Showing 15001 words to 18000 words out of 159062 words
Chapter 6 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt
ajiyan zuciya gamida dafe 'kirjinta. A hankali ta furta mutumin Allah ya masa Charisma, tunawa da Nilam da tayi yasata saurin nufan stirs..... A daidai stirs suka ci karo shi na sau'kowa ita kuma tana haurawa.... Tarota yayi bata fa'di 'kasa ba sai akan hanunsa......" Kallon kallo suka bi juna da shi, yana sanye cikin inner black shirt me Vneck wanda ya fito da asalin farin fatarsa da faran three quatre, sai yanzu Deejah ta sami zarafin 'karewa fuskansa kallo, kyakyawan gaske ne yafi kama da Arabs idan ba kaji na hausa ba sai ka rantse balarabe ne, " Shima Irfaan sai yanzu ya samu ya 'karewa fuskanta kallo, chocolate color ce hancinta bai faye tsawo ba saidai tana da manyan ido da pink lips, a tai'kace dai she's average wajen kyau.... wani da'di ne yaji ya mamaye zuciyarsa dama ita ya shigo dubawa sai gashi ya ganta.... Sakinta yayi ta zame 'kasa, ya 'dan yamutsa fuska kafin yace" Are you blind or what? Deejah tayi 'yar 'kara kafin ta tashi tana ri'ke hannunta da ta buge ta furta" Am sorry "Young Master" ban san kana hanya bane..." gajeren tsaki Irfaan yayi ya furta" Annoying, daga haka yasa kai ya wuce.
"Deejah tabi bayansa da kallo yanda yake tafiya kaikace modeling yake, ta ta'be baki tace" tab lallai wnn akwai miskili, mugu kawai shine harda yardani a 'kasa, kai wnn ko ka'dan beyi kirkin Sir ba, sauri sauri ta haye sama ta mu Nilam sai rigima take na rashin ganin Deejah Nadiya na rarrashinta.... da sauri ta 'karaso" Oh my baby am here... Nilam ta mi'ke ta tafi a guje ta rungume Deejah, Nadiya ta galla mata harara kafin tace" Wai ke Deejah me kika dauki kanki a gidan nan ne, don't you know your obligation again, kin tafi kin barni da Nilam tana faman mun kuka, gidan uwar wam ma kika je a daren nan. Deejah na rungume da Nilam tana rarrashinta ko kulw Nadiya bata yi ba, tsaki Nadiya ta buga kafin ta fice tana fa'din duk daddy da Amma ne suka baki fuska, useless kawai.
"Nilam tace Deejah where have you been,.... Deejah ta kwantar da Nilam bisa gado tace" am here Angel pls stop crying, bazan sake fita na barki ba kinji...." gyada mata kai tayi ta kwanta lup a jikinta......
πΈπ»Queen Samyπππ..........
[8/19, 06:23] Umar Dalha: ππππ *Mallakin waye*
πΉ11
"Irfaan yana shiga 'dakinsa fuskan Deejah ke masa gizo haka kawai yaji ya tsinci kansa cikin farin ciki, zama yayi yana tuna fararen 'kwayan idonta, gajeren tsaki yayi gamida dafe kansa yace" ohh goshh why all this, why do I always have to think about her, ever since I set my eyes on her aikin kenn tunaninta,... "Tsaki ya kuma yi dan shi ko ka'dan mata basa gabansa, har zaman da yayi a US dukda kawo kansu da sukeyi amma ko ka'dan Irfaan bai ta'ba fa'dwa relationship da wata ba saidai friends kawai which is norms...
"Laila na kwance jikin Safwan yana shafa gashin kanta bayan sun gama aikata alfashansu, tallafo kanta yayi kafin yace" Swt baby kinsan meye, girgiza kai tayi gamida yin fari da idanu dan ba 'karamun da'di take ji ba idan ya kirata da sweet baby tinda a zahiri ta fisa. Sai ka fa'di 'dan cuty na. Zama yayu sosai kafin yace " ji nake kamar cin amanata yayi yawa, kefa matar yayana ne wanda ya kasance gata a gareni, har ya mutu baisan ina cin amanarsa da matarsa ba, yanzu kuma yaya kike idan Aziza tasan ni kwarton mahaifiyarta ne....." Dalla dakata 'dan Cuty, haka kawai muna tsaka da jin da'din rayuwarmu ka fara kawo tunanin nadama, Aziza bazata ta'ba sani ba haka su Hajiya da Yakumbo.... Zaiyi magana Laila ta sakalo kansa gamida zira harshenta cikin bakinsa, nan fa suka mance da komai suka ci gaba da aikata masha'a....
