Showing 108001 words to 111000 words out of 159062 words

Chapter 37 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10393

takaici.




"Kamar munafuka haka tasa hannu tana k'ok'arin bud'e marfin motan, wani mugun kallo yake watsa mata kafin yace" Da uban wa ya kawoki, ko tare dani kikazo, wama ya baki izinin fita in the first place hum???
"Kasa amsa masa tambayarsa tayi ganin yanda fuskarsa ta koma jazur, "tsawa ya kuma daka mata koba dake nake magana ba, uban waye ya baki izinin fita cikin daren nan..
"Kwallan munafunci ta soma sharewa kafin tace" wllhi na razana ne sanda naga ka fita cikin sauri shiyasa nayi tunanin zuwa gida.
"Gajeren tsaki yayi dan yama rasa kan wani dalili yake tambayarta, duk da matarsa ce, bud'e marfin mota yayi kafin ya dubeta yace" ki koma a yanda kikazo amma ba'a motata ba, and let me warn you for the last time, duk randa kika kuma sa k'afa kika fita bada sani na ba toh a bakin aurenki, useless kawai, daga haka yasa kai ya fice daga gidan a guje..


"Tsayuwa cak Azee tayi tana binsa da kallo kaman ta saka hannu aka ta runtuma ihu ko zataji sanyi, wai duk sabida me Irfan ke wulak'anta ta, wata zuciya tace mata Deejah.. A fusace tasa kai ta shige sashen Laila fuuuu.


"Sun k'ule a d'aki ita da d'iyarta Azeeza, jimami suke ganin mazajensu na neman kufce masu duk kuma dalilin wann tsinanniyar yarinyar Deejah, wai shin yaya zasuyi su rabu da ita gaba d'aya ne, dole su nemo hanyar rabuwa da wnn jarabebbiyar wacce gaba d'aya sun rasa ita d'in *Mallakin Waye*...






"Washe gari koda Azee ta koma gida bata sami Irfan ba ya tafi office, dama tasan hakanne zata kasance. Zama tayi bisa sofa tana wani girgiza k'afafu sanda ta tuna kusan kwana sukayi suna neman yanda zasu b'ullo wa lamarin, k'arshe suka yanke shawarin zuwan wajen bokansu cikin satin nan....






"A b'angaren Deejah, fah sosai wann karan Daddy ya mata fad'a dukda lallashin ta da yayi ya nuna mata idan dai har ta d'aukesu iyaye toh ta mance komai.
"Ammah ma lallashinta tayi ta kuma nuna mata suma iyayenta ne, snn kan magan nan aurenta kar ta saka komai ranta, komai muk'addari ne daga Allah, Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi.....
"Hawayen tausayin kanta da soyayyan ahalin gidan Engr shi ya wanke mata fuska, su Nilam ne suka shigo cikin shirin tafiya sch gaba d'aya suka rungumeta... "Ammah da Nadiya suka bisu da kallo cikeda tausayawa....


*********************************
"Haraban gidan cike yake mak'il da mtane 'yan d'aurin aure, banda busa da hargowar mtane baka jin komai, Azee da Laila a sace suka samu suka fice daga gidan dan niyyanr su ta zuwa gidan bokan su, hayaniyar jam'a bazai bari a fahimci basa nan ba..


"Ammah ta dubi Engr tace" Nazif anya hukuncin da ka yanke yayi daidai, gyd'a kansa yayi kafin yace" insha Allah hakan shine daidai, zamuga alkhairinsa daga baya. Shiru Ammah tayi kafin tace" Toh Allah yasa hakan Alkhairi ne...... "Mikewa yayi ya sab'a babbar rigarsa kafin ya fice filin d'aurin aure..




