Showing 102001 words to 105000 words out of 159062 words

Chapter 35 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10371

ina zan sani, nima waya akamun aka ce nazo nan asibitin, an samesa a gefen bridge yayi accident..... "Ahidjo ya bud'e ido daga suman da yayi ya waresu tass kan iyayensa. Da sauri suka soma rige rigen rungumesa suna tambayansa jiki.
"Auchhh! Yake kan fad'i dan rungumansa da sukayi sun fama masa ciwon.
"Dad yace" Champ me ya faru da kai, Ammi tace" baby me ya sameka, what cause the accident?
"Murtuk'e fuska Ahidjo yayi kafin yace" Dad Ammi, am Okay now, ni Deejah nake son zuwa na gani..... "Kallon juna sukayi kafin suka ce wacece kuma Deejah?
"Ahidjo yace" 'yar gidan Engr. Nazif Mumtaz..... She's the love of my life, wnn accident da kukaga nayi saboda ita ne, tace bata sona, kuma wllhi idan ban aureta ba, kunji na rantse kashe kaina zanyi...... "Salati Ammi ta soma, yayinda Dad kebin Ahidjo da ido.
"Da sauri ta toshe bakin Ahidjo kafin tace" Baby ka daina fad'in haka kasan kai kad'aine d'anmu we can't afford to loose you, ai yazo ma gidan sauk'i idan dai d'iyar Engr, kasha kuruminka, a yau zanje da batun neman aurenka gida.
"Ahidjo ya mik'e ko zafin ciwon baiji ba yace really mum, murmushi ta masa kana tace" Ofcus my Precious, komai zan maka a duniyan nan.
"Dad ya shafi kansa yace" Champion you shouldn't have done that, da zuwa kayi ka sameni da batun.
"Ahidjo ya turo baki yace" Dad kai always baka da time ne ai, baka zama dani, baka san damuwata ba, baka san me nake ciki a rayuwa ba, always meetings commitments you don't have time for your only son, yanzuma dabadon ance maka ina gadon asibiti ba rai hanun Allah da baraka zo ba.
"Ammi ta yamutsa fuska tace "Baby kayi hak'uri kasan Dad dinka politician ne sai a hankali. "Dad ma hak'uri ya kuma bawa Ahidjo kafin yace" Champion am truly sorry, I promise you zan kashe gaba daya schedules dina na wann week din na zauna da kai naji problems dinka, snn zanyi iya k'ok'arina naga Engr Nazif ya baka d'iyarsa. I'll make it up to you I promise kaji Champ.
"Murmushi me cike da ma'anoni Ahidjo yayi kafin yace" thanks Dad you are the best Dad on Earth. Likita ne ya shigo yayi discharging Ahidjo daga nan suka wuce gida baki d'aya.....






"Yamma nayi Ammi ta kira k'awarta Hajiya Farida ta rakata gidan Engr. Hakan kuwa akayi.


"Ammah suka samu da batun, Ammah tayi shiru tana nazari kafin tace" Um um kunsan yaran yau idan suka ce basu son abu to barinshi shi yafi alfanu amma bacin haka Ahidjo ai ya wuce wann a gidan nan, mu masu fita mu nema masa ne ma.
"Hajiya Farida tace" Pls Hajiya wann had'i akwai alkhairi acikinsa, 'ya'yan manya sai y'a'yan manya, idan muka biye na yaran yau sai suje su kwaso mana talakawa suce su suke su aura, kinga irin wann had'i ai shi yafi alkhairi..... "Kan Hajiya Farida tayi shiru suka jiyo sautin kukan Ammi mahaidiyar Ahidjo tana fad'in" Shikenan yace wallhi mutuwa zaiyi idan har ba'a aura masa ita ba.... "Hajiya Farida ta soma bawa k'awarta hak'uri yayinda jikin Amma yayi lak'was sosai. Ammah ta mik'e kafin tace kiyi hak'uri Hajiya Jamila, barin kira maku yarinya kuji daga bakinta dan bazamu tak'urata ba...



