Showing 24001 words to 27000 words out of 159062 words

Chapter 9 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10419

karba a dakile, jikin hanger dinsa ta karasa ta ratay masa.
"Zama yayi bisa kujeransa daidai lokacin da landline dake saman table dinsa tayi kara, dagawa yayi ya kara a kunnensa, daga daya bangaren wacce nake zaton sakatariyansa ce tace
"Good morning sir, should I make your coffee?
"Morning Lanita, yes please.
"Ok sir, right the way.
"Har zaiyi hanging kuma sai yace" emm if my dad ask me, tell him I already left ok. And if someone wants to me tell them I'm not around.
"Ok sir Lanita ta fadi kafin Irfaan ya ajiye wayan.


"Tsaki Deejah tayi a hankali kana tace" mutum sai sharara karya yake ko kunya babu.
"Dago ido irfaan yayi yana kallonta, gani yayi ta hade rai sosai kaman zata fashe, murmushi yadanyi kafin yace a ransa, yarinya I'll make you pay for what you did, you won't just get away with it.
"Em Deeeejah kike ko wa, ya fadi yana yatsina fuska, ko tankasa batayi ba. Ki ciro files din can kiyimin rearranging nasu.
"What! Ta fadi gamida kallonsa,
"I suppose you heard me right, ya fadi yana ci gana da rubutun da yakeyi.
"Kallonsa kawai Deejah keyi, this Rude Irfaan is unbelievable. Da sauri tazo gabansa ta tsaya tana kallonsa kafin tace" toh ai ni sakatariyarka bace malam.
"Ajiye biron hanunsa yayi ya mike tsaye, yanda Deejah ta gansa dogo a gabanta take kwarjininsa ya cike wajen. Kauda kai gefe tayi tana ci gaba da kunkuni cikin ranta. "Irfaan kuwa gabanta ya matso sosai, take taji kirjinta na bugawa da sauri da sauri, tayi saurin matsawa baya nan taga shima ya matso, runtse idonta tayi ta soma fadin naji wllhi zan gyara maka, dan Allah kayi hakuri. Dariya ne ya kusan kufcewa Irfaan ko babu komai yasan weak point din Deejah, saman table dinsa ya dan zauna kadan gamida folding hanunsa a kirji yana kallon yanda ta runte idanunta, murmushi yayi da gefen bakinsa a hankali ya furta" she's more beautiful when she gets scared.
"Ok fine ki bude idanunki and do as I said, daga haka ya mike ya koma wajen zamansa, " bude ido tayi a hankali ta gansa idonsa naga computer yana shigar da documents. Gajeren tsaki tayi tace ruddy gamida yamutsa fuska tayi masa gwalo. Caraf kuwa ya dago kai suka hada ido, da sauri ta dauke kanta ta karasa wajen files din ta shiga fito dasu, dan mugunta salon yasata aiki ne kawai amma bataga abin rearranging a nan ba.


"Lanita ce ta shigo masa da coffee dinsa sai faman kwarkwasa take, Sir here is your coffe. Thanks Lanita, ya fadi a hankali, tsayuwa Lanita tayi tana wani turo kirji hadi da ban'karewa tace" Sir is there anything you want? Kansa naga computer yace no tnx..... Deejah kuwa kaman ta sami tv haka take kallonsu.
"Lanita ta kuma fadin " are you sure sir....." Sai snn irfaan ya dago kai yana mata mugun kallo wanda ma'anarsa shi ne _am gonna fire you_...
"Da sauri ta shiga basa hakuri gamida juyawa sai snn ta hangi Deejah daketa faman jera files, dariya Deejah ta mata , maras sauti dan kuwa taji dadin abinda Irfaan ya mata, irinsu ne sakatarori masu seducing boss dinsu, idan aka samu maras imani ya fada tarkonsu. Da wnn hali na Irfaan taji ya burgeta for the first time, dan da Kallon dan iska take masa wanda ya taso cikin kazantarciyan wayewa irin na turawa, ashe ba haka yake ba.
"Sipping coffee din yake yana satan kallonta yanda ta galabaita, Deejah kuwa sai hamma take dan kuwa azabebben yunwa ce ke azalzalanta.

