Showing 54001 words to 57000 words out of 159062 words

Chapter 19 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10374

karan tsada iri daban daban harma da magungunan mura na yara, tsaki ya kumayi sanda ya juyo yanama Ahidjo mugun kallo, kauda kansa gefe Ahidjo yayi dan yasan yanzu zasu haura da Irfan balle dama already ransa a b'ace yake.
"Meye kake wani juyar da fuska, Ahidjo you'll never change will you? By the time alcohol ya saka maka wani ciwon ko ya maidaka mental nan ne zaka gane shan barasa ba abin burgewa bane, for goodness sake baka tsaya kan wines ba harda drugs kake sha abinda ka sani haukatar da mutum yake, ya kuma yin gajeren tsaki kafin ya suri car keys dinsa zai fice.
"Har ya kai door yaji muryan Ahidjo yana fadin" baka gaya mun ba wa ya bata maka rai har kake sunbatu kai kadai,
"Ba tareda ya juyo ba yace" is non of your business malam. Ahidjo ya murmusa kafin yace " koda baka fada mun ba na riga na sani kan wnn yarinyar kake wahalar da kanka, for goodness kaje ka nemi level dinka Irfan, kafi k'arfin wnn yarinya by far, of all people ka rasa wace zaka so sai wnn mere girl of a thing din........ " A zuciye Irfan ya juyo yayiyo kan Ahidjo na huci yake fad'in" how dear you called Deejah a thing, idan ban fada maka ba barin fada maka yanzu" I love her with all of my heart ka gane, I don't care what's her status in life, I loves her for who she's..... "Daga haka ya fice zuciyansa na ci gaba da zogi yanda yaji son Deejah na neman zautar dashi, ko da wasa aka ce masa zai so wata haka zai musa sai gashi yanzu ya rasa mind dinsa kan wata yarinya. A tsaitsaye ya shiga ya gaida Ammi mahaifiyar Ahidjo kafin ya fito yanda yayi parking motarsa, nan ya tarar Ahidjo na tsaye jikin motar na jiransa, ko kallo be ishi Irfan ba ya bude motar sa ya fizgeta da k'arfin gaske.
"Ahidjo ya bisa da kallo yana mamakin irin son da Irfan ke ma Deejah, tunanin yanda zai raba Irfan da Deejah ya soma dan kuwa sha'awarta dad'a ruruwa yake a zuciyarsa mussaman yanzu da yaga yanda Irfan ya haukace kanta shed'an sai ya da'da k'awata masa sururar Deejah, wani murmushi yayi gamida shafa sajensa kafin ya shige sashen Amminsa.....




"Sosai hankalin Deejah ya tashi jin gaba d'aya mutanen Orphanage babu wanda yasan yanda Yusra ke rayuwa a yanzu, k'walla suka ciko idanunta a hankali ta mik'e jiki babu kwari ta dubi su iya Delu tai masu sallama gamida barin sak'on gaisuwanta zuwaga Aunty Larai...


"Gudu yaken falfalwa bisa titin Aso Drive, can ya hangi wata kamar ita tana neman abin hawa, so yake ya wuceta amma inaa zuciyarsa ta hanasa aikata hakan, dole yaja wata birki a gabanta wanda saida ya razanata.....!
"A firgice ta d'ago idanunta da suke rikirkita Irfan tana duban sa, ta razana da ganin yanayin da taga Irfan, huci yake idanunsa naga kan titi, bae cemata komai ba sai horn da ya soma mata, fuska a turmuk'e tasa kai zata wuce duk da da'di da farin cikin ganinsa da tayi,
"Irfan yabita da kallon mamaki ganin yanda ta wucesa abinta, a zuciye ya bude marfin mota ya nufota, ba tareda yace mata komai ba ya shiga fizgo hanunta ya nufi mota da ita.
"Malam lafiya kar ka sake tab'a min jiki ni ba er iska bace, ta fadi tana k'ok'arin fizge hanunta, ko kad'an Irfan beji mamakin kalamanta ba dan yasan Deejah akwai kamun kai, saida ya jefa ta cikin motar kafin ya soma tuki tamkar me shirin tashi sama......
"Sosai abin yabawa Deejah mamaki, idanunta ya sauk'a kan fararen hannayen Irfan wanda jijiyon sukayi green shar suka tashi...... burkin da zaiyi kuwa Deejah ta hantsalo cikin jikinsa.....


