Showing 33001 words to 36000 words out of 159062 words

Chapter 12 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10416

ya kasance, saidai bai fada masa yanda sukayi da Engr ba, Sosai Ahidjo ya tausaya masa..." Kai friend am so sorrry, danasan haka zata kansance wllhi da ban kiraka ba.
"Kallonsa Irfan yayi a kaikaice kafin yayi murmushi yace" just look at your self, jibi yanda kake wani apologizing as if you were at fault. Allah ya kaddara hakan zai faru koda kai ko babu kai.
"Ahidjo yayi murmushi yace, Dude da'dina da kai akwai tawakkali da matso da Allah kusa, Irfan yayi murmushi ba tareda yace komai ba.
"Sun jima suna fira kafin suka mike suka nufi gidansu Ahidjo dake Asokoro....




"Misalin 'karfe 8:pm Engr yayi kiran Deejah dan tin dawowansu magana bata shiga tsakaninsu ba, sosai ta tsinci kanta da mugun fa'duwan gaba, zaune ta samesa a garden hasken fitulu ya gauraye ko ina yana sanye da fara kal din jallabiya haka nan idonsa manne da medicated glass hannusa dauke da news paper yana dubawa.
" 'Kirjinta ya tsananta fa'duwa sanda taga ya dago kai sukayi ido hudu, yau kam fuskansa a 'dure tamkar bashi ba, muryansa me cike da 'kwarjini taji ya mabato sunanta yace bismillah,
"A hankali ta soma taka 'kafarta tana sanye cikin doguwar riga ta atampa da hijabi daidai gwiwarta, tsugunawa tayi ta soma gaishesa, a dake Engr ya amsa kafin yace tashi ki zauna, 'kirjinta na ci gaba da bugawa da sauri da sauri haka ta mi'ke da kyar ta zauna a 'daya daga cikin kujerun.
"Shi kansa Engr ya lura da yanayin Deejah bata sake yanda ta saba sakewa dashi a da ba, zuciyansa ta shiga tambayansa wai me kake ji gameda Deejah ne, wata 'bangare na zuciyansa tana son kallon Deejah a matsayin uwa gasu Nilam, amma 'bagare mafi rinjaye 'kasan zuciyansa tafi kallon Deejah a maysayin 'yar uwa gasu Nilam. Sun jima kaman babu wanda zai yi magana cikinsu, sai jiyi sautin rufe jarida taji alamun yana rufe news papers din, ajiyewa yayi bisa table din dake gabansa kafin yayi gyaran murya. Dai dai lokacin da motar Irfan ta sako hancinta cikin farfajiyan gidan........




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.....
[8/19, 06:26] Umar Dalha: πŸŒ˜πŸŒ˜πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin *Waye*


25




"Gaba daya Deejah da Engr kallonsu ya koma ga Irfan dake faman parking mota cikin parking lot, tun daga nesa ya tsare Deejah da idanu, besan meyasa ba ganinta da yayi yasa zuciyansa yin sanyi saidai haka kawai zuciyansa bataji da'din ganinta da Engr zaune a garden ba. Yana isowa kusa dasu dauke kai yayi snn yayi wucewarsa sashensa.
"Engr yamaida dubansa ga Deejah wacce ta bi irfan da kallo har ya 'bace ma ganinta, Sau'ke ajiyan zuciya Engr yayi kafin ya furta "Deejah".
"Da sauri ta bar kallon sashen Irfan gamida saita hankalinta waje guda tace" Na'am Daddy,
"A zuciyansa ya maimaita "Daddy", bata ta'ba kiransa da daddy ba sai yau, kullum Sir take ce masa gashi yau ta kirasa da daddy, kawar da tunanin yayi kafin yace" tashi kije we will talk some other time.
"Cikin sanyin jiki ta mi'ke cike da rusunawa tayi masa sallama ta shige ciki......
"Nadiya dake tsaye window din 'dakinta kan idonta komai ya faru, girgiza kanta tayi kafin ta furta " now I get it, so that was the reason why daddy was so panic sanda Deejah da ya Irfan suka 'bace.... sauke labule tayi kafin ta furta " no way dole nasan meke shirin faruwa a gidan nan, daga haka ta sauko down stirs ta nufo waje....


