Showing 48001 words to 51000 words out of 159062 words

Chapter 17 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10372

ina masa wa'azi da Addu'an shiriya, Irfan ya dafa kafadun Sadiq wanda damuwa ya nuna sosai a fuskansa kafin yace" Friend worry not pls, babu abinda zai faru insha Allah.... "Sauke ajiyan zuciya Sadiq yayi kafin yace" toh Allah ya shige mana gaba..... suna cikin hiran ne wayan Irfan ya soma ringing. Yana ganin Engr ne gabansa yace rassss, da kyar ya iya saita kansa ya daga wayan da sallama, amsa sallaman kawai Engr yayi kafin ya soma fadin" Irfan lafianka kuwa, har yaushe zakayi hankali, ashe fadan da na maka kwanakin baya bai shiga kunnenka ba, ina ka kuma daukan Deejah ka tafi da ita huh.
"Murya a sanyaye Irfan ya soma fadin" Daddy gidansu Sadiq muka je emm emm dama yayimin waya kan binciken da muke na bata wa'dan can kayan da aka shigo dasu din nan, shine naje muna sorting wasu Documents, Deejah kuma tace tana son zuwa gaida Mamie shine muka taho tare.
"Engr yadaiji Irfan ne kawai but hankalinsa be kwanta ba, "next time sai ka fada irin haka especially idan zaka fita da one of your sisters, hankulanmu duk sun tashi,
"Cikeda jin dadi Irfan yace" Okay daddy, am sos sorry hajan bazata sake faruwa ba, ka fadawa Ammaj she shouldn't worry kaji daddy, gamunan dawowa gida ma right the way
"Murmushi kawai Engr yayi kafin sukayi sallma ya kashe wayar.
"Engr ya dubi su Ammah da sukayi tsuru tsuru ya sanar dasu babu komai, Nadiya taja su Nilam suka wuce sama a zuciyarta tana tunanin kenan gidansu Sadiq su ya Irfan sukaje, Aziza kuwa dan takaici idonta tab hwaye ta fice tayi nata dakin tana matsan kwalla. Ammah ma wucewa sama tayi dan hankalinta ya dan kwanta dataji yanda suke....


"Mamie ta mike hannuta rike da robar ruwa data gama matsawa Yusra a jiki, gaba daya sun jinjina irin wnn al'amari, wa'azi sosai Mamie tayiwa Ruqayya da Deejah me shiga jiki, Deejah kam gaba daya ji tayi rayuwar ba komai bace, ganin yanda a lokaci k'ank'ani aminiyarta ta lalace, ta k'udiri niyyan itada Club har abada, a d'an zuwa rawan da suke ne suna ganun kaman ba komai ba shi ya jefa k'awarta ga wnn babban halaka. magunguna Mamie ta ajiye gefen bedside ta dubi Deejah tace mamata idan ta bude ido ga prescriptions din anan ni zanje duba Dada naji motsinta dazu, cikeda ladabi Deejah ta amsa da toh Mamie sannu da d'awainiya, Mamie tace kune da dawainiya Deejah keda irfan, baku santa ba kuka taimaka mata, Allah ya biyaku ya biyamu gaba daya. A sanyaye Deejah ta amsa da Ameen Mamie.
"Bayan Mamie ta fice Ruqayya suka ci gaba da tadi itada Deejah dan yanzu kam sun saba sosai,Ruqayya na mata labarin sabon sch dinsu, ta sami gurbin karatu a University of Abuja Gwagwalada. Deejah kuwa cikeda jin dadin labarin ji take inama itace ta sami ci gaban karatu a university take sauraren hiran Ruqayyan. Kiran da Mamie ta kwala wa Ruqayya ne yasata mikewa ta nufi kiran Mamie.

"Deejah ta dawo da dubanta ga Yusra, cikeda tausayi take duban Yusra, rayuwarsu a baya take tunowa, a hankali taa Yusra na mutsu mutsu da sauri ta matso kusa da ita ta rike hanunta, ta shiga kiran sunan ta a hankai....






πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„.........
[8/28, 13:55] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye*


36




"A hankali Yusra ta soma bud'e idanunta har ta waresu tsaf kan Deejah, kallon mamaki ta shiga bin Deejah dashi da kuma yanayin wajen da take, Deejah ta goge k'wallan da suka zubo mata tanama Yusra mugun kallo kafin tace" ba mafarki kike ba nice dai that your very friend of yours, yanzu zakimin bayani kan wani dalili kika zab'i wann rayuwar.
"Mik'a Yusra tayi gamida tab'e baki had'e da yin gajeren tsaki tace" Deejah dama nan ne gidan da kike aiki, ta daga kai tana bin yanayin gidan da kallo fanka ta gani saman kanta nata wainuwa, tab'e baki tayi kafin tace" idan dai nan gidan ai gwara maki Orphanage dan ni banga alamun kayan more rayuwa ba a nan.
"Cike da al'ajabi Deejah ke kallon Yusra tama rasa da wanni kalma zata soma mata magana. Tabe baki Yusra ta kumayi kafin tace" nasan mamaki kike yaushe na soma zuwa dirty clubs ko, kar ki damu friend na zab'a wa kaina rayuwar data fiye mun, harkar da babu talauci......"Enough Yusra! Deejah ta katseta, cike da b'acin rai take fadin," tashi muje ina tara maki ko taxi ne, nidake dloe mu zauna muyi magana, maza tashi muje....."Galala Yusra ke kallonta kafin ta sheke da dariya tace" Deejah kenan, ba sanin da kika mun da nake ba, sunan Yussy the hot beb in the town, a da ne nake zaman orphanage amma a yanzu na gairmi Orphanage, ta mike ta dau yar jakarta wanda shirgin kayan maye ne a ciki kafin tace" anyway thanks for your help friend, ban damu naji yaya akayi kika san ina wajen ba dan nasan kema 'yar uwa ce a fannin zuwa club, ni yanzu zan tafi na gode da taimakonki... daga haka Yusra tasa kai ko ajikinta ta fice.... "Kallon al'ajabi Deejah tabita dashi hawaye na zarya a fuskanta..... a haka a zaune Ruqayya ta shigo ta sameta, da sauri Ruqayya ta karaso tana tambayanta lafiya Deejah, meke faruwa ina yarinyar?.... Deejah ta kasa amsa Ruqayya sai kuka kawai take. Da sauri Ruqayya ta shiga leke leke bataga Yusra ba, cikin sauri ta nufi sashen Sadiq dan Mamie na tareda Dada tana mata hayakin habbatul sauda kaman yanda Ustaz Salih ya basu sabida jinyar hauka da take fama dashi....
"Sadiq sosai yasha mamakin guduwan da Yusra tayi, Irfan kam tab'e baki yayi ba tareda yace komai ba, ya kalli agogon hanunsa, k'arfe takwas da rabi,.... Deejah kam banda kuka babu abinda take, d'ago kyawawan idonsa Irfan yayi yana dubanta, a hankali ya sau'ke ajiyan zuciya gamida zura hannayensa a aljihu ya k'araso gabanta, d'an rankwafowa yayi yana mata rad'a" Deee why do you care so much about that girl, ko kinsanta ne?
"A zabure Deejah ta dago kai kana ta soma girgizawa, murya na b'ari take fad'in "a'a bansanta ba, kawai na tausayawa rayuwarta ne,
"Irfan ya d'an murmusa kana yace" Deee you don't have to worry your self about her, besides abinda ta zab'a wa kanta kenan, Allah yaga niyyanki mu na taimako, oya wipe those tears muje muyi wa Mamie sallama Daddy ma ya kira, ya kmata mu tafi...
"Da sauri Deeja ta dago kai ta soma zare idanunta me jikan hawaye" Daddy ya kira, ya salam, kosu Ammah fah ban fada masu zan fita ba, na shia uku, i know they must be worried.
"Murmushi Irfan yayi kfin yace" karki damu nayiwa daddy bayanun komai, oya tashi muje.... "Jiki a sanaye ta mike, Sadiq da Ruqayya kuwa dake tsaye jikin kofa sosai su Deejah da Irfan suka birgesu, soyayansu me shiga rai ne.
"Mamie ma sosai ta jinjina lamarin jin Yarinyar ta gudu... a gurguje suka masu sallama suka fice........