"Kasancewar yau zai fara halartan Office yasanyasa ya shirya da sassafe dan Irfaan akwai respecting time, bai yarda da African time ba, kai tsaye ciiin gidan ya nufa yanda ya samu Hajja ne kawai a parlor tana displaying warmers bisa dinning, da murmushinta suka soma gaisawa tana fa'din 'karamin Alhaji badai tafiya zaka yi ba. Murmushi ya 'danyi yace" no hajja, office zanje, Amma ta tashi kuwa? Bai gama rufe baki ba Amma ta nufo downstairs fuska fal fari'a, jikan nata ya mata kyau sosai yau, girma da 'kwarjininsa sun kuma fitow.
"Morning Pretty, Irfaan yace sanda yake zama bisa dinning, Amma ta 'karasao ta manna masa peck a kumatu tace morning my boy an fito, kai ya gya'da sanda yake 'daura tsillin pancake bisa plate, Amma ta kallesa tana murmushi tace" Irfaan don't tell me har yanzu kana nan da 'dabi'ar ka na 'kin cin abinci. "Murmushi yayi sanda yake zuba zuma bisa pancake 'din kafin yace" Nothing has changed Amma na, mi'ka mata plate din yayi yace have some, girgiza kai kawai tayi tace" pancake da zuma abincin turawa ai sai ku. Murmushi Irfaan yayi ya soma cin pancake din suna hira da Amma har ya gama, mikewa yayi yayi pecking hannun Amma kafin yace toh Amma na ni na wuce. Amma tace Allah bada sa'a 'dan Amma kafin Irfaan ya fice.
"Amma tana haurawa sama zata wuce zuwa 'dakinta taji kaman sautin kuka daga 'dakin Deejah, a hankali ta tura 'kofan ta shiga, Deejah na zaune 'kuryan gado ta kifa kai da gwiwa tana sharan kuka.... " Amma ta 'karaso da sauri, Subhanallahi Deejah lafiya?...
"Da sauri Deejah ta 'dago kanta ta shiga share hawayen kafin tace" lafiya lou Amma......" Girgiza kai Amma tayi tace ba lafiya ba, kuka fa kikeyi, ko bakida lafiya ne, maza tashi mu tafi asibiti.... girgiza kai Deejah tayi kafin tace" lafiyata lou Amma, toh kukan me kikeyi...
"Deejah ta kalli Amma kafin tace zan gaya maki Amma wata 'kila na sami sau'ki, Amma ta matso gamida ri'ko hannayen Deejah tace" ina saurarenki fa'da mani meke faruwa may be I can help.
"Deejah ta soma fa'din" Amma tun ina 'karama nake mafarki da wata mahaukaciya, kullum nayi mafarki da ita nakan tashi najini cikin farin ciki mars misaltuwa, akwai wani abu dake dam'ke hannun mahaukaciyan tun ina 'karama nake binta ta bani bata bani ba, gashi yau tana 'ko'karin mi'ka mun kenan mota tabi kan mahaukaciyan nan..... kuka ya kuma kufce ca mata, Amma cike da al'ajabi take rarrashin Deejah, Deejah taci gaba da fa'din, Amma ba rashin kar'ban abun bane yasani kuka a'a kuka nake kardai mahaukaciyan nan mutuwa tayi..... ina sonta Amma, ina jin sonta har cikin raina...... "Amma ta rungumo Deejah ta soma fa'din" kiyi ha'kuri Deejah, mafarkin ki na tareda tarin al'ajabi da ban mamaki, amma kar ki damu addu'a zakitayi abun da kike gani a mafarki ya zame maki alkhairi, idan sharri ne kuma Allah ya ka'de maki shi. Deejah ta amsa da Ameen. Amma tace maza ki tashi kije kiyi kalaci nasan bakici komai ba, Deejah ta 'dan murmusa tace" naci tareda Nilam kafin su wuce sch,....
