Showing 9001 words to 12000 words out of 159062 words

Chapter 4 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10401

'karfi..." A'a me yayi tsanani zan fice...." daidai nan Hajiya Karima tayi sallama ta shigo, kallon hadarin kaji Hajiya Karima tabi Yakumbo dashi kafin tace" 'Dan nasuma ya mace bazasu barki ki huta da jaraban tsiyaba., tayi maganar tana duban Laila, ta'be baki Laila tayi tace wllhi ko Hajiya dama isowarki nake jira, wnn matan tazo sai cikani da hayaniya take...." Yakumbo ta girgiza kai kafin tace" Karima ku kiyayi duniya keda 'diyarki...." A hasale Laila ta matso ido a tsefe take duban Yakumbo kafin tace" Ke tsohuwar banza karki yarda ki gaya wa uwata magana dan yanzu zan iyar watsar maki da hak'ora a nan...." Hajiya ta ri'kota tace" 'kyaleni da ita, ni na isheta... 'gyalen kanta Hajiya ta cire tace Shege ka fasa..." Girgiza kai kawai Yakumbo tayi kafin tace" ni bazanyi fa'da daku ba, ai kun tari fa'da da wanda ya fi 'karfin kowa yake iko da kowa, wnn fa'da kuka tara da mahallicin mu, tinda shi ya 'diba wa mace kwanakin da zatayi na idda, kunga kuwa dan kunce zakuyi fa'da dani ai bana mamaki ba, duniya tsaf xata koya maku hankali dan kuwa _Tafi gabaruwa iya jima_....." Dangin mayu kwa'dayayyau ana jira uban 'yata ya mutu aci arziki toh sai 'dan naku ya riga mutuwa, babu yanda zaku sami gadon 'yata shine kuke ba'kin ciki da hassada, dan mayunwata, idan banda 'kaddara da rabo mema zaisa 'yata ta auri 'danki. Cewan Hajiya cikin masifa da bala'i.... shigowan Aziza ne tana sanye cikin uniform din makarantar ta yasanya Hajiya yin shiru. Da gudu Aziza ta tafi ta rungume Hajiya tana fa'din Hajiyata yaushe kika zo. Hajiya ta wani rungume Aziza tace 'diyar Hajiya an girma an kusa zama 'yar jami'a ko aure zakiyi... Aziza ta tsoke baki tace " Tab wani aure ai sai naci duniyata da tsinke ko yaya kikace mum....Yakumbo na murmushi tace" yaki uwata.... wani harara Aziza ta wurga wa yakumbo kafin tace" Mum tace ke mayya ce ke kika cinye daddy na, ki fice mana a gida kafin muma ki cinyemu. Da mugun al'ajabi Yakumbo ke kallon Aziza wasu hawayen takaici na zubo mata. Girgiza kai tayi tasa kai zata fice, Hajiya tace " wuuu ashe abin haka ne toh kuwa kurwan 'yata da jikata kur kije can ki 'karaci maitanki gwara da Allah yasa ya tsaya akan 'danki dan kunfi kusa.... Yakumbo kam bata iya 'karasa jin zantukansu ba dan kuwa juwa ta soma gani, wnn shine a dake ka a hanaka kuka....


"Tana zaune tana tunanin ta yanda zata samowa Amma nanny wato me raino, tayi tunanin duniya ta rasa wacece zata kai mata, wani tunani ya fa'do mata ga Deejah tunda Deejah akwai son yara tasan zata iya. Murmushi tayi ta mi'ke ta soma aikinta cike da 'kwarin gwiwa.


"Da yamma lis, yau Deejah a gajiye take dan yau sun gyara ko ina a orphanage sun share sunyi sanitation, Anty Larai ta dubeta tace 'diyata akwai maganar da zamuyi, da zumu'di Deejah ta mi'ke tana fa'din toh Momy Larai na matso knn kar su o'o sujimu dagaji abun 'yar sirri ne, Anty Larai ta kai mata dukan wasa tace ja'ira me hali baya canzawa. Dariya Deejah tayi tace ina sonki Anty larai, Anty larai ta rungumeta tace nima ina sonki. Gaba daya mutanen wajen suka sa dariya. Baaba Saude tace uwa da 'ya sai Allah, kowa yasan irin sha'kuwan da Anty Larai tayi da Deejah a gidan marayun nan.


