Showing 153001 words to 156000 words out of 159062 words

Chapter 52 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10370

ciki cikinsu....
Alhj Abdullah saida ya digar da kwallan farin ciki..


"Dr yace kar a ringa barinta tana yawan shiga damuwa, snn ta rage yin wasu ayyuka har sai cikin yayi kwari. And da zaran ta farfado she will be discharged....




"Wann labari ba k'aramin faranta ran family din yayiba,
Kwance take a dakin Ammah tana cin grapes. "Nadiya na zaune kasan rug har tayi uploading a status dinta sai faman kiran waya tana sanar wa mutane, Deejah ta turo baki tanai mata mitan ta daina yad 'ata itakam bata so.... Sai dariya Nadia take tana zolayarta mmn twins, ai ta gaji twins ta ko ina, ... Sai surutu take batasan Irfan ya shigo ba,... Bata ankara ba taji rankwashi a kanta......
"Awchh, wayyo ya Irfan da zafi wllhi...... "Hanyar waje ya nuna mata kafin yace oya fita mijinki na nemanki kinzo zaki takurawa mata koh..... Zatayi magana yace "Get out jor..... Simsim ta fice, Deejah harda mata gwalo.....




"Karasowa yayi gamida zama gefenta, tuni ta shige jikinsa don yau ba turaren can ya saka ba.
Tana kwance lupp cikin jikinsa tace "Babh yau ina turarsn naka.
"Muushi yayi yana shafa sumarta yace" Ai nama kyautar tunda kikace baki so. Murmushi kawai tayi gamida dada lumewa cikin jikinsa.


Dan karakatowa yayi suna facing juna kafin ya soma fad'in" Baby your Dad Luvs you, pls ki yafe masa, we all made mistakes in our past, Ki ja kannenki dama kina sonsu tuntuni, and Aunty Bilki, Baby kodaga irin karban da suka mna a Manchester zaki gane Dad nada kirki, I worked with him and I see how generous and trustworthy he is. Baby He's your father no matter what, you can't change the fact you can't deny it, remember this is your dream to meet your own real family your parents, now that you finally met them both is that how you express your appreciation to our Lord, Shi dan Adam ne, and remember We are all born to make mistakes and to learn from it.. Pls sweetheart give your Dad a chance to be your father, Kar ki bari sedan ya rinjaye zuciyarki. I know you have
[11/13, 6:24 AM] 0mmer Farouk: πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’ Continuation of page 104




I know you have a good heart and a pretty soul, I know My Real Dee can easily forgive and forget, I know she never hold grudges....
"Hawaye tab idanunta take kallon Irfan..... Rungumeshi tayi sanda hawayen suka soma zuba sosai ya rungumeta shima, Sun dan jima a haka yana lallashinta, kafin ta mike ta rik 'o hannunsa tace "Take me to him pls.....
"Fari 'a ya cika fuskar Irfan, Rungumota yayi cikin kafad 'una suka nufo downstairs, ga mamskinta tabb taga mutane a parlorn, shi kuwa Irfan bai nuna sing na mamaki ba dake yasan komai. Su Alhj Abdullah sunzo sallama ne zasu koma England.


"Har gaban Dad dinta Irfan ya kawo ta, mikewa yayi yana kallonta idonsa tabb k'walla... "Murya na rawa ta furta *Daddy* wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyar Dad dinta, hawayen farin ciki suka shiga kwsranya masa.... Rungumeta yayi yana kuka yake fad 'in *Daughter* "Gaba daya jama, 'an parlorn farin ciki ya mamaye zukatansu.
"Murya na rawa Deejah take fad 'n ka yafeni Daddy ka yafe mun don Allah, inaso na zama mai albarka a rayuwana,, Goge mata hawayen yayi gamida tallafo fuskarta da duka hannayensa biyu kafin yace " Baki min komai ba Kahdeejah, Ke me albarka ce, Ke diyar Albarka ce, Allah ya kara lullube ki da blessings dinsa, You went through alot a rayuwa, kinga jarabawa kala kala Allah ya maki albarka, ki sani dukkanmu nan muna sonki, Ki sani Allah ya lullube da rahama da samun miji kamar mijinki, Allah ya maku Albarkar gaba daya.... A tare jama 'an parlorn suka amsa da Ameen


"Su Ayla da Afnan tuni suks karasa suka rungumesu. Hadasu duka Alhj Abdullah yayi ya rungume, Twins dukda yarintar su harda dan yin kukansu......