"Daga can Deejah ta tsaya jiki a mace tana kallon babban mata tana kuka sharshar da hawaye. Ammi tana hangota ta k'arasa gabanta da sauri ta durk'usa gamida kama k'afafun Deejah tana kuka take fad'in" Dan Allah Deejah ki amimce zaki auri tilon d'ana Ahidjo, dan Allah karki bari na rasa tilon d'ana sabida ke......
"Kan Deejah yayi mugun d'aurewa, wani irin abune wann, bazata iya jure ganin babban mata durk'ushe haka gabanta tana kuka ba...... "Da sauri ta shiga k'ok'arin d'aga Ammi tana fad'in" Dan Allah ki daina durk'usa min ki daina kuka..... "Ina kaman cewa tayi Ammi ta k'ara kukan.... "Saosai take kuka tana fad'in" bazan tashi ba sai kin amince zaki auri Ahidjo, a sabida ke yayi had'arin mota, yanzu kuma ya tabbatar mun kashe kansa zaiyi idan baki amince da aurensa ba, ki taimaka mun kar na rasa sa....."
"Hankalin Deejah sosai yayi mugun tashi, itakam bata son Ahidjo snn wann baiwar Allah ta bata tausayi, da k'yar ta iya furta mama ki tashi naji na amince ZAN AURI AHIDJO.
"Kaman a mafarki haka Ammi taji batun nan ta mik'e tana godiya ma Deejah gamida rungumeta.
"Ammah ta kalli fuskar Deejah cike da tausayawa tasan kawai amincewa tayi sabida tausayi ba har cikin ranta ba....






"Sanda Ammi takai wa Ahidjo wann labari gani yayi tamkar a film, nan da nan ya rok'i Dad a san yanda za'ayi a saka bikin nan da sati biyu.
"Dad din Ahidjo ya tafi har gidan Engr sun jima suna tattauna lamarin yanda Dad din Ahidjo ya rok'a asaka bikin sati biyu masu zuwa.


"Su Hajiya Farida an had'a lefi na gani na fad'a an kai gidan Engr Nazif Mumtaz. Ammi kuwa sai yad'awa take d'anta zai auri 'yar president na M&M Builders. Hankalinta ya kwanta Ahidjo ya zab'o kyakkyawa d'iyar masu arziki......




"A b'angaren Deejah fah, gaba d'aya abun ya dameta, shikenan ta amince da auren Ahidjo, shikenan Irfan ya tabbata ba *Mallakinta* bane. Anya batayi ganganci ma rayuwarta ba.... shin wai tanada wani zab'in da yafi wann ne, wasu hawaye masu zadi suka shiga zubo mata......


********************************


"Sadiq zaune gaban Engr, yayi gyaran murya kafin ya soma fad'in" Sadiq abunda uasa nayi kiranka shine naji daga bakinka shin kana son Nadiya.
"Sadiq ya d'an sosa k'eya kafin yace "Eh Daddy, I luv her with all of my heart.
"Engr yace Alhamdulillah, jiya nayi mata magana na tambayeta wa take so dan ina so a had'a aurenta dana 'yar uwarta Khadeejah, ta tabbatr mun kai take so.... "Tunani Sadiq ya soma wacece Khadeejah kuma?... Muryan Engr ya dawo dashi yanda yake fad'in" Sadiq na *Mallaka* maka Nadiya d'iyata ta zamto matarka ta sunnah, zanyi komai da izinin Allah, kaidai kawai naka ka sanar da magabantanka nan da sati guda mai zuwa za'ayi biki......"Sadiq da murna ya gama lullub'esa shinnda gaske Nadiya zata zama *Mallakin sa* da sauri ya rusuna ya soma godiya wa Engr.
"Engr ya murmusa kafin yace" kafi k'arfin wann a wajena Sadiq, inajinka tamkar Irfan koda bani na haifeka ba....
"Hankalin Sadiq yayi mugun tashi sanda ya tuno da batun Ruqayya... "Kaman daga sama ya tsinkayo muryan Daddy yana fad'in" Kar ka damu Abubakar nasan da batun Ruqayya 'kanwarka da kuke soyayya, Nadiya ta sanar dani kuma ta buk'aceni da na tsaya maka har Allah ya *Mallaka* maka su duka biyu, dan haka ba zallan Nadiya nake nufin zaka aura ba, harda ita Ruqayyan, za'a had'a bikin duka rana guda..... " Sadiq bai iya k'arasa sauraren batun daddy ba, Allah sarki wani irin so Nadiya ke masa, tana son farin cikinsa fiye da nata, duk kishi irin na Nadiya ta hak'ura ta zab'i farin cikin sa fiye da nata.
"Goge hawayen idonsa ya soma, Engr ya shiga buga kafad'unsa cike da tausayawa, kafin yace " cikin gidaje na na *unguwsr Apo* ka zab'i guda d'aya mai section biyu ka soma renovating. "Yanzu kam Sadiq ya razana da karama da mutunci irn na Engr Nazif, hak'ik'a ya mance zafin maraici da ya d'and'ana tun bayan had'uwarsu. Sosai yayi godiya wa Engr gamida jero masa addu'o'i na samun nasara.




