rabbi gifirli wal walidain_..... Sosai abun yayi wa Engr da Amma da'di, Irfaan yayi murmushi ya ri'ko Nilaam yace good Angel, na gode koh, thank you for the gift, by the way, who taught you how recite a wonderful prayers like this. " Da sauri tace masa Deejah taught me.
"And who is she? Ya tambaya yana wani bu'de manyan idanunsa..... caraf Nadiya tace " she's good for nothing nanny, ya Irfaan wllhi kasa Daddy da Amma su koreta, she's nothing but annoying...... kallon da Irfaan ya watsa mata ne yasa ha'diye maganarta. Tsaraban su ya ciro ya shiga raba masu kafin Amma tace su fito su barsa ya huta.


"Da daddare Engr. Nazif Mumtaz ya ha'da 'yar 'kwarya 'kwaryan liyafa na dawowan 'dansa daga America, snn uwa uba yanaso yayi introducing 'dinsa wa abokan kasuwancinsa masu shears a M&M BUILDERS da kuma ma'aikatan company din.

"Wayan da Safwan ya dameta dashi duk shi yafi 'daga mata hankali, Yusra ta sake kiranta a karo na biyu, hello Deejah idan bazaki samu zuwa bane sai ki fa'da mun ba kisa nayi sneaking ba kizo ki 'ki zuwa. Deejah ta 'dan rage muryanta tace ke dalla zanzo, chance nake nema na samu na fito, zan zo da kaina nasai kunzo 'daukata ba. Mu ha'du kawai a Amazing Club. Yusra tace toh shiknn ina baza ido kafin ta kashe.
"Safwan ya kalleta yace me tace maki? Yusra tace waide tace zata yi sneaking ta fito, murmushi Safwan yayi ya shafi kumatun Yusra, Yusra ta dan kallesa bata ce komai ba, dan dama ta jima tana son Safwan shi kuwa ya tsaida hankalinsa kan Deejah....


"A farfajiyan gidan aka shirya komai, hasken wutan lantarki ya gauraye ko ina, flowers sai haske da she'ki suke, kujeru masu kyau ko wanne da table a tsakiyansa aka sa. 'Karfe 7:30pm daidai mutane suka soma hallarowa, su Nadiya an sha gayu cikin kayan alfarma kowa de yayi dressing me kayu harta Amma tayi kyau cikin shigarta.
"Hajiya Karima da jikarta Aziza sun samu hallarowa, Laila taso biyo su amma babu hali, nan Amma ta tarbesu ha'de da basu masau'ki.


"Irfaan yayi kyau cikin ba'kar suite sosai ta kar'besa, shida Engr kamaninsu sai ya fito sosai, nan da nan aka soma gudanar da event, Engr ya soma speech tare da bu'de fili da addu'a kafin Irfaan ma ya hau yayi speech cikin muryansa me da'din saurare me cike da miskilanci da 'kwarjini, daga nan Engr ya soma introducing 'dinsa wa abokan aikinsu tare da fa'din shine New Architect na M&M Builders..... "Duk wasu 'yan matan dake wajen irfaan ya tsole masu ido, ko ina yayi ido akansa, Aziza kam kasa daina kallon Irfaan tayi musamman dataji yanda ya gudanar da speech dinsa cikin turancinsa da babu maraba dana turawa, itafa bata ta'ba ganin mutum me kyaun Irfaan ba, take sonsa da 'kaunarsa suka cika mata zuciya damm
. Cikin takunsa ya 'karaso table 'dinsu tare da Amma, ta sakar masa murmushi shima ya maida mata martani, saitin kunnenta ya matso yace" Amma banga Nilaam ba kuma anjima ka'dan zamu soma pics... Amma ma take ta soma waige waige bata hango Deejah ba balle Nilam, kana tace inaga bata fito ba, barin sa Hajja ta dubota... mi'kewa yayi yace barin dubota Amma, da kansa ya nufi cikin gidan. Aziza tabisa da kallo har tana zubar da drink a jikinta, Hajiya karima kuwa tsaf tana lura da Aziza hakan ya mata da'di....

