Showing 6001 words to 9000 words out of 159062 words

Chapter 3 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10403

turaki makarantar gaba da sakandare da na turaki, kin sani nan foundation zuwa sakandare kawai ake biya maku, nima 'dawainiya sunmin yawa ne ga iyayena ga marayun 'ya'yana, bacin haka kinsan babu abunda bazan maki ba....." rungumeta Deejah tayi kafin tace" kiyi ha'kuri Anty larai, nima ina sonki donke uwace a gareni, mutane ne kawai suke neman rabamu, insha Allah bazan ta'ba baki kunya ba.
"Anty larai tayi murmishi tace" that's my girl, maza jeki koyar da yaranki nasan suna can suna jiranki. Da murmushi ta wuce ta shige ajin yaran nan suka soma tsalle ita da yaran dan dama rabin karatunsu talle ne da rawa a ajin Deejah...


**************************************
*Maxico*
_Chicago_


"Yana zaune kan wata benchi dake gefen hanyan street 'din da zai kaika _mexico city_ dake a birnin _Chicago_, shigan da yayi zai tabbatar maka lokaci ne na sanyi, yana sanye cikin gray shirt da blue jeans, ya 'daura ba'kar jacket a sama hannayensa rufe ciki hand gloves, 'kafarsa sanye cikin ba'kar booth, gashin kansa sai fifituwa yake alamun iska na ka'dasu. Kallon mutane yake yanda suke ta wucewa a lokaci guda kuma yana sipping hot coffee 'din dake hanunsa.
"Wayansa ne ta soma ringing, ya ajiye coffe din a gefe kafin ya 'daga wayan da fari'ansa ganin granny dinsa ce me kira.
"Hello my amazing granny, how you doing pretty.
"Murmushi Amma tayi kafin tace" Irfaan bazaka canza ba knn, yanzu kuma me ya kaika Mexico daga Los Angeles, jiya daddynku yace mun kana Chicago,
"Murmushi Irfaan yayi kafin yace" there you go again granny,.... da sauri Amma ta katse sa, kaga ni idan kana magana dani kayi hausa dan nasan yanzu da kyar idan baka mance hausa ba.
"Dariya me sauti Irfaan yayi kafin yace" Come on granny you know am not use it, I can't speak it fluently. Koma de yaya ne haka nake so kamin, Amma ta fa'di,
"Murmushi yayi yace" Alright fine, na gama final exams dina so sai na 'karaso nan Mexico zan 'danyi spending couple of days, sai na koma States, daga nan kuma idan na kammala ha'da takarduna zan zo Nigeria na ganku, dan am damin missing you guys.
"Murmushi Amma tayi tace" muma muna son ganinka Irfaan, nan suka soma hira sosai da Amma kafin ya tambayi kowa, Nilam ne ta shigo ta girma tayi wayo, yarinya 'yar shekaru hu'du, Amma ta bata wayan ta shiga masa surutun gwalamniya...





"Aziza ne kwance jikin Mum dinta Laila sai shar'ban kuka take, Laila ma sai matso hawayen 'karya take. Hajiya Karima sai faman basu baki take, itama tana sharan hawaye.
"Amma tayi sallma ta shigo cikin parlorn dake cike da mutane 'yan kar'ban gaisuwa, rabonta da Hajiya Karima tun mutuwan mijinta Alhj Mumtaz sai yau suka ha'du wajen kar'ban ta'aziyan mijin 'yarta Laila, ga mamakin Amma sosai Hajiya Karima ta tarbeta sai nan nan da ita takeyi. Amma ta masu ta'aziya gamida shawarwari na ban ha'kuri wa Laila. Amma ta dubi Hajiya Karima tace Nazif yana tare dasu Alhj yana so ya shigo ya maku ta'aziya, da sauri Laila ta 'dago kanta jin an ambaci Nazif. Hajiya Karima ta washe baki tace ya shigo mana, ta dubi wata yatinya dake gefe tace maza ce masa ya shigo. Amma tace a'a barin masa waya sai ya shigo.
"Engr. Nazif Mumtaz wanda a halin yanzu yake da shekaru 52 a duniya idan ka gansa zaka zata dan shekara 40 ne, yana sanye cikin ash din jampa da hula sallamansa cikin muryansa me cike da charisma ya daki dodon kunnuwansu, aiko nan Laila ta 'dago kai tana binsa da kallo, bata yi tsammanin haka ya koma ba, ko gasan matasa ya shiga wnn zai lashe, sanda yake gaida Hajiya Karima sai nan nan dashi take, koda tace masa ga Laila su gaisa, bai ko kalleta ba 'kasa yake kallo har suka gama gaisawa, Laila ko wani mayen kallo ta bisa dashi har ya fice, ta gama ayyanawa a ranta ta samesa an gama. Haka har bayan kwana uku Hajiya Amma tana zuwa kar'ban gaisuwan mijin Laila, ita kanta Amma tana mamakin canzawan da kishiyar marigayiya aminiyarta tayi wato Hajiya Karima, wani sabon ala'ka ne take son 'kullawa a tsakaninta da Amma.