"Koda yaje wa Mamie da batun saida ta zudda 'kwalla, dole ta tashi takanas ta tafi har gidan Engr tayi masa godiya, Ammah kuwa sosai wann abu yayi maata dad'i, dukda Engr ya d'auke komai ma Sadiq hakan bai hanasa had'a kayan lefe daidai gwargwado aka kawo ba.


"A b'angaren Ruqayya fah, taci kuka kamanmzata mutu, yanzu da wulak'anci da cin mutunci ace rana d'aya za'a d'aura aurenta da kishiyarta kuma ak'ofan gidan su kishiyar.
"Badiyya kuwa sai faman zugata take yanda k'arshe suka yanke shawarin zuwa gidan boka a basu maganin kashe Nadiya....






"Kallon katin yake da mugun mamaki, zuciyarsa ta shiga barazanar tarwastewa, a guje ya mik'e ya nufi upstairs ya dauko keyn motarsa. Azee ta sha gabansa kafin tace" Haba my one ka k'yaleta tayi aurenta mana tunda dai cewa tayi bata sonk...... "Had'iye maganarta tayi sanda taga kallon da ya watsa mata. Bai kuma cewa komai ba ya fice daga gida....






"Yanda yake falfala gudu bisa titi zai tabbatar maka yana cikin tsananin tashin hankali, hango motar Ahidjo da yayi pake k'ofan wani shopping mall yasa sa saurin cin birki ya fito a guje ya nufi mall d'in.... can ya hangosa yana zuba kaya cikin basket.
"Kaman daga sama Ahidjo yayi tozali da Irfan fuska babu walwa.... "Murmushi ya sakar masa kafin yace " Buddy what's up....... Kafin yayi shiru yaji sauk'ar naushi a gefen fuskar sa wanda zaida yakai sa k'asa......








Queensamy ceπŸ‘ŒπŸ½
[8/28, 14:14] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


72


*©Sameena Aleeyou......✍🏽*


_Queen Samy Novels Forum......πŸ“–πŸ“š_




" Jan Ahidjo Irfan ya shiga yi har ya fito dashi wajen mall d'in" wata wawan naushi ya kuma kai masa nan take jini ya soma fita daga hancin Ahidjo... "Irfan ya cukumo wuyar rigarsa yana huci yake fad'in" How dare you! How dare you Ahidjo, how dare you betrayed me just like this......" Let go of me!!!!! Ahidjo ya fad'i gamida fincike wuyar rigarsa, hannu yasa ya shafi hancinsa yaga jini, mugun kallo ya watsa wa Irfan kafin yace" banci amanar ka Dude, in fact taimakon ka nayi abin ka gode mun ne, Irfan shiyasa tun farko nak'i yarda da shawarinka, what saida na yarda nabi son zuciyarka zaka juyan baya... ..... "Bai rufe baki ba Irfan yakai mai wata naushin, da sauri Ahidjo ya rik'e hannunsa yana girgiza kai yake fad'in" I've had enough Irfan, auren Deejah kuma bazan fasa ba.... "Tsalle Irfan yayi ya tokare sa a ciki da k'afarsa, tuni Ahidjo ya rik'e cikinsa da 'yan hanjin suka soma sujayawa..." 'Dagosa Irfan yayi da kwalan rigarsa yana huci kaman zaki yake fad'in" You Coward bance ka aureta ba dating nata nace kayi, but you proof to who you really are, you are nothing but a Coward Ahidjo, you live to regret this, Mark my Words..... "Daga haka yayi jifa dashi yayi wucewarsa zuwa motarsa, da gudu ya finciki motar ya bar street din.


