Showing 132001 words to 135000 words out of 159062 words
Chapter 45 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt
Azee lib'is kafin suka k'yaleta yashe a wajen tana neman d'auki, tsaban k'warewarsu a iskanci harda yima malam Audi kyauta me tsoka dan gaba idan sunzo ya k'yalesu su shiga.
"Azee ta nemi kuka ta rasa, banda azaban ciwo babu abinda gabanta ke mata, mata hud'u sukayi fingerings d'inta, ta lura abun nasu harda mugunta, babu wanda take son gani a halin yanzu sai Irfan, da yanzu tana kwance cikin jikinsa tanai masa shagwab'a, kewar mijinta da tsanar Ahidjo su suka taru suka cika zuciyarta.. haka ta mik'e tana tafiya da k'yar ta nufi d'aki dan yin jinya ma kanta.
"Yesmin zaune gefen Ahidjo har lokacin baya iya zama sai kwanciya dan ta kashinsa ba k'aramin ciwo yaji a wajen ba, taunar cingam take lokaci lokaci tana kwashewa da dariya idan ta kallesa. "Da k'yar cikin mawuyacin hali Ahidjo ke fad'in" Dan Allah ki taimaka ki kaini asibiti a min d'inki wllhi wann ko basir me sturo ne iyakaci...."Yesmin ta kuma kwashewa da dariya kafin tace" Ka dai ji kashedin da na maka wllhi wllhi maganar nan ya fita naji shi a gidanmu ko a gidanki ko kayi gigin sakina, wllho kashinka ya bushe, duk wani iskancin da kake da matar abokin ka zan fad'a komai, kai kama sanni yanzu kam kasan what I'm capable of, I don't have to explain my self to you, k'aramin d'an iska kawai, c'mon tashi muje na kaika a maka stitches ba don halinka ba, da naso barinka kayi sati a haka harta kashi sai ya gagareka amma yanzu tumda ka mik'a wuya ka yarda nice gaba da kai fine, oya let's go..." marairaice fuska yayi cike da fargaba yake fad'in bazan iya tafiya ba ki taimaka ki rik'e ni, tsaki ta d'anyi kafin tace kaci darajan kai kyakkyawa ne kasanni da son kyawawa dan shi ma na aureka, jawoshi ta shiga yi kaman wani kashi ta nufi waje da shi tana k'walla kira wa driver dinta.....
"Ciwon Laila sai da'da ruruta yake, hankalinta idan yayi dubu ya tashi babu yanda Engr baiyi ba taje asibiti amma tak'i, ita bama wann ba canzawan da yayi ne ya dameta, da k'yar ta d'au mayafi tana dingisawa ta fito waje, a haka ta tada mota da k'yar take driving har ta isa gidan Hajiya Karime.
"Hajiya Karime na kwance shem shem a parlor ta d'aga hammatarta dan k'urjin yaja ruwa sosai k'ik'aiyi da zogi kullum k'aruwa yake ko riga bata iya sakawa, Da k'yar ta mik'e tana jan zani k'irjinta take bin Laila dake k'ok'arin shihowa da kallo, Laila tana shigowa ta shiga toshe toshen hanci tana fad'in" Hajiya meke wari a gidan nan..."Harara Hajiya ta galla mata kafin tace" Ubanki ne ke wari....sai snn ta lura da d'ingishin da Laila keyi, da k'yar ta mik'e ta gyara zamanta bisa kujeran kafin ta bud'e baki tace" Me nike gani a k'afarki ciwo ne haka kikaji???
"Zama Laila tayi da k'yar kafin ta dubi Hajiya nan taga mulelen k'urjin da ya cike hammatar Hajiya, "Zaro ido waje tayi kafin tace" Hajiya wann k'urji fah, inaga shi yake wari a jikinki...."Tsaki Hajiya tayi kafin tace" Ke bakiji warin da gyanbon k'afarkin nan keyi ba. Wai me ya sameki.
"Hajiua wllhi bansani ba, kinga abunda ya kawo ni kenan, dama ki rakani naga likita don ni bazan iya zuwa asibiti da mijina ba wann ciwo nawa kunya yake bani..."Karime ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace" shikenan ai sai dreba ya kaimu... Haka suka sa k'afa suka fice a gidan..
