Showing 66001 words to 69000 words out of 159062 words

Chapter 23 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10375

daidaita kanta kafin ta soma lallashinsu. Gaba daya suka rungume juna.
"Addu'a sosai Ammah tayiwa mummyn su irfan gaba daya suka amsa da ameen Ammah.


"Engr na kallon Irfan yana murmushi shi kadai yake ayyanawa a zuciyarsa _"koda ace son Deejah yake toh kuwa hak'ik'a zaiyi yak'i da zuciyarsa ya kalleta a matsayin d'iya danta kasance da Irfan, hak'ik'a farin cikin y'a'yan sa shine nasa_.
"Dafa kafadan Irfan yayi kafin yace" Son na amince ka auri Khadija na amince Son...... "
"Kallon Engr Irfan yake full of surprise kafin ya mike yana fadin " Really daddy, you mean ka amince na kasance da farin cikin rayuwata. Gyada masa kai Engr yayi yana murmushi kafin yace" yes Irfan na amince zan cikawa Khadeejah burinta na sanya yaranta cikin farin ciki ko yaushe, forgive me Son akan abunda na maka earlier I lost my mind ne that's why, I don't know why did that......... "Irfan kam baisan sanda ya rungume Engr ba yana masa godiya"
"Ammah ta goge hawayen idonta tana kallonsu cike da si kauna, kaikace yaya ne da k'ani.


"Ya karaso ya rungume Ammah kafin yace" Ammah I'll be with her forever...... Murmushi Ammah tayi ta shafi kansa kafin tace " farinckinku shine namu Irfan.
"Engr yana kallonsu yana murmushi ya k'araso ya dafa kafadun Irfan yace" suna hada ido Irfan yaji kunya ya dan suke kansa k'asa yana sosa k'eya.
"Murmushi Engr yayi kafin yace zamuyi maganar ranar auren da Granny dinka kaji, for now ka mayar da kayanka mazauninsu.
"Rungume Engr Irfan ya kuma yi yanai masa godiya.


"Ammah ta jawo kunnesa tana fadin " ko kunyata bakaji ko oya wuce bathroom kayi wanka ka hau doki...... zaiyi magana ta mika masa towel ta jefa sa cikin toilet. Tana murmushi sanda ta jiyo shi yana fad'in " I'mmmmmmmmmmm in looooooooooveee.
"Murmushi kawai tayi ta shiga tattara masa dakin tana fadin "Silly boy hadi da girgiza kai......




πŸ‘ΈπŸ»QueenSamyNovelsπŸ˜πŸ’„πŸ‘„...........
[8/22, 14:47] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


47


*Β©Sameena Aleeyou*


"Na shiga uku momy yanzu inaji ina gani shegiyar yarinyar nan zata auri Irfan..... gaskiya momy bazata saku ba, ni danaga auren Irfan da wata ai gwara naga mutuwata.. cewan Azee da damuwa ya nuna k'arara a fuskarta.
"Murmushi Laila tayi kafin ta dafe kafa'dun Azee tace" yaro dai yaro ne, idan banda abinki ina kika tab'a ganin anja damu, ki daina sarewa kinaba dani Azee saikace ba d'iyar Laila jikan Hajiya Karime kike ba, ki kwantar da hankalinki, idan sunsan wata basu san wata ba, idan mun b'ulla masu ta sihiri da asiri baiyi aiki ba sai mu b'ulla masu ta makirci kissa da kisisina...." shiru tayi na d'an lokaci kafin ta d'ago tana duban Azee tace " yawwa ina abokin Irfan da kwanaki ya amshe pride d'inki na d'iya mace.
"Azee ta d'an tab'e fuska kafin tace " wai Ahidjo tabb niko me zanyi dashi...
"Laila tayi murmushi kafin tace" ai kuwa dole yanzu yayu mana aiki tinda dama kince son Deejah yake...." tsalle Azee ta daka kafin tace " ai kuwa nama tuna momy turn dinsa yazo dole ya bani something in return na abinda na basa kwanaki, dole yasan yanda za'a k'ulla sharri wa jarabebbiyar Nanny din nan.
"Dariya Laila tayi tana kallon d'iyar tata yanda farin ciki ya mamayeta kafin tace" Oh Azee bansan wani irin so kike wa Irfan ba... "Azee ta murmusa kafin tace" Wllhi momy ina masa son da bana maki yanzu dai I should get rid of that so called nanny din dan ita taimin cikass....." Laila kam dae baki sake take kallon Azee cikeda mamaki( _Wai tafi son shi akan uwar data haifeta... what a mess πŸ˜•_)...


