Showing 147001 words to 150000 words out of 159062 words

Chapter 50 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10406

Alhj yayi kafin ya bud'e masu hannuwanshi yace Ku zo nan 'ya'yana. Gaba d'aya suka k'arasa sukayi hugging nasa..
"A tare Irfan da Deejah suka rik'e hannun wheelchair din Baba Alhj suka shiga turasa yayinda Mr n Mrs Engr Nazif Mumtaz suka take masu baya hannayensu sakale cikin na juna, annuri ya cike fuskokinsu....




"Azee zaune a reception ta rapka uban tagumi abin duniya ya taru ya Mata yawa, ga mutane said habaici suke mata wari ya cika masu ciki dukda yanzu babu war in sosai an riga an yanke k'afar Laila Mai ciwon, Hajiya ma an yanke hannun..

"Hangosu da Azee tayi ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, sunyi kyau har sun gaji like a real family.... "Cikin sauri ta mik'e zata gudu amma tuni Ummi ta hangota. Kaman daga sama ta jiyo muryar Ummi tana fad'in "Azeezah zo mana....
"Sunne Kai Axee tai sum sum ta k'araso gabansu..
Kasa d'ago ido tayi ta dubesu, murya can kasa ta soma gaida su Daddy, sika amsa mata da sakin fuska gamida tambayarta mash jiki...."Jiyo muryar Deejah tayi tana tambayarta masu jiki...."Bata amsata ba sai d'ago Kai da tayi ta bisu da kallo, sun mata kyau har sun gaji, shakka babu sun dace da juna, wani kishi ne taji ya taso mata ya tokare mata mak'oshi.. Tuni ta sunkuyar DA idanunta, Gogan kam bai masan DA wata hallitta Azeeza a wajen ba yana rik'e da Dee d'insa cikin kafad'unsa


"Azee ce tayi directing nasu had d'akin da su Laila suke....




"Karime ce ta soma hangosu ta kasa gane mafarki ne ko a zahiri.....


*Manage this vabu yawa, ba haka naso kawo maku shafin nan ba, har yanzu banida k'oshin lafia, dafatan xaku min uzuri Na ringa Baku koda Rabin shafi ne har Allah ya nufe mu DA kammalawa . Tnx all for your support 😘*


Sameena ceπŸ‘ŒπŸΎ


πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’ *Mallakin Waye*


101


*©Sameena Aleeyou...✍🏾*


_Queen Samy Novels Forum...πŸ“–πŸ“š_




"Cike da al'ajabi Karime ke bin k'ofar da kallo, ganin Alhj Ma'aruf a raye bai d'aga mata hankali ba kaman sanda tayi tozali da Fatimah, tabbas itace, shakka babu itace...."Zabura tayi gamida kurma wani uban ihu tana fad'in" Wllhi k'arya ne bazai tab'a sakuwa ba, wllhi dukanku biyu kun mutu, ni na sani bazaku tab'a dawowa rayuwata ba... ta kuma zabura kamar sabuwar kamun hauka nan fa ta fama wajen ciwon ta ihu ta k'walla sabida azaban zafin da taji..."
"Laila kam kasa motsi tayi sabida tsaban al'ajabi, ganin hannun Engr sakale cikin na Fatimah yasata kurma wani uban ihu, a zauce take fad'in" Hajiya wllhi aurenta yayi na shiga uku na mutu na lalace, wayyo Allah na, My Engr u two can't be married, she's my sister... pls don't do this to me, i can't live without you. ...




"Tausayin halin da suka tsince su yasa su zubda k'walla, Deejah ta kalli Irfan hawaye na bin k'uncinta, a hankali ya kwantar da kanta bisa k'irjinsa.. ganin haka yasa zuciyar Azee karaya, Allah sarki shikenan she lost him forever, bata san sanda hawaye suka shiga zarya a fuskarta ba.,,


"Ganin irin kukan da take harda shesshek'a yasa sa tallafo fuskanta, kallonsa Ummi tayi gamida sunkuyar da kai, da sauri ya rik'e hannunta gam cikin nasa yana mai jin rad'ad'in zuban hawayen ta.




