Showing 114001 words to 117000 words out of 159062 words

Chapter 39 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10387

d'umin ya k'aru.
"Ai kuwa baturen nan suna had'a ido da Irfan, Irfan ya sakar masa murmushi gamida d'aga gira sama alamun, "Yes she's my wife, dan murmushi baturen yayi gamida ci gaba da karanta news paper dinsa.


"Can ta farka ta ganta cikin jikin Irfan tana bacci shima baccin yake gamida kewaye jikinta da hannayensa, Innalillahi dama jikin Irfan take bacci, k'ok'arin tashi tayi amma saiji tayi ya rik'eta sosai, a hankali ta rufe idanunta ba don taso ba taci gaba da bacci cikin jikinsa.....




"K'arfe shida na asuba suka isa K'asar *England* babban birnin *Manchester*, Kamam basune suka sha bacci cikin jikin juna ba, ko kallon arziki bata ishesa ba sanda suka fito daga Arrival, sauri sauri take ta faman binsa dannkar ya b'ace mata ga wani azaban yunwar da takeji dannita bata iya taci abincin cikin jirgin ba, tana ganinsa ya tsaya da wani bature suna magana ashe me taxi ne, k'arasowa wajenta mutumin yayi gamida karb'an luggage d'inta gamida sakawa bayan booth. Tana ganin Irfan ya shige motar tayi saurin k'arasawa baturen nan shi ya bud'e motar ta shige ciki. Kallon ikon Allah kawai Deejah keyi yanda Irfan yakeyi sai ka rantse tafiyarsu ba tare bane. Wata zuciya tace karfa Irfan ya maki babban walak'anci a k'asar da babu wani naki, tunani kala kala su sukata ziyartar zuciyarta har suka iso bakin wani makeken Hotel saman an rubuta *Welcome to Hilton Hotel Manchester, England*


"Nan ma sauri ta ringayi tana bin bayan Irfan dan kar ya b'ace mata, tumda take bata tab'a ganin gini masu kyau irin haka ba, ma'aikatan Hotel dinne su suka karb'i luggage d'insu gamida directing nasu zuwa room d'insu, room d'in k'ato ne very huge ciki da parlor harda wani waje kaman waiting, komai na d'akin abin kallo ne abin burgewa.
"Deejah kam zubewa tayi a nan parlor gamida rapka uban tagumi.
"Shi kuwa Irfan wanka yayi dan already lokacin k'arfe 8:12am, ya kamata ya fita ya soma gudanar da abinda ya kawo sa, shiryawa yayi tsaf cikin wata suite din ta daban kunsan babban shigar alfarma a wajen turawa tofah suite ne, sauri sauri ya gama shirinsa ya fito yanda ya tarar bacci yayi gana da Deejah nan kan kujera, daki ya koma ya dauki intercom ya kira room service gamida mata placing order kafin ya fice.




"Cikin bacci taji k'aran waya ya dameta, a hankali ta mustuke idonta gamida d'aga wayar, nan room service ya soma mata magana, itakan wann turancin nasu yayi mata girma dan haka yes kawai ta dinga jero masa cikin mintuna k'alilan taji ana nkckn a hankali ta isa k'ofa dan duk a tunaninta Irfan ne dan bataji motsinsa ba, room service ta gani rik'e da abinci, wani hamdala tayi a ranta dan dama yunwa takeji... cikin sauri tasa hannu ta karb'a gamida masa godiya, d'an murmushi baturen yayi kafin yace" at your service ma'am".
"Ko zama bata gama yi ba ta hau bud'e abincin tana mai addu'an Allah yasa zata iya ci.... "Chips ne da ketchup sai sausage a gefe, gefe guda kuma kaman sandwich ne da dukkan alamu an cika cheeze a ciki saman kuma an shafe Nutella, Oh Allah haka Deejah tace a zuciyarta dan gaba daya warin spices din bai mata ba babu yanda ta iya dan wani azabebben yunwa takeji, dole ta toshe hancinta ta hau tura abincin, ai batayi loma biyu masu kyau ba ta hau k'waza amai...




