Showing 51001 words to 54000 words out of 159062 words

Chapter 18 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10379

babu musu Deejah ta wuce kitchen ta soma had'a masa delicious coffee....
"Zulai dake lab'e window taga komai akan idonta sauri sauri ta isa d'akin Aziza ta sanar da ita... kaman wacce aka zabura haka Aziza ta fito lab'ewa itama tayi daidai lokacin da Deejah ke ajiye coffee gaban Irfan.
"Murmushi yake sanda yake bin fuskanta da kallo kafin yace" thank you, murmushi kawai itama tayi .....zata tafi ta jiyo muryansa yana fad'in "Zauna muyi magana..... '" 'Kirjinta na lugude ta nemi waje can gefe dashi ta zauna.
"Irfan ya kurb'i coffee d'in yana d'an kashe ido kafin yace" woow this tests good, ita dai Deejah kasa cewa komai tayi sai kurawa tv ido tayi kaman wacce take fahimtar me akeyi. Kallonta yayi yanda tabada hankalinta sosai ma kallon, dan murmushi yayi kafin yace" Kema kina kallon ball ne? "Da sauri ta girgiza kai alamun a'a... Toh kuwa soon zaki fara kallo dan zan koya maki.
"Murmush kawai tayi bata furta komai ba....."Wai yaushe kika zama silent haka ne huh? Irfan ya tambaya, Ok dan abinda ya faru da yarinyar can koh, pls kar kisa wani damuwa for nothing ma rayuwarki, Allah ya shiryata da masu hali irin nata. Daga haka bai kuma cewa komai ba saida ya gama shan coffee dinsa kafin ya tattaro hankalinsa yana fuskantan Deejah, saida ya rage muryan tv din. Shiru ya ziyarce su na d'an lokaci kafin Irfan ya soma fad'in.....
"Deeee! Deeee d'ago pls ki kalle ni.....! Ya sake fad'a wann karan murya can k'asan mak'oshinsankaman me yin rad'a,...."K'irjinta na fad'uwa sabida abubuwa da dama da suka ziyarceta, a hankali ta d'ago ido tana kallon Irfan.... bata iya jure kallon nasa ba da sauri ta sunkuya. Irfan kuwa wani k'warin gwiwa ne yaji ya ziyarcesa dan haka dad'a gyara zama yayi sosai kafin ya soma fa'din
"Deejah inaso ki fad'a mun if you've ever been in a relationship..... I mean kin tab'a soyayya da wani. "Idonta na bisa carpet ta shiga girgiza kai alamun a'a.
"Wani da'di da farin ciki su suka ziyarci Irfan dukda zai wuya mace kaman Deejah ace bata tab'a soyayya da kowa ba.
"But how? Ya tambaya cikeda mamaki...... kasa amsa masa Deejah tayi. Muryamsa ta jiyo yana fad'in " Ko kema baki yarda da abun bane before just like me. Nan ma shiru sai faman wasa da yatsun hanunta take. "Bata ankara ba sai ganin Irfan tayi durk'ushe gaban kujeran da take, da sauri ta d'ago kai sanda taji tattausan hannayensa bisa nata. Kallonsa take cike al'ajabi, innalillahi meke shirin faruwa, irfan da kansa durk'ushe gabanta....... "Muryansa ya katse mata tunani sanda yake fad'in......
"Deeee.....! Na jima ina k'aryata wann kalma "Love" na jima ina d'aukan wann kalma a matsayin Ridiculous thing, abu maras amfani, na jima ina k'aryata luv, na jima ina fad'in love doesn't exist, I never thought it will happen to me, not even my in dreams, I never thought this time will come ni Irfan Nazif Mumtaz zan sauk'e idona kan wata mace, I never thought a day will come that I might have feelings for any girl......." shiru na d'an sakwanni sai bugun zuciyoyi kawai wanda harda Aziza dake lab'e bayan window wacce da kyar idan k'afanta zai iya d'aukanta....
"Irfan yaci gaba da fad'in" Deeee na jima ina avoiding dinki ina k'aryata abunda nake ji gameda ke, but I just couldn't help it anymore, I must admit it. Deeejah I fell for you from the very time I saw you. I love you Deejah with all of my heart, and am ready to give you the care and love a lady desires most. Tell me Deee do you feel the same for me?????
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un...."kaman a mafarki haka Aziza ke kallon wnn al'amari, dama mafarki ne dayafiye mata sauk'i, shikenan itakam ta shiga uku ta mutu ta lalace, da kyar da jan k'afa ta wuce d'akinta ta shia tattara kayanta tana zubawa a akwati........


