Showing 123001 words to 126000 words out of 159062 words
Chapter 42 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt
me where she is...."Nan fah baturen nan ya soma k'ak'arin amai don ba k'aramin shak'a Irfan ya masa ba, nan hankulan sauran receptionists d'in ya tashi k'ok'arin kwace d'an uwansu suke daga hannun Irfan amma abu yaci tura. Da k'yar suka samu suka kwace sa, macen ta soma fad'in" Calm down sir, just calm down pls,... "Fizgewa yayi daga rik'on da suke masa yana fad'in" How could you expect me to calm down, you all don't know your job you don't know your obligation, "Kan kace me turawan nan duk sun rud'e sunsan akan haka ba aikinsu kawai zasu rasa ba wann abun sai ya kaisu gidan yari, cikin sauri suka soma kunna CCTV security camera, Irfan ya k'urawa cameran ido wanda yake kan nuno mutane da sukayi zarya a tsakanin reception d'in....."Can yaga wata kaman ita tana sanye da black jacket wanda ya sauka zuwa gwiwarta had'i da neavy blue jeans, ta yane kanta da bakin mayafi idanunta rufe cikin bak'in glass....." Har ta wuce yace wa mutumin ya kuma playing, idanunsa sunyi jazur yake kallonsu kafin yace" If something bad happens to my wife you gonna pay for it..... "A sittin ya fice zuwa security Office dake cikin hotel din nan aka kuma kunna CCTV ana ganin mutanen da sukayi shiga da fice a hotel d'in amma babu alamun Deejah, anyi playing yafi sau abinda yafi basu ganta ba, take a aka kukkuna cameras din da suke gaba daya cikin hotel din ana bincike dan Hotel din yanada tsananin girman gaske. Can tsakan kanin flowers suka hangota tana kwance bayan flowers din kaman bata numfashi ga snow ya zuba sosai a jikinta....."A tare suka fice gaba d'aya suka nufi yanda suke zaton anan take......
"Wani tsallen da Irfan yayi gamida d'agota ya rungume cikin jikinsa.... hawaye na bin k'umcinsa yake fad'in am sorry dee am so so sorry, I'm here now jin bata mosti yasa hankalin Irfan mugun tashi, girgizata ya soma yi yana fad'in Deejah Deee pls wake up, hey u can't do this to me, am not gonna loose you, ji yayi duk jikinta ya sake ..." Juyawa yayi yana Kallonsu yanda suka masu k'uri suna kallon yanda yake sunbato shi kadai, a harzuk'e yake fad'in" What are you all looking at you idiots, just call an ambulance, hurry...."Kan kace me ambuceππΎta iso, cikin sauri ya nufi ambulance din tana rungume a hannunsa har lokacin hawaye bai daina zuba a idanunsa ba snn bai dana sunbato ba......
Sameena ceππΎ
ππππ *Mallakin Waye*
87
*Β©Sameena Aleeyou...βπ½*
_Queen Samy Novels Forum....ππ_
"Hannunta na rik'e cikin nasa, a hankali ta soma bud'e idanu har bud'e su tsaf kan kyakkyawan fuskar Irfan, murmushi ya sakar mata gamida kissing hannunta yace" Baby kin tashi, d'an muskutawa tayi gamida kau da kai gefe. A hankali komai yake dawo mata...."Irfan ya tsareta da manyan idanunsa ko kad'an baison tak'urata amma ya zama dole ya fad'a mata what she didi was wrong..."Shafa suman kanta ya soma a hankali kafin ya soma fad'in" Baby why did you do that, you risky your life... why Dee do you hate me that much. Kiyi hak'uri kar ki sake risking life d'in ki haka, idan akan buk'atanki da kike nema daga gareni ne na yarda na amince da zaran mun koma Nigeria I'll do as you wish kinji, but for now kiyi hak'uri har na gama abinda ya kawo ni England I promise I won't bother you again kinji...."A zabure take kallonsa yanda yake maganar babu alamun wasa a tattare dashi, ji tayi zuciyarta ya tsinke hawaye suka ciko idanunta, did she just hear him right, Goodness she just couldn't believe it wai ya Irfan ke fad'in da zaran sun koma Nigeria zaiyi abinda ta umarce sa yayi, kenan zai rabu da ita yake nufi... tuni hawaye ya soma ambaliya a fuskarta...."Cike da tashin hankali yake fad'in" Com'on Dee kiyi hak'uri just couple of weeks zamu kara nasan kina son komawa Nigeria, but pls this is all I'm asking of you pls, matse hannunta ya kuma cikin nasa kafin yaci gaba da fad'in" Ganinki cikin farin ciki ya fiye mun komai a rayuwata zanyi abinda kike so sweetheart ya k'arashe maganar yana mai rungumota cikin jikinsa yana fad'in" Oya stop crying, ki daina min asaran hawayenki it hurts me alot...."luf ta kwanta cikin k'irjinsa sai ajiyan zuciya take, sonsa take ji kaman kar ya saketa daga rungumar da ta masa..."Kowa da nashi sak'e sak'en da yakeyi cikin zuciyoyin su.. Dr na zuwa yayi discharging nasu...