"Engr kuwa mikewa yayi ya nufi sashen Irfan nan Nadiya tabi bayansa a hankali ta la'be jikin windown parlorn Irfan.
" Zaune ya samesa yana shan fresh milk ga pic din momyn sa ri'ke a hannunsa. Kallo 'daya Irfan yayi wa Engr ya kauda kansa gefe.
"Engr ya fuzar da iska kafin ya zaune kusa da Irfan, ya 'bata lokaci sosai kaman bazaice komai ba sai kuma yayi gyaran murya ya dafa kafa'dun Irfan yace" Son regarding what happened earlier am sorry, nasani duk da ni mahaifinka ne, I shouldn't have slapped you, I should have let explain first......." Dakatar da Engr Irfan yayi ta hanyar girgiza kai ya soma fa'din" Daddy you don't need to apologies to me, you're my father, besides marina da kayi it doesn't hurt me, what hurts me the most shine zargin da kayi min daddy, and sai yanzu na gane saboda me kayimin wnn mummunar zargin, it's because of Deejah.
"Engr ya dan fuzar da iska dan baya so zancen yayi nisa tsakaninsa da 'dansa, a hankali ya furta" ya isa haka Irfan na mareka ne sabida banaso na rasaka sabida next time kasani akwai hanya me kyau da maras kyau na aiwatar da komai, you need to get some rest......
" Idanuwan Irfan sun ka'da sunyi jazur yake kallon Engr kafin yace" Yes Daddy sabida Deejah ne, because you love her, because you don't wanna loose her......." Da mugun mamaki saman fuskan Engr yake bin Irfan da kallo, shi yake kalla yake cewa son Deejah yake, a hasale ya katse Irfan " Enough Irfan!
"Irfan ya mike yana ci gaba da fadin" gaskiya na fadi daddy son deejah kake yi idan ba haka ba meyasa bazaka kebe ka tattauna da ma'aikatan gidan nan ba sai ita, just admit it....,,, " Wata mari meji da lafiya Engr ya sauke wa Irfan saida ya dur'kusa, dafe 'kuncinsa yayi ya dago yana duban daddynsa, bai ta'ba ganin 'bacin ran da ya gani kwance samar fuskansa ba,
"Are you stupid or what, ni kake tuhuma ina mahaifinka, you better be careful. Idan shaye shaye ka fara gwara tun wuri ka daina kafin kaga asalin 'bacin raina, daga haka Engr yasakai ya fice daga sashen Irfan. Har ya fice Irfan bai sake 'kuncinsa ba snn bai daina kallonsa ba.
"Zuciyansa na masa wani irin zafi, for the first time da ya ta'ba samun sa'bani da mahaifinsa tun tasowar sa, this is all because of mace, macen ma Deejah nanny, why why this, da gaske son Deejah yake, meyasa ko ka'dan feelings din da yake ji for her baya raguwa saidaima 'karuwa da yake each and every second, toh idan kuwa daddynsa son Deejah yake he needs to get far away from her. A hankali yayi tsaki ya furta" she's my problem here....
"Nadiya dake la'be jikin window sosai lamarin ya bata al'ajabi, kama kumkuminta ta 'danyi tana me ri'ke ha'barta kafin tace" Toh wai shin Zuciyan Deejah *Mallakin Waye*, I needs to find out, da wnn tunani ta wuce cikin gida....
"A parlor ta samu Ammah na kallon labarun tara, Ammah ta bita da ido kafin tace ina kika fito, Nadiya ta dan langa'be kai ta 'karaso ta kwanta jikin Ammah, kafin tace na fito wajene na dan sha fresh air.
"Ammah ta jinjina kai kana tace" kin ganemun yayanku ya dawo? Tashi Nadiya tayi ta zauna kafin tace" ya dawo Ammah, but he seems depressed, I wonder meke damunsa haka, ko dan marin da daddy ya masa ne.
"Ammah tayi shiru kafin ta ynkura ta mike tana fadin" I need to check on him. Nadiya tace gaskiya kam he needs you granny, barin lekasu Deejah dasu Nilam.
"Dakin Deejah Nadiya ta wuce yanda take jiyo hargowansu Nilam dasu Amir, Deejah na tsakiyan su tana masu story nan Nadiya ma ta zauna aka ci gaba da ita, kaman ba ita bace da ke hantaran Deejah, ita kanta Deejah saida abun ya bata mamaki...