"Engr yace" Detective Haidar inajinka, ka tabbata sun fice a gidan, toh maza ka aiwatar da aikinka Detective make sure babu wanda ya ganka, I don't need to tell you all this tunda aikin ka ne. "Daga d'aya b'angaren Detective Haidar yace an gama Sir.
"Kallonta ya jiyo yayi yanda gaba d'aya damuwa ya nuna a fuskarta, Allah sarki inama zai iya rungumeta a halin yanzu ka zataji sanyi, inama zai iya kwashe duka damur zuciyarta ya dawo nashi, a hankali ya kira sunanta cikin sigan da ta jima rabonta da taji an ambata don shi kad'ai ya iya ambato yanda yake mata dad'i" Fateee pls don't stress out your self kinji, things will go back the way they were, Baba Alhaji will soon get well, and zaki kasance da mahaifinki insha Allah....."Dagowa tayi tana kallonsa kafin tayi saurin sunkuyar da kanta sakamakon abunda ta tuna. Nan hawaye suka soma zarya a fuskarta..
"Innalillahi bazainiya jure ganin hawayenta ba, sassauta murya yayi kafin yace" Na fad'i wani abunda ya b'ata maki rai koh, kiyi hak'uri pls bana son ganin hawayenki,...."Kallonsa ta kuma kafin tace" Nazif don Allah ka min wani alfarma d'aya bayan mun gama da issue din Baba Alhaji.
"Murmushi yayi shi kuwa me Fatee zata nema a wajensa ya kasa maya, ai ko ransa ta ne, a zai iya *Mallaka* mata.
"Fad'ad'a murmushinsa yayi kafin yace" What is that fatee, just tell me what ever it is, am willing to do it.
"Sa hannu tayi ta share hawayen fuskarta kafin tace" So nake kayi nesa dani pls....."Ai bata gama yin shiru ba ya soma girgiza kai yanai mata mugun kallo ya mik'e tsaye, (Ni kuwa Samee nace Engr ya juye mun Irfanπ)... "Murya na rawa yake fad'in " No Fatee, you can do this to me, you know this is something that I'll never do, sama da shekaru talatin inandakon soyayyarki kin san haka, kin sani, yanzu da na sameki bazan k'ara bari ki kufce mun ba, Fatee for my whole life I spent it thinking about you duk na san bazan tab'a samunki ba, but for once soyayyarki bai tab'a gogewa a zuciyata ba, no I can't do this ki rok'i wani abun.... "Kuka take tana fad'in "Nazif we can't be together, ..."Girgiza kai ya soma tamkar yaro d'an ashirinda yake fad'in" Why Fatee why, we have all the right to be together, nothing can separate us apart again.
"Of course there is, akwai abunda yasa bazamu kasance tare ba, Nazif you are already married to my own sister *Laila*
"Dumm haka k'irjin Engr ya buda, shi gaba d'aya ma ya mance da wata Laila, yama mance Laila is her sister ya ma mance baka auren ya da k'anwa lokaci guda, soyayyanya rufe masa idanu baiji bai gani sai zallan soyayyan Fateen sa, take zufa ya soma karyo masa, jiki a sanyaye yake kallonta bai iya furta komai ba ya soma tafiya har ya kai k'ofa ya juyo yana kallonta kafin yace" I'll never stop loving you... daga haka sa kai ya fice..."Durk'usawa tayi a wajen tana kuka mai tsuma zuciya.....
Sameena ceππΎ
[10/11, 10:05 PM] βͺ+234 803 864 9695β¬: ππππ *Mallakin Waye*
93
*Β©Sameena Aleeyou....βπ½*
_Queen Samy Novels Forum...ππ_
"Zama tayi dirshan a wajen tana hawaye, hak'ik'a soyayyan Nazif cikin jininta yake, shakka babu idan akace ta cire soyayyarsa a zuciyarta yana daidai da rasa rayuwrta ne, take abinda ta haifa ya fad'o mata, Allah sarki ko yana raye ko yana mace sai Rabbi.