"Wani kulawa na musamman Irfan ke bata, da kansa yake bata abinci sann ya tabbatar tasha maganinta, dare yanayi kuwa mik'ewa yayi ya d'au pillow ya bud'e wardrobe ya ciro wani bedcover kafin ya k'araso wajenta gamida manna tama peck a goshinta yace" If you need anything ina parlor kinji princess daga haka bai kuma cewa komai ba ya d'au jakar laptop d'insanya wuce parlor......"Kallo Deejah ta bisa dashi har ya fice, ji take kaman tace masa ya dawo ta kwanta cikin jikinsa, tana son mijinta tana missing nasa, amma idan ta tuna abinda yayi mata wani takaici da haushinsa ne yake tokare mata mak'oshi, a hankali ta kwanta tana mai kukan zuci.....
"Kasa bacci tayi dan kuwa tunanin Irfan ya addabeta a hankali ta mik'e tana sand'a kaman wata b'arauniya ta shiga lek'ensa ta ramin k'ofa, "Yana zaune yana sipping coffe lokaci guda yana aiki bisa computer.... A guje ta koma ta kwanta gamida lumshe ido ganin ya taso ya nufo d'akin ashe wayarsa ya mance gefen bedside.....
"Kallonta yake kanyi sanda ya sunkuya don d'aukar wayarsa, kwad'ayin matarsa yake yana tsananin buk'atar ta burinsa bai wuce ya kwanta cikin jikinta ba amma yasan hakan ba mai yuwuwa bane a hankali ya sunkuyo gamida mata light kiss akan lips dinta kafin ya furta I luv you Dee pls don't leave me, I can't imagine life without you... daga haka ya fice ba tareda ya kuma yin komai ba..."Hawaye ne suka zubo daga idanunta anya batayi ganganci ba kuwa wata zuciya tace dad'in baki kawai yake maki dan yana son jikin ki, da sauri ta toshe kunnuwanta dan bata son tunanin ko kad'an.....
"Washe gari da safe farkawa tayi ta gansa yana shiryawa gaban dressing mirror, abun mamaki yau jampa ya saka sky blue harda hula dark blue zanna bukar ba k'aramin kyau yayi ba, ji tayi ta kasa d'aga idanunta daga barin kallonsa, ta jikin madubi yake kallonta yanda tai masa k'urillah sandanyake d'aura agogo, a hankali ya juyo gamida sakar mata murmushi kafin yace"Good morning baby...."Da sauri ta kawar da kanta gefe wai kar ya gane kallonsa take, murmushi ya kuma kafin yace" Ki tashi ki shirya we are going somewhere....." A zabure ta mik'e dan dama ta gaji da zama waje d'aya tunda tazo tana nanik'e waje guda, har bata san sanda murmushi ya subce mata ba, murmushin shima yayi kafin yace" Ina parlor idan kin gama daga haka ya fice zai baza k'amshi yake.... "Yana fita Deejah ta mik'e tana fad'in" Yes yeey yau zan fita nasha iska..."Irfan na lab'e yana kallonta harda wani tsalle da rawan ta, dariya sosai ta basa yanayin ta na burgesa....