β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…

*"Two weeks later*


"Zaune suke a Cafeteria suna cin snacks fitowarsu kenan daga Enxamz yau sukayi last paper gaba d'aya jinsu suke cikin farin ciki dan kuwa zasu samu hutun zangon karatu na farko wato first semester.
"Nadiya sai faman nunawa Deejah pics din brides take wai ta zab'i shigar da zatayi a bridal shower dinta.... "Azee kam gaba d'aya ji take tamkar zuciyarta zai tarwatse dan tsananin tashin hankali, gaba d'aya k'arfin hali take tana dannewa musamman da yanzu aka tsaida maganar auren Irfan da Deejah.

"Shigowan su Mus'ab Turaki course mates dinsu cikin Caf din ne ya katse masu hiran da suke... Take Deejah ta had'e rai dan kuwa ko kad'an bata son yanda su Mus'ab dasu Nadiya ke shaking hannaye tamkar ba yaran musulmai ba, ko tai masu magana cemata suke ai sch life ne so let's be social, gwarama Nadiya zata iya cewa tashin Turai ne har yanzu a jikinta amma Azee kam zunzurutun son wasa da maza ne kawai snn itake dad'a influencing Nadee. Dan haka nema ko kadan Deejah bata sake masu Mus'ab.
"Table din gefe suka k'arasa suka zaune, Mus'ab ya d'an tab'a k'afar Sudais gamida kashe masa ido d'aya alamun kar ya spoiling masa mission dinsa.
"Murmushi Sudais yayi kafin ya d'aga masa gira d'aya ya mik'e ya nufi table d'in su Deejah.
"Guys you're all invited to the farewell party of MUS'AB TURAKI (VICE PRESIDENT SON) As you all know that he's living the country tomorrow.
"Cikeda masifa Deejah tace" and who cares, kaga mun maka kama da masu zuwa party ne..." da sauri Azee ta katse ta da fad'in " Aaa haba Deejah zamuje mana, miye a ciki dan zamu partyn ban kwana da d'an ajinmu.
"Murmushi Sudais yayi kafin yace" Your presence is very important must especially you Arab girl.... yayi nuni da Nadiya da tun tsayuwarsa take faman danna wayarta. Sai snn Nadiya ta d'ago tana dubansa. Nuni tayi zuwa k'irjinta da phon dinta tace "Mee!! Surprisingly!
"Sudais ya gyad'a kansa kafin yace" yeah the vice president son have a surprise for you, anyway idan kun gama deciding ku samemu wajen cars dinmu sai kuji venue din. Daga haka Sudais ya juya ya wuce wajen zamansu..