"Mamie ce ta turo k'ofa ta ganta a haka, tausayinta ya cika zuciyar Mamie, a hankali ta k'arasa gamida dafa kafad'unta, Fatima ta dago tana kallonta tuni taji wani sabon kuka yazo mata, zama Mamie tayi gefenta hannayensu na rik'e cikin na juna kafin ta soma fad'in" Fatima ki fawwala wa Allah lamuranki dan shine majib'icin al'amuran mu, na sani you're going through a difficult time, Na d'aukeki tamkar k'anwa duk wani abunda ke damunki we can share it, I'll always be there for you.
"Goge hawayen idanunta tayi kafin ta rungume Mamie tana fad'in" Banida gatan da ya fiki, Ubangiji yasa *Zumuncin Mu* (Sabon littafina mai fitowa insha Allah) ya d'aure har a Aljannah. Murmushi Mamie tayi suna jin soyayyar junansu kaman ciki guda suka fito.
"Duk gwaje gwajen duniyar nan Drs sunyi amma basu gano kan ciwo Karime da Laila ba, k'arshe dai had'asu sukayi da ampiculos da paracetamol Likita yace su dawo bayan kwana biyu idan babu improvement.
"Kai tsaye gidan Hajiya suka nufa su duka biyun suka yada zango, Laila ce ta mik'e da k'yar tana jan k'afa tace Hajiya barin duba tsohon nan, Karime ta tab'e baki kafin tace "Wa'adin da na d'ibar masa nike jira su cika na aikasa lahira dan naga alama na tsaya jiransa ran k'arfe ne dashi. Laila bata tankata ba ta wuce tana d'ingisawa dan yanzu ita ta lafiyarta take.
"Sallama Laila ta rink'a yi a k'ofar d'akin amma shiru, d'an gajeren tsaki tayi sanda ta tuna ashefa baya magana, kai tsaye ta kutsa kai cikin d'akin" Ga mamakin ta babu shi a d'aki, mutumin da ko toilet baya iya zuwa toh ina yaje, dube dube ta shiga yi harsu k'ark'ashin gado babu alamun shi, ta bud'e bathroom ta lek'a nan ma baya nan, wani uwar ashar Laila tayi a maimakon innalillahi kafin ta fice cikin sauri tana jan k'afarta.
"Hajiya! Hajiya!! Hajiya!!!... haka ta rink'a k'walla kira wa Karime, a zabure Karime ta mik'e tana tambayarta lafiya meke faruwa, "Hajiya banga Baba Alhaji ba, cewar Laila.
"Karime ta ware idanunta kafin tace" Yo mutumin da ko motsi me kyau baya iyawa ina yaje.
"Laila ta tab'e baki had'i da bud'e hannaye kafin tace" Yo ina zan sani kina gani yanzu muka dawo tare dake daga asibiti,
"Zufa ne ya shiga keto wa Karime ta ko ina.. "Jar ubancan, kodai sace shi akayi amma kuwa da an fallasheta..."Cikin sauri ta budbi Laila dake tsaye kanta tana mata kallon tuhuma, Maza yi sauri ki tambayo Uwa waye ya shigo gidan nan.
"Laila ta tab'e baki kafin tace" Hajiya anya ba kece kika k'arasa tsohon nan ba.
"Karime ta watsa mata harara kafin tace" Ai da nasan abinda zai faru kenan da tuni na murk'ushe d'an banza, .."Bud'e murya gaba d'aya tayi tana k'walla kira wa Uwa mai mata aiki. Cikin sauri Uwa ta iso ta zube a k'asa tana fad'in Hajiya gani.
"Anyi bak'i ne a gidan nan ko kinga wani ya shigo, Hajiya ta bid'a.
"Girgiza kai uwa tayi kafin tace" Hajiya tun bayan fitarku babu wanda yazo gidan ga.
"Karime ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace tashi kije aikin ki... "Da sauri Karime ta mik'e ta fice don dama warin gyambon su ya cika mata ciki.