"Ayla ta dubi Deejah ta goge mata hawayenta kafin tace *Aunty sis* did you forgive our Dad... Rungumeta tayi tana murmushi, Afnan kuwa cewa tayi Aunty Sis muna son zama a Nigeria trrda ke. Itama rungumeta Deejah tayi kafin tace " Zamu zauna tare dear sis I'll ask Daddy about that.
"murmushi mai bayyan hakwara Alhj Abdullah yayi kafin ya rik 'o hannayen Girls dinsa yace" You three are my pride, you're all I've I'll do anything for you till my very last breath. We are staying here in Nigeria.... Yarna harda tsallen murnanrsu. Nilam ta karaso ta rike hannayen Twins tace "Zaku shiga school dinmu, ana kaimu vacations different islands around the world..... Gaba daya sukayi dariya...
"Aunty Bilki ta goge hawyen da suka zubo mata kafin ta karasa ta rungume Deejah a hankali tace Daughter... Mjrmushi Deejah ma tayi kafin tace Best Aunty...


"Alhj Abdullah ya karasa gaban Engr rike hannu sukayi kaman masu musabaha kafin yace " Bani da bakin maka godiya Engr Nazif, you're indeed a Hero ma Al umma baki daya,Allah ya biyaka da mafificin Alkhairi.
"Engr na murmushi yake fad 'in babu abin godiya Mr chairman, Deejah yata ce ma kaina nayi, Allah ya wuce mana gaba.
"Ameen ya amsa dashi suka dan rungumi kafadun juna kafin ya karasa gaban Irfan.... "
"Irfan ya Dan dukar da kansa alamun rusunawa da sauri Alhj Abdullah ya rungumosa yana murmushi yake fad 'in kar ka damu Son in-laws babu surkunta a tsakanin mu, you'll always be that Friend of mine da mukayi kasuwanci tare a kasar England.....Gaba daya saida suka dara.....


"Kowa na cikin farin ciki kafin wayar da aka yiwo wa Engr ya gusar da farn cikin,
"Gaba daya suka tattara suka nufi National Hospital, yanda aka sanar dasu jikin Baba Alhaji yayi tsanani.....




Sameena ceπŸ‘ŒπŸΎ
[11/13, 6:24 AM] 0mmer Farouk: πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’ *Mallakin Waye*




105




*©Sameena Aleeyou.... ✍🏾*


_Queen Samy Novels Forum... πŸ“–πŸ“š_




*Ina kuke masoyan Mallakin waye here comes your chappy...*


Sis Rally Garba😘
Maman SadiqπŸ’…πŸΌ
Sanah πŸ‘Œ
Najaat
Zainab 🌷
Maman Khairat
Bintu Abiha
Barr Asmy πŸ‘©πŸ»β€πŸŽ“