"Deejah ta gallawa Azee harara tace" haba Azee meyasa kika biyesa ya maidamu 'yan iska ne masu zuwa party.... " kai Deejah meye iskanci a ciki dan munje farewell party din Mus'ab, kina gani mu kadai suke kulawa dukda ji da kai da 'yan click dinsu sukeda.... "Ringing din da wayar Deejah tayi ne yasata tashi ta nufi restroom ganin Sahibinta ne me kiranta,...
"Haka Azee tayita zuga Nadiya wai she's special tunda har Mus'ab na shirin bata surprise duk fadin Nile, nan kuwa Nadiya ta biyeta tana jin yes kenan duk tafi sauran 'yan matan sch din haduwa, mikewa sukayi suka nufi yanda Su Mus'ab suka pake Luxurious Cars dinsu.
"Suna isa wayan Azee dake cikin jaka ya soma ringing tana ganin Ahidjo ne tace wa Nadiya bari taje amsa wayan Hajiya, hajiya ke kiranta, nan Ahidjo ya sanar da ita su had'u a guest house dinsa urgent.
"Sudais ne ya bud'e wa Nadiya bayan Range Rover din Mus'ab take ta soma jin jiri bata san yaya akayi ba sai shigewa cikin motan da tayi...
"Sadiq da shigowarsa Nile kenan ya hangi wata kaman Nadiya ta shige bayan range rover da wasu maza take yaji k'irjinsa na dukan uku uku, sauri sauri ya ajiye Mamie wajen aikinta wato Cafeteria ya juya da kan motarsa nan ya tarar motan da Nadiya ta shige na k'ok'arin ficewa daga Nile, take ya soma binsu a baya cikin sauri dan kar su b'ace masa.


"Deejah tana dawowa Caf ta tarar babu su Nadiya, layinsu ta soma kira amma bai shiga, na Azee nema ya shiga sau d'aya ba'a d'aga nan tayi tunanin ko Department suka koma dan dama sunyi missing examz guda d'aya, tayi tunani ko sun koma yin complain ne. Ganin Mamie na shigowa da kaya yasata saurin k'arasawa ta amshi wasu kayan suka soma gaisawa.


"Yana shigowa cikin Nigerian Turkish Nile University ya shiga neman layinta, tana d'agawa yace gashi ya iso tana ta ina ne, nan ta sanar dashi tana Caf.
"Kai tsaye Irfan ya wuce Cafeteria, yana gama parking ya fito ya nufi cikin Caf din,
" Daga yanda take zaune ta hangosa... "Sanye yake cikin k'anan kaya Royak blue shirt wanda ya k'ara fito da hasken fatarsa yana sanye da wando ash chinos, gashin kan nan nasa sai shek'i yake as usual, idanunsa sanye cikin bak'in sunshade, yana hangota ya sakar mata murmushi nan itama ta maida masa martani, ganin yamda emmata kai harma da samarukan da suke zaune a caf din sun k'urawa Irfan ido wasu na faman fad'in "Woow handsome" yasa Deejah jin kishi sosai har saida taji dama bata ce ya shigo caf din ba, ita kanta bata son tana son Irfan tana kishinsa irin haka ba.
"Kan ya k'araso ta mik'e ta nufi yanda yake dan bata isa ya zauna a Caf din nan ba emmata su cinyesa da kallo. Gaishesa tayi sai ture turen baki take,
"Irfan ya sunkuyo da kansa ya rage tsayinsa saitin kunnenta kafin yace" Why the long face baby, I hope the examz was sweet like you,.
"Turo baki ta kumayi kafin ta gyada masa kai alamun examz yayi dadi.
"Murmushi ya kuma yi kafin yace" toh ture turen bakin me ake bayan examz was fine, ko ba'ayi murnan gani na bane... "zatayi magana yayi saurin sunkuyo da bakinsa saitin kunnenta cikin sigan rad'a yace" Ohh na tuna baby you must be exhausted kina buk'atan massage,.... muje gida nayi maki tausa....
"Zaro ido waje Deejah tayi tana kallonsa, irin yanda yake so yaga tayi da idanunta.. harara ta b'alla masa kafin tace " ya irfan muje ka gaisa da Mamie gata a can. Irfan ya amsa da toh yana binta da kallo me kashe mata jiki.
"Bayan sun gaisa da Mamie ta tambayesa aiki dasu Ammah, Irfan ya amsa da lafia lou Mamie, yaya Dada da jiki, Mamie ta amsa masa dacewa " Da sauki Irfan, kaida Deejah kun gujemu kwana biyu ko duk shirye shiryen bikinne.. "Irfan ya murmusa yana sosa k'eya kana yace" zamuzo insha Allah Mamie musamman mu duba jikin Dada, Deejah kam sunne kai tayi a k'asa . Mamie tace "toh Allah ya kawo ku Allah kuma ya sanya alkhairi, gaba daya suka amsa da ameen.
"Deejah ta bar sallahu wa Mamie cewa" Idansu Nadiya sun dawo ta sanar dasu ta tafi tareda ya Irfan.....


