Showing 36001 words to 39000 words out of 159062 words
Chapter 13 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt
yaso ko aso shi, baisan ta'kamemmen abinda yake ji gameda Deejah ba, dan haka dole ya 'dibar mata lokaci, sannan maganan aure kuma yanzu yake jin zaiyi aure, take Laila ta fa'do ransa. Ji yayi kawai ya dau wayarsa ya shiga neman layin Laila.
"Laila kuwa kaman a mafarki haka taga wayan Engr, haba nan fah ta fita da gudu tana 'kwala kira wa Hajiya, Hajiya na zaune tana bawa Alhj Ma'aruf abinci a baki Laila ta shigo da gudu tana nuna mata screen din waya. Haba nan fah Hajiya ta saki shewa tace kinga abinda nake fada maki ko, magpza dauki ki kalallamesa da kalaman soyayya. Da gudu Laila ta fice balcony ta dau wayan....
*Washe gari*
"Kaman yanda ya saba yauma 'karfe 8:30ama ya gama shirinsa tsaf cikin Jampa coffee brown yasha hula zanna bukar, yayi kyau sosai sai ya fito babban mutum, jampa tana kara masa kyau da 'kwarjini,
"Hajja ta gama jera breakfast saman dinning, gaisawa sukayi da Irfan kafin yace" pls Hajja inason fresh blended pineapple, cike da jin dadi Hajja ta amsa dan itama kwana biyu da Irfan yayi yajin cin abinci bataji da'di ba, daidai nan Ammah ta sau'ko daga stirs nan suka gaisa da Hajja cike da girmama juna kafin Ammah ta karaso dinning wajen Irfan, cikin sauri Hajja ta shige kitchen ta tarar dasu Deejah da Zulai suna cin nasu break din, 'kamshin turarensa kawai Deejah ta jiyo saida gabanta ya fa'di,
"Hajja ta dubi Deejah tace" dan Allah Khadijatu tashi ki markada wa 'Karamin Alhaji abarba kin sansa bature ne wai shi zai sha da safen nan, ni zan hada abinci Hajiya ne ta sau'ko 'kasa.
"Deejah ta danyi shiru dan bata son musuwa Hajja, a dan kasalce ta mike ta ciro abarban cikin fridge ta shiga wankewa,...
"Bayan ta gama ne ta shirya cikin cup ta dora kan karamin tray tace Hajja na gama, Hajja tace toh Khadijatu kai masa yana kan teburin cin abinci, Deejah ta danyi shiru dan bataso ta hadu da Irfan dukda songaninshi da zuciyanta keyi, ta 'dan langa'be kai tace Hajja ga Zulai bata komai ta kai masa man. Zulai tace cab'di wnn me turanci wa mutanen, yanzu kana zuwa zai hau fada maka abu da turanci gwara dai ke ki kai masa tinda ke kinaji idan ya maki zaki gane. Deejah ta dan harari zulai kawai a dole tasa kai ta shige dan kai wa Irfan drink dinsa.
"Irfan kayi kyau kaman kullum ka rin'ka saka manyan kaya Ammah tace tana duban Irfan. Murmushi ya 'danyi kafin yace" no Ammah bazan juri saka wadann kayan ba, gaba daya yanzuma am not comfortable sun takurani. Ammah tayi murmushi daidai lokacin da Deejah ta karaso wajen,
"Yana ganin ita ce ya mi'ke yana gyara hular kansa ya rijo hannun Ammah ya manna mata peck yace" Ammah am leaving, idonsa naga Deejah yana jefa mata mugun kallo. A'a ka tsaya mana kasha drini din, Ammah ta fadi, girgiza kai yayi yace no Ammah am Ok ya isheni, besides nayi latti ma already. Daga haka yasa kai ya fice daga parlorn.
"Ammah ta juyo ta kalli Deejah yanda tabi bayan Irfan da kallo, a hankali tace Deejah bishi dashi waje, kinji kai masa.