"Kanne ido Ahidjo yayi yana bin motar da kallo har ya b'ace masa kafin yayi murmushi yace" Let's see who will win among us.. daga haka ya mik'e ya nufi motarsa shima.....






" Kaman daga sama Nadiya ta kansa fuskan nan nasa tayi jazur haka idanunsa, baki na rawa ta soma fad'in" Sann sannu da zuwa ya Irfan, gyad'a mata kawai yayi kafin yasa kai ya wuce..... "Kallo tabisa dashi zuciyarta na tambayanta anya lafiya...




"Deejah na d'aki tana gwada kayansu da Nadiya ta karb'o masu a d'inki kawai sai jin an banko k'ofa tayi.... duk a tunaninta Nadiya ce " Da tsiwa ta soma fad'in" Woo what again Nadiya, gashi dai kin matsa mun na gwada kayan fine na gwada will you pls leave me in pe...... ta karashe maganar tana juyowa had'i da bud'e hannaye" Muryarta ne ya sark'e sanda ta gansa cak tsaye jikin k'ofa, tsanin tashin hankali ne zalla a fuskar sa...
"Duk da tashin hankalin da yake ciki hakan bai hanashi ganin tsan tsan kyaun da tayi ba, OMG kayan sun karb'e ta cikan suranta ya kuma bayyana.... "da sauri ya kauda kai hefe, Deejah kuwa saurin jawo mayafin dake gefenta tayi ta rufa a jikinta. Ganin Irfan na matsota yasata fara ja da baya dan yanzu tsoronsa take tunda yayi kissing nata.
"Saida ta isa jikin bango kafin ta tsaya cak. Take mayafin yayi da k'fafunsa... yana mata mugun kallo kafin ya ciro card d'in ya nuna a face d'inta yace" Saboda wann d'an iskan kika k'ini, banji mamaki ba, k'ila kun jima kuna soyayya ban sani ba, if not why the sudden wedding, kun jima kuna ha'inta ta. Fine, but let me remind you wann aure da zakiyi you'll never have peace, I ruin it and make your damn life miserable just like the way you ruined my life. Kallon face d'inta yayi yanda yaga tsan tsan tsoro ya nuna, jin fuskarsa dap da nata yasata saurin runtse idanunta.... "Kallon pink lips dinta yayi, da sauri ya runtse idanu gamida had'iyan miyau.... "Tana jin sanda ya fice daga d'akin gamida rufo k'ofa da I'arfi..... "Sai snn ta bud'e idanun ta gamida zama gijif a kan gado, ganin Irfan a yau ta tayar mata da mik'in soyayyar sa, hawaye suka shiga zarya a fuskarta sanda ta tuna shikenan yanzu Irfan ya tsaneta baya sonta, gashi zatayi aure, shikenan da gaske bazasu kasance a tare ba, durk'usawa tayi tana kuka mai tsuma rai... nan Nadiya ta shiho ta tarar da ita ahaka, durk'usawa tayi gamida rungumeta ta shiga rarrashinta, Deejah ta rungume Nadiya sosai tana kuka take fad'in" Nadiya I lost him forever, he'll never come back to me, na rasa Nadiyaaa.... kuka mai k'arfi ya kufce mata... sosai Nadiya taji tausayin su itada Irfan, dan shima taga ficewarsa daga gidan cikin tsananin tashin hankali......





"A parlor ya zauna, abubuwa suka shiga dawo masa, kama kansa yayi dan ji yake kaman a cire a rabasa da shi ko zai sami sauk'i.... "Kaman zararre haka ya soma fad'in" Why this why all this, why is this happening.... "Azee dake tsaye saman stirs tana kallonsa, take taji hawaye ya ciko idanunta, da gaske Irfan bazai tab'a sonta ba, gashi dai ta auresa amma har yanzu bai zama *Mallakin ta* ba, why this, take zuciyarta ta soma raya mata Deejah Deejah ce sanadin da yasa baya sonki. Zuciyarta na tafarfasa, wani tsanar Deejah ne ya kuma tokare mata mak'oshi, she can't stand her, she really needs to get rid of her, koda kuwa hakan na nufin ta rabata da rayuwarta ne. Murmushin k'eta tayi a bayyane kafin ta saita kanta ta k'arasa wajen Irfan.


