Showing 27001 words to 30000 words out of 159062 words

Chapter 10 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10403

hanunsa bisa madaidaicin center table din dake parlorn.
"Yaya na kawo maka abinci ne, Ruqayya ta bida,
"Kai lil sis da kin kyauta kuwa dan na kwaso yunwa sosai, cewan Sadiq. Da sauri Ruqayya ta wuce kitchen dan hada wa Sadiq abincinsa.
"Mami ce ta shigo parlorn sanye da hijabi da alamun sallah da ida, Sadiq an dawo, ta fadi sanda take zama bisa sofa... mikewa yayi daga kishingi'dan da yayi yana murmushi yace " eh mami na dawo, nan suka gaisa mami tace Allah sa dai an dace.
"Gyara zamansa yayi sosai kafin yace" mami Allah ya amshi addu'an mu, daga ziwana aka bani mu'kami mai tsoka, Mami ta daga hannu sama tama Allah godiya, kai Alhamdulillah masha Allah, Allah na gode maka, Allah ya wuce maka gaba a wajen aikin ka, inama yau babanka na nan da yafi kowa farin ciki, matsowa Sadiq yayi kusa da mami ya ri'ke hannunta yana girgiza mata kai alamun kar tayi kuka... Daidai lokacin da Ruqayya ta ajiye masa tren abinci a gabansa...." 'Karan da suka jiyo daga 'dakin Dada ne yasa su rugawa duka a guje suka nufi 'dakin,
"Zaune suka sameta ta ta'kure jikin gado tana rungume da 'yar tsananta da tun tsintarta da sukayi da 'yar tsanar suka tsinceta. Da'da rungume 'yar tsanar tayi sanda mami ke 'ko'karin matsowa kusa da ita ta soma fa'din" Kar ku zo nan kar kuzo zasu 'kwace mun 'diyata, ta da'da matse ta cikin jikinta nan ta kwanta rungume da 'yar tsanar ta soma fa'din" sleep sleep my baby, my baby da haka har bacci ya 'dauke ta...." Su mami Ruqayya da Sadiq zukatansu cike da tausayin Dada, Allah sarki jinyar hauka ba 'karamin jarabawa bace, Ruqayya ta 'karasa ta gyara mata kwanciyarta dan jin sanyi ya sau'ka a garin alamun ruwa na zuwa. "Mamie ta dubi Sadiq tace" Sadiq kana ganin bazamu canza mata asibiti ba,
"Sadiq ya jinjina kai yace ba laifi idan muka canza amma ni a ganina mu dage mata da na islama, Mamie tace hakane Allah ubangiji ya bata lafia, Allah sarki ko shekaru nawa tayi cikin jiyar hauka sai Allah.
"A parlor Sadiq ya ha'du da Ruqayya, murmushin da ita ka'dai tasan fassaransa ya sakar mata, sunne kai tayi tana mai mayar masa da murmushin itama, takardun saman center table ya nuna mata ba tareda yace komai ba, kallon takardun take taga anyi approving masa aiki, murna sosai tayi ha'di da jero , asa addu'o'i.
"Wnn kyakkyawan 'dabi'a na Ruqayya na burgesa sosai, hakan nema yake ji bazai iya rayuwa babu ita ba, shi ko ka'dan kyau bai damesa ba, kyawawan 'dabi'u sunfi burgesa.
"Kallonta yake yana jin tsantsan sonta har cikin ransa.




"Sosai hankalin Irfaan ya tashi ganin motan ta shiga danger, besan me ya sami motarsa ba shan mai take sosai kwana biyun nan, a hankali ya furta ya salam, dole ya nemi hefen titi yayi parking.
"Deejah da hawaye suka soma zarya a fuskanta juyowa tayi tana masa mugun kallo kafin tace "Ina ne nan?
"Irfan da ransa ya gama jagilewa gaba 'daya ko kulata beyi ba ya ciro wayansa "unfortunately babu chargi, " Shit" ya fadi gamida buga starry da hannunsa....." Ruwan sama ne ya soma zubowa tamkar da bakin 'kwarya....




