Showing 39001 words to 42000 words out of 159062 words

Chapter 14 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10413

shewa suka tafe hannu.... duk wann abu a idon Alhj Ma'aruf akeyi, hawauene kawai ke fita a idonsa soboda zafin da zuciyansa ke masa.
"Laaaa kinga makirin nan wai kuka yake, hajiya Karima tace, tsuka laila tayi kafin tace bakin ciki yake mun dan ba shi ya haifeni ba,. Kece ma me biyesa Hajiya , ki daina basa magani ki karasa banza ki huta.
"Hajiya ta tabe baki tace kyale maye babu abinda zai iya sai hawaye..... wata shewan suka kuma sakawa kafin Hajiya tace muje yanzu zasu taho su tafi dake.... A parlor suka tarar da Aziza shigowarta kenan tana fadin momy masu daukan amaryan sun iso..... take wata kawar hajiya karima Hajiya Delu ta shigo tana guda...




"Har gidan Engr Aziza ta raka momynta burinta bai wuce ta zama close to Nadiya ba ko zata samu ta sami gurbi a zuciyan Irfan,


"Engr zaune gaban Ammah tayi masa nasiha sosai ba fuskan kowa yake tuniwa ba illa Fatima, Allah sarki Fatima Allah yayi ba matarsa bace, baisan sanda idonsa suka soma zuban hawaye ba, sosai Ammah ta tausaya masa da kanta ta rakasa har kofar sashensa, zuciyanta na cike da tausayin dan nata,
"Laila tanajin rufe kofa alamun shigowan Engr tayi saurin rage muryanta cikin waya, kai Safwan my Engr is here, you need hang up... Safwan ya kece da wata dariya yace, ni kinsan ma meke damuna, duk wann gyaran da kika sha wa tsoho akayi, I wish na sameki yanzu nan, kai tsoho zai kwasa ganima, toh nidai damuwata shine na mallaki kaso a M&M Bulders.... tsaki Laila tayi kafin tace zamuyi waya gobe, daga haka ta katse wayan, ta shiga duba fuskanta a madubi, bayan tayi duk abunda Hajiya ta umurce ta.




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹........
[8/21, 06:18] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye*


30




"Washe garin da Laila ta tare gidan Engr da sasafe ta tara gaba daya ma'aiktan gidan kowa taji aikinsa, kallon Deejah take cike da tsana dan Zulai ta fada mata komai gameda Deejah, tsayuwa tayi a gaban Deejah tana kare mata kallo, Deejah kuwa ganin irin kallon da Laila ke mata yasata dauke kai gefe.
"Deejah kike kowa? Laila ta fadi tana mai yatsina fuska, biyo ni zuwa dakina.... daga haka tasa kai ta wuce.
"Hajja da asabe suka kama baki suna masu zullumin yanda rayuwar gidan zata kasance. Zulai kuwa wani murmushin 'keta tayi tana juya ido.


"Kinajina so nake ki fito da kayana daga cikin akwatina sann ki jera minsu cikin wardrobe, idan kin gama ki share dakin nan tsafa ki wanke toilet, snn bana son 'kazantar ku ta masu aiki, ki tabbata kin tsaftace ko ina idan ba haka ba, sakewa zakiyi daga farko.
" 'kerere Deejah ke kallonta kafin tace" Anty nifa ba wnn ayyukan nake a gidan nan ba, ni aikina kulada yara ne, amma akwai su Zulai sune ayyuka irin wnn ya shafesu.


"Kanbuuu! Shaye da mamaki Laila ke kallon Deejah ita take fadawa wann ba aikinta bane, murmushin 'kasaita tayi kafin tace" I don't care ko wani irin aiki ne ya shafe a gidan nan, as far as you're a Maid here, kome nake son saka ki zan sa ki a lokacin danaga dama, kar ki mance I'm the Lady of this house dan haka sai abinda nace. If you don't want your self to fired, sai kiyi abinda na saka.... Har ta soma tafiya ta juyo tana watsa wa Deejah kallon 'kas'kasnci snn tace" this should be the first and last time da zan saka ki wani abu kimin musu. Daga haka Laila ta fice parlor cikin takun isa.
"'Kwalla ne suka ciko idon Deejah a hankali ta goge ta soma aikin da Laila ta sakata...