"Dukda driving yake amma hankalinsa na kanta ganin tasha kunu ta turo baki,
"Baby wai waya tab'a min kene na ganki haka, ko exams dinne.
"Girgiza kai tayi ba tareda tace komai ba,
"Toh ko dai baki son surprise din da nace zan nuna makin ne.
"Nan ma ta girgiza kai....
"Ok na gane ganina ne knn baki so.
"Da sauri ta dago tana dubansa gani tayi idonsa naga titi. Zaiyi magana tace " ba kaine kazo duk emmatan dake cikin Caf sun kare maka kallo...... " Dariya sosai Irfan yake harda buga starry kafin ya juyo yana dubanta yace" ashede duk acikin kishina ne, toh kiyi hak'uri zan fara saka emmmm what's thay ting that women use to ware... yayi shiru kaman me tunani.... Deejah tace" me kenan.
"That black thing like ningers......
"Ohh nikab.
"Ehen nikab timda bakiso a kalle maki ni......" Dariya suka fashe dashi gaba dayansu.... gwanin ban sha'awa kana ganinsu kaga masoyan juna.
"Master ina zaka kaini ne..... tayi maganan cike da shagwab'a.
"Ya kwaikwayi muryanta yace" am not gonna kidnap you baby, just wait and see.
"Murmushi kawai tayi tana kallon yatsun hanunsa masu kyau dasu yanda yake driving, sonsa da k'aunarsa na ratsa illahirin jikinta.


"Sadiq na ganin sun shige gate din wanu gida a asokoro yabi bayansu shima ya shige kasancewar samari ne da emmata keta faman zarya a gidan gaba daya babu wanda ya lura dashi.
"Yanayin da yaga emmatan da samarukan ya basa tsoro take yaji k'irjinsa ya tsanan bugu.......


"Azee ne kwance saman k'irjin Ahidjo tana wasa da sajansa yayinda shikuma ke shafa gashin kanta.
"Gaskiya Ahidjo you need to do something..... we can't let that happen, we can't let them get married we need to stop them kota halin k'ak'a, dan gaskiya I can't bear loosing Irfan, shine rayuwata.... Azee ta fad'i sanda ta soma yi masa wasu salo.
"Murmushi Ahidjo yayi kafin ya dad'a matsota cikin jikinsa ya d'aura yatsansa kan lips d'inta ya shafawa yake fad'in " just calm down baby doll na gaya maki, auren Irfan kaman kinyi an gama as far as ina raye, yanzu dai bala'in yu warki nakeji feed me kafin ayi wancan zancen..... ya k'areshe maganar yana saka bakinsa cikin nata..........


*Muje zuwa readers.... luv you all😍😘*


Queensamynovelsβ˜…
[8/22, 14:47] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