"Deejah kuwa kasa motsa koda d'an yatsan tayi sabida wani irin shocked da bata tab'a experiencing ba. Take tunanin nasihan da Anty Larai ta mata kan ta fara aiki gidan Engr ya fad'o mata.....
_" Ki kula sosai da kanki, musamman idan gidane me samaruka, so tari yaran masu kud'in nan sukan d'auki ma'aikata a matsayin 'yan iska, idan sunga ba layinki bane su b'ullo maki ta hanyar soyayya su yaudareki da kalmomi su samu abinda zasu samu daga gareki daga baya kiji ana zai auri 'yar gidan wane abokin mahaifinsa, ki tsaya a yanda aka umarceki. Ita rayuwa daidai ruwane daidai gari_....... Da sauri ta fizge hannunta daga rik'on da irfan yayi mata, ta soma girgiza kai kwalla na shirin ciko idanunta take fad'in." Bana sonka..... bana sonka master, aiki nazoyi gidan nan dan Allah kayi hak'uri dan ina ganin girmanka........ daga haka tasa kai ta wuce hawayen dabata so su zubo suka shiga zarya a fuskanta......" Kallo Irfan yabita dashi har ta haye sama......






πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„..........
[8/28, 13:56] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye*

38


*I Sincerely dedicated this Spectacular Chapter to All my Adorable Fans around the Universe........ 😍😘 #Allah bar Zumunci#πŸ’—*




"Kasa motsawa Irfan yayi sabida wani irin shock da ya ziyarci illahirin jikinsa, haka yabiya da kallo har ta b'ace masa, gaba d'aya ya kasa gasgata abinda ya faru abinda kunnuwansa da idaniyansa suka gane masa " Wai shi Irfan har akwai yarinyar da zata kalli tsaban idonsa tace bata sonsa, in the first place meyasa ya fara yarda da wnn ridiculous thing so called love din,.....
"Dafe kansa daya masa nauyi yayi yana so ya daina tuno kalman "Bana sonka da Deejah ta fad'i masa amma ya kasa, kalman sai yawi take masa a kunnuwansa da kwanyansa. Why all this, meyasa na yarda da zancen Sadiq cewa Deejah sona take, Oh my Goodness yarinyar nan shikenan ta rainani.... jifa da remote yayi yana firta " Shitt dammnn everything!!!.... Jiki a mace ya mik'e ya nufi sashensa...




"Deejah kuwa tana fad'awa d'aki kwanciya tayi ta soma kuka da gaske, banda son Irfan dake azalzalanta babu abunda take ji musamman da ya furta mata kalman so a yanzu, anya tayi daidai ma kanta, anya bata tafka babban kuskure ba, meyasa tak'i amince ma buk'atan Irfan.... take ta soma furta innalillahi wa inna'ilaihirraji'un.... da taimakon Allah ta sami sauk'i cikin zuciyanta, wata zuciyan twce" Abinda kikayi kinyi daidai dan kuwa Irfan ba daidai ke bane, take maganganun Nadiya suoa dawo mata _Ke da ya Irfan kuna son junanku_ toh ko da gaske Irfan sonta yake, take wata b'angare na zuciyanta tace" yanzu ne zaki gane idan yana sonki, he'll surely comeback to you,..... A hankali ta kwanta gamida runtse ido dan kuwa ko kad'an bata jin baccin mai zuwa ne.......