"Knocking Ammah keyi a kofan Irfan yaki budewa, saida yajiyo muryanta kafin ya mike ya bude mata, kallo Ammah ta bisa dashi fuskan sa tayi jazur haka nan idanunsa wande suke farare sol sun koma jazur.
"Komawa Irfan yayi ya zauna bisa sofa bayan ya bu'de mata, ajiye plate din abincin dake hanunta tayi saman center table kafin ta zauna daf dashi, kallonsa takeyi a lokaci guda tana nazarin yanayinsa, hannayensa ta rike tace" I now you must be hungry maza kaci abinci, ta dauko plate din da spoon ta diba cikin spoon tace" oya open your mouth,
"Murmushi Irfan yayi yana kallon Ammah tun yana yaro idan yayi fushi ita ke calming dinsa, girgiza kai yayi yace" Ammah banida appetite, I can't eat anything now.
"Ammah ta ajiye plate din bisa table dan tasan bazaicin ba ko yaya tayi, ta dawo da hankalinta ga Irfan kana tace" Irfan, duk 'da na gari baya fushi da mahaifansa, abunda kayi shi kannenka zasu gani suyi koyi, snn har yaushene zakuyi watsi da wnn mummunar 'dabi'a ta turawan yamma huhm Irfan.
"Ammah pls, ni ba fushi da daddy nake ba, am just tired of this place ne kawai, am going back to the States......" What! Ammah ta 'katsesa kafin tace" no way Irfan, babu yanda zaka je kaji na fada maka, kar na sake jin kace zaka koma America, daga haka Ammah ta mike ta barsa nan wajen. Bayanta yabu da kallo kafin ya girgiza kai yace" dole na tafi I can't stay here, mikewa yayi saman sofa gamida lumshe ido.....




*Two days later*......
"Ko Office bezuwa tin bayan faruwan wnn al'amari, Sadiq ya dubasa a Office dinsa yauma baya nan, yana jin nauyin tambayan Engr dan haka ya yanke cewa kawai bzi dubosa a gida yau ida ya tashi a aiki.
"Hakan kuwa akayi, daga Ofiice gidansu Irfan ya wuce, tin daga nesa ya hangota yauma cikin shigar data saba wato shigar turawa tana tsaye gefen yanda aka ke'be Ostriches tana jefa masu abinci.
"Tsaki yayi a fili ya furta" maras kunyar yarinyar nan tana nan, dan ji yayi dama baizo ba sabida ganin Nadiya dayayi but babu yanda ya iya tinda ya shigo.......






πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.........
[8/19, 06:26] Umar Dalha: πŸŒ˜πŸŒ˜πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


26




"Kallo Nadiya tabi Sadiq dashi har ya shige, tsuka tayi gamida ta'be baki" shikuma wann sai shegen girman kan tsiya gashi ba kowa ta fa'di sanda taci gaba da jefawa Ostrich abinci.