Badiyya Dan Isah 😍
Mrs Fawaz Kaita
Badariyya luv
Mom Ihsan n Kamal


_sameena tana sonku tana ji daku.. Ubangiji ya bar kauna 😍😍😘😘_




"Kuka Ummi take shar shar da hawayen ta, hannunta na rik 'e cikin na mahaifinta, daga jin irin hudubar da yake mata zaka gane wasiyya ce. Hannun Engr ya kamo snn ya kamo na Irfan da Deejah.
"Cikin muryarsa da bai fita sosai yake fad 'in " Alhamdulillah Allah ya hada kan zuriyan Ma'aruf da na Mumtaz, no matter what ku rik 'e junarku da amana, kunga iftila'i iri iri a rayuwanku ubangiji yasa ya zama darasi ga bayi.... Allah shi maku albarka gaba d'ayanku..... Ire iren hudubar da Dattijo Baba Alhj kenan ya masu.......
"Kaman wasa chan zuwa jimawa na ura da yake nuna bugun zuciya ya soma kara.... Gaba daya suka fice kiran likita a kidime. Hannun Engr ya rike yana murmushi yake fadin "ba sai kun kirasu ba, a yau basu da wata dabaran da zasu min. Nazif ka kula da wnn family dama kanayi , Allah ya sadamu a darulsallam...... Daga haka yayi kalimatusshahada snn ya cika..... ALLAHU AKBAR ko wani mai rai mamaci ne....


"Saiga hawaye na zuba idon Engr abu mai kamar wuya kaga hawayensa. Hannu yasa gamida shafe fuskan Baba Alhj daidai lokacin da Ummi da Dr's suka shigo.... Ai tana ganin haka ta sulale kasa tana hawaye, Engr ya k'arasa ya tallabo ta ya shiga rarrashinta dukda shima da za 'a lallashesa tabbas zai so don kuwa wani sabon rashin uba yayi..




"Allahu Akbar mutuwar Baba Alhj ya girgiza kasa baki daya, dan kuwa dattijon kirki ne mai yawan alkhakri.
"A b'angaren Deejah kuwa abin yayi affecting nata sosai haka Irfan yake wuni lallashi musamman duba da yanayin da take ciki......






***************


"Yau kwana hud'u kenan da rasuwar hankulansu ya soma dawowa jikkinnsu.....
"Irfan da Sadiq ne zaune saman tapkeken carpet din Turkey dake mamaye a parlorn Engr, yayinda Engr ke zaune saman kujera by the center of the parlor, wasu Documents suke kan sorting musamman takardun da ya shafi dukiyar Baba Alhj, Mal Habu ne yayi sallama cikeda rusunawa kafin yace ana sallama a waje.
"Engr ya tambayi sunan sa mal habu yace "Umm toh dai gaskiya ba bak'in fata bane ranka shi dade don ban tsamman naji hausa ba, turanci dai suka min shine nace barin zo na fad 'a.


"Engr ya dan yi Jim, kila abokan kasuwancinsa ne na kasashen waje suka zo masa ta 'aziya, duban mal Habu yayi kafin yace a shigo dasu.


"Irfan ku koma can parlorn gefe inada guest. Irfan ya amsa da toh Daddy, tattara Documents din suka soma yi shida Sadiq snn suka koma can gefen parlorn da shike girman parlorn ya kwashi saitin kujeru kusan kala hud 'u, so sai suka koma daga can gefe suka ci gaba da aikinsu .




"As'ad da wasu escorts dinsa ne suka soma shigowa gaba daynsu cikin bakaken suits, Engr ya mik 'e yana tarbansu.... Cak ya tsaya sanda yayi tozali da Dattijon balaraben yana sanye cikin manyan kaya irinta larabawa harda irin abinda suke daurawa akansu. Tsufan mutumin bai hanasa gano tsantsan kamaninsu da marigayiyar matarsa Khadeejah ba, tabbas a yau ya ga fuskar Khadeejah a tareda wnn balarabe...
"Da murmushi Datijjon balaraben ya mik 'a masa hannu sukayi musabaha. Engr ya dan saita kansa kafin ya bawa Datijjon wajen zama cikeda karammawa.