"Ta kusan awa guda tana abu daya, tana gamawa ta zube kasa a wajen alamun ta gaji, har lokacin Irfaan bashida niyyan maidata gida. Wajajen 12:pm lokacin ta gama galabaita ya mike yace " are you good to go. Ko kallonsa batayi ba dan kuwa idonta tab yake da kwalla, murmushi yayi ya matso kusa da ita ya rada mata" next time don't mess with my stuff. Daga haka ya wuce kofa da sauri ta biyo bayansa itama.


"Laila da Aziza ne keta faman cathwalking a farfajiyan company din, idan ka gansu ba ka zata 'ya da uwa bace zaka dauka ya da kanwace. Daidai kofan fita zuwa waje suka hadu da Irfaan Deejah na biue dashi, Aziza ta bisa da mayen kallo, har laila ta wuce Aziza na nan tsaye tana faman kallon Irfan.
"Laila ta juyo da niyyan kiran Aziza nan idonta ya gane mata abinda Aziza ke kallo, suna gani akan idonsu Deejah ta bude front seat ta shige ta zauna bayan Irfaan ya zauna a kujeran driver. Duk da Aziza batasan ko wacece ta zauna a gaban motan Irfaan ba saida taji wani irin kishi ya turnuketa, sarai tasan wnn ba kanwarsa Nadiya bace, to wacece wnn, Aziza da Laila tambayan da suke wa kawunansu knn. Irfan kuwa ko kadan baimasan suna existing ba. A hankali yake driving motarsa har ya fice daga cikin company din......


πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹......
[8/19, 06:25] Umar Dalha: πŸŒ“πŸŒ“πŸŒ”πŸŒ” *Mallakin waye*


17




"Momy wllhi Irfan ne, my goodness he's always handsome, toh wacece ta shige gaban motarsa ko itama knwarsa ce. Sai snn Laila ta bar kallon luxurious car din Irfan da ya fice daga company din, ta dawo d dubanta ga diyarta Aziza kana tace,
"Hm I was just thinking of who she might be, amma dai kam wnn ba kanwarsa bace, dan kuwa 'ya'yan Engr babu ba'ki dukansu fararene tas kaman larabawa, uwarsu balarabiyar Yemen ce snn shi kansa Engr ba baki bane kinga kuwa ban tsamman wann yar gidan bane.
"Aziza tayi kicinkicin da fuska tace" wllhi momy ko wacece ita bata isa ta hanani samun abunda nake mafarkin samu ba, wllhi bata isa hanani kasancewa da Irfan ba. "Laila tayi kasaiteccen murmushi tace" kisha kuruminki 'diyata, da zaran na zama *Mallakin* Engr shikenan Irfan me sauki ne. Yanzu mu karasa ciki mu gaida sanyi idaniyana wato Engr Nazif.

"Engr yana ganinsu ya mike yana murmushi gamida nuna masu kujera yace bisimillah. Laila sai faman kwarkwasa take tana wani sunne kai irin mai kunya din nan. Aziza ta bude baki ta gaishe da Engr, Ina yini daddy ta fadi tana zama bisa kujera. Engr ya amsa da sakin fuska kafin suka soma gaisawa da Laila, tambayanta yayi jikin Alhaji Baba nan tace masa da sauki sosai saidai har yanzu baya magana snn baya feeling ko ina ajikinsa face kansa. Engr ya jinjina lamarin yace Allah ubangiji ya kara masa lafiya, sauki sai a hankali.
"Dama zamu wuce ne shine Aziza tace we should drop by tanaso ta gaida daddy dinta, kasan tun bayan rasuwan mahaifinta bata da burinnda ya wuce samun sabon daddy.. " Dan murmushin yake Engr yayi yace Allah sarki na gode sosai, ya kalli Aziza yace na gode daughter. Wani dadi ne ya ziyarci zuciyan Laila da Aziza musamman da suka ji Engr ya kira Aziza da daughter.
"Koda suka mike da tafiya Engr ma mikewa yayi yace" I'll walk you out, Laila tayi wani far da ido tace a haba dai yaya Nazif wllhi da ka barshi ka zauna kayi aikinka. Girgiza kai yayi yace ba damuwa muje, a tare suka fito har waje Engr yace pls subi can gidansa su gaida Amma, cike da zumudi Laila ta amsa.