_Kuyi hak'uri da wnn babu yawa...... luv you all 😘_


πŸ‘ΈπŸ»QueenSamy........πŸ˜πŸ’„πŸ‘„
πŸŒ˜πŸŒ˜πŸŒ”πŸŒ” *Mallakin Waye*


40

*Na Sameena Aliyu*


"Wani irin wawan birki yaja qiiiiiiiiiiiiiittttt a tsakiyar titi dan kuwa ba zata yaji fad'owan Deejah cikin jikinsa, sa'ansu guda babu mota dab dasu, Kallon Deejah yake babu ko kyafta ido, cikin azama ta mik'e tana k'ok'arin gyara zamanta.
"Bece mata komai ba yaci gaba da zabga race bisa titi bai staya ko ina ba sai wani wajen shak'atawa da yake a cike flowers...... " Kallon mamaki Deejah tabisa dashi, gani tayi fuskan nan nasa tamau sai d'an pink lips dinsa dake kan shinning uwa ya shafa jan baki saurin kawarda idonta tayi dan bata iya juran kallon k'urilla wa Irfan, da kyarta iya furta "ina ka kawoni.... "bece komai ba sai parking motarsa da yayi, cike da miskilanci ya furta" ki sauk'o muyi magana, daga haka ya fice ya nufi kan grass carpet ya zauna gamida crossing legs dinsa ya daura hannayensa bisa gwiwoyinsa.
"Tana zaune gaban mota take hangosa, kai shikam komai nasa me kyau harta yanda ya zauna ya burgeta, tsan tsan son Irfan ne ke azalzalanta, runtse idanunta tayi k'irjinta na dumm dum haka ta fito ta k'araso yanda Irfan yake, can gefe dashi ta zauna sunfi minti biyar babu wanda yayi magana cikinsu..... " can ta tsinkayo killing voice dinsa yana fad'in" Khadija me yasa kika min k'arya, " d'ago idanunta tayi da sauri kafin tace k'arya kuma? Ni kuma?...,..
"Irfan ya karkato yana fuskanta ta kafin yace" Of course Deejah you lied to me, kince min baki sona bayan kuma ni na gani a kwayar idonki kina sona,.
"A hankali Deejah ta sauk'e ajiyan zuciyadan duk a tunaninta Irfan yasan tayi yawon Club ne, girgiza kai ta soma tana fad'in " you've got this wrong bana son....,,, " Kafin ta k'arasa magana yayi saurin dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu" Don't you dear lie to me again, why can't you just admit it, you love me Deejah I can read your mind, na sani kina sona, just tell me why do you keep insisting sayin baki sona, you must have your reason for that.
"Kasa cewa komai tayi sai kallon k'asa da takeyi..... "Irfan yayi gyaran murya kafin yaci gaba da fad'in" Deee ki yarda mun jima muna son juna tun sanda muka soma had'uwa, ki tuna those moments da mukayi a tare, ba komai muka nuna wa juna ba sai tsantsan soyayya, nikaina banyi realizing hakan ba sai yanzu da na tabbatar yess sonki nake, Dee a da can, da za'ace min ni Irfan zanso wata mace zan k'aryata, gashi yanzu ya faru da ni and I'm suffering for love. Dee ki fada min meyasa kika k'i yarda kina sona...... " Hawaye ya hango na digowa daga idanunta, da sauri ya matso kusa da ita ji yake tamkar ya rungumeta, cikin sanyin murya ya soma fad'in" Na tak'uraki ko, am sorry pls ki dena asaran wnn hawayen naki masu tsada, farin cikinki yafiye mun komai, idan de akan wnn maganar ne bazan sake ba, just stop shading those tear okay..... "Yanda yayi maganar yasata kuma jin tausayin kanta, A hankali Irfan ya furta tashi muje na maidaki gida. Har zai mike ya jiyo muryanta me cike da kuka a ciki tana fa'din" Ina sonka ina sonka master, saidai nida kai bamu dace ba ko kad'an....,," Tamakar a mafarki haka yaji batun Deejah.