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹.........
[8/19, 06:25] Umar Dalha: πŸŒ“πŸŒ“πŸŒ”πŸŒ” *Mallakin waye*


19




"Kifa kanta tayi kan cinyarta kuka na shirin kufce mata, Irfan ya 'dan kalleta tausayinta ya kamasa, ji yake dama gida ya soma kaita duk da haka bai faru ba, so yake ya lallasheta but besan ta yaya zai soma ba.
"Dekewa ya danyi da kyar ya iya furta" muga wayarki. "Ba tareda ta dago ba tace ai ban fito da waya ba,
"Tsaki ya kumayi a hankali, daidai lokacin da kuka ya kufcewa Deejah, ko kadan Irfaan baison jin kukan nata, it hurts him sosai, cikin 'kulewa yace" will you shut your trap! Kin cika wa mutane kunne. Ko saurarensa bata yi ba balle ta tanka sa,
"Kinsan Allah idan bakiyi shiru ba zaki fice mun daga mota, kaman bada ita yake ba haka tayi, tsaki yayi gamida bude kofar motan ya fice duk da ruwan da ake tsulawa, ya zagayo mazaunin Deejah. To her greatest surprised bu'de marfin motan Irfaan yayi ya fincikota waje yace" idan kin gama kuka let me know, daga haka ya zagaya ya shige cikin motarsaw.
"Banda tsanar Irfan babu abunda Deejah keji, lallai ma yaron nan sai ta koya masa hankali ta yanda gaba ko hanya bazai ha'da da ita ba.
"Kallonta yake ta miro ta takure cikin hijabinta ga ruwa na lugude a kanta, runtse idonsa yayi bazai iya ganinta a haka ba,Oh Shit shit! Ya fadi yana mai dukan starry da hannunsa. Ganin Deejah ta soma tafiya yasa Irfan saurin bude motan yana fadin" My goodness ina kuma zataje, gabanta yasha yana mata mugun kallo yace ina zaki." Zuciyanta na tafarfasa take fadin" wai miye ruwanka dani, me nayi maka da tsanani, idan akan so called project dinka ne, na baka hakuri, let me be pls ka fita harkata pls. Bai saurareta ba ya fizgo hanunta ya bude mota ya jefata ciki.
"Kallonta yake yanda take rawan dari duk sai ta basa tausayi, kauda kansa gefe yayi bai kuma cemata komai ba, dukansu biyu da abunda suke sakawa a zukatansu. Har wajajen karfe shida na yamma kafin ruwan ya tsagaita, da sauri Irfan ya fito ya shiga sawa motoci hannu alamun su tsaya amma babu wanda ya kulasa, sosai hankalinsa ya tashi ga duhu ya soma yi....




"A can gida kuwa hankulansu ya kai kololuwan tashi izuwa yanzu, wayan Irfan baya shiga ga wayan Deejah a gida, Nilam kuwa sai kuka take a kaita Deejah, gaba dayansu hankalinsu ya tashi, Engr kusan wuni yayi a station babu labarin Irfan da Deejah, abu kaman wasa har dare yayi babu su Irfaan.