"Haba Irfan abunda kakeyi kwata kwata be dace ba, for goodness sake akan me zaka dauki fushi da mahaifinka, ko meye yayi maka bai kamata kayi judging dinsa ba matu'kar ba dokan Allah ya take ba, da ka dena zuwa Office, are you planning to quit the job or what, haba Irfan kayi tunani kaifa Allah ya maka gata tunda ya bar maka naka mahaifin a raye, snn yana tsananin sonka yana kula da kai, inaga wa'enda babu nasu iyayen, duk wann ni'ima da Allah yayi maka sakayyan da zaka masa kenan, ka tuna yardan Allah na tareda na iyaye, kaman yanda ka rabu da momynka lafiaya kayi fatan rabuwa da daddynka lafiya.
"Kallon Sadiq Irfan yayi kafin ya murmusa yace" na gode friend, you're indeed a good friend Sadiq, I was planning to back to the States, amma kalamanka sun karyan gwiwa, na fasa tafiya snn zan nemi afuwa wajen daddy da Ammah.
"Sadiq yayi murmushi gamida jinjina kai, Irfan ya dan gyara zamansa yace" Friend ya kamata na fa'da maka komai dake faruwa, nan Irfan ya kwashe komai ya fa'dawa Sadiq bai 'boye masa komai ba gameda Deejah....
"Sadiq ya sau'ke ajiyan zuciya kafin yace" Friend the truth is that you're in love.... " What! Irfan ya fa'di yana me duban Sadiq, gya'da kansa Sadiq yayi yace" Of course you're in love aboki na, you love Deejah.
"Girgiza kai Irfan ya soma kafin yace" No no, that can't be, ni bana sonta, as a matter of fact bana son mata, they are always causing trouble, na fa'da maka she was the reason da na sami matsala da daddy na for the first time snn kace sonta nake, in short I want her out of my life.
"Murmushi Sadiq yayi me bayyana ha'kwara kafin yace" abokina just admit it, wllhi sonta kake amma idan ka kasa ganewa with time zaka gane, snn daddy ba irin son da kake tunani yake mata ba, no sonta yake tamkar 'yarsa yanda yake son sauran yaransa.
"Shiru Irfan yayi yana nazarin maganganun Sadiq, Sadiq ya dan dubi agogon hanunsa ya mike yana gyara hulan kansa yace " kasan abunda nake so da kai, tashi muje mu samu Oga, and apologies to him.
"Ba musu Irfan ya mike suka nufi sashen Engr wanda yake can tsakiyar gidan daga center.


"A parlor suka samesa yana shirya wasu documents, da sallama suka shiga, Engr ya amsa yana cire glasses din idanunsa.
"Yana ganin Sadiq fari'an fuskarsa ta 'karu, yana jin son Sadiq tamkar 'dan da ya haifa na cikinsa, dan kwana biyi da fara aikinsa a 'karkashin company dinsa ya gane Sadiq nada gaskiya da ri'kon amana, dan kuwa duk wasu cuku cuku da akeyi a fanni accounting an rage, komai na tafiya yanda ya kamata.
"Rusunawa sukayi suka gaida Engr, nan Irfan ya nemi gafaran mahaifinsa kuma ya yafe masa, take komai ya koma normal dama Engr mutum ne me tsanain damu da damuwar iyalinsa, nan Irfan da Sadiq suka ci gaba da shirya documents 'din aka kuma 'barke da hirar Company gaba daya.
"Sosai Engr yaji da'din abota tsakanin Sadiq da Irfan ko babu komai Sadiq yaron kirki ne, zuwan Sadiq cikin ruwarsu ha'ki'ka alkhairi ne.



"Kai tsaye wajen Ammah Irfan ya wuce da Sadiq dan su gaisa.
"Ammah ma sosai ta sake da Sadiq dashike yanada barkwanci, Ammah ta dubi Sadiq tace saifa kayita fama da abokin naka dan miskili ne bana wasa ba, Irfan ya dan langabe kai yana kallonta ba tareda yace komai ba, Sadiq murmushi kawai yayi kafin sukayi sallama da Ammah.