"Deejah ta gama shirin tafiya club dinta cikin 'kanan kaya riga da wando ya kamata sosai ya zauna a jikinta, ta 'danyi makeuo a fuskanta, kana ta 'dauko abaya ta ajiye.... har lokacin Nilaam na ri'ke da duska tana kallonta, tace Deejah kinyi kyau, baki ta'ba yin kyu irin na yau ba, Deejah ta narka mata hararan wasa tace, ni babu ruwana dake tinda bazaki tashi ki shirya ba, ya Irfaan zaiyi fishi ai... Nilam ta da'da turo baki tace" toh ni duk kayan bana son saka su..... (Deejah tasa ma Nilam kaya sunfi kala goma amma duk ta'ki yarda).... can Deejah ta 'dauko kayan Frozen tace I know you'll like this,.. ta fa'di tana ka'da ido da kai.... tsalle Nilam tayi tace yeee I love Frozen, nan Deejah ta saka mata harda crown ta 'dora mata a kanta ta saka mata silver cover shoe mai tsini... Nilam ta kalli kanta a mirrow tace woow... ta bata hannu suka tafa kafin Deejah tace" you looks like a fairy.... Nilam ta rungumeta tace you the best Deejah. Deejah tace So shall weee, Nilam ta gyada kanta.... juyowan da zasuyi tayi ido hu'du da kyakkyawan saurayi wanda a'kalla bazai wuce shekaru 27, ko ba'a fa'da ba shine Irfaan, dan kuwa ga kamanninsu da Engr. "Da gudu Nilam ta tafi ta rungume irfaan da shima yayi mutuwan tsaye yana kallon Deejah....Sai snn Deejah ta tuna da yanayin shigarta, tayi saurin jawo abayarta ta rufa a jikinta,... " Shi kuwa Irfaan baice komai ba sai 'daukan Nilam da yayi suka soma tafiya, Nilam gana 'daya ta mance da Deejah ta shiga tambayan Irfaan " ya Irfaan nayi kyau. Irfaan da har lokacin nai komo daidai ba yace kinyi kyau Angel... da haka suka 'karasa filin yana mai tuno yarinyar da ya gani a tare da Nilam.


"Deejah kuwa tana gain hankalin mutane ya tafi wajen hidima nan ta samu ta sulale ta fice daga gidan gabanta na ci gaba da fa'duwa idan ta tuno Fuskan Irfaan....


πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.....
[8/19, 06:22] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ–πŸŒ– *Mallakin waye* 09


_Written by QueenSamy_.......✍🏻




"Bayan anci ansha ne aka soma 'daukan pictures, Irfaan sai raba idanu yake ta ina zaiga Deejah ta fito amma shiru bai ganta ba, kasa ha'kura yayi ya nufi cikin gidan... nan Aziza ta bisa da mayen kallo har ya 'bace ma ganinta lumshe ido tayi ta furta " *Irfaaan* a fili.
"Yana shiga ya shiga neman ta ina zaiga Deejah amma shiru bai ganta ba, wata zuciya tace toh waima kan wani dalili yasa kake nemanta, take zuciyansa ta shiga raya masa ganinta nake son sakeyi. Gajeren tsaki yayi ya nufi sashensa, freshing up ya 'danyi kafin ya jawo wayaryasa ya shiga duba Mail 'dinsa.