"Cak Nadiya ta tsaya ta bar driving din da take sakamakon hango Engr da tayi yana bude wa Laila 'kofan mota, " Jarrr uban chaan, wasu 'yanmata take gani da daddynta, dama daddy neman matansa yake a Office. Zuciyanta ne taji na tafarfasa rivers din da zatayi taji ta bugi wata mota,
"Wani kyakyawan saurayi ne ya fito daga cikin motan yana kokarin duba yanda Nadiya ta buga masa, ko fitowa batayi ba balle tasan tayi laifi ma wani, kallon 'keyar daddy kawai take har ya shige cikin company yayinda 'yanmatan nan suka kwashi motarsu suka bar haraban wajen.
"Saurayin ya karaso jikin motan Nadiya yasa hannu ya dan buga glass din, sai snn tayi rolling glass din motan tana kallonsa fuska a tamke, shima tamke fuskan yayi kafin yace "are you blind or what, kin buga wa mutum mota and you can't even say sorry....." Hannu ta daga masa gamida katsesa tace" dalla malam ka daina min shouting akai ka gane, in the first place meyasa kana staff zaka yi parking a nan, ko baka san yanda staff dinku ke ajiye rides dinsu bane hum. You should be the to apologies, am pretty sure motata ta sami virus da wnn kwarabebbiyar so called car din naka...." Sadiq tsayuwa kawai yayi yana kallon Nadiya yama rasa me zaice mata, kaman ance wa Engr ya dawo waje ai kuwa hango Nadiya yayi da sabon ma'aikacin su tana faman balbala masa masifa.
"Da sauri Engr ya karasa wajen" Sadiq na ganinsa ya karasa ya rusuna yana gaishesa, Engr ya amsa kafin yace" malam Sadiq yaya dai." Sadiq yace a lafia Sir, dama.... bai karasa ba Engr ya kai dubansa ga Bamber din motarsa yaga har glass ya fashe, subhanallah garin yaya haka ta faru, ya dubi Nadiya data cika tayi fam ywce" Sweedy me kike yi a nan, fuska a daure tace dama zuwa nayi na duba ko ya Irfan nan ya zo da deejah we were all worried about her at home. Engr ya jinjina kai kafin yace Irfaan ya maidata gida, garin yaya kika bugawa Sadiq mota. Yatsina fuska ta kuma yi kafin tace" it was unintentional daddy, besides ai na basa hakuri. Daga haka ta kunna motarta alamaun zata tafi, Engr ya dubeta yace mu karasa ciki toh yau sai ki tayani aiki. Girgiza kai tayi tace No daddy ni gida zan tafi, I just saw something that ruins my day completely. Daga haka taja motarta ta bar wajen. Engr da Sadiq suka bi bayanta da kallo, Sadiq mamaki ne kawai ya ishesa yanda yaga Nadiya tayi wa Engr kwatakwata wnn ba dabi'a da al'adan hausawa bane, hashi mahaifinta very nice somebody, wnn shine albasa batayi halin ruwa ba.
"Engr ya dubi Sadiq yace kayi hakuri pls malam Sadiq, you know how kids are....." Da sauri Sadiq ya katse Engr yana fa'din dan Allah ka daina bani hakuri, it makes me feels embarrassed. Besides ba sosai motar ta bugu ba, murmushi Engr yayi yana jinjina hankali da dattako na karamin matashi kaman Sadiq. A tare suka karasa cikin company din, kai tsaye office Engr suka wuce wato office din Mr President.
" Engr ya karbi Cv din Sadiq yana gani, yaron akwai kwazo, Engr ya dago kai yana kallonsa da murmushi saman fuskansa yace" your qualifications are incredible, zaka ri'ke position na assistant accountant, Sadiq kam farin cikinsa ya gaza boyiwa baisan sanda ya mike ya hau nuna godiyansa ba, bai taba tsammanin zai samu karbuwa har haka ba,
" Na gode Sir, na gode Allah shi saka, Allah ya raya family... ire iren addu'o'in da Sadiq ketayi knn, Engr ya dafa kafadun Sadiq yana murmushi yace" congratulations again, kafin ya kira sakatariyansa tayi directing Sadiq zuwa Office dinsa.