"Deejah tayi saurin saita kanta kafin ta iya furta toh Ammah.
"A parking lot ta samesa har ya kunna mota, tana tsaye gefen kofar mazauninsa ta kasa cewa komai, tana ri'ke da 'dan tray din data 'daura cup din akai.
"Har yayi rivers zai tafi kome ya tuna kawai sai gani tayi glass din motar yana sau'ka, kaman bazaiyi magana ba yace" are you deaf or what, bakiji sanda nace na koshi bane ko me, yayi dan karamin tsaki kafin ya daga glass din yaja motarsa ya bar wajen, yana kallonta ta glass yanda tayi tsaye tabi bayan motarsa da kallo, zuciyansa ne ta shiga masa zafi ko ka'dan baison yayi hurting dinta, tsaki yadan kuma ja a hankali ya furta" dammn everything, kaman zararre ya soma magana shi kadai yana driving , "no way, bazaki zame mun nightmare ba, I need to do something.......
"Jiki a sanyaye Deejah ta shige cikin gidan, gaba daya su Hajja basu gane mata ba, misalin 'karfe 11:08am ta shirya tsaf cin doguwar rigar abaya ta yane kanta da mayanin abayan ta fito.
"A parlor ta samu Ammah ta rusuna ta gaisheta kafin tace Orphanage take son zuwa wajensu Anty Larai, Ammah tayi murmushi tace yayi kyau Deejah, Ashiru na waje ya kaiki sanda kie son dawowa sai kiyi min waya aje a daukeki, ki gaishe da Larai din.
"Cike da ladabi Deejah ta mike ta nufi waje, Zulai dake la'be tana kallon komai a idonta ya faru, tayi kwafa tace shegiya kaman ta shanye kowa a gidan jin kanta take tamkar ba me aiki ba, Allah ka shigo da Anty Laila gidan nan taci ubanki...
"Tun daga gate din Orphanage ake oyoyo wa Deejah Anty Larai bata nan sun tafi wani taro na gidajen marayu a cikin Abuja, kai tsaye class din 'yan ajinta ta wuce ta shiga raba masu sweets haba nan Orphanage ya dauka gaba daya, Anty Deejah tazo Anty Deejah tazo. Yusra tana dawowa daga sch ta tarar da Deejah, haba nan fah aka 'buge da hirar club.
"Waike yaushe zaki koma zuwa club ne, Yusra ta tambaya sanda ta kafe Deejah da ido dan ba karamin kyau ta kara ba, kana ganinta kasan hutu ya kama jikinta.
"Deejah ta danyi murmushi dan yanzu duk wasu abubuwan tashancin da takeyi a da ta daina kafin tace" tab aikam babu rana dan gaskiya iyayen yaran da nake raino suka sani zai iya shafan aiki na.
"Yusrah ta tabe baki tace" uhum lallai kam, koda yake ba laifinki bane irin wnn hutawa da kike yi, kinga yanda skin dinki ya koma kaman ba aiki kike ba, ke nima na sami irin aikinki wllhi yi zanyi.
"Deejah ta kaima Yusraha dukan wasa a cinya tace" Yussy you will never change, will you.
"Yusrah tace ah toh ai gaskiya ne, ki dubi kanki tun daga kayan jikinki ai ansan baki shan wahala.
"Ke wai ina labarin Safwan? Deejah ta tambaya.
"Kice 'dan iska, cewan Yusrah. Nan suka buge da hiran Safwan saida suka tsayar da ranar leka club kafin Deejah ta wuce wajen Anty larai dan ta dawo lokacin.
"Sosai Anty larai taji dadin ganinta, ta tambayeta babu wata matsala, Deejah tace babu komai, Saida Anty larai ta kara mata en nasihohi da shawarwarin zama da mutane kafin Deejah ta mike dan tafiya lokacin an sauko daga jumma'a.
"Har waje Yussy ta rakata kafin ta soma takawa dan neman abun hawa dan tana jin nauyin kiran Ammah tace azo a dauketa...