"Banda surutan surkullen Laila da Hajiya baja jin komai... i zuwa lokacin takaicin su ya cika Azee, da sauru ta k'arasa gabansu tana hawaye take fad'in" Haba, haba ENOUGH of this, ta k'arashe maganar cikin kakkausar murya.. "Kaman an d'auke ruwa haka d'akin yayi d'if Karime da Laila suka yi tsit baka jin sautin komai sai na kukan Deejah da Ummi..




"A hankali ya k'arasa da wheelchair dinsa gaban gadonta, kallonta yayi yanda lokaci guda ta d'aid'aice, duniya tai mata juyin waina, hannu yasa gamida goge hawayen da suka zubo masa don kuwa ganin Karime ya tuno masa abubuwa da yawa ciki harda mutuwar matarsa masoyiyar sa Hindatu, da kuma mutuwar aminin sa Mumtaz.

"Muryarsa ya gauraye cikin d'akin sanda yake fad'in"Karima ki sani ALLAH baya bacci, ki sani ita duniya ba waje ne na tabbata ba, snn duk abinda ka shuka shi zaka girbe, Karima hak'ik'a kinyi ta'addanci a doron k'asa kinyi fasadi mafi muni, kin aikata laifi mafi girma, Karima kin d'auki ran d'an adam ba abakin komai ba, duk a sabida Duniya.. Toh ki sani shi Allah ba azzalumin bayi bane, ya haramta ma kansa zalunci snn ya sanyata haramun a tsakanin bayi.
"Fasali ya d'anja kafin ya goge fuskarsa yaci gaba da fad'in" Karima duk wani zalunci da ha'inci da kika min na yafe maki, tsakanin nida ke na yafe ki...."Muryarsa na rawa sanda yaci gaba da fad'in" Amma bayin Allahn da kika yanke masu rayuwa fah, wanda kika zab'i rabasu da rayuwarsu...."Shin su sun yafe ki, anya Karima kina tuna kwanciyar kabari," Kin rabani da Hindatu, kin rabani da Mumtaz, kin rabani da tilon 'yata da jikata ta hanyar haukatar da ita, Fatimah ta rayu babu d'iyarta, taa rayu cikin jinyar hauka, shin kinsan illan bawa ya haukata bawa..."Kuka ya kufce wa dattijo Baba Alhj.. "Da sauri Ummi ta tsuguna gamida rik'e hannayensa, d'agowa yayi yana murmushi yana dubanta still hawaye na kwaranya a fuskarsa, a hankali yaci gaba da fad'in" Alhmdulillah, Allah ya kuma had'ani dasu, Allah ya dawo min da Fateemah da d'iyarta cikin d'an sauran rayuwan da ya rage mun... "Karima yau ga Fateemah ga d'iyarta a tare dani...."
"Idon Karime da Laila tsuru tsuru suke kallon Ummi da Deejah, babu alamun nadama a tattare dasu saima wani sharrin da suke shirin k'ullawa a zukatansu.




"Maganganun Baba Alhj sun d'aure kan Azeeza, da sauri ta k'araso gabansa gamida durk'usawa tana hawaye take fad'in" Grandpa, ban gane ba, meyasa kake fad'in Ummi is ur only daughter? What about my mum, and Deejah ce kawai jikarka, what about me grandpa, are you going to deny me, nasan nayi kuskure mafi girma, but na gane laifi na, and na canza halayyata, i'll start a fresh....." Tausayin Azeeza ya cika zuciyarsu "Rik'o hannayenta yayi yana tuno kalan k'auna da soyayyar da ya nuna mata a baya, a matsayinta na jikarsa k'wara d'aya, " a hankali ya soma fad'in" Azeeza kiyi hak'uri, har gobe ke jikata ce, keda Deejah bazan banbance ku ba, Azeeza ur grandma cheated on me,.."muryarsa ya soma rawa don baya son tunawa take yaji heart dinsa ya soma masa nayi,.."A zabure Azee ta mik'e gamida k'arasawa wajen Karime, kallon wulak'anci ta soma mata kafin tace"
"Tell me the truth, ki fad'a mun gasky nace.... ta k'arashe maganar cikin d'aga murya.,"Karime ido yayi tsuru tsuru.. Baki na rawa ta soma fad'in" Azeeza babu yanda na iya ne, Hindatu zata cinye gida dole na nemo mafita, dole na bada kaina wa boka na...."Ai bata gama rufe baki ba Azee ta sulale a k'asa tana hawaye, sautin kukan ma bai fita..."