"Tafe yake a motarsa 'kirar Infinity 2016, a nutse yake tu'kin har yayi parking a farfajiyan M&M Builders, da sauri wani security ya 'karaso ya bu'de masa 'kofa kana ya kar'bi car key 'din ya wuce da ita parking lot, shi kuma Irfaan ya nufi building 'din, Kai tsaye Office 'din Engr ya wuce.
"Engr yana ganinsa ya mi'ke ya rungumosa kana yace" welcome to the company Architect. Irfaan Mumtaz. I hope you'll enjoy working with us. Murmushi Irfaan yayi yace thank you daddy. Ya jima a office din Engr suna tattaunawa kafin akayi directing Irfaan zuwa Office dinsa.....
"A 'bangaren Yusra kuwa sosai taji haushin Safwan, ko waya ya mata bata 'dagawa, haka rabonta da club tun ranar da sukayi fa'dan, Deejah ma bata kuma komawa ba haka ta bar 'daukan wayan Safwan, Shiko Safwan hakannya nuna masa Deejah tana sonshi knn tinda gashi har tayi fushi da shi sabida kishi, Yusra ma knn kishinsa take, lallainya zama champion. Ya 'dau alwashin bazai ha'kura da Deejah ba haka bazai janye 'kudirinsa akan yusra ba.
******************************************
Kwanci tashi babu wuya wajen Allah, yau gashi Laila ta fita daga takaba, haka su Nadiya da Aziza sun zana jarabawan waec 'dinsu.
"Tana zaune gaban Hajiya suna tattauna lamarin, Hajiya ta dubi Laila tace toh mun wuce sira'di 'daya, yanzu mun kashesa mun kashe banza abunda yake gabanmu shine shiga gidan Engr Nazif, ina mai tabbatar maki idan muka kame Engr Nazifa toh fah shiknnn komai zaizo mana da sau'ki, kinga idan kin auresa Aziza ma zata samu ta auri Irfaan.
"Laila tayi wata murmushin jin da'di tace" wllhi Hajiya bakiji wani da'din da nake ji ba, ace yau na zama matar Engr nifa shiknn burina ya cika... Hajiya Karima tayi dariyan basawa kafin tace" haba 'diyata ai ki kwantar da hankalinki kisa maranki Nazif ya zama mallakin ki an gama, kar ki mance ni Karime nice uwarki, kar ki mance irin ba'ka'ken ayyukan da nayi a baya, akan na mallaki M&M babu abunda bazanyi ba, na Shanye Ma'aruf, na kashe matarsa, na salwantar da tilon 'yarsa da ya mallaka nan fa'din duniya da abinda ke cikinta, snn na kashe Alhj Mumtaz, na kashe mijinki...... toh meye ku, a zai gagareni ai babu shi..... Laila tasa dariya da gu'da tace" kai Hajiya shiyasa nake sonki, duk wanda yaci tuwo dake miya yasha......
"Innalillahi wa inna ilaihirra'ji'un..... abinda Alhj Ma'aruf ya iya fa'di knn, abubuwan dayaji daga bakin Karima sun matu'kar razana sa..... Suna tsaka da zance ya banke 'kofa ya shigo idanuwansa sunyi jazur gaba 'daya ya sauya....." Take cikinsu ya 'duri ruwa dan sunsan yaji komai..." Alhj ka min rai ka tsaya na maka bayanin komai, Hajiya Karima ta fa'di sanda take dur'kushe kan gwiwoyinta...." Girgiza kai Alhj Ma'aruf ya soma kafin yace" kin cuce ni Karima kin rabani da mutane masu 'kaunata, Karima anya ke mutum ce, kin cika babban azzaluma wacce ko a labari ban ta'ba jin me hali irin naki ba. Amma yau Allah ya toni asirinki, ki sani daga lokaci me kaman ta yanzu babu aurena akanki na sake ki snn laifukan da kika yi bazaki gudu dasu ba... Kuka suka kurma ita da laila... Alhji Ma'aruf kiwa ko ajikinsa ya shiga dialing lambar Engr Nazif. Engr yana dauka Alhj Ma'aruf yace maza kazo gidana ina nemanka urgently, daga haka ya kashe wayan.