*Nigeria, Abuja*


"Kanajina aure babu fashi, na fad'a maka jibi d'aurin aurenka da Yesmin idan kaga dama in an d'aura auren ka kasheta ka kawo min gawarta, sha sha kawai wanda baisan abinda yake so ba.
"Ammi try to understand me ni ba cewa nayi bazan auri Yesmin ba but a d'an k'ara min lokaci, I'll prove to you the kind of girl she's, wllhi 'yar shaye shaye ce jiya Kasim yake ce min da suke Malaysia babu namijin dake shaye shayenta balle macce....."Rufe min baki Ammi ta katse sa mik'ewa tayi ta nufi stirs tana ci gaba da fad'in na gama magana jibi aurenka da Yesmin you can do your worse.
"Wani k'atutun bak'in ciki ne ya tokare mak'oshin Ahidjo he has no choice yanzu ya rasa Deejah and dole ya auri wancan trash din, dan gajeren tsaki yayi daidai sanda wayarsa tayi k'ara ganin numbern Azee ne yasa sa saurin d'agawa dannsun kwana biyu basuji daga juna ba.
"What Azeeza am not in the mood.
"Gajeren tsaki Azee tayi kafin tace" Toh maza kazo zance ne da d'umi d'uminta,
"dan tsaki yayi kafin yace" kinsan tunda Irfan ya auri Deejah na d'auke k'afa daga gidansa, I can't stand seeing them together......"Wani tsaki Azee tayi kafin tace basa nan they went on a trip dan Allah kazo we really need to talk.
"Ahidjo ya fuzar da isaka kafin yace" okay gani nan zuwa, gwara ma yaje ko zai samu ya huta da Azeen sa ko zai sami relief dan dama yayi missing Azee.



"Tochilanta ta shiga lalub'a dan jin sallamar tayi yawa, ko kusa bata d'ago muryan d'an nata ba, a daddafe ta fito parlor dan lafiya bai isheta ba.
"Ganin Safwan tsaye da wata budurwa a gefensa yasa Yakumbo d'aure fuska tamau, badon ganinsa da tayi da wata ba ko shakka babu da ta patatteke sa daga gidanta.
"Daki ta koma gamida dauko masu shimfid'a ta baza masu, kafin tace bisimillah ku zauna.
"Yatsina fuska Yussy tayi kafin tace" ni bazan zauna kud'in cizo su cinyeni ba........"Batayi shiru ba Safwan ya watsa mata wata uwar harara wanda yasata zama babu shiri, Yakumbo bata bi takansu ba ta tafi dan kawo masu ruwan sha.
"Safwan yanama Yusra mugun kallo yake fad'in" Kina jina this woman here is my mum, na fad'a maki and kar ki mance kashedin da na maki wllhi if you dare misbehave babu ni babu ke na fasa auren naki, 'yar rainin hankali ke ina naki uwar da har zakiyi wa nawa kallon banza, be careful kinji na fad'a maki. Tura baki Yussy tayi gamida yin ko oho.


"Koda Yakumbo ta dawo saida Safwan yayiwa Yussy Ido kafin da k'yar tana toshe toshen hanci ta iya furta ina yini.
"Yakumbo ta amsa mata da sakin fuska, kafin ta juyo kan Safwan, gaisheta yayi ta amsa masa da sakin fuska wann karan kunsan d'a da uwa.
"Safwanu wacece wann?
"Safwan ya d'an k'ak'aro murmushi kafin yace" Yakumbo dama na kawo maki matar da zan aura ce Yusra, nan fara'an Yakumbo ya fad'ad'a, Ayya 'yan nan, Oh haba Safwanu ai sai ka fada mun zaka kawo mun sirkar tawa sai innshirya mata wani abin, Safwan ya dan murmusa kafin yace" ai bazata dama naso na mako. Haba nan fah Yakumbo ta mik'e ta shiga lalume a shirgin d'akinta tana neman abun bawa Yussy.
"Duk wani iskanci Yussy yau saida ta sarawa Safwan, yanzu duk kud'in da yake samu amma jibi yanda yabar uwarsa lallai Safwan bashida imani, ko wutar lantarki babu balle ruwannlayi..ai kuwa duniya zata koya masa hankali, haka kurum Yussy ta sauk'o dan kanta ta shiga nan da Yakumbo dan tsohuwar ta bata tausayi, ace tanada d'a kaman Safwan ya banzantar da ita haka, ta d'au alwashin taimaka wa Yakumbo koda Safwan baya so.....