"Har wajen da Sadiq yayi parking motar sa Irfan ya raka sa, har lokacin Nadiya na tsaye wajen jiminan sai kallon Sadiq take har ya tada motarsa ya fice.


"Daidai 'kofan shiga sashensa suka kusa yin karo hannunta dauke da tray na abinci, kallonta ya tsaya yi itama haka kallon nasa take, sun jima a haka suna aika sa'kon kallonsu ma juna kafin ta sunkunyar da nata idon, dan kuwa gaba 'daya 'kwarjinin sa ya cika wajen.
"Gajeren tsaki yayi gamida sa kai ya wuce cikin parlornsa, jiki a sanyaye tabi bayansa, kaman baisan ta shigo ba haka yayi hayewarsa sama dakinsa, so yake ya rin'ka avoiding 'dinta ko zai 'karyata abinda zuciyansa da Sadiq suke gaya masa gameda Deejah.


"Ta jima tana zaune parlorn sa ganin alamu bazai fito ba yasata mikewa ta fice, bata san me takeji gameda Irfan ba, amma kasancewa da sukayi na kwana guda a tare yasata jin wani irin babban al'amari gameda shi, zuciyanta ne ta shiga garga'dinta" _Ke Deejah ruwa ba sa'an kwando bane, ina ke ina Irfan, matashi meji da ku'di da kyau, komai ya hada a rayuwa saidai wanda ba'a rasaba, tsaya yanda Allah ya ajiyeki matsayin Nanny_. Da wann tunani ta isa zuwa 'dakinta, wayanta ta ciro ta shiga neman layin Anty Larai haka kawai taji tana son magana da wani nata itama....




*08:13pm*
"Engr ne zaune a Office dinsa na cikin gidansa wanda yake a cikin sashensa yana gudanar da wasu 'yan ayyukan sa, Nadiya ce tayi knocking a door din, da shike kofar na glass ne tuni Engr ya ganta, murmushi ya sakar mata kafin yace" come in sweedy.
"Tura kofar tayi dashike irin me zugewan nan ne sann ta shiga, kujera me kallon na Engr ta zauna kana tace" Daddy sannu da aiki, idonsa naga computer yace yauwa sannu Sweedy, is anything the matter, ya tambaya har lokacin yatsunsa na kan keyboard idon sa naga screen din computer din.
"Daddy dama so nake muyi wata magana.
"I guess about your school right? Ya fadi sanda yake ci gaba da aikinsa.
"No daddy is about Deejah..... cewan Nadiya......
"Take Engr ya bar abunda yake gamida cire glasses din dake manne idonsa, ya karkato kacaukwam yana duban Nadiya......




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹........
[8/19, 06:26] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye*


27




"Nadiya taci gaba da fa'din" Daddy so nake nasan meke tsakaninku da Deejah.
"Shaye da mamaki Engr ke kallon Nadiya kafin yace" Nadiya are you incense, kin kosan da wa kike magana.
"Daddy na sani, Deejah tazo gidan nan a matsayin Nanny wanda kowa baya sonta, bayan kai da Ammah babu wanda ke sonta cikinmu amma kywawan halayyarta da 'dabi'unta yasa kowa ya fara sonta, kuma naga yanda kayi reacting sanda suka 'bace da ya Irfaan, Daddy ina so nasan ko kaima......"Enough! Engr ya daka mata tsawan da saida ta firgita, get out of here now stupid girl kawai, ya fadi yana nuna mata kofa.
"Jikin Nadiya har na 'bari ta mi'ke ta nufi 'kofa dan bata ta'ba ganin haka daga mahaifinta ba.
"Tana ficewa Engr ya zauna yana jinjina lamarin, wai me 'ya'yansa suke nufi ne, shikenan shi bashida daman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login