"Yau ta kama alhamis, Anty Larai ne zaune tana kallon labarun tara a NTA, nan ta hango gidan wani ta'aziya ana nunawa, kaman daga sama aka hasko fuskan uwar 'dakinta da ta jima da barin 'kasar nan ta koma America, zama ta gyara tana kallon, ai kuwa ba gizo take mata ba, ita ce dai Hajiya Salma jwar 'dakinta a da kafin ta soma aiki da cibiyar goya marayu......


πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹............
[8/18, 20:41] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye* 05


_Written by QueenSamy_


"Yau kwana biyu da komawar Patricia nanny n Nilam 'kasarsu America, kuka sosai Nilam keyi, hardasu Aiman da Amir, harta Nadiya saida tayi kukan tafiyan Patricia, Amma kam hakan yafi mata yanzu zata samu nanny musulma ta kula mata da rayuwar jikokinta.
"Gaba 'daya hankalin Engr.Nazif ya gaza kwanciya, musamman idan yaji sautin kukan Precious Nilam, tana kwance kan 'kirjinsa yana aikin rarrashi," Daddy I want her back.... Nilam ta fa'di cikin kuka,
"Oh my Precious I promise you I'll find you a new nanny here, a very good one, who can take good care of my Precious, ya 'karashe maganar yana kwantar da ita bisa 'kirjinsa.
"Nadiya ce ta turo 'kofa ta shigo, Good morning daddy, ta fa'di sanda take 'karasawa kusa dasu, murmushi Engr. Yayi kafin yace " good morning Sweed, are you ready for the sch?
"No daddy am stayin at home with your Precious, ta 'karashe maganar tana shafa kan Nilam tace" right daddy's precious?
"Take mood din Engr ya canza dan kuwa idan akwai abunda baiso to yaro yayi missing sch.
"Girgiza kai Engr yayi kafin yace" No Nadiya zakije sch, you know you're writing your Waec examz soon, so I don't want you to be missing classes ok.
"Nadiya ta 'dan turo baki tace" Daddy am tired of wearing this uniform for heaven sake is awkward, su a nan Nigeria wai dole mutum yayita saka uniform, am dammn sick of it dad.
"You'll soon graduate sweedy and shiknn kin daina sakawa, oya jeki shirya barin saka ma Precious nata kayan. Ok daddy ta fa'di sanda take fita.
"Engr da kansa ya shirya Nilam suka sau'ko downstairs nan Amir da Aiman suka nufosa a guje suka rungumesa, good morning daddy suka fa'di, rungumesu yayi yace" good morning my boys, how was your night. Amir yace daddy we're missing Patricia so awfully, aren't she coming back to us?
"Engr ya zaunar dasu bisa dinning yama rasa me zaice ma yaran nasa, Amm na tsaye tana kallonsu daga stirs, tausayin 'dan nata ne ke damunta, a 'bangare guda kuma laifinsa take gani, kwata kwata baison 'bacin ransu, ya sadaukar da farin cikinsa garesu, ya ha'kura da aure sabida yaransa basa so.
"Hajja cook dinsu ne keta faman jere abincin bisa dinning din bayan ta gaida Engr. A gurguje yaran suka gama karyawa dan sun kusan makara. Engr. Kuwa da kansa yayi feeding Nilam dinsa. Saida ya tabbatar sun shige mota driver yaja su zuwa sch kafin ya dawo danyin nasa break din.
"Zaune ya tarar da Amma bisa dining da alama dawowarsa take jira. Gaisar da Amma ya fara yi kafin ta soma zuba masa abincin. Kallon Amma yake sosai yana son gano abunda ke damunta, murya a hankali yace" Amma na are you alright? "Kallonsa Amma tayi kafin ta tura masa plate din abincin tace" am fine son, kaci abinci zakayi lattin office, kasan bai kamata shugaba yana latti ba.
"Hannunta Engr ya ri'ko cikin nasa kafin yace" pls Amma tell me, is something bordering you? You seems quite depressed.
"Amma ta gyara zama tace" Nazif to be honest with you, halin dake ciki ya fara isata, this is too much Nazif, yeah na sani kana son 'ya'yanka but that doesn't mean you can't be happy, you're a human Nazif, a iya sanina kai lafiyayyen namiji ne, wanda ko wani na miji me lafiya na bu'katar mata, I'm your mother and I'll not goin to allow you to ruin your life just like that.... "Da mugun mamaki Engr ke kallon Amma bata ta'ba masa magana makamanciyar haka ba, gyara zama yayi kafin yace" Amma what you thought of me was wrong, yeah precisely abunda kika fa'di gaskiya ne, duk na miji me lafiya na bu'katar mata, but to Amma matar da nake so na kasance da ita guda d'yace, FATEEMA ce, you perfectly knew that, so ever since I lost her, wani maganan soyayya ya fice daga raina, aurena da Khadija rabon 'ya'ya ne, and I ason yaran nan with all of my heart, Fatima ta rasu, Khadija ma ta rasu, Amma keda yarana you're my only family, babu abunda ya rage mun yanzu a rayuwa bayan naga na kyautata maku, I Devoted my entire life to you and my kids Amma, so pls ki daina kawo mun zance aure kinji Amma.
"Girgiza kai kawai Amma tayi cike da tausayawa danta Nazif, a tare suka gama cin abinci da Engr kafin ya fice zuwa Company.