"Laila ta dubi Karime kafin tace" Barin kira My Engr ya sanar da hukuma ayi bincike..."Wani uwar ashar Karime ta malmalo ta jefa wa Laila kafin ta ci gaba da fad'in" Ashe ke har yanzu sha sha sha ce, so kike asirinmu ya tonu ko me, ai babu mai jin wann batu bayan mu biyun nan, babu wanda zaiji batun b'atan nasa, da zaran na d'anji k'arfin jiki zan koma wajen Boka ya salwantar mun dashi a duk yanda yake.
"Laila dai tab'e baki tayi kafin ta mik'e tana kallon agogon bangon dake manne a parlorn tace" Hajiya zan tafi lokacin dawowar Engr ya kusa kar ya dawo ya tarae bana gida.
"Karime ta kuma ja mata kunne kafin Laila ta fice,
"Koda ta fito kasa driving tayi gashi dreban Hajiya da ya ajiyesu ya wuce aike, ta rasa wa zata kira Safwan ne ya fad'o mata nan ta shiga dialing lambarsa...
"Yussy na cikin goge kayan kallonta a parlor wayan Safwan dake ajiye bisa center table ya d'auki ruri, da sauri ta k'arasa tana dubawa, ganin Laila ce yasata yin murmushi kafin ta d'aga wayar.
"Daga d'aya b'angaren Laila ke fad'in" Darling Saf pls kazo gidan Hajiya mana kayi dropping d'in a gida, ina da wound a k'ata I can't drive....." Toh dan uwarki bazai zo ba, shegiya karuwa me bin mazan mutane, na rantse da Allah idan baki daina bibiyan mijina ba sai na tona asirinki shegiya ballaga 'yar ballagaza uwar ballagaza...."Kutuman ubancan wann zagi da Yusyy tayiwa Lailamba k'aramin k'ona ranta yayi ba, ai babu shiri ta kashe wayar..."Yussy taci gaba da kwararo ashariya tana watsa wa Laila... daidai nan Safwan ya fito daga toilet d'aure da towel..."Da sauri ya fizge wayarsa hannun Yussy, juyowar da zatayi ya kwasheta da mari meji da lafiya wanda saida ta durk'ushe a wajen. Wani k'ara ta sake gamida rik'e kuncinta, cikin kuka take fad'in" Allah ya isa na kan na fad'i gaskiya shine zaka dakeni.
"Huci yake kaman wani kububuwa yana watsa mata mugun kallo kafin yace" Dan ubanki akwai karuwar data fiki ne, shegiya munafuka, na maki iyaka da tab'a wayata bakiji koh, toh wllhi ki kiyayeni, kwanciya da mata ne bakinisa ki hanani ba koda a cikinngidan nanne, haka kika ganni kikace kin amince.... "Kuka Yussy keyi take taji zuciyarta na tashi don ji tayi bata son warin sabulun da Safwan yayi wanka dashi kan tayi wani yunk'uri tuni ta soma kwararo amai ai kuwa sai k'afar Safwan,..."Kan bala'incan duk wankan da yayi ta kware masa amai a k'afa, sabida tsaban takaici baisan sanda ya tokareta da k'afafunsa ba.
"Kallonta yake yana nazarin kafin ya d'ago kanta da duka hannayensa biyu ya kafe ta da ido kafin ya soma girgiza kai yana fad'in" Don ubanki me zan gani don't tell me you're pregnant, dama kinsan kinada ciki kika bari na aureki, shegiya gantallalliya,.."Dago ido tayi a galabaice tana kallomsa kafin tace" Ka ringa saka minjaye Shegu gantalallu dai... Hura hanci yayi yana huci yake fad'in ni kike mayar wa magana, harara ta kuma galla masa kafin ta ci gaba da k'waza aman ta.
"D'aki Safwan ya shiga ya zaro belt din wandonsa, haka ya ringa zabga wa Yussy belt din nan ko tausayin halin da take ciki baiyi ba.
"Saida tayi laushi kafin ya k'yaleta, wani mugun kallo yake mata kafin yace" Ki fad'a mun waye uban shegen dake cikin ki.?