"Zama Laila tayi a parlor gamida kunna Tel ta soma kallon program din The Drs a mbc4, AC na dukan 'bargo da tsokarta yayinda drink me sanyi yake ajiye gefenta, sallaman Azee ne ya dawo da ita daga duniyan kallon da tayi nisa a ciki, da gudu Azee ta fado kan Laila ta rungume, "Momyyyyy, rungumeta Laila ma tayi kafin tace" Azee baby wani irin abune zaki zo min gida yau, jiya jiya fa na tare, turo baki Aziza tayi kafin tace" kai Momy keda kika ce da zaran kin tare nima zaki zo ki daukeni, toh naga bakizo ba shine nima na biyo ki, ga luggage dina can a waje, Uncle Saff ne ya kawo ni, momy wllhi na 'kagu na dawo gidan nan na soma rayuwa tareda Irfan Handsome,
"Laila bake sake take bin Aziza da kallo, kai amma ke wnn yarinya akwai ki da jaraban tsiya, kuma yanzu Hajiya tana gani kika taho harda kayanki gaba daya,
"Aziza tayi kicin kicin da fuska, haba momy, idan bakison ganina a gidan nane fine sai na tafi kuma wllhi bani 'kara dawowa.
"Jawota jikinta Laila tayi kafin tace" kwantar da hankalinki 'yar lelena, gidan nan gidanku ne, ki saki jiki tamkar na ubanki, shewa Aziza tasaka gamida tafe hannu da Laila tana fadin" Sai momyyyy,
"Laila tayi murmushi tace, ke ba wani momy dalla, sekace wata tsohuwa, from now on, kema Aunty zakina kirana, Aziza ta kuma saka dariya tace kuma fah hakane, ki ganki wazaice kin haife ni, gaskiya Aunty ne ya dace da ke... dariya suka saka gaba daya yauwa koke fa.... Kira Laila ta shiga rangadawa Zulai, nan da nan Zulai ta bayyana a gabanta, tana mai durkusawa hadi gaisuwa, Aziza ta kalli Zulai ta she'ke da dariya tace" shegiya zulai anyi kilin, ji yqdda fatarki ta canza, dariya zulai tayi tace" Anty Aziza kiyi shiru kar a jiyo mu kinsan 'ywr sirrine abin ba'asan nida Auntu munsan juna ba, Laila tace kawo mata drinks da snacks... babu musu Zulai ta wuce dan aiwatar da umarnin Laila.
" tadi suka ci gaba da yi ita da Aziza, Aunty yanzu ina ne dakina, gacan wani daki nan cikin sashena ba saiki zauna ba, girgiza kai ta soma kafin tace" no Aunty nifa nafi son daki kusa da Nadiya dan kinsan so nake ta zama best friend dina, so nake duk mu zama close da yan gidan nan sabida Handsome Irfan, murmushi Laila tayi tace sha kuruminki, duk yanda kike so zaki zauna gidan nan...Allah Aunty Aziza tace tana me zaro ido, tafewa sukayi dukansu biyu sekace wasu 'yan tasha....