"Rungumesa tayi ta baya ta soma masa salo tana tambayansa meke faruwa.. "A hasale ya d'ago yana mata mugun kallo kafin ya daka mata wata tsawan da saida ta birkice.." Get out of my sight, idiot, get out I said... "Jiki a sanyaye ta mik'e dan kuwa tasan kad'an ne da aikinsa ya lallasa mata duka tsiya, stirs ta haura da gudu ta fad'a d'aki ta shiga rusa kukan takaici......






*Three days to Biki*


"Hajiya Farida ta dubi Delu me mata aiki cike da mamaki tace" Delu ban gane ba, da gaske kike kodai k'aryarki da kika saba.
"Delu tayi murmushi kafin tace" wllhi Hajiya ikacin gaskiyata nike fad'a maki, Deejah ba 'yar gidan bace, a gabanmu aka kawota Orphanage cik7n tsumman goyo, k'arewarta gefen bola aka tsimce ta mahaukaciya ta yasar da ita, kinga kuwa tabbacin ma shegiyace kenan .
"Hajiya Farida tayi dariya gamida tafe hannaye kafin tace" To kuwa bazata tan'a sakuwa ba, tabb lallai kam "yo ina k'awata tasan da wann zance, duk a tunaninta d'anta ya zab'o matar nuna ma sa'a 'yar dangi 'yar gidan masu hannu da shuni... "Delu ta kwashe da dariua kafin tace "wllhi Hajiya nasha mamaki danaji kina cewa 'yar gidan masu ku'di, yo da 'yar talakan ne ma akwai sauk'i akan wacce mahaukaciya ta jefar da ita, kinsan dai mahaukaci dole wanine ya d'irkq mata ciki ta haifa ta jefar... "Mik'ewa Hajiya Farida tayi kafin tace" ashe dai da rabon Yesmin zata auri Ahidjo, barinki gani yanzu zan tafi gidan.
"Mayafin ta ta d'auka da makullin mota ta fice... ta nufi gidan k'awarta hajiya jamila...




"Yesmin d'iyar Hajiya Farida ce, wacce tayi k'aurin suna wajen shaye shaye da mama samari, a maleysia ta gama karatun ta, zata kai tsaran su Ahidjo, sabida tsaban shaye shayenta idanunta har juyewa sukayi, duk wani shaye shayen Ahidjo da iskancin sa a bayan Yesmin yake, tunda ta dawo daga maley ta k'yallq ido kan Ahidjo, shi kuwa atafau yak'i yarda baya sonta, tsananin son da iyayensa suke masa yasa su watsar da zancen, dan basu k'aunar abinda zai b'ata ran Ahidjo,, Hajiya Farida babu yanda batayi da aminiyarta ba, karshe dole ta hak'ura....






"Mik'ewa Ammi tayi gamida dafe hannu biyu a k'irji tace" Shegiya! Shegiya fah kika ce Hajiya Farida,.......






QueenSamy ce πŸ‘ŒπŸ½
[8/28, 14:14] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*


73


*©Sameena Aleeyou......✍🏽*


_Queen Samy Novels Forum.....πŸ“–πŸ“š_


*Assalam readers kaman yanda na baku hak'uri na rashin jina da bakuyi ba kwana biyu, hakan ta farune sakamakon 'yan wasu matsaloli da suka kunno kai, Amma yanzu insha Allah komai ya koma normal zakuna jina akai akai da izinin Allah. Allah ya bamu ikon idda wannan littafi lafia dani daku masu karantawa.. #1luv*




"Zufa ya shiga ketowa Ammi tako ta ina, girgiza kai taci gaba dayi kafin tace" Yo dama ba d'iyar Engr Nazif bace,... "Haj Farida ta kuma tab'e baki kafin tace" ba d'iyarsa bace, hasalima kwanakin baya d'ansu yaso aurenta suka hana sa lokacin kun tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login