"A mota ms lallashin Deee dinsa yake kanyi sai wani ririta ta yake, wani bakery ya tsaya saya mata d'an snacks dan yasan bata ci komai ba, tinda tun yamma suka fice......




"A b'angaren Laila kuwa abinne yayi matuk'ar d'aukan hankalinta, sosai abin ya dameta ganin yanda hankalin Engr yayi mugun tashi, wai kawai dan Irfan ya fita da Deejah ba tareda sanin kowa ba, toh me Engr yake nufi? Shin shima son wann kucakr yarinyar yake kome? Dan kuwa gaba daya hr yanzu bata gane kan Engr ba tinds akace Deejah ta fita tareda Irfan...Da sauri ta soma girgiza kai tana fadin " aiko bazata tab'a sakuwa ba. A hanzarce ta wuce sashen ma'aikata ta kirawo Zulai.
"Zulai wai me tsinaniyar yarinyar nan tayi wa 'yan gidan nan kowa ke sonta, Zulai ta yab'e baki tace" ah ah toh kema dai Aunty kya tambaya, wnn yarinyar da shirinta ta shigo gidan nan, kinsan Allah Aunty bakiga yanda Ammah take sonta ba tamkar jikanta haka ta d'auketa, yaran kuwa gaba daya idan bata nan tod fa basu da kwanciyan hankai sai ta dawo, kinga kuwa ai akwai wani abu a k'asa, kuma kinsan wani abu Aunty wllhi daga gidan marayu aka kawota aiki gidan nan.
" Laila ta jinjina kai kafin tace" toh kuwa ta tari fad'an da duk danginsu sunyi k'adan su rik'e mata, sai taji rayuwar gidan marayu yafiye mata dadin rauyuwar wnn mansion din...... "Daidai nan Hajja ta b'ullo daga kitchen, wani uwar harara Laila ta watsa mata kafin tace" Ke a ladabce Hajja tazo har gabanta ta rusuna, a yatsine Laila tace maza ki daura min ruwan shayi yanzun nan, Hajja ta wuce tana fadin an gama rankishi dade, zuciyanta kuwa fal tunani, zargin da take gameda zulai ya tabbata, lallai kuwa ya zama dole ta taimaka wa Khadijatu daga sharrin wann mata.....


"Parlorn Engr Laila ta koma yanda ta samu kallo yake amma lokaci bayan lokaci yana duba agogo, shigarta ma saida ya tambaya ko su Deejah sun dawo, daurewa kawai Laila keyi tana k'ak'aro murmushi ta matso kusa dashi ta rungume cikin jikinta cikin siga me d'aukan hankalin d'a namiji ta soma fad'in" Haba my Engr, wai duk kan wnn yarinyar ka damu kanka haka, Irfan ya kamata ka soma tambaya ba wann tambatsetsiyan yarinyar ba wacce ta saba yawo a titi.
"Ajiye remote control din hanunsa yayi kafin yace" dole na damu mana Laila, yarinyar nan mace ce, what if wani abun ya samesu, gwara Irfan namiji ne he can take care of him self, amma ita kuma fah, snn kome ya sameta It will be my responsibility tinda a k'ark'ashin family dina take a halin yanzu, snn kar ki sake kiranta tambatsatsiya me yawon titi, Deejah yarinyar ce me nutsuwa da sanin yakamata, zuwanta family na alkhairi ne, Deejah itace" ta nusar da yarana d'abi'u da al'adu na musulnci sab'anin wanda suka tashi dashi a k'asar Amurka, wnn dalili yasa nake bata matsayi sosai, snn bana fatan randa Deejah zata bar wnn family nawa........ "Ai gana daya Laila ta daina gane me Engr ke cewa, lallai kuwa zarginta yana gab da tabba ta, wai meke shirin faruwa ne, shin wai zuciyan wnn tsinanniyar mayyan yarinyar *Mallakin Waye*.......... da wnn tunani Laila ta fice dan kawo wa Engr ruwan shayi...