"Tafe suke cikin motar Irfan suna dawowa daga masallaci, kai guy wallahi 'kasan nan babu ha'da'd'dun bebs, jiya na zaga clubs sun fi kala nawa amma duk banga wata beb da zance tayi mun ba, haba bebs kam ai se Los Angeles, cewan Ahidjo dake zaune gefen Irfan mazaunin me zaman banza.
"Ta'be baki Irfan yayi kafin yace" there you go again, bazaka ta'ba canzawa ba Ahidjo, kaidai maganan mata kawai, mtsw baka da aikinyi wllhi, pls change the subject I beg you.
"Dariya Ahidjo yayi yace, guy bazaka gane bane kawai, ina missing los Angeles wlhi,........ Muryansa ne ya tsarke sanda ya hango bayan Deejah dake tafe gefen titi..... taba Irfan yayi yana fadin" Kai Dude ga wata hot fah, yi parking yi parking pls.....
πΈπ» Queen Samyπππ.........
ππππ *Mallakin Waye*
28
"You perfectly well known that bana daukan mace a titi, so babu abinda zai sa na tsaya, cewan Irfan dake shirin hayewa Flyover.....
"Ri'ke starry din Ahidjo yayi yana fa'din haba guy don't do this to me pls, ok is it because you giving me a ride? Irfan ban wulakance mana......
"Dole Irfan yayi parking gefen titi badon yaso ba, Ahidojo yace guy rivers fah zakayi, A kufule Irfan ke kallonsa kafin yace" are you trying to annoy me what, tsaki yayi a hankali kafin ya bude motan ya fice ya zagayo mazaunin Ahidjo yace" oya fita kayi driving motan, babu musu Ahidjo ya koma mazaunin driver nan da nan ya shiga yin rivers da motan.
"Deejah kam taji anata horn amma ko juyawa batayi ba, Irfan ya ta'be baki gamida turo hulansa gaban goshinsa ya dan kishingi'da jikin seat.
"Daidai gefen Deejah Ahidjo yayi parking, 'Yan mata barka dai, ya fadi yana fito da kansa ta glass, juyowan da Deejah zatayi a kufule dan tayi niyan wanke me motan nan, idonta ya gane mata Irfan..., Ahido sai zuba yake inaaa Idon Deejah nakan Irfan ko kyaftawa batayi, Nan fah Ahidjo ya gane hankalinta gaba daya naga Irfan,
"Jin shiru yasa Irfan matsar da hulansa yana me jan tsaki, dago kan da zaiyi sukayi ido hudu da Deejah wacce ta kafesa da idanu..., Kallon juna suka shiga yi dukansu biyu, Ahidjo kam sai suka zame masa tv,
"Ina kika fito tsakar ranan nan, Irfan ya tambaya sanda Deejah ta dauke idonta daga dubansa.
"Gajeren tsaki tayi a ranta shikuma wnn sai kace wani ubana, jibi yanda yake wani tambayan mutum, wnn ko ya girme mun ai befi ya bani wani shekara biyar ba.
"Ba tambayanki ne ke ba, ya kuma fadi,
"Sai snn tace" Orphanage,
"Orphanage" ya maimaita a hankali kafin yace, Oya shige mu tafi, babu musu ta bude backseat ta zauna, Ahidjo kam gaba daya sai abun ya masa wani iri, shidai baisan Deejah a gidansu Irfan ba, zuciyansa ne ta shiga tambayansa to wacece ita... Da haka har suka isa kofan gidansu Irfan, a gate suka ajiye Deejah kafin suka nufi gidan su Ahidjo.
"Kai guy itama wnn din kanwarka ce, shiru kaman bazai amsa sa ba sai kuma yace, itace yarinyar da nake fada maka, she's my worse nightmare here, she causes nothing but trouble.
"Ahidjo yayi dariya har yana buga starry kafin yace, oh kace mun she's your crush, .... "What my crush, no never, Allah sawake mun, on the contrary she's always annoying me, snn kace she is my crush,
"Wani murmushi Ahidjo yayi yana nazarin Irfan, kafin yace" guy yarinyar nan ta sace zuciyanka, I can see it from your eyes.