"Engr yasha mamakin rashin ganin Deejah a filin nan, 'karasowa yayi kusa da Amma kafin ya 'dan sassauta murya yace" Amma Deejah fah, me ya hanata fitowa dinner din. Amma ma waige waige ta 'danyi, ta hango su Nilam dasu Amir tare waje guda babu Deejah, tace 'kila tana cikin gida, akwai wani abu ne. Girgiza kai yayi alaman a'a, amma fuskansa tab yake da damuwa. "Nadiya dake gefensu taji komai tsaf, take tayi kicikicin da fuska tace" Daddy wai meyasa kake damuwa da hidiman Deejah fiye da sauran ma'aikatan da suke gidan nan.
"Engr ya kalli Nadiya fuska babu alaman wasa yace, because she's looking after my precious, sabida tana kula da Nilam. Nadiya ta kuma turo baki tace" amma haka bai isa ka rin'ka treating 'dinta as if she's part of our family..... "Enough! Engr ya dakatar da Ita kafin yace" as far as she's living here with us she's part of us, ba ita kawai ba harta sauran ma'aikatan da suke 'kar'kashin mu are part of us, bazan lamunci ki ringa cin zarafin mutane dan suna 'kasanki ba, be very careful ki gyara wnn bad habit 'din naki if not nida ke ne. Daga haka Engr ya wuce ya bar wajen zuciyansa naci gaba da son ganin Deejah.
"Amma dake zaune saman kujeranta wani da'di ne ya mamaye zuciyarta, yanzu kam Nazif ya soma zama uba akan 'ya'yansa, tinda gashi har ya fara tsawatar masu. Nadiya kuwa fushi tayi bata tsaya wajen party din ba ta shige gida abinta.




"Tana tafe cikin taxi ta hangi mota kaman na Safwan pake gefen titi, ta dubi 'dan taxi 'din tace malam dan Allah 'dan paka a nan. Me taxi yayi yanda tace. Deejah ta sau'ko ta nufi motan Safwan,..... Cak ta tsaya sakamakon abin da idonta ya gane mata, Safwan kuwa ko ka'dan basuji isowan Deejah ba, suka ci gana da kissing juna suna rungume rungumensu cikin mota....Tab'dijam ashe dama Safwan tantirin 'dan iska ne, take taji wani irinnhaushe ya mamayeta. Ta juya a fusace ta koma cikin taxi din tace malam maidani yanda ka 'dauko ni..... " Kasa ha'kura tayi ta ciro wayanta ta shiga neman layin Yusra bugu biyu yusra ta 'daga.
"Hello kin iso ne..... yanayin da taji Deejah a ciki ya hanata 'karashe maganarta... " Yusra ashe Safwan ri'ke'k'ken 'dan iska ne, ashe dama munafuki ne neman matamsa yake a gari...." Yusra tace hold on Deejah meke faruwa, wani Safwan 'din kike magana. Deejah ta goge hawayen dake 'ko'karin zubo mata tace " Bana son tambayan iskanci Safwan guda nawa kika sani..." Yusra tayi dariya tace" Kai 'kawata wllhi watarana idan kikayi wani abin dariya kike bani, akwaiki da fa'dan 'karfin hali, yo dama what do you expect daga na mijin da yake 'kone darensa a club, aikema kinsan dan kema kin hanasa jikinki ne da tuni ya nuna maki maitansa. Anyway ba wnn ba me kika ji a gameda shi.
"Deejah taja tsaki tace" baji nayi ba ganau ce ni, ganinsa nayi da ido na suna kiss da wata mata cikin motarsa,...." Gaban Yusra ya fa'di, tayi saurin saita kanta tace ban gane da wata mata kika gansa ba, yanzu fah ya ajiyeni bakin Club yace bari yaje Anty din shi tana kiransa urgent, kafin nan kin iso... "Deejah taja dogon tsaki tace, toh wllhi 'karya yake maki, yana can yana watsewa cikin motarsa shida karuwarsa ya barki bakin club kina jiran gawon shanu, ni kinga na koma gida dama sneaking nayi na fito, kafin Nilam ta nemeni.
"Yusra ta sau'ke ajiyan zuciya tace shiknn, nima zan tafi yanzu. Daga haka sukayi sallama. " Jarrr uban chann! Abinda Yusra ta iya fa'di knn, wato Safwan da ya ce mata bari yaje ya kama masu 'daki a hotel, ashe wucewa yayi wajen wata karuwarsa, lallai Safwan ya cika 'dan duniya, wayanta ta ciro ta shiga neman layimsa......
"Suna tsaka da kissin juna shida Laila kawai sai ganin kiran Yusra yayi... yayi saurin 'daga wayan kafin yace" My Yussy gani nan wllhi holdup ne ya tareni kinsan titin Abuja yanda yake bare dare yayi...." Dalla malam dakata, ka shanyani ina jiranka kana can kana watsewa da wata koh, toh bari kaji Safwan niba irin 'yan matan nanne da ake wula'kantasau kan titi ba, kuma kar ka sake nema..... bai bari ta rufe baki ba yace pls Yusra ki tsaya kiji ki sairareni.... tsaki Yusra tayi ta kashe wayan kafin tayi tafiyarta....
"Safwan ya juyo yana kallon Laila rai 'bace yace" inace kinga irin rashin ha'kurin naki gashi yanzu kin jaza mun na rasa wacce zan rage dare da ita..." Laila ta jawo cikin jikinta cikin yanayi na gogaggun mata 'yan bariki tna wasa da yatsanta saman le'bensa take fa'din" Haba 'dan Cuty na, kar ka mance kanada ni, yau Aziza bata nan tabi Hajiya can gidanta zata kwana, kaga daga nan gida kawai zamu wuce mu sha soyayyan mu. Safwan ya 'dan ta'be baki yace" nifa na fa'da maki account 'dina yayi low sosai ya kamata naji alart ko baki ganin wata yaja ne.... " Laila ta wani da'da matsesa cikin jikinta kafin tace" kasha kuruminka har mota zan canja maka soon, na kusa zama matar President na M&M BUILDERS kaga kaima ka kusa zama young millonier....." Safwan yayi wata 'kasaitaccen mirmushi kafin yace" na 'dauka babanki shine president na kampanin ai..." Laila ta girgiza kai tace a da kenn..." Safwan ya jinjina kai yace" Toh Wai M&M *Mallakin waye* Laila tayi wani 'kasaitaccen murmushi tace lokaci ne zai tabbatar mana *Mallakin waye*, tada mota Safwan yayi suka nufi gidan Laila....