"Bayan Anty Larai ta gama yawa Deejah bu'katan ta, Deejah jiki a sanyaye tace" Anty dama zaki iya kaini aikatau gidan wasu, Anty na 'dauka tamkar 'ya kika 'daukeni...." Anty Larai ta ri'ko hannayen Deejah tana girgiza kai tace" ko ka'dan ba haka bane daughter, kinsan ina sonki snn bazan ta'ba maki abunda zai cutar dake ba, Deejah ba aikatau nake niyyan kaiki ba, gidan matar da zakije mata ce me mutunci da sanin darajan _'Dan adam_ ko ka'dan bata wula'kanta mutane ko talaka ne ko me ku'di, Deejah kinsani idan kina zaune a nan Orphanage bazakici gaba da karatu ba kaman yanda kike da burinyi, kinsan nan dawasu lokuta za'a soma maki maganar aure, sa'anki 'daya kina koyar da yara amma da tuni anyi bikinki. Deejah kinsan da inada halin saka ki a makarantar gaba da sakandare da nayi amma babu hali, kinga kuwa gidan da zakije na tabbata zasu sakaki, idanma basu sakaki ba zaki samu da ku'dinki na aiki ki soma karatu, Deejah kar ki mance burinki na tallafa wa marayu wa'enda suka taso a irin rayuwar da kika taso, baki sani ba 'kila wann shine damar da kika samu.
"Deejah ta sau'ke ajiyan zuciya tace" na fahimce ki Anty Larai na kuma amince zanyi, toh amma wani hanzari ba gudu ba, idan organization suka tambaya me zaki ce masu. Antu larai tayi murmushi tace wnn duk me sau'kine dama a samu amincewarki shine me wuyan, zan ce masu nayi adopting dinki zaki cigaba da rayuwa a gidana, zaki bar zaman Orphanage, nasan mutanen da zaki zauna dasu bazsu ta'ba cutar dake ba sai alkhairi. Abunda yasa na za'beki shine kinfi kowa ilimin addini dana boko a gidan nan, kuma jikokin matar daga America suka dawo so suna bu'katar me kula dasu wacce tasan addini da al'adunmu. Deejah tayi mur ushi tace tab yo ni wani al'adunmu na iya, Anty larai ta jefa mata harara tace " wllhi saura kije kina masu halin naki keda ni ne... dariya Deejah tayi tace shiknn Antu Allah ya wuce mana gaba... ameen anty larai ta amsa....




"Kwana biyu da faruwan wnn al'amari Anty Larai ta kai Deejah ma Amma a matsayin Nanny din da ta samo mata, sosai Amma taji da'din hakan, Deejah kuwa tun daga waje take bin gidan da kallo, a ranta tayita ayyana dukiya na mutanen nen, ashe Anty Larai tasn mutane nsu ku'di irin haka.
"Anty Larai seda tayi nasiha sosai wa Deejah kafin ta tafi barta, Amm da kanta ta nuna wa Deejah dakinta kusa na Nadiya, ba'a kai Deejah sashen ma'aikata ba cikin gidan aka barta, tundaga nan su Hajja suka gane lallai Deejah ta sami kar'buwa wajen Amma.