"Tana zaune gefen Nadiya can k'uryar d'akin Ammah, dukda ta sani cewa an fasa aurenta amma haka kurum ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, zuciyarta bata gama yankewa ba saida taji marok'a suna ambato sunanta dana Nadiya a matsayin amare, toh kodai marok'an basusan anfasa nata auren bane.... "tunaninta ne ya yanke sanda taga Ammah ta shigo da fareren lafayya guda biyu Aunty Larai na biye da ita tana rangada guda, Ammah ta umarcesu dasu tashi su shirya..."Kallon mamaki Deejah ke binsu dashi da k'yar ta iya furta " Aunty irin kayan amarya fa kike umurtana na saka.
"Aunty Larai ta murmusa kafin tace" kema amryarce maza ku shirya ina nan dawowa, daga haka itama tabi bayan Ammah, gaba daya suka fice...
"Kallon Nadiya tayi fuska cikeda alaman tambaya, Nadiyan ma kallonta tayi dan bata fahimci komai ba..zatayi magana Nadiya ta girgiza mata kai alamun a'a kafin tace" Dee ki shirya kaman yanda suka umarce mu. Jiki a sanyaye hawaye na bin k'uncinta ta soma saka laffayar....






"Kan kace me zance ya gauraye cikin gida tsakanin ma'aikata, ai Engr Nazif ma kansa ya d'aura aure da Deejah, tuni Zulai ta d'au waya ta shiga neman layin Laila.
"Laila suna kan hanyarsu ta shiga Garko taga wayar Zulai, a hasalae ta soma mata magana, zancen dataji zulai na fad'a mata ne yasata kurma wani uban ihu tana zame gyalen kanta.....




QUENNSAMY CEπŸ‘ŒπŸ½
πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


75


*©Sameena Aleeyou...✍🏽*


_Queen Samy Novels Forum....πŸ“–πŸ“š_




"Azee ta dubi Laila tace" Momy wai lafia miye kiketa sunbatu ke kad'ai, Laila bata iya amsata ba sai kallon Kamilu driver d'inta na sirri tayi kafin ta malmalo masa wata ashar tace" Kamilu dan ubanka idan bazaka tuk'a motar nan ba ka bani na tuk'a,
"Kamilu duk ya daburce ya soma fad'in" Hajiya hanyarce bata da kyau amma ai yanzu zamu isa... duk gudun da Kamilu keyi Laila gani take kaman ba tuk'a motar yake ba, duk wani sanyin ac dake tashi cikin motar hakan bai hana zufa karyo mata ba tako ta ina,
"Azee dai tab'e baki tayi dan tun jiya take fama da ciwon ciki, gashi yanzu kaman ciwon k'aruwa yake neman yi, dan haka bata kuma bin takan Laila ba...