*England, Manchester*
"Tunda tayi aman nan jikinta ya soma karkarwa tana rawan d'ari, ga mamakinta tana lek'a window taga snow na kan sauk'a, ko shakka babu lokacin winter ne wato yanayi na sauk'an k'ank'ara, Sanyi ya dameta banda rawan d'ari bata komai gashi har lokacin Irfan bai dawo ba, haka ta yaye bedsheets ta hada bedcover duk ta tak'ure ciki amma konkad'an sanyin bai ragu ba. Duk addu'an da yazo bakinta yi take Allah ya kawo mata d'auki.




"Sun jima sosai cikin Conference hall din *Abdullah Musa Construction Company* suna gudanar da meeting din, jin an kukkunna heaters ya tabbatr masa k'ank'ara ya soma sauk'a, Alla alla yake su k'areshe meeting din yaje ya dubata.
"Alhj Abdullah sosai yaji dad'in meeting dinsu da Irfan, yaso ya bisa gidansa yayi introducing nasa ma familynsa amma Irfan ya gwada saidai wani lokacin zaije insha Allah, dole alhj Abdullah ya hak'ura musamman da ya gane shi Irfan d'in was on a hurry.


"Kai tsaye boutique ya shige yanda yayi masu sayyayan kayan sanyi dangin su booth sweater da sauransu, sauri sauri ya baro boutique din ya nufi hotel d'insu.
"Shi kansa rawan d'ari yake sanda ya shigo parlorn ya tarar bata parlor, da sauri ya nufi bedroom can ya ganta k'udundune kan gado.......






Sameena ceπŸ‘ŒπŸ½


πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin Waye*




83


*©Sameena Aleeyou......✍🏽*


_Queen Samy Novels Forum.....πŸ“–πŸ“š_




*#TEAM IRFANDEE*




"Wurgi yayi da ledojin dake hannunsa cikin sauri ya k'araso gamida yaye bargon, ji yayi ta k'ank'anme bargon sosai, da sauri ya mik'e gamida kunna room heater, kafin ya dawo ya soma k'ok'arin d'agata ji yayi jikinta zafi sosai alamun zazzab'i, kayan jikinta har kamannsun jik'e da hazo dan sunyi damshi zab'an sanyin da ake rapkawa, cikin sauri ya mik'e ya nufi ledojin daya shigo dasu ya d'auko kayan da ya sayo,
"Dawowa yanda take yayi kafin ya soma kiciniyar rabata da kayan jikinta, dukda azaban da take sha hakan bai hanata rik'e hannun Irfan gam ba, alamun kar ya cire mata kaya,.. "D'an fuzar da iska yayi kafin yace" can't you see you're freezing and you're having a fever, and kayan jikinki ya jik'e, wann sanyi ba kalan sanyi da kika saba dashi bane, bai kuma saurarenta ba ya soma zame rigarar jikinta idon Irfan ya sauk'a daidai k'irjinta" Ya Salam, gaba d'aya ya susuce ya kasa d'auke idanunsa daga kallon k'irjinta, tunawa yayi yanzu fah wani banza wofi ya rigasa ganin jikin Deejah ya rigasa sanin Deejah,... "Wani irin kishi da takaici su suka tokare mak'oshin Irfan, ji yake da zaisan mutumin nan shakka babu da ya aikasa lahira. Da sauri ya zura mata rigar da ya dauko gamida d'aura mata wani tapkeken jacket a saman had'i da wani kakkauran hula , nan da nan ta soma jin d'umi. Idonsa ya sauk'a kan plate d'in abinci ko tab'awa batayi ba, haba no wonder zazzab'in nata yayi yawa,
"Mik'ewa yayi ya k'arasa gaban plate d'in yana kallon yanayin abinci, gajeren tsaki yayi a fusace ya fice ya nufi reception.