"Kuka Karime da Laila suke suna ro'komsa gafara.. Inaaa nan shima yaji kwalla ya ciko idonsa, ya kasa gasgata abin da yaji, take yaji 'kirjinsa na masa zafi zuciyansa kaman zata fito.... "Dur'kusawa Alhj Ma'aruf yayi a wajen yana dafe da 'kirjinsa.... Laila tayi kansa a guje tana fa'din Baba Baba meke damunka.... Hajiya Karima ta tuntsure da dariya ta jawo Laila baya tace barshi ya mutu ai hakan ma yafi mana sau'ki....Laila ta kalli Mahaifiyar nata ta tabbata babu 'dan'danin imani a tattate da ita, tace Hajiya kiga fah yanda yake shur shure mu taimaka masa, Karime ta watsa mata harara tace toh ya mutu ma mana, idan ya mutu kinada asara ne, kar ki mance ba ubanki bane, da ya farfa'do ya toni asirinmu ki rasa gadonsa ai gwara ya mace kawai abinsa.
"Laila ta girgiza kai tace" a'a hajiya ko babu komai shi na tashi na sani a maysayin ubana, kuma ya nuna min so maras misaltuwa..... "Tsaki Hajiya Karima ta buga kafin ta lailayo wata uwar ashar ta juye wa Laila.....
πΈπ»Queen Samyπππ.........
[8/19, 06:25] Umar Dalha: ππππ *Mallakin waye*
πΉ12
"Pillow Hajiya Karima ta 'dauko ta shiga danne fuskan Alhaji Ma'aruf dashi, Laila kam jikinta yayi sanyi sai kuka take, Alhaji Ma'aruf sai shure shure yake... jin ana ta'ba 'kofa ha'de da sallama yasa Hajiya saurin jifa da pillown muryan Hure me masu aiki ta jiyo, Hure ce ta shigo parlorn tana fa'din hajiya Alhaji nada ba'ko a waje..... ai Hure bata gama rufe baki ba ta shiga doka salati ganin Laila tsugune gaban Alhaji Ma'aruf dake kwance 'kasa a wajen tamkar maras numfashi, Hajiya Karima ta ci gaba da kukan 'karya tana runtumo salati... Da sauri ta dubi Hure tace ce masa ya shigo ya taimaka mana Alhj babu lafiya. A tamanin Hure ta fice ta kirawo Engr.
"Ganin Alhaji kwance a 'kasa yasa Engr saurin 'karasowa yana jijjiga shi yana fa'din Alhj Baba Baaba.... Hajiya Karima tace duba mani Nazif Allah sa yana numfashi ta kuma fashewa da wani sabon kuka, Laila na tsugune gefe na kuka. Cicci'ban sa Engr yayi yace bai mutu ba mu tafi asibiti.... " Jarr uban chan salatin arna, abinda Hajiya Karima tace a zuciyanta knn. Ido wuri wuri ita da Laila suka bi bayan Engr, addu'an Karime bai wuce Allah sa Alhaji Ma'aruf ya cika a hanya ba....
"Suna isa asibiti likitoci suka kar'besa, Karime da Laila suna zaune reception ciki a tsure, Engr ya 'karaso yana fa'din" Hajiya lafiya me ya samesa, 'dazu mukayi waya dashi lafiya lafiya yace yana nemana urgently sai ga abinda na tadda kuma.
"Karime ta yarfe zufan da ya 'keto mata tana sharan 'kwallan 'karya kana tace" wllhi Nazif am shigowansa knn yace mana tinda Laila ta gama Idda bashi da sauran birin da ya wuce yaga Ka auri Laila....." Da mugun mamaki Engr ke kallon Hajiya karima kafin ya furta aure kuma? Laila kam tuni ta mance komai ta shaga da kallon fuskan Engr. Karime tace ey Nazif kaji abinda yasa yace yana nemanka da gaggawa toh kafin ka iso ya 'dibi jiki ya fa'di.... " Inna lillahi wa inna ilaihirraa'jiu'un abinda Engr ya iya furtawa knn.... suna a haka Dr ya fito a tare suka nufi Dr suna tambayan yaya.