"Mintuna k'alilan ya kaisu gidan Boka Wargaji, Wargaji yana ganinsu ya kwashe da wata dariya kafin yace" an sanar dani kuna hanya, Laila dai har lokacin bata koma daidai ba, kan su fad'i meke tafe dasu tuni Wargaji ya labarta masu abunda ya kawo su, nan fah Shedan ya masu jagora suka kuma yarda da aikin wargaji,
"Laila dai tayi tsur tsuru jin Wargaji bai ambata mata batun auren Deejah da Engr ba, dan haka tuni ta ware baki ta soma fad'a masa iyaka abinda taji.... wata dariya Wargaji ya bushe dashi kafin yace" Bana tsamman mijinki shi ya auri yarinyar nan, saidai koma waye ya aureta hak'ik'a makusancin ku ne, hasashe na yak'i nuna mana waye tak'amemmen mijin yarinyar,
"Yanzu me kuke so ayi. Wargaji ya tambaya. "Da sauri Azee tace" kawai a kasheta ni kurum jikina na bani nawan mijin ta aure mun.
"Wargaji ya bushe da dariya kafin yace" Kasheta bamai yuwuwa bane, kurwarta yanada tsananin k'arfi bisa rik'o da Alqur'ani da tayi, kudai canza wani abin...
"Hankalin Laila ya d'an kwanta tunda wargaji yace mata ba mijinta Deejah ta aura ba, amma dai dukda haka akwai sauran fargaba atattare da ita, "Azee ta dubeta fuska fal damuwa tace" Momy na shiga uku idan Irfan ta aura, shikenan kashina ya bushe dama yaya balle ta shigo gidan...."Tsawan da wargaji ya daka masu ne yasa su yin tsit suna saurarensa.... "Wata magani ya ciro cikin wani kwasko ya mik'awa Laila kafin yace" Ungo karb'i wann duk yanda za'ayi ki zuba mata a ruwa ko abinci idan taci shikenan zata mutu, idan kuma bata halak'a ba, sharad'i biyu ne, Ko ni na mutu ko kuwa asirinku ya tonu.... "Girgiza kai Laila tayi cikeda tsoro kafin tace" um um boka ba lallai na tirsasa mata ci ba da asirina ya tonu ai gwara taci gaba da rayuwarta ko 'yan daba ne nasa su kashe min ita....
"Dariya wargaji yayi kafin ya mik'o masu k'ok'o mai cikeda ruwa a ciki... gabansu ne yayi mugun fad'i ganin fuskan Irfan da Deejah sun bayyana a ciki...."Wanene wann mutumin, ya tambaya cikeda karaji..."Azee baki na rawa tace mijina ne...." Wani dariya wargaji ya kumayi kafin yace" Toh wann shine mijinta shine aka aura masa ba tareda saninsu ba.
"Mik'ewa Azee tayi tana kutuntumo ashariya, kaman wata zararriya haka ta koma, saida wargaji ya daka mata tsawa guguwa ya kewaye wajen kafin ta nutsu ta zauna. Rungume Laila tayi ta fara rusa kuka. "Tuni Laila ta soma rok'on boka wargaji kan ya taimaka masu, wann yarinya muddin Irfan ya zauna da ita toh fah kashin 'yarta ya bushe.
"Wargaji ya ciro wani magani kwalba biyu cikin wani bak'in kwasko snn ya mik'a wa Laila yace" Ungo wnn turare ne guda biyu, duka kalolinsu bak'ake... kallon kwalban tayi kafin ta kalli boka alamun tana son k'arin bayani.
"Dariya yayi yayi wasu sunbatu kafin ya soma fad'in" Irfan mutumne wanda baya son Kenwa ko kad'an, d'aya turaren da na mik'a maki da hannun hagu da jini da gashin bak'ar Kenwar aljanu aka had'ashi, d'aya kuma dana baki da hannun dama wa 'yarki zaki bada tayi amfani dashi idan tayi amfani dashi Irfan bazai kuma tuna yanada wata mata ba bayanta, ita kuma wancan datayi amfani da had'in bak'ar kenwa toh zai tsaneta har abada ko kusa da ita yaje k'urajene zasu faso masa, kinga daga haka dole ya saketa ya rabu da ita...."Azee tana jin haka ta d'ago tana murmushi... "Boka ya kuma jaddada masu kan kar suyi gangancin had'a turarrukan dan kar a samu akasi, sosai sukayi godiya suka cika masa mararsa da kud'i suka nufo mota...




"Ciwon cikin Azee abu kaman wasa sai kuma k'aruwa yake kan su iso cikin gari Azee ta sume masu, hankalin Laila idan yayi dubu ya tashi, a tamanin suka wuce asibiti yanda likita yayi gaggawan karb'anta, gwaje gwajen su sukayi yanda suka gano zunzurutun magungunan hana d'aukan ciki masu k'arfin gaske da take sha sune suka lalata mata mahaifarta, wanda idan ba'ayi minor surgery ba zata iya rasa rayuwarta, koda likita ya fad'awa Laila hannu ta saka aka ta shiga rusa kukan babu mai rarrashi......




"Misalin k'arfe 8:30pm suna zazzaune gaban Daddy sosai yayi masu fad'a da nasiha me ratsa zuciya dukda har lokacin Deejah bata san waye mijin nata ba, a nasihar da Engr ya mata shine tayi hak'uri da zab'in da ya mata insha Allah zataga alfanun hakan, abinda ta sani kawai shine takan tsinci kanta da matsanancin fad'uwar gaba, kuka sosai sukayi sanda aka tattara su don kaisu gidajensu, Ammah dasu Hajja ma saida sukayi kukan, Nilam kam dole tare da ita aka tafi kai Deejah gidanta.
" Sadiq me amare guda biyu, wato Nadiya da kuma Ruqayya, Nadiya na lullub'e cikin yelwataceccen mayafinta daga ita sai wata course mate dinsu Haiza,..
"D'akin Ruqayya kuwa daga ita sai aminiyarta Badiyya, Badiyya ta ciro maganin da suka karb'o gidan boka ta mik'awa Ruqayya tace" toh na gama nawa saura naki, idan ba kuma so kike ki zama 'yar kallo a cikin gidanki ba, kina ganin wann amaryar taki tamkar balarabiya haka take, kika kuskura kika barta da mijinki sunanki sorry.
"Wani dariya Ruqayya tayi me juya idanu kadin tace" haba k'awata ai kema kinsan idan dai kan wann ne na gohe saidai nayi lecture ma wasu, Badiyya ta mik'a mata hannu suka kashe, (Allah sarki duk wani huduba da nasiha da Mamie tayi wa Ruqayya k'awar banza ta wargaza mata su, Allah ka bamu abokai na k'warai ameen).