"Receptionist ya tarar ya soma balbaleta da masifa dan Manager dinsu ya tashi dashi ya samu, fad'i yake" You all don't know your job, how comes I told you something to do you did something different, manyan chefs din restaurant nasu suka karaso suka soma bawa Irfan hak'uri, Sorry sir, it won't happened again, it's just a misunderstanding.
"Gajeren tsaki kawai yayi dan sunyi mugun b'ata masa rai, saida yace masu kar su saka spices a abincin da yayi placing wa Deejah su kuma suka saka dashike sun saba. Dayan ya karaso kaman zai durk'usa yana bawa Irfan hak'uri dannsunsan akan haka sai su rasa aikinsu,
"Girgiza kai kawai yayi kafin yace" it's okay but be careful next time don't repeat same mistake. Cikin murna suka soma gyad'a kawunan su suna godiya,


"Kai tsaye ficewa yayi ya sayo mata magani snn ya biya wani bakery ya saya mata meatpie da cake, sanda ya dawo tana bacci bai tasheta ba saida ya had'a mata kakkauran tea kafin ya k'arasa ya d'an zauna gefe da ita.
"Kallonta yake kan yi yana nazarin abubuwa da dama, video na bluefilm din nan ya tuna take yaji tsanarta na cika zuciyarsa. Baisan sanda ya daki sidelamp ba saida ya tarwatse....
"A firgice Deejah ta mik'e tana muzurai, gani tayi hannun Irfan jini na zuba yanda ya daki sidelamp din da hannunsa yaji masa ciwo, da sauri ta nufo sa tana fad'in" You're bleeding me ya sameka, does it hurt????..... "Dubanta yayi yanda yaga duk hankalinta ya tashi, mik'ewa yayi da sauri kafin yace ga snacks da tea maza kici ki sha tea din and take your prescription daga haka ya fice daga d'akin yana rik'e da hannunsa.


"Kallo ta bisa dashi har ya fice, sauk'e ajiyan zuciya tayi tana mai tambayan kanta kardai har yanzu son Irfan take, kallon sayyayan da ya mata tayi kafin ta dauko da sauri ta soma ci sabida dama yunwa takeji.....




"Juyi kawai yake a parlorn ya kasa runtsawa, idan ya rufe ido jikin Deejah yake gani na masa gizo, wani irin mugun sha'awarta yake ji, shi a halin yanzu babban burinsa shine ya kasance da ita, throw pillow ya dauko gamida danne kansa ciki had'i da yin tsaki, he just couldn't control himself, yana cikin yanayi na tsananin buk'ata, kan kace me marar sa ta soma masa ciwo, innalillahi wa inna'ilahirraji'un yau ya jangwalo wa kansa ya gano abinda yafi k'arfinsa, toh wai shin sonta ne yake har yanzu kokuwa sha'awarta yake, meyasa har yanzu ya kasa mata duk wulak'ancin da ya tanadar mata, meyasa a kullum yake dad'a jin son kasancewa tareda ita. Wata zuciya tace k'ila dai sha'awarta kake, ka tashi kaje ai matarka ce, wata zuciya tace waya sani koma tanada cututtuka tunda tayi yawon banza yawon club.
"Haka kurum kuma wata zuciyar ta shiga raya masa lafiyar Deejaj k'alau kaje wa iyalinka.... "Da k'yar a galabaice ya mik'e ya nufi bedroom d'in.