"Crackers da bottle water dake a back seat din motarsa ya dauko ya mikawa Deejah, babu musu tasa hannu ta karba nan ta dinga rusawa dan kuwa bakin yunwa ne ke azalzalanta, sosai Irfan ya tausaya mata ganin yanda take hadiyan crackers din nan.
"Bayan ta gama ci ne taga yana folding hannun rigarsa, kaman bazata masa magana ba sai kuma tace" me zakayi, ba tareda ya kalleta ba yace zan matsar da motan ne is dangerous barinta nan gefen titi. Fitowa Deejah tayi tasa hannu zata tayasa, ba tareda ya kalleta ba yake murmushi kafin yace" wayasaka ki, " kallon yanda yake murmushi mai class Deejah keyi kafin tace" kawai zanyi ne, toh ni bana son taimakon Irfan yace. " yatsina fuska tayi itama kafin tace" toh ai dama ba tayaka zanyi ba kawai nayi ra'yi ne. Bai kulata ba ya shiga matsar da motan har ta sauka gefen titi, ga wani sabon hadari dake haduwa.
"Bakin titi Irfan ya kuma komawa yana waving wa motoci, cikin sa'a mota daya ta tsaya, da sauri Deejah ta fito daga motan ta karaso wajen Irfan.
"Haka kawai Irfaan yaji bai yarda da mutanen da suka tsaya ba, motan gaba daya maza ne snn dukansu gabza gabza ne...." Deejah zata karasa jikin motan da murnanta tana fadin" Alhamdulillah at last mun samu taimako....." Irfan ne yayi saurin riko hannunta yana ja da baya... daidai lokacin da mutanen nan suka cimmasu.
"lay down! Lay down or I'll shoot, abinda mutanen suke fadi knn. Da sauri Irfan ya 'kan 'kame hannun Deejah yace muyi yanda suka ce, hakan kuwa sukayi. Searching motar Irfaan suka soma yi wasu kuma suka karaso suna fadin" ina cell phones dinku, da sauri Irfaan ya ciro ya mika masu, aljihunsa suka soma searching suka ciro dan canjin kudin dake jikinsa, wallet dinsa suka shiga dubawa sukayi filla filla dashi suka watsa masa ID dinsa da dangin su Atm card dinsa. Cikin motar kuwa sun sami kudi kusan 20k.
"Tsaki Ogan yayi yace" kai wani irin matsiyaci ne, kana tafiya da luxurious car irin wnn snn a samu just 20k a safe din motarka, you must be stupid, zakayi tafiya bazaka ajiye mana namu ba. Irfan bai ce komai ba har lokacin suna kwance a kasa, dayan yace Oga ga matarsa nan ai ita bazamu rasa yankunne na gold a kunnenta ba,
"Oga yace good badguy. KE! ya daka wa Deejah tsawa, dama kadan ya rage bata saki fitsari ba dan tsoro, ina wayarki, da sauri irfan yace bata taho dashi ba, dayan ya buga masa bakin bindiga a keya yace kai aka tambaya shut up.
"Runtse idonta tayi baki na bari tace wllhi banida waya a hida na barta. Fizge hijabib jikinta badguy yayi nan fa jikinta ya bayyana gashi dama ruwa ya jikata. Murmushi suka soma ganin yanayin jikin Deejah gashi kayan barci ne dama a jikinta.
"Oga ne ya matso yace" a baby zaki famshi kanki da jikinki.... bai gama rufe baki ba Irfaan ya mike a zuciye.... yana masu mugun kallo yace" don't you dear mess with my wife, daku ta'bta gwara ku kasheni..... " dariya suka kwashe dashi, suna kallon Irfaan da fuskansa ta koma jazur sabida bakin ciki.
"Oga ya dafa kafadun Irfan yace" relax lover boy, matarka tana da sura me kyau wanda duk lafiyayyen namiji idan ya gani sai yaji sha'awarta, yanzu dai ka za'ba, ko mubaka fuel ka zuba amotarka mu dana matarka, ko mu bar maka matarka mu tafi da ride dinka mu barku a nan in danger.
"Key din motarsa ya ciro ya jefa masu ya fizge hijabin Deejah daga hannun badguy ya rufawa Deejah dake kankanme da jikinta a gefe. Sunaji suna gani am rubbers din nan suka daura igiya wa motar Irfan suka bar wajen.
"Kuka take kanyi a hankali maras sauti, sosai ta basa tausayi, cire suite din jikinsa yayi ya rufa mata, hannunta ya rike suka karasa wajen wani checkpoint dan bukkan securities suka shige, ya dan kalleta yace ki zauna a nan barin fita ko zamu samu wasu, da sauri ta riko hanunsa tana girgiza kai kar ka kuma taro mana 'barayi.
"Murmushi ya dan sakar mata kafin yace karki damu na gari basa 'karewa....


πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹......
[8/19, 06:25] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye*


20




"Irfan yafi minti shabiyar na tsaye na waving wa motoci but babu motan da tayi attempting tsayuwa, zafi yaji hannunsa na masa aiki yana dubawa yaga ashe yankewa yayi, wajen yayi jazur ya tara jini, tunda uwarsa ta haifesa bai ta'ba shan wahala irin ta yau ba, dafe kansa ya 'danyi yana karanto iyakan addu'an da sukazo bakin sa. Karshe dole ya koma yanda ya baro Deejah.
"Zaune ya sameta ta ta'kure kan wani itace har lokacin rawan sanyi take tana faman kuka, ko ka'dan Irfan bai son jin kukan nata, a hankali yayi gajeren tsaki ya furta" what a fuck! Duk ransa ya gama jagulewa, a harzu'ke ya juye yana mata mugun kallo yace" Ke dan Allah kiyimin shiru haka nan.
"Harara Deejah ta galla mai kafin tace" this is all your fault, mugu kawai duk ba kai ka jawo ba,..... shiru tayi sanda ya taso a harzu'ke yayo kanta, mugun kallo ya watsa mata kafin yace" idan da baki 'bata min project dina kika sani bada ha'kuri the worse abinda nafi tsana ba da baki zo nan. Kuma kika dameni da kuka kiyi waje coz this is my palace.
"Harara Deejah ta galla masa gamida kifa kanta bisa cinyoyinta, tunanin Nilam take kan yi 'kilama kuka take kanyi yanzu haka, Allah sarki my little Nilam ta furta a hankali.
"Wasa wasa har wajajen karfe tara, Kallon Irfan take kanyi yana sallah a dan bakin bukkan, fratan 'kafarsa take kallo dogaye dasu farare sol, kai Allah yayi hallita a wajen nan, kana gani zaka san 'dan hutun gaske ne, gashi yau jarabawan waha ta sau'ko masa. Har ya sallame Sallahn sa kafin Deejah ta dena kallonsa.
"Cikinta ne ya fara mata azaban ciwo, ta sani period dinta ne, innalillahi itakam ta shiga uku yau yaya zatayi da wnn rayuwan azaban.....




"Engr sai kai komo yake a parlorn da suka hallara gaba daya ahalin gidan, waya ne a hannunsa sai faman dialing lamabar Irfan yake but baya shiga, wayan colleagues 'dinsu na company ya shiga kira but babu wanda yaji dutiyan Irfan, masu kuka sunayi masu ban hakuri sunayi, gashi Irfan bashi da wani ta'kamemmen aboki a nan balle su kirasa, hankulansu ya kai koluluwa wajen tashi.
"Ammah Irfan bashida hankali ko ka'dan, yanzu idan ya salwantar da rayuwan 'yar mutane yaya zamuyi, could you imagine wai kan ta bata masa project shine ya dauke ya kaita har office tayi defending, tun safe nace ya dawi da ita gida ban san ina ya kaita ba gashi ya kashe wayansa, duk yanda yaje zaizo ya sameni ne a gidan nan..... Ire iren fa'dan da Engr kekanyi kenan.
"Nazif ya isa haka ka daina fa'din maganganu haka, bamu san wani hali suke ciki ba, nasan Irfan bazai abunda zai cutar da ita ba, mudai muyi addu'an Allah bayyana su......
"Nadiya kuwa cike da mamaki take kallon dad din nata, zuciyanta na raya mata wani al'amari daban...