"Murmushin jin dad'i yayi kafin yace" Ni da ke munfi kowa dacewa....." Girgiza kai ta soma kafin taci gaba da fad'in " Kaid'an gata ne, ni kuwa er wahala ce, kai kyakkyawa ne, ni kuwa ban kaika ba, kai me kud'ine ni kuwa talaka ce, kai m...... " Enough of this Deee, Irfan ya katseta da fad'in haka, kar na sake jin wad'an nan kalamai daga bakinki, I don't care what your status, all I know is that I love you for who you're, na sani you're from Orphanage snn na sani kin rasa iyayenki ne sanadiyan zaizayan k'asa, Deee am ever ready to be your father your mother and husband a the same time. Bana so wnn maganar ya kuma damunki,and koda wasa kar ki sake furta haka a gabana, I love you for who you are.
"Murmushi ta d'ago tanayi shi kuwa Irfan harda kashe mata ido d'aya, me keken ice cream yazo wucewa nan ya saya masu suna sha suna firan soyayya, Suna zaune suna sipping ice cream irfan na mata fira jefi jefi dan shima ba wai ya saba da surutu bane... can Deejah tace Ya Irfan, dagowa yayi yana duban cike da mamakin sunan da ta kirasa dashi dan bata tab'a ba, nan taci gaba da fadin " Alfarma daya nake so ka min, Irfan ya murmusa kafin yace" Ke kin wuce neman alfarma a wajen abinda kike so ayi kawai zaki fadi" Deejah ta dan sunne kai kafin tace " pls kar kowa yasan muna soyayya yanzu ko su Ammah banaso su sani
"Cikeda mamaki yake kallon kafin yace meyasa, dan kinji nace za'a samo new nanny wa Nilam ne. Dan girgiza kai Deejah tayi kafin tace" pls kayi min wnn alfarman.. _Soyayya kenan( ni kuwa Samy nace ikon Allah ba abin mamaki bane yau ga Deejah da Irfan ana soyayya ☺) ...._
"Sun dan jima a park din kafin suka dawo gida dap ana kiraye kirayen magrib, yana gama parking ya d'an jiyo yana dubanta gaba d'aya yanzu kunyansa takeji, murmushinsa me class yayi kafin ya d'an rank'wafi saitin face dinta yace " Deee am hungry asan yanda za'ayi dani" Far tayi da idanunta abunda ke kashe Irfan kafin tayi saurin sunne kanta ganin mayen kallon da Irfan ke binta dashi tayi saurin bude mota ta fice, duk wnn abun a idon Aziza ya faru, ji take kaman shak'e Deejah ta huta tayi kwafa sanda ta tuna kalaman mahaifiyarta Laila cewa komai ta gani a gidan ta kauda kai har hak'ansu ta cimma ruwa.


"Cikeda farin ciki ya fito daga motan ko ba'a fad'a maka ba yau daban take ga Irfan dan kuwa gaba d'aya ya kasa b'oye farin cikinsa harta Engr da Ammah kai harma da k'annensa kowa ya gane yau Irfan na cikin farin ciki.