"Cikin bacci take jin nishin mutum a kunnenta, da sauri ta soma k'ok'arin mik'ewa dan ya soma rabata da kayan jikinta... "Nan ma kokawa suka shiga yi da iya k'arfinta take turesa tana fad'in" Me zakayi da karuwa me kwanan club baka tsoron cututtukan zamani ne...."Matse ta yayi cikin jikinsa sosai tana jin yanda numfashinsa ke fita da sauri da sauri, a kunnent yake rad'a mata " Taimakon zanyi prostitute, na fad'a maki ni Irfan Mumtaz bazan tab'a kusantarki dan biyan buk'atata ba saidai na taimaka maki, kan ta ankara saiji tayi ya sakala harshensa cikin bakinta, tun suna kokawa har ta saduda ta mik'awa Allah lamarinta.... "Tabbas idan yana tareda Deejaj ko shakka babu hankalinsa gushewa yake yi "k'aran ringing d'in iPhone d'insa ne yayi distracting nasa, jin haka yasa Deejah yunk'urin tashi amm inaa ji tayi ya rik'ota gam, Azee ce mai kiransa yana da'aga wayan Azee ta hau masa kukan shagwab'a lokacin tayi d'ad'aya jikin Ahidjo, da ace Azee tai masa farin sani tabbas da ta gane yanayin da yake ciki, murya a daddashe yake amsata har lokacin bai daina wasa da albarkatun k'irjin Deejah ba, sosai ya danne ta da k'afafunsa hannunsa d'aya na sakale da waya d'aya na kan boobs d'inta.
"Ga mamakin Azee jinsa tayi cikin farin ciki da annashuwa, nan ta zak'e sai zuba masa shagwab'a take harda cewa kar ya kwana d'aki guda da Deejah bata san yanzu hakama a jikinta yake ba, itama Azeen jikin Ahidjo take dan yau tildown zasuyi.
"Da gayya Irfan yayita fad'an kalaman soyayya ma Azee alhalin yana kwance da Deejah, tasan duk hakan dan ya b'ata ranta ne, ai kuwa ji tayi kaman ta kurma ihu dan takaici.
"Suna gama waya da Azee yaci gaba da sarrafa Deejah kuka kawai take sharshar da hawaye.
"Haka kawai taji ya mik'e ya nufi bathroom batasan me ya tuna ba amma taga yana murmushi.


"Yana shiga bathroom din ya fad'a jercuzy, yana mai murmushin mugunta, tsaf yasan abinda zaiyi ma Deejah, har shine zata nuna masa tsoron namiji take bayan tasan maza iri da kala, zai shirya mata zai koya mata hankali, da sannu zata gane kurenta, saida yayi wankan tsarki yayi alwala kafin ya fito dan shiryawa, sanda ya fito bata nan yasan bai wuce tana parlor ba, dan haka shiryawarsa yayi kafin ya fice parlorn, tana ganin ya fito ta mik'e da sauri ta nufi bayan kujera, ko takanta baibi ba ya tada sallah, tana ganin haka tayi saurin shihewa daki harda saka key kafin ta shige bathroom dannitama dole tayi wanka...


"Washe gari bata san yaya akayi ya bud'e dakin ba hala yanada spire key ne, dan taji alamun anyi wanka a toilet din, yana shiryawa ficewa yayi dan yasa a kawo mata breakfast kuma ya masu warninh kar su sake bata abunda bazata iya ci ba, ...




"Yau ganawarsu da Chairman na *AA. Musa construction company* harda wasu bak'in turawa yanda Irfan ya wakilci company d'insu wato *M&M Builders* ganawar tai masu dadi sosai yanda duka company biyu din zasu samu alfanu sosai, Alhj Abdullah haka kurum yaji aiki da Architect Irfan Mumtaz ya kwanta masa da da dukkan alamu yaron akwai hazak'a, mahaifinsa yayi dacen samun d'an arziki irin Irfan.


"Architect yau dai ya kamata ka bini ku gaisa da family na, I'll be glad if we had lunch together, cewar Alhj Abdullah, murmushi Irfan yayi kafin yace "Okay Mr Chairman I can't reject your offer yau kam, I'll meet them insha Allah. Da murnan sa ya shiga yiwa Irfan godiya.. bud'e masa gefen Alhj Abdullah driver yayi kafin suka nufi gidansa.






"Yaran sunajin k'aran tsayuwar mota alamun dad dinsu ya dawo suka fito a guje suka nufo waje, kaman yanda suka saba haka suka soma hayewa jikin mahaifin nasu yana wullasu sama, sosai suka burge Irfan, shi mutum ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login