"Misalin 'karfe 2:00pm suka soma shigowa alamun sun dawo daga sch. Amma ba zaune a parlor suka soma hayewa jikinta, Amma ta rungumesu tace Kids albishirinku, yaude an kawo maku Nanny... Gaba 'daya sua mi'ke suna fa'din Patricia ta dawo Patrica ta dawo. Amma tace no ba Patricia bace I know you guyz will like her more than Patricia, a tare suka ha'da baki wajen cewa " whare is she.......basu gama rufe baki ba Deejah ta sau'ko daga stirs fuskanta rufe da mask din Dora... Kai tsaye wajen Nilam Amir da Aiman da sukayi tsaye suna kallonta ta wuce ta shiga wasa da yatsun hannunta gefen fuskanta take fa'din" Hello kids here I am, nice to meet you guys, ta mi'ka wa Nilam hannu tace " I'm Deejah and you..... Kallonta kawai suke Amir da Aiman sun wani har'de hannu a 'kirji suna kallonta, Amma kuwa sosai abun ya mata da'din ganin Deejah ta iya zama da yara.... Kuka Nilam ta saka a guje ta haye jikin Amma tana fa'din" I don't like her, she's annoying I don't like Dora too, ni Baabi nake so not Dora. Aiman da Amir suka kalli juna suka furta" this is rubbish gamida tura baki gaba. Deejah kam kasa motsowa tayi daga yanda take sai kallon mamaki data bisu dashi, daidai nan Engr yayi sallama ya shigo.... Ai da gudu Nilam ta fa'da jikinsa tana kuka, Amma kam dan takaici mi'kewa tayi ta haye sama.
"What's wrong my Precious, Engr ya fa'di sanda ya 'dagota, Aiman da Amir suka kuma kallon juna kafin suka maida dubansu ga Deejah da tayi mutuwan tsaye tana kallon Engr da Nilam. A tare suja maida dubansu ga daddynsu da Nilam dake ta faman zuba masa shagwa'ba,
"Angek what's wrong, what happened to you, why are you crying my baby.
"Amir yace" that's monster makes her cry.... ya 'karashe maganar ya nuni da Deejah dake tsaye tamkar gunki.... Shi kansa Engr saida ya razana da ganin Deejah sanye da mask din nan. A daburce Deejah tayi saurin cire mask din kafin tace" Sannu da zuwa Sir..... Kallonta Engr keyi babu ko kyafta ido, her face looks familiar to him, bai iya amsa mata ba sai kallon da ya bita dashi..... Ita kanta Deejah ta tsargu da kallon da Engr yabita dashi tayi saurin gyara tsayuwanta dan kuwa mutumin Allah ya masa 'kwarjini, sadda kanta 'kasa tayi kafin tace" ni... ni ce sabuwan Nanny da aka kawo masu.
"Murmushi Engr yayi kafin yace" Alright I see, pls ki ringa kula da abunda suke so da wanda basa so, especially this little Angel that I'm holding ok.... da sauri Deejah ta gya'da kanta kafin tace " Ok Sir zan kiyaye. Aiman ya ri'ko hannun Nilam yace" Daddy you came back so early today. Gya'da masa kai kawai Engr yayi yace oya ku wuce upstairs ina zuwa ko, babu musu yaran suka wuce gaba 'daya.
"Deejah dake tsaye sai faman 'kirga 'yan 'yastun hannunta take, Engr ya sake dubanta a karo na biyu ya rasa gane ina yasan me irin fuskanta, bai kuma cewa komai ba ya fice ya wuce side 'dinsa.
"Aiko yana wucewa Deejah ta sau'ke ajiyan zuciya tace " wai Allah wann wani irin mutum ne haka. Da sauri tahaye sama wajen yaran.