"Engr ne yayi sallama ya shigo cikin shirin fita, take Laila ta mike tana masa sannu da shigowa, da fari'a saman fuskansa ya ansata, a'a yau daughter tazo mana ne.... murmushi Aziza tayi ta dur'kusa har 'kasa tana gaida Engr, Laila tayi caraf tace" Wllhi My Engr wai ta kasa zama babu ni shinefa daga kwana guda har ta biyoni, murmushi Engr yayi kafin yace" ai ni na dauka tun a jiyan itama zata dawo nan, ai yanzu batada gidan daya fi nan, ko ba haka ba daughter. ?.. murmushi kawai Aziza tayi tana sunne kai, kai kace me kunyar gaskiya ne, Laila ta murmusa tace kai Azee new daddy dinki na sonki...... Dai dai nan Deejah ta fito da Mop jkiknta duk ya ji'ke tayi gumi zata shanyawa.... " Kallo duka suka bita dashi, take taji kunyan yanayin data fito babu Hijabi ga Engr a wajen, dan durkusawa tayi ta soma gaishesa.... " A a Deejah ya na ganki haka da mop, ina sauran masu aikin gidan...... kan Deejah tayi magana Laila tace, wllhi my Engr ita tayi insisting wai zata ke mun ayyukan dakina ta karashe maganar tana me gallawa Deejah harara tace maza tashi mana kije ki shanya, mugun kallo Deejah ta watsa mata kafin ta mi'ke.... girgiza kai Engr yayi snn yace" no ba aikinta bane, aikin Deejah a gidan nan shine kula dasu Nilam, pls next time ki saka wata cikin sauran ma'aikatan, Azee baki sake take kallon Engr yanda yake defending Deejah.
"Laila kuwa ba'kin ciki ne ya turnu'keta a fili murmushin ya'ke tayi tace, toh my Engr amma ai yanzu kula dasu Nilam ya dawo hannu na tunda na iso, ko baka so na zame uwa a garesu ne...
"Cike da jin da'din kalaman Laila yace" gaskiya naji dadi, idan kikamin haka kin gama mun komai, maganarki haka ne, ke uwace a garesu, ya mike yana gyara agogonsa yace ni zan fita.
"Mikewa Laila tayi gamida saka fuskan tausayi tace, my Engr I thought yau bazaka fita ko ina ba, dan murmushi yayi yace" kiyi hakuri hakane ya kamata, na zauna maki a gida yau, fitan ne tazo min urgent, akwai kaya da mukayi ordering dinsu daga Turkey, toh an sami short shiyasa zan fita.
"Murmushi tayi tace" toh Alllah bada sa'a ya kuma dawo min dakai lafiya.
"Sosai yaji dadin addu'an nata har cikin ransa, har wajen motarsa Laila ta rakasa saida taga fitarsa, Ammah na kallonsu ta window din dakinta, wani dadi taji ya mamaye zuciyarta, yanzu kam tilon 'danta ya sami mai kula dashi....


"Sauri sauri ya gama shirinsa cikin suite dinsa, kana ganinsa kasan he's in a hurry, kaman ance ya kalli backyard ya hangota tana wanke mop, tsayuwa yayi yana kallonta, cikin takunsa na 'kasaita ya 'karasa gabanta, Deejah kam batasan da zuwansa ba saida ta dan razana, kallo daya ta masa ta sunkuya gamida gaishesa, a takaice ya amsa kafin yace" me kikeyi a nan,
"Kaman bazata amsa ba tace aiki nake, na gama ma. "Daure fuska ya kumayi kafin yace" yaushe kika soma irin wnn aikin a gidan nan, snn kinzo nan waje yanda securities zasu iya ganin ki babu ko mayafi, next time idan zakiyi aiki a nan make sure kin rufe jikinki da nayafi, tsayua kawai Deejah tai tana sauraren 'jarfin hali irin na Irfan...... Har ya soma tafiya ya juyo ya dan kalleta yace" kar ki sake aiki a nan, shiga ki kawo mun fresh drink ina mota ta, idan Amma ta tambayeki kice mata na makara, sauri sauri ya wuce parking lot.
"Mamaki ne ya ishi Deejah shi kuwa wn bawan Allah akwai krfin hali sekce wani ubanta, ji tayi bata iya masa musu, snn kwarjininsa ya zarce tunanin mai karatu.
"Sauri sauri ta wuce cikin gida, a parlor ta hadu da Nadiya saukowanta 'kasa kenan, Nadiya ta bita da kallo ganinta a jike kfin tace, Deejah yau ina kika shiga kika jike haka, nasan dai su Nilam sun tsufa a sch balle nace wasan ruwa kukayi, ta karashe maganar tana dariya...... Dariya Deejah ma tayi sanda suka nufi kitchen a tare kafin tace" wllhi Anty ce ta sakani aiki gyaran sashenta.... "Shaye da mamki Nadiya ke kallon Deejah hfin tace wacece kuma Anty. Ci gava da hada drink din Irfan tayi tana fadin" Aunty Laila mana, tsaki Nadiya ta buga tace, ai inajin sanda take assembly wa ma'aikata, toh wayce mata ke aikinki kenan, wllho yanzu zanje na sameta bazata sake sakaki irin wann aiki ba... Deejah ta nufi kofa tana fadin" wlhi idan kikaje mun 'bata kenan, gwanda ke master na jiran drink dinshi, daga haka ta wuce waje.