49


*Β©Sameena Aleeyou*


_Queen Samy Novel Forum......πŸ“–πŸ“š_


"Irfan na murmushi ya dubi Deejah data rufe idanunta da tafukan hannayenta yace" Oya open your eyes....... "Deejah na bud'e idonta tayi tozali da makeken gida me kyaun gaske wanda zamu iya cewa is more of glass kaman dae ginin k'asashen turawa. A hankali ta furta" Woooow! Masha Allah this is so amazing.
"Irfan na murmushi yana kallonta hannayensa hard'e a k'irji yana karkad'a d'an makullin mota yace" yayi maki???
"Kallonsa tayi da mamaki kafin tace" Kai ya Irfan this is awsome infact this is spectacular. Babu wanda zaiga wnn gida yace bai masa ba. Gidan waye?? Ta k'arashe tambayar tana d'an satan kallonsa.
"Murmushinsan nan mai tsada ya kuma yi kafin yace" this is your house, our house...... Yanda zamu building namu family din yanda zaki haifa mun yara masu kama dake, tun ranan dana d'ora idanu na akanki na soma zanamana gidan da zai dace da rayuwarmu, toh finally yau an gama ginawa shiyasa na d'aukoki ki gani, idan akwai abinda be maki ba sai a canza shi right the way......." Kasa daina kallonsa tayi har saida yai mata far da idanu.
"She just couldn't believe it a bit, wai wani irin so irfan ke mata haka, a hankali ta sauk'e idonta zatayi magana sai jiyo muryansa tayi yana fad'in" let's go in, mu shiga kiga yanayinsa... "jiki a sab'ule Deejah tabi bayan Irfan....




"Duk abin duniya ya dami Sadiq yama rasa wanne zaiyi, ya kai Nadiya gida ne ko ya koma can sch dinsu wajen Mamien sa ne, yana tsaka da wann tunani ya jiyo muryanta idonta a lumshe take fad'in" plssss don't take me home, I beg of you pls kar ka kaini gida a haka am sure Daddy da ya Irfan kasheni zasu yi.....tana maganan cikin magagi tamkar me maye tana lumshe idanu......
"Shiru Sadiq yayi yana nazarin kalaman nata.... Bai tab'a k'are mata kallo ba sai yau, a shekare bazata wuce 17 ba dan su Deejah sun girme mata, farace tass irin na larabawa kaman dai Irfan saidai bata kaisa hasken fata da kyau ba. Sadiq ya lumshe ido dan kuwa take yaji ya rasa tunanin me yake gameda Nadiya, kai tsaye gida ya wuce da ita dan ya tabbata by now Ruqayya ta dawo daga sch.




"Laila ce ta fito cikin shiri ta k'arasa sashen Ammah ta sanar da ita ta tafi gidan Hajiya, Ammah tace a dawo lafiya ki gaida min Kariman, nima inason zuwa duba jikin baba Alhj yau nake cewa idan Nazif ya dawo gwara ayi maganar fitar dashi waje baza a biye nashi ba ai shi Baba Alhajin dukda baya so gwara a jaraba wani k'asar ko za'a dace.
"Laila da k'irjinta ya soma harbawa a tsaitsaye ta amsawa Ammah duk ta dabirce kafin ta fice sai faman sauri take ta k'wala wa Habu kira ya fito mata da mota daga parking lot.
"Habu yace Haj ina muka nufa kinsan Alhj baya so kina driving......."Galala Laila ta kalle sa kafin tace" Dalla fice ka bani key if you dont wan to get your self fired. ?.. ban son iayayi me ya shafeka tsakanina da mijina, ...... Habu cikin sauri ya fice jiki har na b'ari ya mik'awa Laila key.... "tsaki tayi ta fizge key din gamida jefa masa harara tace"en shishigi d sa ido.......




"Yaya wacece wnn Ruqayya ta tambaya fuska cike da damuwa, Sadiq ya sauk'e ajiyan zuciya yace" k'anwar Irfan ce wasu yarane suka so suyi attacking nata shine na kawota nan ta d'an warware kafin na kaita gida.
"Ruqayya dai bata gamsu da batun yayan nata ba gaba d'aya mood dinta ya canza dan kuwa tana kishin Sadiq sosai..... "Ya d'an kalleta yaga yanda ta had'e rai murmushi kawai yayi dab abun ma dariya yaso basa..... ganin ta mik'e zata fice yasa sa cewa" lil sis zo mana, dawowa tayi ba tareda tace komai ba. Shima din dan dakewa yayi kafin yace" kawo min ruwa a bowl da d'an towel....... "Zaro ido Ruqayya tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login