"Da daddare suna zaune bisa dinning ana dinner, Aiman ya kalli Nadiya yace" Adda Nadiya gues what, Nadiya ta 'dan hararesa tace you I don't like guessing games, just go straight to the point jor. Amir yace" Our new Nanny is finally here. Nadiya ta ajiye spoon 'din hanunta ta kalli Amma tace" Amma da gaske ne. Nilam ta turo baki tace" I don't like her, she's annoying. Mikewa Nadiya tayi tace" where is her room..... bata gama rufe baki ba Aiman yace" Next to yours......." What!! Nadiya ta fa'di kafin ta soma girgiza kai tace" that can't be, I can't stay under the same roof with a maid,..... " Rufewa mutane baki, Amma ta katseta, sabida ita ba mutum bace, toh barikiji na fa'da maki tare zamu fara cin abinci akan this very table, idan kinsi kar ki zauna a gidan babu canza 'dakin da za'a mata..... " Baki a ture Nadiya ta wuce fuuuu tayi hanyan sashen Engr.
"Yana zaune gaban laptop 'dinsa tayi knockn a kofa, yana bata izinin shigowa kuwa ta shigo tana kuka gamida bubbuga 'kafa. Da sauri Engr ya ture laptop 'din gefe yace" Sweedy what's wrong, waya ta'ba mun ke...." Daddy for goodness sake nayi kama da wacce za'ace ta zaune 'daki kusa da maid, haba Daddy..... shiru ya 'danyi kafin yace" Sweedy this is Amma's decision, let her be, babu komai a ciki, besides nan ya kamata ta zauna sabida kulada Nilam. Har lokacin bakin Nadiya na nan a ture, but daddy.... ringing din da wayansa yayi ne ya katseta. Yana 'dauka yace " Architect how you doing,
"Daga 'daya 'bangaren Irfaan yace" daddy am doing great, nan suka soma gaisawa da daddy, Nadiya tasan wayan daddy da Irfaan baya 'karewa dan haka badan taso ba ta wuce.
"Tana komawa 'dakin Deejah ta banke 'kofan tashiga binta da kallon 'kas'kanci kafin tace" let me make this clear to you, ko Patricia ma bata zauna next to my room ba har ta 'karashi zamanta balle ke, barin fa'da maki first thing tmrrw mornin ki tattara ya naki ya naki ki tafi fannin ma'aikata. Daga haka Nadiyata fice kaman zata tashi sama.
"Kallo Deejah tabita dashi har ta shige, ...." Tab'di jam lallai ni Deejah inada aiki ja a gidan nan.
"Wayanta dake ajiye saman gadonta ya soma ringing...... Yusra ce me kiranta, da sauri ta 'daga, " Yuseee na ina missing dinki.
"Yusee tace" Deejah knn tafiya babu ko sallama, ai se ki jira na dawo daga sch kafin ki tafi amma kawai naji wai kin koma gidan Anty larai.
"Deejah tace" Yusee tsaya kiji wllhi ba haka bane, tafiyan ne tazi a haka, akwai labari me yawa, zan kiraki da safe sai mu tattauna. Yusra tace toh shiknn sai najiki, ya batun club fah. Deejah tace shima zamu tattauna akai, nasan anjima ka'dan safwan zai kirani so zan kashe wayata, pls idan ya kiraki kisan abunda zaki fa'da masa kadin muyi waya gobe.
"Yusra tace toh shiknn Allah kaimu, Deejah ta amsa da Ameen kafin tayi hanging up...




"Duk iya 'ko'karin Deejah ta samu kar'buwa a wajen yaran Engr abu yaci tura, tsangwama iri da kala take gani,.
"Yau Saturday basuda sch, suna zaune a gardeen ta fito tana son zuwa wajensu tana tunanin abunda ka iya zuwa yazo, rufe idonta tayi ta fuzar da iska kadin tace" Deejah you can do this, you can do it.... murmushi tasa a saman fuskanta kafin ta 'karaso tace " Hi everyone, Amir da Aiman suka bar wasan da suke suka 'dago ido suna dubanta, sanye suke cikin wata riga iri 'daya an rubuta problem maker da manyan harufa. Amir ya 'karasa yayi ra'da wa Aiman a kunne kafin suka sa dariya, Nilam nata 'ko'karin gyara hannun toy dinta daya fice ta kasa ta mi'kawa Nadiya dake faman charting da wayarta ga earpiece manne a kunnenta tace" Adda pls will you fix my toy..... " Nadiya ta danyi tsuka, Nilam ta dad mika mata tana bubbuga 'kafa.... " Tsaki Nadiya ta kuma tace" what's this Nilam, you knw I hate distraction. ?.. pls Adda Nadiya Nilam ta kuma fa'di. Tsaki Nadiya tayi ta mi'ke ta bar wajen.
"Zata wuce Deejah ta watsa mata wani mugun kallo tace" am gonna make this house a living hell to you..... daga haka ta wuce abunta.
"Deejah ta 'karasa wajen Nilam dake wasa da toy dinta tace" hello Angel, kallonta Nilam tayi kafin ta kau da kai, hannun doll baby dinta daya dita taketa 'ko'karin maidawa, Deejah tayi murmishi tace lemmi fix it for you. Nilam tace " go away I hate you..... Deejah ta 'dauko wani hanki na Baabi ta mi'ka mata tace" you like this, da sauri Nilam ta kar'ba tana murmushi tace" yeee ina son wnn, Deejah ta mi'ka mata tace" ok kawo toy din naki na gyara maki, babu musu Nilam ta mi'ka mata. Ai kiwa nan ta gyara mata. Sosai Nilam tayi murna harda 'dan tsallenta kafin tace " thank you Deejah,... Deejah tayi murmushi ta mi'ka mata hannu tace " Friends, Nilam ma ta mi'ka mata tace yes friends..... Daidai nan su Aiman da Amir suka taho da ruwan foster color da suka gama coloring drawing dinsu suka she'kawa Deejah a jiki.....