"Suna tafe a mota babu wanda yake cewa kowa cikanka, sai sautin music dake tashi a hankali, wayan da aka masa ne yasa daga phone din,
"Guy don't tell me har ka sauka a Nigeria,
"Daga daya bangaren Ahidjo yace guy na sauka wllhi, gashi ban samu na kiraka ba, ni kadai nazo Nija, su mom sai zuwa next week, sun tsaya dad ya gama clearing issues dinsa da turawan nan, kasan miye...
"Irfan yace no sai ka fadi,"
"Ahidjo yace" wllhi gani nan ina shirin fita daga Abuja koma nace maka na fita, I made a promise to mom cewa ina sauka a Nigeria Gombe zanje naga grandma, kudin jikina dollars ne, Naira din kadan na canza kuma sun kare, dole na shiga wata motan zuwa Gombe din, guy wllhi is awkward duk ban saba ba, gashi motan ma ta tsaya a hanya, could you imagine, am pretty sure yau sai nayi jinya, and most annoying part of it munfi 1hr muna jiran mechanic har yazu bai iso ba, pls ka karaso kazo ka daukeni, I couldn't help it anymore, na yafe zuwa Gombe din,
"Dariya mai sauti Irfaan yayi wanda har saida yasa Deejah kallonsa, a ranta tace dama yana dariya haka. Kafin yace welcome to Nigeria bro.... Ahidjo ya katsesa da fadin that's not funny guy, do something pls.
"Irfan ya rage dariyan da yake kafin yace alright fine, bama driver din ya fada mun location naku.
"Hakan kuwa akayi, Driver ya fadi wa irfaan yanda suke.
"Tunani Irfan ya danyi, gaskiya wajen is pretty far dan sun shiga kwaiyukan Abuja. Kallon Deejah dake zaune gefensa yayi kana yace" Ok gani nan zuwa right the way.


"Kallon sa Deejah tayi galala kafin tace malam ina muka nufa, baice mata komai ba ya canza hanya....


"Amma na zaune a parlor tareda su Laila da Aziza Nadiya ta shigo rai 'bace,..... Ai daga kofa taha tayi burki sakamakon ganin su Laila datayi zaune a parlorn gidansu, wato ma har sai sun biyo daddynta gida suna tallen kansu, aiko basu isa ba, a zuciye tayi cikin parlorn rai 'bace......




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.........
[8/19, 06:25] Umar Dalha: πŸŒ“πŸŒ“πŸŒ”πŸŒ” *Mallakin waye*