9:32pm
"Mamie gobe insha Allah zanje Garko na kar'bo magani wa Dada, Sadiq ya fa'di sanda yake jefa lipton cikin mug, Mamie ta jinjina kai kana tace amma motar naka zaije kuwa naji kaci ka buga ta,
"Gya'da mata kai Sadiq yayi yace zataje Mamie bamba ne kawai ya dan bugu, Toh Allah ya kaimu ya sa kuma a dace, Mamie ta fadi sanda Ruqayya ta shigo parlorn. Sannu yaya Ruqayya ce. Murmushi ya sakar mata me cike da fassarori kadin yace yauwa sannu lil sis ya shirye shiryen fara jami'a. Murmushi tayi ta dan sunne kanta kana tace ana kai yaya. Toh Allah ya taimaka Sadiq yace. "Ameen suka amsa gaba dayan su.
"Wani takarda Ruqayya ta mika wa Mamie kafin tace" Mamie dama dazu mutanen nan suka kawo maki daga *Nile University* Da sauri Mamie ta kar'ba tana dubawa, murmushi ta soma tana fa'din alhamdulillahi, ku gani sunyi min approving zan fara girka abinci a Cafeteria din Nile University. Gaba daya farin cikinsu ya kasa 'boyiwa, Allah sarki haka Allah kanyi lamarinsa, lokaci guda sai kaga 'kofan samu na bu'de maka. Ga Sadiq ya samu aiki a M&M Builders ga Mamie ta samu sana'a Babban University a Nigeria kaman Nile University.....




"Gani yayi ta takure tana faman cije le'be, ta'be baki ya 'danyi kafin yace " Ke meke damunki. Ba tare da ta kallesa ba tace cikina ke ciwo. Cikin ko in kula yace ciwonku na mata I guess... Kallon mamaki ta bisa dashi yaya akayi ya gane, girgiza kai tayi fuska a tamke tace ni bance ba.
"Ai dama bance kince ba, ya fa'di sanda ya mike ya saka hannu a aljihun wandansa yaji alamun abu, da sauri ya ciro yana kalla, Shortbread biscuits ne guda biyu, baisan sanda murmushi ya kifce masa ba, Allah sarki, Allah maso bayinsa bacin haka, baisan wani dalili bane zaisa sa saka shortbread cikin aljihunsa ba, quiye alright ya sani yana son shortbread shine best biscuit dinsa amma me zai kawo shi cikin aljihun wandonsa, wata zuciya tace wnn shine taimakon Allah, hamdala yayi kafin ya bude biscuit din, daya ya dauka ya mikawa Deejah daya, kasa kar'ba tayi sai juyi take, nan fah Irfan yaga abun nata da gaske ne, nan hankalinsa ya tashi sosai, zama yayi gefenta yana mata sannu, duk ya rasa wanne zaiyi, wani goran faro ya hango can gefe, da sauri ya dauko yaje waje yanda ruwa ke tsiyaya da shike har yanzu ana dan yayyafi, wanke goran yayai kana ya taro ruwa a ciki.
"Gefenta ya zauna yace" tashi kisha ruwa, girgiza masa kai tayi alamun a'a, ya 'danyi shiru yana binta da kallo, bai kuma cewa komai ba ya koma gefe ya rafka uban tagumi, lallai babu nawan da yafi karfin jarabta daga ubangiji, yau shi Irfan shine mota abinci ruwan sha wajen barci duk suka fi karfinsa a 'dan lokaci 'kan'kani lokaci, lallai Allah ya isa bawa yaji tsoronsa, zai iya canza lamarun bawansa a lokacin daya so...... tunaninsa ne ya yanke sanda sukaji karan tafiyan mutane sun doso yanda suke. Da sauri ya mike yana leke leke, itama Deejah mikewa tayi da kyar tana raba idanu.
"Muryan mutanen suka soma jiyowa, kai Oga yaufa bamuyi kamu ba, nifa a bu'kace nake ma, gashi yau Ester bata fito patrol ba, ko wacce irin mace na samu zan sauke bukata na..... " Tashin hankali gobaran gemu, tashin hankalin da Deejah ta shiga ko 'kafan kama na Irfan beyi ba.......




πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’‹πŸ’„........
[8/19, 06:25] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye*




22


_I sincerely dedicated this chapter to all my fans, you guyz ave no idea how much you mean to me, ILYSM❀_ *#Always 2gedaπŸ‘ŒπŸΌ*

"Mamie

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login