"Tana zaune gabansa tana hada masa shayi su Nadiya da kannenta suka shigo, Nilam ta fada kan Engr tana kuka tana ambato sunan Deejah, Amir da Aiman ma sai matse ido suke suna ture turen bakin rashin ganin Deejah,
"Laila kuwa wani katutun bak'in ciki ne ya tokare mata mak'oshi, da kyar ta iya saita kanta ta nufi su Amir tana lallashinsu, Nadiya kuwa harara kawai ta jefawa Laila gamida tab'e baki. Engr hankali tashe yake lallashin yaran nasa. Suna a haka suka ji k'aran bud'e gate......






πŸ‘ΈπŸ»Ueen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„..........
[8/28, 13:55] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ—πŸŒ˜ *Mallakin Waye*


37




"Tun kan Irfan ya ida parking su Nilam suka fito waje, aiko Deejah na sako k'afa suka nufota a guje suka rungumeta, d'aya bayan d'aya Deejah ta ringa hugging dinsu cike da so da k'auna, Irfan kuwa sosai abun ke burgesa yanda Deeee da k'annensa suke tsananin son juna, murmushi yake kanyi sanda yake binsu da kallo.
"Aziza dake kife da kanta kan gado tana sharb'an kuka, jin motsin mota yasata yasata saurin mik'ewa ta nufi window, zuciyanta kaman ya fice dan takaici sanda ta hangi Irfan ya hard'e hannaye a k'irji yana jingine jikin mota sanda yake kallon Deejah fuskansa d'auke da murmushi.... kasa jurewa tayi dole ta zube k'asan d'akin tana me ci gaba da kukan takaici.
"Mamaki ne ya ishe Laila sanda taga Engr ya mik'e ya nufi k'ofa, tana fad'in" my Engr kar shayin naka ya huce, ko kulawa Engr beyi ba ya bud'e k'ofa ya fice.... Kaman ta zunduma ihu ko zataji sanyi cikin ranta haka taji.


"Irfan ne ya fara k'arasawa ya gaida Engr, sai snn Deejah daketa faman oyoyo dasu Nilam ta lura da Engr wanda shima jin da'din yanda Deejah da yaransa ke son juna yake. Da sauri ta k'arasa gamida rusunawa ta gaida Engr, fusaka a sake ya amsa mata snn yace yaya kua samesu familyn Sadiq din, Deejah ta amsa da lafiya lou Daddy sunce ma a gaidaku, Engr ya amsa da madalla yayi kyau, daga haka Deejah taja hannun su Nilam suka nufi cikin gida.
"Engr da Irfan suka soma takawa zuwa garden dan tattaunawa.


"A parlor Deejah ta tarar da Ammah nan ta zauna ta shiga gaisheta, Ammah ma fuska sake ta amsa mata ta kuma tambayeta iyayen Sadiq,
"Allah sarki Sadiq yaron arziki cewan Ammah,..... "Nadiya dake zaune gefe jin an ambato Sadiq yasata saurin zame earpiece dinta tana fadin" hm Ammah wnn ne yaron arziki lallema baki sansa ba, girman kan tsiyane dashi shi ba dan kowa ba.... Pillow Ammah ta jefa mata gamida dakuna fuska tace " rufewa mutane baki, ke har zakice wani nada girman kai, da wnn hali naki naga me auranki idan baki canza ba.
"Nadiya ta turo baki ta soma fad'in "ai dama Ammah ni ba aure zanyi ba, gani ga ke forever and ever........
" Draman Nadiya da Ammah shi ya saka Deejah dariya har ta d'an mace damuwan da take ciki. Mikewa tayi ta nufi d'akin Nilam bayan tayi sallama da Ammah.