"Laila cike da makirci ta soma kuka tana fad'in" Hajiya kin cuce mu nida 'yata, waann duk munanan ayyukanki ne, ashe Fateemah ba yayata bace, ashe zamu iya kasancewa KISHIYOYIN JUNA, Anty Fatee, y'ar uwata, dan Allah kar ki bari mijina ya sake, don ba yin kaina bane that i turn to be baster ... hawaye ya soma kwarara mata, tuni zuciyar Ummi ya karaya, hannayen Laila ta rik'e tana tunosu a da lokacin da suke a matsayin yaya da k'anwa..
Ana cikin wann yanayi Sukaji an banko k'ofa an shigo....




"Ba kowa bace illa Yusrah. Kan ubanchan! K'irjin Laila ya shiga dukan tara tara, sikenan wnn tsinanniyar Yarinyar tazo tarwatsa mata rayuwa. Tuni zufa ya shiga keto mata tako ta ina,,,


."Kallonsu ta shiga yi one by one, hango Deejah tayi rungume jikin Irfan da sauri ta k'arasa gamida rik'o hannunta." Sai snn Deejah ta d'ago suna hada ido suka rungume juna.., sosai suke kuka su duka biyu..
"Cikin kuka Yusrah ke fad'in" Ki yafeni Deejah, naci amanarki, na cutar dake, duk wani sharri da tuggu da suka k'ulla maki da taimako na ne, ki yafe mun k'awata, na sani hakkin ki shike bibiyata, gashi na auri wanda nake so din amma ban huta ba, sabida na ci amanarki,.."Kuka yaci k'arfinta.
"Kasa furta komai Deejah tayi sai hawaye dake ambaliya a fuskarta, da k'yar ta iya furta" Yusrah ban tab'a ruk'eki ba, you always be d Yussy i knw, the one we always had that beautiful moments together, Allah ya yafe mu gaba d'aya..
"Yussy ta d'ago tanai mata godiya caraf idanunta ya sauk'a kan Azee dake durk'ushe a k'asa, k'arasawa tayi yanda Azee ke kife da kanta tana hawaye. Dago fuskan Azee tayi tana kallonta, Azeen ma ita take kallo.
"Yussy tace Azeeza yau zan fad'a maki sirrin da aka b'oye maki shekara da shekaru....
"Jar ubanchan! Cikeda masifa Laila take fad'in" Ke munafukar Allah me zaki fad'a mata, aki wuce ki fice tunda Deejah ta yafe ki duk irin cin amanarta da kikayi, ki fice ki bar family dinmu in peace...


"Mikewa Yussy tayi tana murmushi kafin tace" Kiyi hak'uri my husband mistress i won't take much of ur time, sak'o nazo badawa.


"My husband mistress" Abunda suke nanatawa kenan a zukatansu. Laila kuwa sai faman kumfan baki take.
"Enough mummy! I'm insists to hear what Yusrah's about to say.. Azee ta fadi a hasale.


"Murmushi Yusrah tayi kafin ta soma fad'in" Azeeza kin tab'a sanin wanene ainihin mahaifinki.,,"Kutuman uban chan "Laila ta fad'i a zuciyarta, mikewa ta soma yi tana fad'in" Azeeza kar ki yarda da duk abinda makiran nan zata fad'a maki, dangwala k'afarta da zatayi taji Azaban zafi, ihu ta sake tana rik'e k'afar.


"Azee na kallon Yussy cikin wani irin yanayi, a hankali tace" Eh na sani ya rasu shekaru biyu da suka wuce..
"Yusra ta murmusa kafin tace" *No ba shine asalin Dad dinki ba, your uncle Safwan kwarton mahaifiyarki tun na d'an shekaru sha shida a duniya shine mahaifinki*... "Zukataansu suka girgiza, innalillahi wa inna'ilaihirraj'iun, anya Karime da Laila mutane ne..