"Tun daga wann rana rauywa taci gaba da tafiya wajen masoyan nan gwanin sha'awa saidai babu wanda yasan suna wann soyayya.
"A 'yan kwanakin Engr ya sayawa Nadiya Deejah da Azeeza Form na *NILE UNIVERSITY* yanda ko waccensu zata sami gurbin karatu, wai zo kaga murna wajen Deejah, ko a mafarki bata tab'a hangota a wani university yau sai gashi zata shiga makarantar da sai d'an wane da wane itakam batada bakin godiya wa familyn Engr.Nazif Mumtaz saidai ta masu addu'an Aljannah. A b'angaren Aziza ma tayi murna saidai wani irin tsanar Deejah k'aruwa mata yake bayan ko wani second, Nadiya kuwa dama dama London taso akaita Ammah ne ta hana fir dan haka bata waniyi farin cikin samun Admission din ba.
" misalin k'arfe 8:30pm Zaune suke bisa dinning table me kujeru goma sha biyu rus, Laila da kanta tayi girkin gidan gaba d'aya, faram faram datake ma yaran yasa sun soma rage tsangwama da suka mata, harta Azee ma sun soma sakin jiki da ita, Deejah Azee da Nadiya suketa faman taya Laila jeren Warmers bisa dinning, abin ya birge Engr da Ammah, bayan sun gama ne Deejah zata juya Kitchen Laila tayi caraf tace" Deejah ina zuwa kuma, ina zaki ki baro en ukunki Nadee da Azee maza zauna muci a nan gaba daya, gaba daya illahirin mutanen kan table din sukayi na'am da batun Laila.
"Irfan ne kawai ya rage baya wajen Ammah ta dubi Nadiya dake faman danna waya tace" Miss Instagram maza go and call your brother lokacin dinner yayi... "Laila ta kashe wa Aziza ido d'aya alamun taje ta kirasa. Aikuwa Caraf Azee ta mik'e tana fad'in "Let me call him Ammah.
"Sosai jikin Deejah yayi sanyi ta bita da kallo har Azeeza ta fice kiran Irfan.




_πŸ‘ΈπŸ»QueenSamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„_
[8/22, 14:39] Umar Dalha: πŸŒ˜πŸŒ˜πŸŒ”πŸŒ” *Mallakin Waye*


41
*Na Sameena Aliyu*


"Kai tsaye murd'a k'ofan tayi babu ko knocking ta kutsa kai cikin parlorn, sanyin air conditioner had'i da dadd'an k'amshi shi ya daki hancin Azeeza, parlorn tabi da kallo a fili ta furta woow, dan kuwa sosai tsarin komai ya tafi da ita, can kan center table ta hango MCBOOK dinsa da alama aiki yake bisa computer din, kaman wacce akace ta ta'ba aikuwa ta k'arasa ta shiga k'ok'arin dannawa take screen din ya kawo haske nan hoton Deejah ya bayyana jikin screen din" k'irjin Azee kuwa tamkar zai fad'o k'asa haka take jinsa, tayi saurin runtse ido dan kuwa da ace mafarki take ba zahiri ba da sai yafi mata sauk'i...