"Shiru Irfan yayi bece komai ba, meyasa mutane suke cewa son Deejah yake, kai kode da gaske sonta yake, toh wai dama hakan son yake,. Idan kuwa hakane, he needs to find out zuciyan Deejah *Mallakin Waye* kafin ya dasa soyayyanta dake shirin masa shigar bazata cikin zuciyansa. cire hulan kansa yayi ya jefa a backseat daidai lokacin da Ahidjo ke parking, a farfajiyan gidansu.
"Muje mana Ahidjo ya fadi, girgiza kai Irfan yayi yace" kaje kawai ni zan wuce sai munyi waya, Ahidjo yace alright no prob, gobe dai su mum zasu iso Nigeria insha Allah.
"Ok Allah ya kawo su lafiya, Irfan yace kafin sukayi sallama ya wuce gida.
"Dakinsa ya wuce ya fada duniyan tunanin Deejah,.....
"Nadiya ce zaune a 'dakinta takan tunanin abinda ya dameta, itakam Allah sa Ya Irfan son Deejah yake, idan hakan ta tabbata babu yanda za'ayi Daddy yace yana son Deejah, da daddynta yayi aure ai gwara ya Irfan ya aureta, itafa ta tsani kishiya a rayuwarta, Koda yanzu da babu momynta bata fata daddy ya sake aure itakam tana jin kishin daddy yace zaiyi aure, zuciyanta ya shiga tambayan ta yanzi idan kuma mijin da zaki aura zai maki kishiya fa? Mikewa tayi tana girgiza kai, haba haba never Allah ya tsareni, aiko za'ayi gawa uku a gidan, koni ko shi ko ita kishiyar.
"Lumshe ido tayi sanda ta tuna fuskan Sadiq, tayi saurin budewa tanason 'karyata zuciyanta amma inaa, kai wnn shine dan hakin daka raina shike tsole maka ido, Sadiq data raina masa gashi ta kasa yakishe tunaninsa a ranta...
"Misalin 'karfe 8:30pm, Engr.Nazif Mumtaz ne zaune gaban mahifiyarsa, cikin nutsuwa yaci gaba da fa'din" Ammah kan magann aure na da Laila ne, inaga lokaci yayi da za'a tsayar da rana, na sani ba lalle yayiwa yaran nan da'di ba, dukda bawai son airen nake ba, gwara nayi sabida takai 'ya'ya na nacikina sun fara tuhumata akan abinda nake da dama akai, idan na zauna babu auren nan gaba abun sai yafi haka. Snn Baba Alhj har yanzu babu lafiya, gwara na cika masa burinsa na auri tilon diyarsa.
"Ammah na murmushi tace Alhamdulillah, naji da'din wnn zance naka Nazif Allah ya tabbatar mana da alkhairi, yanzu zan kira Hajiya Kariman mu soma shirye shirye, Engr ya amsa da ameen kafin ya mike jiki a sanyaye ya nufi sashensa..
*Kuyi hakuri da wannan babu yawa, zakujini later idan na sami chance insha Allah.... Luv you all*
πΈπ»Queen Samyπππ.........
ππππ *Mallakin Waye*
29
"Zaune yake a Office dinsa sai juyi yake kan kujera, ba komai yake tunowa ba sai fuskan Deejah, musamman da yanzu daddynsa zaiyi aure, hakan ya tabbatar masa daddy ba son Deejah yake ba, mikewa yayi ya 'karasa jikin dan karamin fridge dake cikin office din ya dau goran ruwa, ya zauna can wasu kujeru ya soma sha yana lumshe ido, bai ta'ba tsintan kansa a yanayi irin ta yau ba tun tasowan sa,.