"A b'angaren Azee kuwa sosai take kuka take had'a kayan cikin akwati itakam bazata iya tsayuwa bak'in ciki ya kasheta a nan ba, gwara ta koma gidan Hajiya kawai abin zaifi mata sauk'i....... "Da wnn tunani ta kwanta ta ci gaba da aikin kuka..... "Cikin wnn dare ma iya cewa mutane ukun nan basu runtsa ba, Irfan Deejah da kuma Aziza......!




"Washe gari sassafe Laila ta tarar Azee tayi waya wa Safwan yazo ya d'auketa, sosai Laila ke lallashinta da ky'ar da yarda ta amimce bazata tafi ba, Safwan na isowa saida yasha tambayoyi wajen securities snn sukayi waya da Laila ta sanar dasu ko da yaushe yazo a bude masa gate uncle din 'yarta ne....
"A parlor Safwan ya sami Laila sai bin gidan da kallo yake, ya d'aga gira sama yana fad'in "Mansion Indeed" Laila zatayi magana yayi saurin cafko ta ya shiga kissing dinta yana juyata..... "Da kyar ta kwaci kanta hanun Safwan kafin ta soma fad'in
"Lafiyanka Safwan kanka d'aya, cikin gidan Engr fa muke snn Aziza na gidan nan fah someone might see us ai. "Murmushi Safwan yayi yana shafa hab'a kafin yace" rabona dake tun yaushe kinsan nayi ko'kari.... ya kuma mastowa yana k'kok'aro cafkota.... matsawa baya tayi kana tace" kaga mijina na gida be tafi office ba, yanzu haka ma yana gab da fitowa dan ya gama shiryawa, dan Allah ka saita kanka.
"Safwan yayi Murmushi kafin yace" toh me miji naji yanzu rubuta check din ki bani tunda Azee baby ta fasa tafiya. " A gurguje Laila ta zaro check din 200,000 ta b'alle ta mik'a masa.... daidai nan Engr ya shigo parlorn da sallama.
"Take suka sha jinin jikinsu.... Safwan yayi saurin rusunawa yana gaida Engr......" haka kawai Engr yaji Safwan be kwanta masa ba...
"Laila tayi saurin fad'in har ka fito.....


"Karasawa ciki yayi be amsata ba saida ya shige cikin d'akinta, nan itama ta biyo bayansa, kallonta Engr yake kafin yace" Wanene wancan kuma a parlor....
"Take Laila ta soma had'o kalmomi tana fad'in" Dama k'anin baban Aziza ce, toh kasan na fada maka batada lafiya shine yazo dubata.
"Engr yayi shiru kaman bazaice komai ba sai kuma yace" Next time idan yazo ya tsaya a parlorn bak'i dan bana so Maza suna shigewa kan iyalina kin gane...... "Da sauri ta gyada kai ta soma gyara masa links dinsa gamida kissing dinsa tana wani manne masa, a hankali Engr ya d'agata daga jikinsa kafin yace" na makara ina sauri, yaya jikin Azizan... sai ku shirya driver ya kaita asibiti. Laila ta dan marairaice fuska twce wai da ni zanyi driving. Girgiza kai Engr yayi kafin yace" how many times do I have to tell you, bana so kina driving, driver ya kaiku period.... daga haka yasakai ya fito dan ransa ya gama b'aci sakamakon ganin Safwan da yayi a parlorn matarsa danma dai k'anin baban Aziza ne da yau ya gane kurensa. Ta biyoshi har waje tana masa sallama daidai lokacin da escort dinsa ke bude masa marfin mota, juyowa yayi kana yace" yaron can ya dawo parlorn bak'i su gana da 'yar shi kinjini da kyau... gyada kanya tai tana mamakin dama haka Engr yakeda kishi...