"Cak ya tsaya daga staircase yana kallon ikon Allah, wann wace irin yarinya ce haka, kai of all people she's disgusting, fuskan nan nasa babu alamun wasa tamkar be ta'aba dariya ba sukayi ido hud'u da Azee wacce tayi saurin saita kanta tana me k'ak'aro murmushi bisa lips dinta.
"Emmm.... Emmm ina yini ya Irfan ......" Shut that your trap, and hold your ina wuni! Ya daka mata tsawan daya firgitata kafin yaci gaba da fad'in" Who do hell you think you are, who gave you the permission to come in here in the first place.
"Baki na rawa Azee ta soma fad'in dama Ammah ce tace nazo na kiraka kaci dinner.
"Gajeren tsaki Irfan yayi kafin yace" let me warn you for last time, kar ki sake gigin shigo min parlor without my permission, just get out of here useless kawai.
"Jiki a sab'ule Azee ta juya kai tsaye sashen Anty ta wuce ta fada dakinta ta shiga rusa kuka.
"A haka Aunty wato Laila ta shigo ta sameta, Azee bata b'oye wa Aunty komai ba ta kwashe ta gaya mata, Aunty ta bata baki snn tace taci gaba da ha'kuri kar ta ruguza masu plan,
"Ammah ko data ga shiru lokacin Engr har ya wuce sashensa , sai cewa tayi Nadiya ko Deejah d'ayarsu takaiwa Irfan abinci dan tasan miskilancinsa ba lallai ya sauko ba, daidai shigowan Laila kenan tayi caraf tace aa barin kai masa,
"Dq kanki aida kin bari yaran sun kai masa cewan Ammah, mayaudarin murmushinta tayi kana tace" a 'a haba dai Ammah gwara na kai masa dan na saba da d'an nawa sosai, Ammah ta murmusa cikeda jin dad'i, kyawun halin Laila na da'da burgeta tana jin tana k'ara sonta, lallai Nazif yayi dacen mata...
Laila da kanta ta shirya abincin Irfan ta d'auka ta nufi sashensa, tafi minti uku tana knocking kafin ya taso da tafiyarsa na k'asaita ya bude yana ganin Laila ce ya d'an saki fuska kana yace" Aunty keda kanki.... Mayaudarin murmushi Laila tayi kafin tace toh yana iya tinda d'an gidana yak'i fitowa muci abinci tare kaga ai dole na biyoka dashi. Irfan yayi saurin karb'an tray d'in yana mai jinjina kirki da faramfaram irin na Laila. Sosai suka jima suna labari har yaci abincin sosai.


"Kwanci tashi babu wuya wajen mai sama yau su Deejah an tafi makaranta dan fara halartan aji, course d'aya suka samu dukansu uku, idan ka gansu dole su birgeka yanda suke gudanar da al'amuransu duka Nadiya halinta na nan haka dai suke shanyewa, dan kuwa idan en rashin mutuncinta na kusa haka nan take watsa masu musamman Azee har yanzu basu faye jituwa na Nadiya ba.

"Parking yayi a k'ofan Cafeteria yanda ya shiga saukewa Mamie kayayyakin aikinta, Mamie ta dube shi cike da kulawa tace kaje kawai Sadiq ai na gode ka bar Ruqayya na kan jira kasan layin nan namu ba'a faye samun abin hawa ba. Sadiq ya murmusa kafin yace " toh Mamie na daga can zan wuce Office snn inaga bazan dawo gida da wuri ba zamuje wani waje da Irfan.
"Babu komai Sadiq Allah dae shiyi maka Albarka, Ameen ya amsa kafin ya juya kan motar sa.


"Ita kad'ai ke tafiya bisa titi dan ta baro su Deejah da Azee a Department, as usual kunnenta mak'ale da earpiece sweet na tsinke ne a bakinta tana tsotsa, riga da skirt ne atampa a jikinta sai er k'aramar vail data rufe kanta dashi zuwa kafadarta dama daura dankwali ba d'abi'arta bane......" Karan horn din da ake mata ya cika mata kunne, a hasale ta juyo da niyyan masife koma waye ke mata horn din nan, Ido hud'u sukayi dashi yana sanye cikin English wears da suka karb'i k'irar jikinsa da fatarsa. Kasa cewa komai tayi sai kallon data bisa dashi, shi kuwa Sadiq har gabanta ya k'araso da motar kafin yace" Har a makaranta ma sai kin gwada hali, kiyi hankali kar ki biyewa mazan jami'a balle su kaiki su baro ki..... daga haka ya fincike motarsa ya wuce.
"Baki sake Nadiya ke kallonsa har ya b'ace ma ganinta, maganarsa ya dawo mata" _kiyi hanakali da mazan jami'a kar su kaki su baro ki_ toh meye dalilinsa na fada mata haka gani tayi dae ba tareda kowa ya ganta ba, ajiyan zuciya ta sauk'e dan a halin yanzu bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login