"No that can't be, is just can't be, uncle Safwan is my only uncle, he can't be my father..." kaman zautacciya haka Azeeza ta koma, hannu Yusrah tasa cikin bakin zaninta kafin ta ciro wata takarda ta mik'a wa Azee, take this, this is d proof


"Kallon takardan tayi kafin ta kalli Yusrah, hannunta na rawa ta amsa, DNA result ne wanda yake tabbatar da cewa Safwan shine real biological father dinta.... "Wani ihu Azeeza ta sake gamida d'aura hannu aka ta zube k'asa, kuka take tamkar ranta zai fita,.. "Kaman wacce aka zabura tayi kan Laila gamida cakumo wuyarta tana fad'in" Laila ki fad'a mun da bakinki, Safwan shine Biological father na, ki fad'a mun Lailaaaaaa....! Daidai nan Safwan ya banko k'ofa ya shigo tamkar wanda aka koro..,




"Had'a idon da sukayi da Irfan ya gane Safwan, a hasale yayi kansa yana fad'in" How dare you blackmail my wife.. naushi ya kai mai a hanci saida ya fashe, ya shiga kai mai naushi ta ko ina, da sauri Deejah tayi kansa tana rikosa, Daddy na k'ok'arin k'watan Safwan don kuwa yaji jiki hannun Irfan.. Kuka Deejah take tana fad'in" Pls let him be, kaji my love, Engr ma gyada masa kai yayi alamun yabi maganar Deejah.. kallonsu Irfan yayi bazai iya kin bin umarninsu ba coz he lubs them, a hankali ya rik'o hannun Deejah kafin ya furta" Lets get out of here baby i can't stand them anymore, daga haka suka fice hannun su sakale cikin na juna.

"Da k'yar Ummi ta k'waci Laila a hannun Azeeza, Azee na kuka take fad'in" Ummi ki barni na kashe wann bitch din bata da wani amfani, she ruined my life.."Ummi bata saduda ba sai faman lallashin Azee take. D'agi idon da zatayi ta sauk'e su kan Safwan, wani tsallen ta kuma yi kafin ta k'arasa ta rik'o kwalan rigarsa da iya k'arfinta..."
"Is it true, tell me, is it true???? "Safwan cike da tashin hankali yake fad'in" Azeeza ki saurareni pls swethrt, yeah it is truem yku are my flesher blood, i'm your dad that's why i can do anything for you, koda zan rasa raina ne,
"But believe me my dear, babu laifina alaifin momyn ki ne, she forced me since from the very beginning, ita tayita samu aikata wann mummunan aiki, snn har bayan mutuwar mijinta my brother bamu daina, har ta auri Engr Nazif bamu daina ba,,,"Ya dan kai kallonsa ga Engr wanda fuskarsa ta koma jazur... A hankali ya k'arasa gabansa zaiyi magana Engr ya d'aga masa hannu kafin yace" She's all yours, you can have her, banida sauran alak'a da ita, shes not longer my wife... Daga haka yaja hannun matarsa ya sakar mata murmushi kafin yace" Lets get out of here Hayatee.." Dan kallonsa tayi fuska cike da damuwa zata yi magana, ya dora mata yatsa a baki gamida cewa shiii, let's go. Kwanto da ita yayi kan k'irjinsa kafin suka fice, jikinta a sanyaye. Ya rage saura yasu yasu don dama tuni an fita da Baba Alhj an kaisa dak'in hutu, sabida heart dinsa yayi weak,


"Tsugunawa Azee tayi wajen tana kuka mai tsuma zuciya, why is this happening, why, meyasa rayuwa ta kasance haka, her own mother is a baster, and now she also turn ti be baster, her so called uncle turn to be her real biological father...