_Around 2:30pm_
"Nilam kwance jikin Amma tana ci gaba da kuka, ta'ki yarda da kowa sai Amma, harta Nadiya ma ta'ki yarda da ita. Kaman daga sama tajiyo sallaman Larai, da mamaki Amma ke kallon larai har ta 'karasa shigowa. Amma ta sake baki tace" Larai dama zan sake saka ki ido na. Anty larai na murmushi ta 'karasa ta tsuguna kan makeken carpet din Turkey dake baje a tsakiyan parlorn tana fa'din sannu Hajiya Amma, ina nan wllhi, ai tunda kika koma America shiknn sai satin bayan can nake ganinki gidan wani rasuwa alabarai shine nace ai ya zama dole na nemeki na gaisheki. Amma tace ayya aiko na gode sosai larai. Nan fah aka soma gaisawa tareda hiran yaushe rabo.
"Anty Larai ta mi'kama Nilam hannu tace yaki 'yan mata, Nilam ta , a'ke kafa'du alamun o'o, Amma tace rigima takeji dashi wai me raininta da muka taho da ita daga America ta koma, tofa shine duk wnn rigimar. Anty Larai tace ayya halan 'yar gidan 'karamin Alhaji ne (haka take kiran Engr Nazif a da lokacin da take aiki ma Amma n sa). Amma tace eh ai itace autarsa, mahaifiyar tasu ta rasu lokacin muna can Amurkan, toh bayan rasuwarta ne muka dawo gaba 'daya. Anty Larai tace ayya Allah yayi mata rahama Amma ta amsa da amin.
"Larai nace yanzu a ina kike aiki? Amma ta tambaya.
"Anty Larai tace" ai tun bayan tafiyarku Hajiya am na soma aiki da cibiyan goya marayu, a can nake aiki yanzu, kuma nice shugaban fannin kula da 'yan mata. Amma tace ayya Allah ya taimaka. Sun jima suna hira ma'aikata suka cika gaban Anty larai da kayan ciyeciye iri da kala, wnn 'dabi'a na karrama ba'ko wajen Hajiya Amma har yanzu na nan, bata damu ko talaka bane ko me ku'du, 'yan adam du 'daya ta 'dauka.
"Koda Larai ta tashi tafiya sosai Amma ta cikata da kayan alheri snn sukayi musayan lambar waya akan ko tana neman wani abu, koda na ma'aikata ne zata nemeta. Sosai Amma taji da'din ziyaran da Larai ta kawo mata.