18




"Kaman wacce bata san da hallittu a parlorn ba haka ta nufi stirs zata haura sama dan ko son ganin fuskokin Laila da Aziza batayi, Amma tabita da Kallo yayinda su Laila ma ita suke kallo.
"Nadiya!" Muryan Amma ya dakatar da ita, juyowa tayi da kyar ba tareda ta furta koda kalma guda ba,
"Baki ganin mutane bakisan ki gaishesu ba and kin shigo without even saying salam.
"Nadiya ta dan yatsina fuska kafin tace" Oh come on Amma, nayi sallama fah.... "Amma ta kalleta cike da takaici kafin tace" toh ina kika baro Deejahn, " Daddy yace sun taho gida tare da yaIrfaan, so I guess probably by now sun iso, though banga motarsa a waje ba. Daidai lokacin data watsa wa Laila da Aziza wani muguwar harara, tsaki tayi kafin ta furta "what a fuck"
"Amma kam cike da kunyan abinda Nadiya tayi ta dubi su Laila tace kuyi hakuri pls kunsan ba anan ta tashi ba ta saba da _al'adun wasu_ sam bata saba da al'adunmu ba.
"Dariyan ya'ke Laila tayi, Gamida mikewa tana fadin "ai ma tafiya zamuyi Amma, Amma tace a haba da wuri haka, eh wllhi Amma dama mukace bari muzo mu gaisheki, cewan Laila... Aziza kuwa bata da buri da ya wuce ta zama kawa da Nadiya,
"Har 'kofa Amma ta rakasu kafin ta dawo ta nufi sama dan yin fa'dawa Nadiya....


"Tafiya suke kan yi har suka fice daga cikin gari, jikinta duk ya mace sabida tsaban yunwa da takeji, wani wawan holdup suka ha'du dashi tun daga cijin gari, shi kansa Irfaan saida yaji haushin kansa da ya sani da bai fara ba, but ba yanda ya iya, Ahidjo bashida kowa sai shi.
"Da kyar suka samu suka rabu da holdup din nan, ashe wata tankace ta lalace bisa titi. Ai kuwa kaman jira yake, nan ya dinga falfala gudu, Deejah kuwa gab tace da fashewa sabida tsaban haushi da takaici....


"Su Laila suna dawowa gida da zancen suka soma wa Hajiya Karima. "Hajiya kinsan akwai aiki jazur a gabanmu, wnn 'yar tasa ko ka'dan bata da ta ido, daga ganinta zatayi rashin mutunci, cewar Laila." Hajiya Karima ta sauke ajiyam zuciya kana tace" ni nasan ta yanda zan bulla masu, tinda dai kin samu kar'buwa wajen shi Nazif din da uwarsa 'ya'yansa ai me sau'ki ne. Laila tayi murmushin jin da'di tace shiyasa nake sonki Hajiyata. Juyawa tayi ta kalli Alhj Ma'aruf dake kwance bisa gado yana so yayi magana babu hali, duk wnn tattaunawan da suke a gabansa suke, yanayin maganar nasa kaman na bebaye haka yakeyi baka gane komai baka fahimtar komai.
"Laila ta kwashe da dariya tana kwaikwayan yanda Alhj Ma'aruf ke magana, Hajiya ta murmusa kafin tace" kina kwaikwayan gwalamniyan wnn azabebben tsohon ne, me shegen taurin ran tsiya, da mutuwa kayi da ya fiye maka wnn rayuwan azaban, magani dai bazan fasa baka ba, amma na sani kalamai da zaka rin'ka ji masu zafi su ka'dai sun isa su 'karasaka har lahira. "Laila ta kuma she'kewa da dariya kana tace Kai Hajjaju na baki da dama. Haka sukamci gaba da hiransu, Alhj Ma'aruf kuwa ji yake kaman ya yun'kura ya tashi ya hana Engr auren Laila, amma bashida iko, yayi kudirin cikin ransa ba zai daina addu'a wa Engr ba.




"Tin daga parlor yake ranga'da mata kira cike da farin ciki, Mami! Mami!! Mami na!!!, Ruqayya ce ta fito daga 'dakinta wanda yake a cikin parlorn kana tace" Yaya sannu da dawowa, murmushi ya sakar wa Ruqayya kafin yace yauwa sanu lil sis, Mami fah,
"Inaga tana sallah dan 'dazu na barta a parlor, gyada kansa yayi kafin ya ajiye takardun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login