"Safwan zai durk'usa gaban Azee kenan Yakumbo ta shigo bayan biye da polisawa har guda uku., kuka take tana nuna Safwan da yatsa, cikin kuka take furta, oficer ku kamasa gashi nan, shi ya kashe mun d'anaa.. "Safwan cike da tashin hankali yake fad'in" Yakumbo nine fah, nine Safwan dinki, meyasa zaki min haka.."Oficer ya tallafo keyarsa kafin yace sajent arrest him. Nan akayi arresting Safwan aka tasa k'eyarsa... Da gudu Azee ta k'arasa ta rungume Yaakumbo, tana kuka take fad'in" Ki yafe mun kaka ta, ki yafeni...."Share hawayen idon Azee Yakumbo tayi kafin tace" Na yafe ki Azeeza, Allah ya yafmu gaba daya,...."Ganin Yakumbo zata fice da Azee yasa Karime fad'in "Ina zaki kaimin jika mayya, zuriyan aljanai, basu ko tanka ta ba suka fice suna rungume da huna,.




"Daki ya rage saura masu shi wato Karime da laila, haba nan suka kaure kowa na tsine ma kowa cikinsu, abu kaman wasa ihu suke sosai kaman mahaukata nan suka shiga fincikan naman jikin juna suna sunbatai wanda har saida yaja hankalin likitoci.




"Suna haraban asibiti suna k'ok'arin shigewa motocin su aka fito za a wuce da Safwan.... "Kallon Deejah ba tare da yace komai ba, oficer ya kwade kafarsa gamida fad'in " Move..!
"Juyows Deejah tayi tana kallon Irfan murmushi ya sakar mata kafin ya bud'e mata marfin mota yace" let's go Mrs Irfan Mumtaz... murmushi ta sakar masa kafin ta shige cikin motar..




"A kan idon Azee komai ya faru, sun burgeta, A hankali ta rik'o hannun Yakumbo sosai suka fice neman adaidaita.












"Sauk'arsu kenan a airport, ko a mafarki bata tab'a zaton Daddyn twins zaizo Nigeria bam yau sai ga shinan a birnin tarayya Abuja, wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Irfan.....




*Kudai k'ara min uzuri masoyana, jiki da sauk'i sosai, na gode k'warai da kulawarku, da wanda suka turo sak'o da wad'an da suka kira harma wanda suka min addu'a a zukatansu, na gode k'warai, Allah bar k'auna.. #1Luv😍😘*


Sameena ceπŸ‘ŒπŸΎ
πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’ *Mallakin Waye*


102


*©Sameena Aleeyou... ✍🏾*


_Queen Samy Novels Forum...πŸ“–πŸ“š_




"Ajiye Deejah Irfan ya soma can family house nasu kafin ya wuce airport d'aukosu Alhj Abdullah,
"Tunda Engr ya sanar wa Ummi batun zuwan abokin kasuwancin nasa hankalinta ya gaza kwanciya. Haka kurum take jin matsanancin fad'uwar gaba wanda ta rasa dalilinsa..


"Deejah da Nadiya sai faman zirga zirga suke tsakanin parlor da kitchen. Motsi ksd'an idan Nadiya tayi Ummi takance maza ta bar aikin nan taje ta huta.... Dukda ita kanta Deejahn ma bata jin dad'in jikinta, k'ok'ari kawai take don bata so a gane batada lafia, Tasan idan Irfan ya sani he won't let her work n zai kaita asibiti a mata allura abinda take matuk'ar tsoro....




"Ammah ta share k'wallan da suka zubo mata sanda Engr ya gama labarta mata halin da suka baro Laila da Karime, tabbass duniya makaranta ce , Allah yasa hakan ya zame wa masu hali irin nasu ishara Ameen...




"Gidan ya gauraye da k'amshi kala Kala, dishes kala daban daban suka girka, kama daga kan na k'asashen k'etere u want namu na gargajiya. Da taimakon Ummi da Hajja suka kammala komai.. "
"farin cikin da Ammah ke ciki bai misaltuwa, burinta Allh ya cika mata shi, Family d'inta ya had'u gwanin ban Sha'awa, Nazif da Fatima Sun cika burin marigaya Ma'aruf da Hindatu. Alhamdulillah.....








"Babu yanda Mr chairman baiyiba kan Irfan ya fara biyawa dasu masauk'i firr Irfan yak'i amincewa, Afnan da Ayla ma sunyi insisting a soma zuwa wajen Aunty Dee, haka Aunty bilki ma. Babu yanda Mr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login