"Cikin motarsa ta sameshi sauke glass yayi ya kar'ba hadi da jifanta da wani asirtaccen kallo wanda ya saukar mata da shock, murmushi taga Irfan yayi ya furta thank you a hsnkali....sann ya juya starry ya wuce.. har ya bar wajen Deejah bata var kallon motar ba, yau Irfan was nice to her for the first time, ji tayi wani da'din da bata sn dalilinsa ba ya dirar mata....
"Duk wnn bidiri a idon Azee akayi shi, tana kallon irin murmushin da Deejah tabi motan Irfan dashi, kutumele si, wllhi bazata taba sakuwa ba, itafa sabida Irfan ta dawo gidan nan ba don kowa ba, wann shegiyar me aikin da ita take zance, a saba'in ta wuce sashen Laila taca kwal mata kira.....




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ’„πŸ’‹..........
[8/21, 06:18] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye*


31


"Jin irin kiran da Azeeza ke dokawa Laila, yasata saurin nufowa 'kasa daga upstairs, meke farua,lafia? Laila ta bi'da.
"Aunty wnn shegiyar er iskar me aikin na lura tafi kowa iyayi da zagwa'di a gidan nan, Laila ta zauna bisa sofa tana fa'din waye kenan.
"Wann munafukar da 'dazu ta gyara maki 'daki mana, ganinta nayi sai karairaya take ma Irfan kaman zata shige motan dan kinibibi.
"Laila ta muskuta tace, ai wnn shegiyar yarinya tinba yau ba zulai ta gama fa'damin komai akanta, kuma tinda yanzu na shigo gidan nan dole na gyara mata saiti.
"Aini wllhi ko baki gyara mata ba, ni nan na isheta, dan wllhi kan Irfan babu abunda bazanyi ba, Azeeza ta fadi tana wani huci kaman kububuwa..... " Laila ta matso kusa da Aziza ta rike hannunta tace" daughter karki damu, kadama ki saka ma ranki damuwa, idandai ina numfashi toh wllhi sai kin auri Irfan, snn wnn 'karamar er iskan ninasan yanda zanyi da ita, tashi muje ki gaida Ammah, ki kama kanki sosai a gabanta ki nuna ke nitsetsiyar yarinya ce dan ki sami gurbi a zuciyanta..... "Wayan da Safwan ya mata ne yasata mikewa ta bar wajen ta nufi sama amsa wayarsa.
"Wai kam lafiyar ka 'dan cutie, nifa amarya ce kasan a kwanakin nan dole na kasace da Engr koda yaushe, idan kana kirana on and on zaka sa ya fara suspecting.... Dariya Safwan yayi kafin yace" Laila duniyar Allah, wato 'dan kwana dayannda kikayi a gidan Don Nazif shine har kin manceni, irin masu kudi haka ba wani lokacin matansu sukedashi ba, ya gama maki na amarci nasan soon zaki soma nemana ni kuma lokacin na wula'kantaki...
"Cike da 'kosawa Laila tace" Haba 'dan cutie ya kake magana haka, kaga niba wnn ba ka kawo mun Cv dinka na mi'kawa Engr a sama maka aiki a M&M, ko yaya kace, wani ware ido Safwan yayi kafin yace" woow are sure Mrs Mumtaz, kai naji dadi Allah barmin ke, ina Azee baby na take, Laila ta dan yatsina fuska kafin tace tana downstairs, dama ina nemanka kawai ka kawo mun Aziza tin kafin na gama cin amarci.
"Safwan ya sheke da dariya kafin yace" dama bana so aci amarcin da kyau ne shiyasa na kawota. Nifa na kagu ma ki fara fita, .. sun jima a phone suna hiran batsa da suka saba kafin suka ajiye...