"Daga can gefen layin su tace wa me taxi yayi parking, ta fito tana faman san'da, ta back door ta shige lokacin har mutane sun wawwatse, sai faman le'ke le'ke take ga takalma a hannu, cikin sauri ta soma tafiya ta nufi Mansion 'din.... " kaman daga sama tajiyi muryan Engr yana fa'din" Deejah" ai nan fah Deejah ta wani daskare a wajen shiknn ya ganta wayyo yau ta shiga uku..." A ki'dime ta juyo har tana inn inna tace" Yeeess yes Sir.... murmushi Engr yayi gani yanda ta wani daburce, ya dubeta ga takalma a hannu alamun dai kaman bata da gaskiya.
"Ina kika fito at this hours, snn meyasa kika cire takalmanki.... " Mur,ushin ya'ke ta soma tana duba agogon hanunta taga 'karfe 10:00pm daidai...." Zari ido waje tayi tace" Laaa ashe har time ya tafi haka, wllhi ban ankara bane sir, am sos so sorry Sir... Murmushi Engr ya kuma a karo na biyu, tana basa dariya sosai,...
"Baki amsa min tambayata ba ina kika fito a daren nan....
"Wulli wulli da ido Deejah ta soma, 'kirjinta na fa'duwa ta shiga nemo 'karyan da zata yanka wa Engr. Take wani dabara ya fa'do mata .. tace" Sir dama daga Orphanage nake, naje dubo wacce na taso a wajenta, Sir kasn bana samun time da rana sosai shiya yau danaga ana hidima nace barin 'danyi using wnn opportunity 'din na dubosu.....
"Kallonta kawai Engr keyi yanda bakinta ke zuba zance. Gy'da kansa yayi kafin yace" Dama daga Orphanage kika zo..." Da sauri ta gya'da masa kai alamun eh. Engr ya gyada kansa a karo na biyi kafin yace" Next time kar ki sake fita a dare irin haka, is not safe idan kina so kije visiting 'dinsu we won't prevent you.
"Da sauri Deejah ta gya'da kanta tana hamdala a zuciyanta, kafin tace" insha Allahu hakan bazata sake faruwa ba sir.... ai bata jiran cewan Engr ba ta sa kai zata wuce...." Deejah" muryansa ya daki dodon kunnenta. Juyowa tayi tana muzurai kafin tace" Na'am Sir, murmushin yanda take duk a razane Engr ya 'danyi kafin ya nuna mata kujerun da suke chan gefe yace can I have some words with you......" 'Kululuuu 'karan da cikin Deejah yayi kenn kafin ya gy'da kanta cikin in...inna tace ye...yess sir su... sure of course.
"Zama sukayi bisa kujerun sai faman 'kirga 'yan 'yastun hanunta take tana addu'a'n Allah sa ba firing 'din Sir zaiyi ba.... Gyaran muryan da Engr yayi ne ya dawo da ita daga duniyan tunanin da ta tafi.....


πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.....
[8/19, 06:22] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye*

🌹10


"Engr. Ya kalli Deejah dake faman 'kirga 'yan 'yatsun hanunta yace" Deejah ina son sanin asalin labarinki..." Fuska cike da mamaki ta 'dago tana duban Engr, gua'da mata kai yayi alaman yes.
"Murya a nutse ta soma fa'din" Sir, ni dai nasan na tashi na ganni a gidan marayu, gaban wata mata da ake kira da Anty larai na tashi, itace ta ri'ke ni tamakr 'diyar data haifa, a yanda naji shine asalinmu 'yan jihar Kebbi ne, wani zaizayan 'kasa daka ta'bayi shi ya kashe iyayena, koda cibiyan kula da 'kanan yara marayu suka 'daukemu yaran da bamu mutu ba sai suka kawo ni nan cibiyar dake birnin tarayya Abuja,.....
"Toh ya akayi aka barki ki zo nan aiki daga Orphanage, Engr ya tambaya.
"Deejah ta 'dago tana dubansa, 'kwarjininsa yasata saurin sadda kanta, kafin tace" dama Anty Larai itace ta kawo nan bayan ta fa'di ma organization tayi adopting dina....." Shine zata kaiki aikatau...Engr ya fa'di rai 'bace.
"Da sauri Deejah ta shiga girguza kanta kana tace" No Sir, wllhi babu laifinta ko 'daya, za'bina ne, snn a halin yanzu na saba dasu Nilam Sir pls kar ka koreni...." Kallonta kawai yake kafin yace" Deejah ba korarki zan yi ba, amma what she did was wrong, bai kamata tayi masu 'karya ba idan suka sani daga sama akwai babban matsala, Deejah a halin yanzu ba aikatau kike a gidan nan ba kema kin zama one of our family, dan kuwa zuwanki alkhairi ne, gobe insha Allah ki shirya zamu je nayi adopting 'dinki legally......" Mamaki tab fuskanta ta dago tana dubansa..." da sauri ta sau'ka 'ka ta dur'kusa kan gwiwoyinta tana fa'din" pls Sir I beg of don't do that, zai shafi aikin Anty Larai dan Allah kar ka je..... " da sauri Engr yace " tashi tashi naji shiknn bazanje ba. But ki sani daga yanzu kema kin zama part of this family labarinki ya bani tausayi.
"Mi'kewa tayi tana masa godiya..... Kallonta kawai yayi yana murmushi kafin ya dubi agogon wayarsa yace shiknn ki 'karasa ciki, .... " Da sauri ta mi'ke kaman me jira dan dama gaba 'daya a ta'kire take 'kwarjininsa ya cika waje... " Saida safe Sir ta fa'di tana tafiyar har tana bugewa da kujera.
"Engr yace ki tafi a hankali.... har ta shige kafin shima ya wuce sashensa....


"Tana shigowa parlorn ta sau'ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login