"Yana zaune parlor yana kallon TV a lokaci guda yana sipping black tea Deejah ta fito cikin wani Arabian gown navy blue mai bak'ak'en duwatsu ta yane kanta da bk'in mayafi... "A hankali ya furta ya Salam, dif ya mance shan tea yake, tayi bala'in masa kyau...."Murmushinya sakar mata, ita kuwa duk sai tajita wani iri sabida irin kallon da yake mata, zo ki karya baby kar muyi latti muryansa ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, babu musu ta k'araso gamida zama duk jinta take a tak'ure hakanta karya, sabida mayen kallon da Irfan ke binya dashi...
"Duk yanda suka wuce kallonsu ake kaman wasu taurari, Irfan kuwa harda sakalo hannunta cikin nasa, sunyi kyau har sun gaji shakka babu sun dace da juna, Yanayin k'asar ya burgeta, ko ina tas tas gwanin ban sha'awa ga gini masu kyau da d'aukar hankali, a hankali take murmushi tana jin annashuwa cikin ranta, Shi kuwa Irfan sai murmushi yake yana son ganinta cikin farin ciki yana saka sa jin dad'i.....
"Ga mamakinta wani gida taga sunzo Irfan ya danna bell, wata baturiya ce tazo ta bud'e masu k'ofa gamida masu sannu da zuwa, haka kurum Deejah taji gabanta na fad'uwa tun zuwarsu Gidan, gabanta bai gama yankewa ba saida taga wata mata bak'ar fata ta fito tana ma Irfan sannu da zuwa cikin harcen hausa, toh su wacece wann a ina Irfan ya santa..."Gaisuwa da zolaya matar ta soma yima Irfan gaba d'aya bata lura da Deejah ba wacce ta kafe wani makeken hoton family picture d'in gidan Alhj Abdullah da idanunta, zuciyarta na harbawa haka kurum sanda take kallon hoton......
Sameena ceππΎ
[10/11, 10:05 PM] βͺ+234 803 864 9695β¬: ππππ *Mallakin Waye*
88
*Β©Sameena Aleeyou....βπ½*
_Queen Samy Novels Forum....ππ_
"Muryar Anty Bilki ne ya dawo da Deejah daga duniyar tunanin da ta tafi yanda take fad'in" Architect matar tamu kenan? Irfan ya murmusa yana kallon Deejah wacce ke k'ok'arin gaisar da Aunty Bilki,
"Itace Aunty na, musamman yau na kawo maki ita ta tayaki wuni kafin su Ayla su dawo daga school. Aunty Bilki ta fad'ad'a murmushinta kafin tace" Kai amma kuwa naji dad'i ya sunan nata. "Khadeejah Irfan ya bata amsa a tak'aice, agogon hannunsa ya duba kafin ya mik'e yana fad'in" Toh Aunty na I'm leaving nasan Mr Chairman yana jira na...,
"Mik'ewa Aunty Bilki tayi cikin sauri tana fad'in"
"Kallo Deejah ta bisa dashi alamun da gaske barinta zaiyi ita kad'ai tare da mutanen da bata sansu ba..."Muryan Aunty Bilki ya katse mata tunaninta sanda take fad'in" Irfan breakfast fah, pls ka tsaya ka sa wani abu a cikin ka, d'an girgiza kai yayi kafin yace" wllhi a k'oshe muke Aunty na, we already have our break.
"Mik'ewa Aunty Bilki tayi tana fad'in " I know you Irfan baka son cin abinci har Chairman ma ya gane ka, so I'll make takeaway for you.... bata jira cewarsa ba tayi wucewarta ciki.
"Juyowa yayi yana kallon Dee wacce tayi shiru tamkar bata wajen, sunkuyowa yayi kafin ya d'an shafi gefen fuskarta yace" Baby I'm going, da zaran na gama da Office zanzo na d'auke ki, just feel at home kinji Aunty Bilki is like a sister to me though a nan na saba da ita, so if you need anything don't hesitate to talk to her, she's very friendly yanda baki tsammani, nasan na barki a safe hand, I love you....ya k'arashe maganar yana manna mata kiss a goshi. "D'ago ido kawai tayi tana kallonsa sai samun kanta tayi da gyad'a masa kai alum toh. Murmushi ya kuma kafin yace "Yauwa baby ta, shafa kanta yayi tamkar wata k'araman yarinya kafin ya fice, Deejah ta bisa da kallo har ya b'ace ma ganinta....."