"Sadiqne ya shigo rike da takardu a hanunsa, koda ganin Irfan yasan he's in a good mood,
" Friend ka iso, Irfan ya fadi sanda ya mike ya nufo Sadiq sukayi musabaha, murmushi Sadiq yayi kafin yace " Architect I can see that you are in a good mood, are you guys started to get along.
"Murmushi Irfan yayi yace" I just don't know Sadiq bansan ta yaya zance mata ina sonta ba, nifa gani nake kaman saita raina ni. Kasan am not used to that love stuff, I'm new in the system.
"Sadiq yayi murmushi kafin yace" kar ka damu Architect that's norms, you'll soon get used to it, tashi muje Daddy na nemanmu, akwai Invitation Cards na magann daurin aurensa da zamu kaima jama'ansa. Mikewa Irfan yayi yana murmushi suka nufi Office din Engr.
"Kuttisi, Nadiya ta fadi cikin zuciyanta sanda ta shiga dakin Engr tana gyara masa, check ta gani na Naira miliyan hudu da note a 'kasan, _Ki saya kayan lefe_.
"Nadiya ta maimaita kalman yafi abunda yafi, yanzu da gaske de daddy aure zaiyi, shikenan za'a rabasu da daddynsu, haka kurum taji jikinta yayi bala'in yin sanyi, a sanyaye ta gama gyaran 'dakin ta fice zuwa nata 'dakin, tinda aka soma maganan bikin Engr Nadiya take avoiding mahaifin nata, gaisuwa kawai ke hada su, itakam ta tsani matan da daddy zai aura,.
"A 'bangaren Deejah ma jitayi kwata kwata bata son auren, ta rasa me hakan ke nufi, shi kansa Engr ko haduwa da Deejah bayaso suyi, snn ranan haka kurum ya sakata gaba yana bata hakuri, gaba daya ta rasa me hakan ke Nufi, hakan kuma yasata yin sanyi sosai, ko Irfan bata so hadu, ji take inama Engr yace ya fasa wnn aure, da tafi kowa farin ciki, gani take kaman idan su Nilam suka samu new momy zasu kyaleta, ita kuwa yaran sun shiga ranta.
"Gaba daya iyalen gidan Engr basa son wnn aure sai Ammah, harta su Hajja ma'aikata basa so sai Zulai wacce itake kulla komai wa Laila a gidan, dan da taimakon Zulai Laila da Hajiya Karima suka samu hakan su ta cimma ruwa. Shi kuwa gogan wato Irfan bai damesa daddy yayi aure ko kar yayi ba, shidai kawai yasan zuciyan Deejah *Mallakin Waye* shine babban burinsa.
"Ranar asabar 12 ga watan September aka daura auren Engr. Nazif Mumtaz (President M&M Builders) tareda amaryarsa Haj. Laila Ma'aruf. Aurene da ya sami hallartan manyan mutane kama daga kasashen ketare zuwa cikin gida Nigeria.
"Amarya Laila tasha huduban cikki burutsi wajen mahaifiyarta Haj Karima.
"Kina jina ko, sakin jiki zakiyi kija kowa jikinki a gidan, 'ya'yan sa kisannyanda zakimsaye zuyansu da kissa da kisisina da makirci da en dabaru irin tamu ta mata, kinsan Nazif babu abunda yake so kaman farin cikin 'ya'yansa da mahaifiyarsa , to ki kula da wann kina jina, Hajiya ta fadi tana mai jan kunne wa laila.
"Laila ta mirmusa tace Hajiya karkiji komai, ai na riga na shirya zaman gidan Engr, babu saki balle yaji, yawwa er garin, Hajiya tace tana me tafe hannu da laila, ina er kullin maganin da na baki,
"Laila ta ciro shi cikin daurin lafayyan ta tace kin ganta nan hajiya. Hajiya karima tayi shewa tace ashe er tawa er garice, toh kina jina, wnn kulli ki tabbata kinyi hayaki dashi kin turare illahirin jikin ki dashi a cikin dakin Nazif, toh fah shida kallon wata mace har abada.
"Laila tasa