"Tana dawowa Safwan ya tsareta da ido yanda duk ta birkice, dariya yayi kafin ywce" wnn tsoho naki akwai kishi,... zama tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin tace "Safwan bana son duk wani abin da zai kawo mishkila tsakanin aurena da Engr...... sai faman magana take bata ankara ba sai ganin Safwan tay7 yana rage belt d'in jikinsa.... mikewa tayi tana fadin "a a meye haka kuma Safwan.... "Bai tsaya saurarenta ba ya janyota jikinsa ya shiga sarrafa sassan jikinta..... Laila tayi missing Safwan dan kuwa Safwan gwanine wajen Sarrafa mace... dole ta biye masa sukw fada dakinta suka aikata masha'ansu.....
"Har Safwan ya bar gidan Aziza batasan yazo ba....!




"Yau Deejaj kowa ya ganta yasan ba daidai take ba, gashi Irfan ya fice office bata gansa ba, bata tsammanin ya shigo yayi breakfast dui saita tsinci kanta da rashin jin da'din haka, ta sami kanta tana me d'aura laifin rashin karyawanshi ma kanta. Haka ta wuni sukuki, harta su Ammah da Hajja saida abin ya damesu, juyin duniya tq fad'i meke damunta tak'i fad'i....




"Shima a b'angaren Irfan kasa tab'uka komai yayi a office, duk yanda yayi ya cire tunanin Deejah a ransa abu ya faskara, shin wann wata irin yarinyace, gaba daya regretting dawowansa Nigeria yake..... yana zaune yana aikin tunani Sadiq ya shigo da sallama, ko kadan Irfan beji shigowar Sadiq ba har saida ya zauna.
"Kallo d'aya Irfan ya masa ya watsar, Sadiq ya masa k'uri yana son gano wani abu. Can dai ganin Irfan bashida niyyan masa magana yasa sa cewa " Architect wai lafiya, meke damunka.
"This is all your fault Sadiq, na gaya maka I don't wanna engage my self into such stupid so called love stuff, kayi influencing dina I should propose yo her, toh gashi nan she let me down, ta kallo tsaban idona ta fada bata sona, na fada maka dama ba sona take but you keep insisting, for goodness sake yanzu raini ma ya shiga tsakanina da ita........" Dariya sosai Sadiq ya shiga yi har yana sunkuyawa..... "Mugun kallo Kawai Irfan ke watsa masa kafin yace" you making a fun of me, good ya maka kyau Sadiq, barin fice na bar maka office din idan ka gama dariyan saika kirani.
"Riko hanumsa Sadiq yayi yana ci gaba da dariya kafin yace" haba Architect take it easy, bani na kar zomon ba fah rataya aka bani... "Irfan ya tab'e baki kafin yace "there you go again with this hausa quotes, mtsw am serious fah Sadiq, I don't know what to do fah now that I fell for her....


"Sadiq yayi k'ok'arin saita kamsa kafin yace" my point exactly, neman solution za'ayi bawai kace shikenan yanzu ta rainaka ba, Architect shifa love babu ruwansa da status na mutum kawai shiga yake, ka ajiye all those girman kanka nan kayi facing reality, kar ka bari macen da kake so ta kufce maka, yeah na sani kana da komai da zakayi yanga wa mace son ranka, shiyasa ma nake ga babu macn da zaka ce kana sonta tak'i Irfan, kawai dai sai sun d'anja ajin nan ne da suka saba... amma ka sani su mata 'yan lallab'i ne dole ka sauk'e kanka ku zama level d'aya.
"Tsaki Irfan yayi kafin yace" To hell with jan ajin nasu, all that I've shown to her, kana nufin saina bita fiye da haka,,,,, kai no never. Yanzu haka ma regretting abinda na mata nake, kai ni dama na rik'e son nata a zuciyana wllhi da yafi mun, kasanni I don't tolerates shitss wllhi.
"Sadiq ya murmusa yana mamakin hali irin na Irfan, koda yake ya cika na mijin da zaiyi haka....