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.........
[8/19, 06:22] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ–πŸŒ— *Mallakin waye* 08


_Written by QueenSamy_ .........✍🏻




"Daga ganin yanda yake mammatse ido zaka gane hasken ranan tai masa yawa be saba ba, hannu yasa a lajihun wandonsa kafin ya ciro cellphone dinsa, lambar daddy ya soma dialing, yana cikin latsawa ne ya hangi mahaifin nasa fuska dauke da murmushi.
"Rungumesa Engr yayi yace" welcome home my son, Irfaan da murmushi yace" thank you daddy, I thought bazaka gane ni ba, murmushi Engr yayi yace" ai baka canza ba Irfaan though ka 'kara girma da 'kwarjini.... Irfaan na murmushin sa mai class yace I take after you daddy. Daidai nan driver yazi ya kar'bi luggahe 'din Irfaan yana masa sannu da zuwa kafin ya wuce dashi mota, Engr ya ri'ko kafa'dun Irfan yana fa'din lets get goin son.... idan ka gansu kaman wa da 'kani haka suka nufi motan.


"Amma kawai suka samu a parlor dan gaba 'daya yaran basa nan sun tafi makaranta. Irfaan yana ganinta ya 'karaso da sauri ya rungumeta yana fa'din" Granny.... rungumesa itama tayi murna fal ranta, take hawayen farn ciki ya soma zubo mata, Irfaan ya 'dago kanta ya soma share mata hawayen kafin yace" why those tears Amma na, come on your husband is here, ko duk kukan misssing dina dinne. Murmushi tayi ta saka hannunta cikin gashin kansa kana tace" Irfaan dole nayi kukan farin ciki, kalla yanda ka girma ka zama cikakken saurayi me kyau, yau burina ya cika gaka a 'kasarka Nigeria, our family is complete again. Maza muje kaci abinci da kaina na girka maka. Hannun Amma Irfaan ya ri'ko yace" I luv you Amma, zanci abinci but sai nayi wanka, whare are my siblings?
"Amma tace suna sch anjima ka'dan zasu dawo, yaumda kyar suka tafi jin yau zaka dawo, Amma ta ri'ko hanunsa tace muje na kaika sashenka, babu musu yabi bayanta. Engr ya kallesu da murmushi saman fuskansa, jin son 'dan nasa yake kaman ya maida shi cikinsa...


"Tunda suka dawo aka ce masu Irfaan ya iso haba zo kaga murna, Nilam ta 'dauko family pic dinnda tayi drawing musamman wa Irfaan zata kai masa suka ha'du da Deejah a stirs, Deejah ta mi'ka mata hannu suka tafa kafin tace Angel sai ina, Nilam ta nuna mata drawing din tace zan kai wa ya Irfaan ne. Deejah ta gya'da kai tace good, ki gaishe shi ko. Nilam tace muje kema ki ganshi su Adda Nadiya dasu Amir duk suna sashena harda Amma ma. Deejah tayi murmushi tace kije Angel zanyi laundry yanzu ne ok, anjima zan gaisa dashi. Nilam tayi nodding kanta kana ta wuce...




"Duk sun zagaye shi suna faman zuba surutu, to be honest shifa bai saba da wnn hayaniyan ba, ya saba zama shi ka'dai a gida, gashi yau ya tarar da hayaniya, shi bacci ma yake ji. Nilam ce ta shigo da gudu ta haye jikinsa.... rungumeta Irfaan yayi yace" oh Angel is that really you... ya fa'di yana zaro ido waje, you're so pretty. Nilam tayi dariya tace welcome yaya. Rungumeta ya da'da yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login