"Fitowar Aunty Bilki kenan da basket a hannu ta tarar Irfan ya tafi, zama tayi gefen Deejah kafin tace Wai tafiyar yayi bai karb'i abincin ba, Deejah ta d'an murmusa kafin tace" Ai munci abinci kafin muka fito, murmushi kawai Bilki tayi kafin tace" just feel at home, Irfan ya zama d'an gida, mijina yaji dad'in aiki dashi, Khadeejah kinyi dacen miji mai gaskiya da rik'on amana and also very hard working, at his age samun matashi mai k'wazo da k'ok'arin aiki irin haka da kamar wuya..."Nan ma murmushi kawai Deejah tayi, Kallonta Aunty Bilki tayi tana nazarinta dan kuwa tsaf taga irin sallaman da sukayi da Irfan, shakka babu akwai matsala tattare da aurensu dukda kodaga gani suna tsananin son sunan su, idan da amana kuwa ya kamata ta taimaka wa Irfan ta gyara masa auratayyar sa, d'an murmushi tayi kafin tace" Khadeejah tashi mu shiga ciki, babu musu Deejah ta mik'e tabi bayanta tana mai fad'in" Toh Aunty...
"Kar ki damu Khadeejah ni wllhi na d'aukeki tamkar k'anwa bance ki fad'a mun sirrinki ba, amma ina so nasan shin kina son mijinki..."Dago ido Deejah tayi tana kallonta kafin ta gyad'a mata kai a hankali k'walla fal idanunta.
"Sauk'e ajiyan zuciya Anty Bee tayi ta rik'o hannayen Deejah kafin tace" Deejah inajin wani al'amari mai girma a tattare da ke dan Allah ki fad'a mun tarihin rayuwarki...."I zuwa lokacin hawaye sun soma bin..."Jikin Anty Bee ya kuma yin sanyi, bata san sanda ta rungumo Dee ba tana lallashinta, Deejah bata b'oye mata komai ba tun girmanta a Orphanage har zuwa yau.
"Hawaye tuni ya wanke fuskan Aunty Bilki, dukansu biyu kuka suke, Aunty Bilki ta saita kanta kafin ta rik'o hannayen Deejah tace" Hak'ik'a Deejah kin had'u da sharrin 'yan adam, hak'ik'a rayuwarki akwai tarin darussa a ciki, amma Irfan baiyi Deserving haka daga gareki ba, duk abinda yayi, yayi ne out of love, yana sonki yana k'aunarki, kar ki kuskura ki *Mallaka* ma wata mijinki, auren Azeeza da yayi makirci ne kawai suka k'ulla ba wani abu ba, yanzu kinsan me nake so dake?..."Deejah ta girgiza kai alaman a'a. Aunty Bilki ta murmisa kafin tace" tashi muje kitchen muyi girki, babu musu Deejah ta mik'e ta ajiye mayafinta fuska fal fari'a tabi bayan Aunty Bilki dake rik'e da hannunta suka nufi makeken kitchen d'inta wanda turawa keta kaikomo a ciki,
"K'aramar tsuntsu ta ciro daga freezer da alama baru ne, wankewa ta kuma yi kafin aka d'aurata bisa wuta, wasu k'ullin kayan manya ta ciro aka soma had'i ma barun nan, Deejah dai sai kallonta take, suna had'a ido ta sakar mata murmushi kafin tace ta bud'e fridge ta ciro kankana da kwakwa da dibino sann ta nuna mata wata drawer tace ta d'auko mark'waila a wajen Deejah sai mamaki take ina ta sami wad'an nan abubuwan ita da take England, wata zuciya tace ba abun mamaki bane tunda a duniya take, nan da nan tayi duk abunda Aunty Bilki ta saka ta kan kace me sun had'a kayan sauk'ar wa macce ni'ima, Deejaj dai gaba d'aya kasa shan parpesun nan tayi dole dole Aunty Bilki ta sakata ta shanye tass, juice d'in kuma tace shi zata wuni tana sha, daga nan ta ciro wani k'ullin ta mik'a mata tace da zaran magrib tayi tayi tsarki dashi, Deejah tana d'an sunne kai ta karb'a Aunty Bilki ta murmusa tace, nifa yayarki ce so kima daina jin kunyata duk abinda ke damunki just let me know ta kashe mata ido guda tace hope kin gane....sosai ta bawa Deejah dariya gaskiya kirkinta ya zarce tunanin mutum, bud'e jakarta tayi da niyyan saka maganin ciki sai ganin kwalban turare tayi a ciki wanda ya sauk'ar mata da fad'uwar gaba....."Aunty Bee ta bita da kallo ganin yanayinta ya canza d'an tab'ata tayi kafin tace yaya dai Deejah.