"Koda ya tashi a office me ba gida ya wuce ba, gidansu Ahidjo ya nufa direct dan kuwa tin bayan daukosa da yayi a club bai kuma ji daga garesa ba........






*Toh 'yan uwa a daidai nan zan dakata da rubuta wann littafi nawa harsai Allah yakai mu bayan sallah...... Inama kowa fata na Alkhairi, Allah yasa muyi azumi lafiya yasanya mu cikin 'yantattun bayinsa, Allah yasa ayi sallah lafiya.....QueenSamy ke maku happy Ramadan Mubarak in advance😍*




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„........
[8/28, 14:01] Umar Dalha: πŸŒ“πŸŒ”πŸŒ—πŸŒ˜ *Mallakin Waye*


39




_Barka da Sallah to all my fans around the world 😍😘..... #Always 2geda ✌🏼_


"Kallo daya Ahidjo yayi ma Irfan ya gane wani abu na damunsa dan kuwa tin shigowansa bai cema Ahidjo kanzil ba sai zama da yayi ya soma buga game PS5, da ganin yanda yake danna pat din zaka gane something is definitely wrong, Ahidjo ya zauna gamida jawo pat daya shima suka soma game din a tare, yanda Irfan yake buga game din da zuci abun har ya bawa Ahidjo dariya, ganin dai tabbas Irfan lost his mind yasa shi ajiye pat din kafin yace" Guy wai meke damunka ne?
"Irfan ya dago kai yana kallonsa galala kafin yace" what sort of question is this, I just came here to get some fresh air, look I don't want disturbance kar ka dameni pls.
"Ahidjo yayi murmushi yana kallon abokin nasa dan idan da sabo to babu shakka ya saba da miskilancin Irfan tun ba yau ba, daga haka be kuma ce masa komai ba ya ciro wayarsa ya shiga dannawa.
" _Bana sonka bana sonka bana sonka master_!!! Kalaman Deejah suka shiga dawo masa kwanyansa, meyasa ya kasa cireta a zuciyansa meyasa yakeji kaman wutan sonta dad'a ruruwa yake a zuciyarsa,..... "NOOO!!! ya furta da k'arfi gamida jifa da pat din dake a hanunsa, toshe kunnuwansa yayi tamkar zararre yake fad'in " you can't take me down, you cannot do this to me Deeee, I know you love me too, just say it, say you love Deee....... "Tamakar TV haka Ahidjo ke kallon irfan se yanzu ya gane dalilin shigan Irfan wani yanayi.... " _Tabdijam ko a mafarki be tab'a zaton akwai macen da Irfan zai zare akanta ba, kai ko zamansu a US babu kalan en matan da basu kawo kansu ma Irfan ba amma fir bae kula kowa bai da lokacin kowa yau ga Irfan dying for a mere girl, yarinya me law class irin Deejah lallai kuwa Deejah ta ciri tuta, duk wnn tunani a ransa Ahidjo keyi, sai yanzu ya kuma jin sha'awan Deejah na dad'a tsargarsa, kai dole ma Irfan yasota dan kuwa koda ace ba wani kyaun fuska bane da ita akwaita da diri wanda duk na miji mai isheshen lafiya yayi tozali da ita sai yaji abu ya tsargar masa, kai dole yasan yanda zaiyi ya sami Deejah kata halin k'a'ka_..

"Take it easy pls Irfan, comfort your self and spell everything, Ahidjo ya fadi sanda ya tsare Irfan da ido. " Gajeren tsaki Irfan yayi gamida mikewa ya nufi d'an madaidaicin fridge din dake a parlorn Ahido, wani karin abin takaici shine fridge din babu komai a ciki sai tarin alcohol masu dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login