"Dr ya dubesu yace" ina iyalinsa ina son magana da ita.... Hajiya Karima dake ta faman addu'an Allah sa ya mutu da sauri tace gani nan likita, kar ka damu ka fa'da mana komai wa'en nan 'ya'yansa ne basai mun ke'be ba...." Dr yace magana ta gaskiya Alhaji ya samu heart attack, snn ya samu shanyewan 'barin jiki wanda yasa zai jima a coma kafin ya dawo daidai, idan ya dawo daidai ma ba lallai ne maganarsa ta dawo ba.... wani ihu me ha'de da sautin kuka Hajiya Karima ta sake a fili, cikin ranta kuwa banda muran da rawan shoki bata komai. Laila ma kuka ta saka me tsuma zuciya. Engr kam sosai suka basa tausayi, kallon Laila yayi sanda maganar Hajiya Karima ya dawo masa cewa, maganr da Alhaji Ma'aruf zai masa kan batun ya auri Laila ne. Sun basa tausayi ainun. Haka ya dinga rarrashunsu yana basu baki. Karime ta dubi likita tace" Dr zamu iya ganinsa, Dr ya jinjina kai kana yace" bazaku iya ganinsa ba dan yanzu haka yana Intensive care ne, saidai ko zuwa gobe....
"Engr yace mu 'karasa office 'dinka Doc ina son muyi wata magana, babu musu Dr yayi directing Engr suka wuce office dinsa.
"Suna wucewa Hajiya Karima ta tuntsure da dariya kana tace" Kai amma fa Ma'aruf akwai taurin ran tsiya, banda 'diba ma kansa wuya ai da mutuwansa yayi da ya fiye masa, amma banda haka ina amfanin wann rayuwa da zai fuskanta wanda shida babu duka 'daya.
"Laila ta goge ragowar hawayenta tace" Kai amma Hajiya kin iya tsara zance wllhi, ga dukkan alamu Engr ya yarda da batunki, wayyo Allah na kusa zama Mrs Nazif Mumtaz. Karime ta har'de 'kafa tace sosai ma kuwa, kede kawai ki jira ki ga ikon Allah.
"Engr ya dubi Hajiya Karima bayan sun fito daga ofishin likita yace" Hajiya muje na kaiku gida ku samu ku 'dan huta... Karime ta girgiza kai tace" um um Nazif nidai kam ina nan bazan iya tafiya na bar Alhaji a irin wnn yanayi ba, saidai ka kai Laila gida. Juyowa yayi ya dubi wacce ta kira da Laila, tsaf ya ganeta wacce taje office dinsa kwanaki. Ba musu yace toh shiknn Hajiya, anjima driver zaizo ya tafi da ke, Allah ubangiji ya basa lafiya. A fili Karime tace ameeen a ba'dini kuwa ba ameen ba tace. Daga haka Engr yasa kai ya fice daga asibitin.
"Hajiya Karima ta dubi Laila data rakasa da ido tace" Me kike jira da bazaki bisa ba, dalla wuce ki bi bayansa ya kaiki gida, daga haka ne zaki samu shiga wajensa. Da sauri laila ta mi'ke tana fa'din " toh hajiua kar fa ya dizga ni ne... " Baki sake Hajiya tace" kaji sha sha ke komai sai na nuna maki, nan gaba Aziza ce zta na nusar da ke hanya ina ga...., toh tsaya nan kar kibi bayansa, a sittin Laila ta fice tabi bayansa.
"Yana zaune cikin motarsa har ya mata key dan gaba daya ya mamce da batun Laila, saiji yayi ta bu'de marfin motan ta shigo. Kallo 'daya ya mata ya 'dauke kansa. Zama tayi cikin motan kafin ya soma driving, sunfi minti goma a haka suna tafe kan titi babu wanda ya iya furta koda kalma guda wa 'dan uwansa. Sautin kukan Laila ya jiyo a hankali. Idan akwai abinda Engr baiso tofah shine kukan mace, "Ya salam" ya furta a hankali, hannu yasa cikin aljihun jampansa ya ciro hankacif ya mi'ka mata... "Hannunsa Laila tabi da kallo, hannun fari