"Yau tana zaune tana tunanin ta aina za'a samo ma yaran nan Nanny dan kuwa fitinan 'yan biyu da Nilam ya isheta, ita ga shekaru yaja ba komai zata iya da fitann su ba, shi kuwa babansu ya'ki zancen aure.
"Tunanin Larai ya fa'do mata nan ta kirata ta tambayeta ina zata samu Nanny matashiya me hankali da nutsuwa da sanin addini sabida rayuwar jikokinta ya inganta. Nan Anty larai tace bazai gagara ba za'a bincika inshaAllah, da Al'kawarin idan an samu zata jita sukayi sallama.


*M&M BUILDERS*
"Yana zaune cikin Office 'dinsa fuskansa sanye da faran tabarau na 'kara 'karfin gani, yana sanye cikin white long sleeve shirt irin wanda ake 'daura suite a sama, sanye yake da ba'kar wando na suite 'din. Files ne gabansa sai bincikasu yake yi..... wayan dake gefensa ne yayi distracting 'dinsa. A hankali cikin nutsuwa ya 'daga kafin ywce" yes Jane what's this? Jane sakatariyan sa tace" Sir you having a visitor, she says you have an appointment.
"Da mamaki Engr yace appointment? and you said it's alady?
"Yes sir, may I let her in.
"Kaman bazaice komai ba sai kuma yace" send her in pls
"Alright sir.......


"Jane ta dubi Laila tace" Miss you may go in now.
"Thank you.... Laila tace cikin kashe murya.


"Tunda ta shiga office din take binsa da mayen kallo, shi kuwa har lokacin idonsa na kan takardun da yake dubawa,Oh mine... He's so cute and handsome, haka Laila tace cikin zuciyanta, 'dago ido Engr yayi yaga ta kafa masa ido, tana sanye ciki riga da skirt na atampa wanda yasha 'dinkin wula'kanci, matashiyar mace wacce bazata wuce shekaru 32 zuwa da 33 ba. Ganin kallon yayi yawa yasa Engr yni 'dan murmushi ya ajiye biron hanunsa yace" Miss may I knw who you are, and what are you here for?
"Laila tayi saurin saita kanta kafin tace" Oh good morning sir, am Laila Ma'aruf Sarki, ya gane surname dinta dan haka take ya sakar mata murmushi, yace pls seat down yana me nuni da kujeran dake gefe.
"Zama tayi tana mayaudariyan murmushi tace" thank you.
"So how may I help you? Engr ya tambaya.
"Laila ta wani juya ido kafin tace" kardai baka gane ni ba,? Murmushi ya 'danyi sanda yake cire glasses idonsa yace" na gane sunanki ke 'diyar aminin mahaifina ne am I right. "Gyada kanta tayi tace" ai nice wacce kazo min ta'aziyan rasuwar mijina kwanaki...." Da mugun mamaki Engr ke kallonta kafin yace" toh me ya kawo ki nan kuma despite the fact kina cikin kwanakin takaban ki, if am not mistaken.
"Murmushi laila tayi tana juya ido kafin tace" yeah hakane, amma ai babu wani aibu a ciki...." Da sauri Engr ya katseta, kwarai akwai aibu, haramun ne mace ta fita babu wani babban uziri ko na ciwo ko makamancin haka alhali tana cikin kwanakin takabanta, yanzu abunda nake so dake ki tashi ki koma 'dakinki snn ki cire wnn ado da kikayi dan kin aikata babban haramun.
"Zuciyan Laila ya cika da mamaki ganin mutumin nan daga America ya dawi amma ashe har yasan addini haka. Ta 'dan sha jinin jikinta kafin tace" Oh dama daga asibiti na fito sai nace barin 'dan tsaya mu gaisa, snn na nemi aiki a companyn nan dan kasan mijina ya bar mun marainiya.
"Engr yasha mur sosai kafin yace" ki tashi ki tafi yanzu snn kiyi yanda nace, what ever should be the case akan maganar aikin zamuyi shi daga baya, mahaifinki nada every right gameda wnn company, so no need to be worried about looking for a job here.
"Jiki a sanyaye Laila ta mi'ke tace" haka ne na gode da tunasrwanka, nima bada son raina nazo ba, Alhj ko ka'dan baison nayi aiki a nan company din tun tuni, yanzuma idan yaji nazo he will very mad at me. So pls Engr do me a favor, he shouldn't know that I was here.
" Engr baice mata komai sai gyada kansa da yayi, jiki a sanyaye ta fice, ta 'dauka turai ya gogesa sosai ya za'bi rayuwarsu, bata ta'ba tsammanin samunsa haka ba. Cike da haushi da takaici ta fice daga Office din.
"Engr kuwa girgiza kai kawai yayi gamida ta'be baki a hankali ya furta" some people don't even know their obligations.