"Hararsa tayi kafin tace" Shegen dake tsaye gaba na shine uban shegen dake cikina, nan fah Safwan ya kuma harzuk'a yayo kanya zai kuma jibganta tuni taji wani k'arfi yazo mata, wuk'ar da ta gama aiki dashi ta janyo ta rik'e tana hararansa take fad'in" Wallhi kayi gigin dukana sai na cakka maka, shege ka fasa, kuma wllhi idan baka daina mistreating dina ba sai na fasa komai, ta d'anyi murmushi kafin tace" Safwan mace nake idan bariki ne mu zuba ni da kai, daga haka ta wuce d'aki tasa key ta barsa nan tsaye yana huci.
"Laila dai k'arshe dole adaidaita ta shiga ta wuce gida, k'irjinta ne yayi mugun fad'uwa ganin Motar Engr a parking lot, haka ta daure ta sa kai cikin gidan.
"Yana zaune parlorn sa yana kallon BBC ta yi sallama ta shigo, kallo d'aya ya mata ya d'auke kansa.
"My Engr yau ka dawo da wuri... ta fad'i sanda take k'arasa shigowa parlorn,
"Daga ina kike ya jefo mata tambayar.
"Saida gabanta ya fad'i kafin tayi k'ok'arin tattaro nutsuwarta tace" Wllhi daga gidan Hajiya nake ta saka ni gana ta kaini asibiti an duba k'afata.
"Gyad'a kansa yayi kafin yace "Allah k'ara sauki. Sam bata son matsowa kusa dashi don kar d'oyi ya damesa, kamar ta sani yanzu haka ma k'arfin hali yake. Mik'ewa yayi kafin yace" Yay jikin Baba Alhj...."Dummm! Haka k'irjinta ya buga..."Daburcewa tayi ta soma en kame kame ... eh yana yana nan da sauk'i.
"Engr ya murmusa kafin yace Allah basa lafiya, akwai dama maganar da nake son maki, Insha Allah zanyi tafiya nan da kwana uku, snn tafiyan zan iya yin sama da one month, Zan tafi da Ammah da shike can Loss Angeles zan tafi, tafiyar ta shafi Office amma na zab'i na tafi da Ammah don lokacin ganin likitan ta a Loss Angeles yayi, snn abunda yasa nake so ke ki zauna sabida yara, bai kamata a barsu su kad'ai ba kin gane, snn Irfan baya nan kar a buk'aci wani abu a company saiki sa ido though Sadiq yana nan amma aikin zai masa yawa,.
"Murmushin yak'e tayi kafin tace" Gaskiya ne, aima yaran dani suka saba, Allah dai ya kaiku lafiya, wani b'angare na zuciyarta na fad'a mata kinyi kud'i tunda yanzu company na hannunki.
"Engr kuwa ko kallonta bai kuma ba yayi hayewarsa sama....
"Cikin kwanakin aka gama visa da komai da komai, Baba Alhaji, Engr Nazif, Ammah da kuma Fatimah suka d'aga zuwa k'asar Germany yanda za'a gudanar da jinyar Baba Alhaji, saidai muce Allah sauk'eku lafiya yasa ayi a sa'a.
*Manchester, England*
"Baby! Baby!! Baby!!! Irfan keta faman k'walla kira wa Deejah daga bathroom,
"Ajiye rigar sa da take ninkewa tayi kafin ta mik'e ta isa jikin k'ofar bathroom din tace" What's that call for, don't tell me yauma baka shiga wanka da towel ba.
"Oh baby kin iya reading mind dina tsaban soyayya, oya do your job, bani towel.
"Turo baki tayi kaman yana ganinta kafin tace cikin sigan shwagwab'a," Ni dai gsky ka daina shiga shower without towel, na sani ina shigowa zaka b'ata min kwalliyata.
"Kwaikwayan muryarta yayi shima a shagwab'e yake fad'inz" Baby pls mana, ni ne fah, Okay fine kina so na fitoh a haka kin san zan iya...."Da sauri har tana gudu ta k'arasa closet ta zaro towel tana fad'in" Oh no gashi wllhi zan kawo maka kar ka fito haka pls...
"Dariya sosai taba