"Shiru yayi gaban Engr bayan ya gama masa nasihan shima, jikin Irfan gaba d'aya yayi sanyi, ganin lamarin yake tamkar a mafarki wai yau Deejah ta zama *Mallakin sa* anya da gaske ne, ko kuwa dai d'ayane daga cikin mafarkan da ya saba. Muryar Engr ya dawo dashi yanda yake masa nasiha kan ya rik'e matansa duka biyu da amana banda nuna fifiko, Allah yayi mana jagora. Da k'yar Irfan ya iya amsawa da Ameen kafin Engr yace maza kaje ka sami iyalanka dare yanayi. Irfan yayi masa sallama kafin ya fice.




"Laila cikeda tashin hankali take duban Dr bayan ya gama masu bayanin Azeeza bazata tab'a haihuwa ba itada Hajiya Karime ne gaban likitan, wani tsuka Hajiya ta buga kafin tace "Yo saime dan bazata tab'a haihuwa ba shine kike wani sallalami kike cewa kun shiga uku, babu ukun da muka shiga, kaga likita baki kawai zamu had'e ace wa mijinta da 'yan uwansa ciki ne da ita, watan haihuwa nayi ka nemo mana jarir ka bamu shikenan an kashe wutar magana, Likita ya kwashe da dariya dan yaga abin nayine kafin yace" Zan maku wann aiki amma akwai kud'i, Laila cike da zumud'i tace" Dr name the price babu matsala, kan kace me sunyi Deal da Dr komai ya tafi yanda suke so..
"Sai lokacin Laila ta sami zarafin kiran Engr tana kuka take fad'a masa Azeeza ce babu lafiya ta sume a wajen biki amma yanzu haka tana asibiti, Engr cike da tashin hankali yake tambayarta asibitin da suke. Cikin sauri ya tafi sashen Ammah don sanar da ita gashi lokaxin Irfan ya fice..






"Ahidjo ya kalli Safwan kafin yace" Dukanmu mun rasata tana can ta zama *Mallakin sa*
"Wani dariya Safwan ya kwashe dashi kafin yace" yaro dai yaro ne, wata waya ya ciro a aljihun sa kafin ya shiga nunawa Ahidjo videos da pictures na Deejah a club, Ahidjo baki sake yake kallon Safwan, murmushi Safwan yayi kafin yace" bazan b'ata kudirina ba, muddin Azeeza zataji dad'i toh sai yanda k'arfina ya k'are wajen mata yak'i, wad'an nan videos da pics yanzu zasu ziyarci mijin Deejah. Kan kace me Safwan ya shiga forwarding ma Irfan through internet.....




"Hankali kwance yake driving, jin k'aran text mssges na shigo masa yasa ciro wayar, ganin whatsapp ne dan haka bai damu da bud'ewa ba, Amigo ya tsaya sayyan snacks yanda ya had'u da Sadeeq sai tsiya suke ma juna barinma Sadeeq dashike Irfan ya zama inlw dinshi, Sadeeq yace guy kaga tafiyata biyu ne ke jirana, Irfan ya murmusa baice komai ba, yaci gaba da jidan abinda yake d'iba. Jin k'aran sak'o yak'i k'arewa yasa sa bud'e sak'wannin yana gani........"Innnalillahi wa inna ilaihirraji'un, mene wann yake gani, meke shirin faruwa dashi, Deejahn shi ne a club tsakiyan maza tana rawa suna shigewa jikinta, kai ko shakka babu itace, jiri ne ya soma d'iban sa sanda yaga wani video na blue film ga fuskarta b'aro b'aro ya bayyana masa.............