*M&M Builders*


"Tin daga nesa Sadiq ya hangosa sai sauri yake, murmushi yayi a ransa yace " Architect Irfan kenan. Hannu ya daga wa Irfan, aiki nan Irfan ya karaso wajensa, gaisawa sukayi kafin Sadiq yace" Architect zaka amsa query fah, kaga time kuwa.
"Irfan ya dan murmusa yace" wllhi ka bari kawai Friend, I woke up very late, kuma nasan hakan nada nasaba da kwanciya late danayi jiya, yanzu haka ma daddy ne ya dago ni wai be ganni a Office ba... Dariya Sadiq yayi kafin yace" ban gane ka kwanta very late ba, kodai tunaninta ka tsay yi, murmushi Irfan yayi kafin yace" kallon prison break fah na tsaya yi, ksan anyi releasing new episode. Sadiq yai murmushi yace" ni ina nakeda wani time din kallo, muje Daddy na jiranmu tin dazu a Office dinsa. Kai tsaye suka wuce office din Engr.


"Gaisar da Engr Irfan yayi, ya amsa idonsa naga screen din computer kafin yace" Irfan ya akayi kayi latti, bayan na fada maka yau za'a shigo da kaya, good thing Sadiq was here early, gashi an samu kayan akwai short,
"Irfan ya dan sosa keya kana yace" daddy na makara ne, yanzu anyi signing duka documents dinne.
"Engr yace Sadiq zai fada maka komai, pls kuyi bincike sosai a fannin menene aka fitar da kudade ba tareda sa hannu na ba, a tare Sadiq da Irfan suka amsa, Sadiq yace mu 'karasa office dinka, Irfan yace no muje naka dai kai da kake fannin account zaifi mana sauki, murmushi Sadiq yayi yace Ok lets go then...
"Engr yabisu da kallo yanda suka jera suna tafiya sun birgesa.


"Chairman ne zaune a kujeransa sai juyi yake komai ya jagule masa tunda Sadiq ya soma aiki da company din, Sadiq da Irfan sosai suke aiki a company, duk wani corruption suna kokari suyi fighting dashi, wayarsa ya dauka ya shiga neman layin yayarsa Hajiya Karima, dan gwara tun wuri su tashi da gaske kafin komai ya jagule masu....




"Zulai dauke da luggage din Aziza ta nufi sashensu Nadiya dashi, a bayanta Laila da Aziza ne ke take mata baya.
"Deejah na zaune saman madaidaicin gadonta taji an banko kofa an shigo, a zabur ta mike tana binsu da kallo,
"Maza ki tattara kayanki ki koma fannin ma'aikata, me 'daki ta iso, nan dakin Aziza ne..... cike da mamaki Deejah ke binsu da kallo, zulai kuwa har ranta da'di takeji dama burinta bai wuce Deejah ta dawo sahun ma'aikata da zama ba,..... "Ko bakiji abinda nace bane kin tsaya kerere akan mutane kina kallonsu...." Nadiya dake ta sauraren music a wayarta da earpiece manne kunnenta kaman daga sama take jiyo hayaniya, dashike dakin Deejah next to nata ne, cire earpiece din tayi ta zura slippers

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login