"Deejah ta ciro turaren tace turare na gani cikin jakata, kuma ni a iya tunani na ba ni na saka ba, Aunty tayi shiru tana nazarin abin, Deejah ta ciro tana k'ok'arin bud'ewa da sauri Aunty ta karb'a kafin tace bazakiyi amfani dashi ba dan kina kewaye da mugaye zo muje, taja hannun Deejah suka fice, can ta baya suka je, Aunty tayi bisimillah ta buga kwalban nan a k'asa ya fad'i tuuuuiii, ai kuwa yana fashewa sai wani hayak'i da wari ne ya gauraye wajen, basu gama shan mamaki ba sai ganin tsutsosti sukayi suna fita daga cikin kwalban, cike da tashin hankali suke kallon juna Deejah ta rungume Aunty Bee tsam cikin jikinta sai b'ari jikin nata keyi, Aunty tace ki kwantar da hankalin ki kinfi k'arfin mugu zo muje muyi alwala muyi sallah raka'a biyu muyi addu'o'i babu musu Deejah ta amsa mata da toh Aunty......
*Abuja, Nigeria*
"Haka kurum Laila taji wani mugun fad'uwar gaba, da firgici kallon agogo tayi taga k'arfe 9:00pm, sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin tace Allah sa dai lafiya, a'a abu kaman wasa sai ganin wani ciwo tayi a tafin k'afarta wanda batama san taji ciwon ba, wani mugun zafi da zogi had'i da k'aik'ayi ciwon ke mata tuni ta soma sosa ciwon tana lailayasa da 'yannyatsun ta....
"Jikin Ruqayya yayi tsanani, tana rik'e da hannun Nadiya da Sadiq a hankali take fad'in" Ku yafe mun, ku rok'a min Allah ya yafe mun koda bayan raina ne, snn dan Allah kuce wa Mamie da Umma Hajja su yafe mun...."Nadiya cikin kuka take girgiza kai tana fad'in" Ruqayya ki daina fad'in haka, you are not going to die, you are a fighter, keep fighting kinji Ruqayya.... "Girgiza kai Ruqayya tayi kafin tace" Nadiya lokaci na yayi bazan wuce lokaci na ba, na gode wa Allah da yasa nayi nadaman abubuwan da nayi tun ina da sauran numfashi tun lokaci bai k'ure min ba, Ba hali na bane *Muguwar k'awa* da kuma son zuciya irin tawa ta kaini ga halaka.."Allah yasa wannan ya zama ishara ga masu hali da son zuciya irin tawa, Ya Sadiq ka rik'e Nadiya amana hak'ik'a matar zama ce, Allah ya baku zuri'a d'ayyiba, Allah ya albarkaci rayuwar aurenku...."Kasa cewa komai sukayi Nadiya kam sosai take kuka, Shima Sadiq tuni yaji hawaye na k'ok'arin wanke masa fuska, salati Ruqayya ta soma kan kace me rai yayi halinsa..."Innalillahi wa inna'ilaihirraji un, ko wace rai sai ta d'and'ani mutuwa...."Kuka mai k'arfi Nadiya ta sake gamida durk'ushewa k'asa, shikuwa Sadiq addu'a yayi ya shafe mata idanunta da suke a bud'e, sosai ya rungumeta cikin jikinsa.....
Sameena