Queensamy ceπŸ‘ŒπŸ½
πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


76


*©Sameena Aleeyou.....✍🏽*


_Queen Samy Novels Forum....πŸ“–πŸ“š_




*#TEAM IRFANDEE*


"Jiri ne ke shirin kada Irfan, why is life always like this, does he really have to suffer for life, meyasa rayuwa take zuwa masa a haka, tun bayan rasuwar mahaifiyarsa rayuwa ta juya masa, tun zuwansa Nigeria yake experiencing horrible tragedies why is all this happening, why why...."Durk'ushewa yayi wajen kan gwiwoyinsa ya shiga kuka kaman k'aramin yaro, saida yayi mai isan sa kafin ya mik'e ya nufi motarsa, da k'yar da taimakon Allah Irfan ya samu ya isa gidansa, bai san dalilin da yasa sa zuwa gidan ba, all he knows is that he want to ask her, he really needs to ask her. Zama yayi a mota ya kasa fita dan idan akwai abinda a yanzu yadi tsana toh kallon fuskar Deejah ne wanda a da yafi komai masa kyau da birgesa, a b'angare guda fuskarta cikin wnn blue video din yafi komai masa ciwo, inama fuskar mutumin yafito sosai ta yanda zai ganesa da ko a ina yake sai ya bisa ya kashesa murus har lahira, wata zuciya tace wann d'aya kenan daka gani ka sani maza nawa tayi haka dasu, wani d'aci da k'una ya kuma ziyartar zuciyarsa..




"Tunda aka sakata a wann d'akin ta kasa yane mayafin fuskarta balle tasan yanayin wajen, zuciyarta kuwa bata sarara ba wajen bugawa da sauri da sauri, shin ita d'in *Mallakin Waye* shin waye aka aura mata, wann tambaya tafi komai d'aga mata hankali, kaman daga sama taji an bud'e k'ofar da k'arfin gaske... "Take k'irjinta ya soma barazanr tarwastewa sakamakon bugu da sauri da ya k'aru, shiru taji na d'an sakanni , k'amshin turaren datajine ya tabbatar mata ita d'in *Mallakin Waye* murmushin da batayi zato ba shi ya kufce mata, a hankali ta furta *Master* kaman wacce aka zabura tayi saurin yane mayafin fuskarta dan tabbatar wa idanunta... "Shid'in ne da gaske, ido hud'u sukayi da juna saidai yanayinsa da yanayin kallon da yake mata yasa gaban mummunar fad'uwa wanda bata tab'a yin makamancinsa ba, idanunsa sunyi turning to red kamar garwashi, haka nan farar fatar jikinsa ta koma tamkar jan gauta, fuskarsa kuwa kaman anyi masa albishir da jahannama babu alamun annuri a tattaredashi. Da sauri ta sauk'e mayafin sabida tsaban razana, toh meke faruwa?.
"Bata gama tunani ba saiji tayi ya yane mayafi da k'arfin gaske gaba d'aya ya fad'i k'asa. Kallon k'yama Irfan ke binta dashi kafin ya soma girgiza kai yana fad'in" Tambaya d'aya nazo na maki, and pls be honest with me, ki gaya min gaskiya kar kimin k'aryarki da kika saba.
"Banbarak'wai abin ya mata me Irfan ke nufi, wani k'arya......"tunaninta ne ya sark'e sanda ya nu a mata video na rawanta a club, muryarsa ya daki dodon kunnuwanta sanda yake fad'in" Is that you in this video? Shiru tayi banda hawaye babu abinda ke bin fuskarta,.. "Murmushin takaici Irfan yayi ganin yanda tai masa shiru tana hawaye. "Matsowa daf da ita yayi ya kama fuskarta k'asar hab'arta yana huci yake fad'in" Ki fad'a mum kece ciiin videonan????
"Shk'an da yayi mata sosai ya matseta har kaman bazata iya magana ba, jefata kan gado yayi... ganin yana k'ok'arin haurowa gadon yasata saurin mik'ewa cikeda firgici tana kuka sosai ta shiga matsawa end d'in gado, kafin ta isa k'arshen gadon yasa k'afa ya take k'afafunta, "Kallonsa take tana girgiza kai alamun ya k'yaleta, wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login