"Deejah na kwance gefen Nilam as usual suna rik'e da hannun juna a haka bacci yayi gaba da Nilam bayan Deejah ta gama mata guntun tarihi na Annabi Musa(AS).
Nadiya ce ta shigo d'akin suka b'uge da hira da Deejah, Nadiya sai tambayanta take gameda familyn Sadiq, Deejah dai sai dariya take tace" kar fah zancen Ammah ya zama gaskiya..... kodai,..... " Harara kawai Nadiya ta wurga mata kafin tace" Never in my life me zanyi da wnn cheap guy din, kawai dai so nake naji a yanda yake rayuwa all this arrogancy nashi, ce maki akayi ni ya Irfan ne da zan so someone lower than my class, I was shocked da na gane ya Irfan loves you Deejah.
" 'Dago ido Deejah tayi a d'an razane kafin tace, ni..... ni kuma no, Irfan ba sona yake ba duk ta wani daburce...." Dariya Nadiya tayi kafin tace" Relax girl, you're surprised na gane ko, it's Obvious dukanku kuna son junanku.... Kar ki damu you have my unconditional support, though you're not that classic, you're somehow local but still kinada good heart. Am quite happy for you dan ya Irfan d'aya ne tamkar da dubu, ke kinsan haka........ Daga haka Nadiya ta mik'e tana mak'ala earpiece a kunne ta fice......" Kallo Deejah tabita dashi har ta fice, mamaki ne ya cikata, wai shin ana ganewa itama son Irfan take, toh waiko da gaske tana sonsa ne. Take murmushin da batasan dalilinsa ba taji ya wanzu a fuskanta. Take kuma taji k'irjinta ya buga da k'arfi, lallai kiwa idan da gaske ne ta kwaso ma kanta abinda yafi k'arfinta dan kuwa Irfan ya wuce ajinta, koda kiwa yana sonta...... *.*
"Jiki a sanyaye ta mik'e dan komawa nata d'akin.


"Kaman ance ta kalli parlor, ai kuwa shi ta hango yana kishingid'e cikin sofa yayi matashi da hannun sofan throw pillow rungume cikin k'irjinsa, yana sanye cikin Black inner Shirt da wando 3quter. Duk sanda taga Irfan sai gabanta yayi mugun fad'uwa mussaman da yanzu ta gansa asalin kyaun halittansa ya fito.. Hankali kwance Irfan yake kallon ball dinsa yayinda Deejah ta soma jan kunne wa kanta bisa fad'awa tarkon son abinda batada tabbacin samu......"Jikinsa ne ya basa ana kallonsa aikuwa juyowan da zaiyi sukayi ido hudu.... Murmushinsa mai tsada ya sakar mata yayinda ita kuma ta daburce ta soma shirin juyawa.
"In a soft Voice taji ya ambaci" Deeee k'araso pls. Kasa motsawa tayi snn ta kasa masa musu, saida ta d'ibi mintuna kafin ta sami k'warin gwiwan sauk'owa daga stirs din......


"Mik'ewa yayi ya gyara zamansa yana binta da kallo tsan tsan soyayyanta na azalzalansa. Ji tayi gaba d'aya kunyansa take ji dan ya ganta sanda ta tsaresa da idanu.
"Kallonta yake sosai kafin yace" why are you still awake, is already late, ko kina wani abin.
Cikin en kame kame tana girgiza kai ta soma fad'in dama...... dama na jira Nilam tayi bacci ne shine yanzu zanje na kwanta.
" D'an murmushi Irfan yayi kafin yace" Deeee inaga dai daddy zai baki Nilam 'yar gaba idan aurenki ya tashi....."Take ta d'ago ido a zabure tana dubansa sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta sabida k'warjini irin ta Irfan. Murmushi me bayyan hak'wara Irfan yayi dan kuwa Deee ta juya masa ido abin da yafi so gameda ita......"Shirun da ya d'an biyo baya ne yasa Deejah fad'in "Master may I...... ta k'areshe maganar tana nuna masa hanyan stirs.
" 'Dan gyara zamansa yayi kafin yace" had'o coffee kafin ki tafi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login