"Tana shiga gidanta ta shiga neman layin Hajiyanta, Hajiya Karima tana dagawa tace yaya kuka yi. "Wani dogon ysaki Laila ta buga kadin tace" Hajiya yanda na samesa banyi tsammanin samunsa haka ba, dagani zamu sha wuya dashi, wani guntun wa'azi ya tsaya yimin saikace badaga America tushen wayewa ya fito ba, yanzu dai kawai kiyi 'ko'kari ki fito kizo gidana, ni na gaji da wnn ta'kuran wai shi takaba. Hajiya tace kwantar da hankalinki ina nan tafe. Bayan sun gama wayan ne taji muryan surkuwanta wato uwar marigayi mijinta tana sallama.
"Wani dogon tsaki Laila ta buga ko amsa sallaman ma bata samu zaradin yi ba. Karshe har Yakumbo ta 'kare ta sako kai cikin parlorn.... Ga mamakin Yakumbo zaune ta samu Laila a parlorn ta 'kure sautin tv tana jin ki'da, ga kwalliy uwa amarya a wajen biki, cingam ne a bakinta sai faman taunasa take. Mamaki ya hana yakunbo furta koda kalma guda........


πŸ‘ΈπŸ»QueenSamy ceπŸ’‹πŸ’„πŸ˜


πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye* 06


_Written by QueenSamy_


"Mamaki ya hana Yakumbo furta koda kalma guda, sallalami ta shiga yi tana tafe hannu sanda taga Laila ta 'dauko waya ta maka a kunne tana fa'din" hello sweetyna kanajina, wllhi nima tsananin sonka, kar ka damu mun kusa zama 'kar'kashin inuwa guda......." Yakumbo bata gama jiba ta shiga rera kuka tana fa'din" Yanzu laila mijin nakai ko wata guda beyi da mutuwa ba shine kike zancen aure da wani...." A hasale Laila ta mi'ke tana fa'din "Would you stop backing like a dog, kinzo sai cika min kunne kike kamar wata kariya, ke barin fa'da maki karkiga da ina ragar maki dan ina auren 'danki, toh yanzu abunda ya ha'da ya raba, ki wuce ki fice min a gida tun kan ranki ya 'baci,...... Sosai abin yabawa Yakumbo tsoro, lallai abunda ake fa'di akan Laila gaskiya ne, ......" Twasawn da Laila ta kuma daka mata yasata saurin dawowa hayyacinta," zaki wuce ki fita ko saina fitar dake da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login