"Gaisawa sukayi cikin harshen turanci kafin shiru ya ziyarci wajen na lokaci guda...
"Engr ya juya gamida kiran Irfan kan yazo yayi serving nasu Drinks.......
"Tunda Irfan ya mik 'e ya nufosu Idon Abbu ke kansa. Hawayen farin ciki suka shiga gangaro masa tabbas wann jininsa ne, tabbas wann jirin Arab ne jinin Little Khadeejansa ne. Baisan sanda ya mik 'e ya nufe Irfan ba.
"Engr dake faman magana dasu As'ad yana tambayarsu daga wata company suke tuni hankulansu ya tattara ya koma kan Irfan da Abbu.....


"Turus Irfan yake bin dattijon da kallo ganin yanda yake shafa fuskarsa yana hawaye yana maganganu cikin harshen larabci Wanda banda su As'ad babu wanda Ya fahimcesa.


"Kallon Engr Irfan keyi cikeda alaman tambaya. Ganin dattijon na kuka sosai ya karyar masa zuciya, tuni yayi kokarin zaunar dashi saman sofa yana mai tunanin kila ya masa kama da wani ne. Sadiq ma dake can gefe sosai abun ya dauke hankalinsa.



"Irfan zai mike Abbu ya rike hannunsa sosai ya soma fadin cikin harshen turanci wann karan " Don't leave me my grandchild, I know you must be my flesh and blood, I know you're Khadeejah's Son, my only daughter, I finally met her family........ "Innalillahi wa inna ilahirraji'un abinda Engr keep maimaitawa kenn cikin zuciyarsa, tablas wann mahaifin marigayiya matarsa khadeejah ne, take yaji hawaye na neman wanke fuskarsa Allah sarki Khadeejah.....




"Irfan da tuni idanunsa sun rine sun koma jazur, jijiyoyin jikinsa sunyi rud 'u rud 'u, haka nan flesh dinsa ta koma tamkar jan gauta.....
"Wani irin tsanar tsohon nan ne ya d'arsu masa sanda ya tuna labarin mahaifiyarsa wacce tasha azaba wajen wann mutumin da matarsa, wanda har saida ya kaita ga guduwa zuwa wani kasa daban rayuwarta ya shiga garari, shine sai yanzu zaizo ya nemesu bayan momy ta riga ta rasu, .....Da karfi
[11/13, 6:24 AM] 0mmer Farouk: πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’ Continuation of page 105.




"Da karfin gaske Irfan ya fuzge daga rikon da yayi masa, Siriryar hawaye wanda zamu iya cewa na kunan zuciya ne ita ke gangarowa daga idanunsa....
"Hannun Abbu ya riko gamida karasawa dashi bakin kofa kafin yace " Get out of here, we don't need you, you've no right to be here. Kai ba Baban momy bane just leeeeeaaaveee... Ya karashe maganar da karfin gaske sands kuka sosai ya kufce masa, ya tuno momynsa ya tuno kalan azaban data sha a baya, ya tuno a iya rayuwar da tayi dasu bata taba kushe iyayenta ba dukda bata taba nuna masu su ba, amma kullum cikin gode masu take tare da masu addu 'an alkhairi, this Man have no idea what she went through. How dare he zaizo neman afuwansu a yanzu.....
"Sadiq ya karasa da sauri ya rike Irfan Engr kuwa jiki a sanyaye ya fice kiran sauran yaran dashike yau Saturday ne babu school duk suna gida.....




"Ba yaran kawai ba harta su Ammah Ummi da Deejah saida sukayi kuka, Allah Akbar abubuwa da dama suna kan faruwa.

"Godiya da nuna nadama sosai Abbu yayiwa Engr da Ammah, a bangaren yaran ma suna son kasancewa da kakansu suji dumin mahaifiuarsu saidai Irfan ya hanasu kebewa dashi infact ya bawa Abbu notice ya bar kasan shine kwanciyar hankalinsu, ya koma yanda ya fito basu da bukatansa. Karshe ma daukar matarsa yayi suka koma gidansu tunda yaga Daddy ya masu masauki a gidan.




"Ammah kuwa kullum sai ta dafa ma Abbu shayi, abu kaman wasa a dan kwana biyun har wata shakuwa ce na musamman ya shiga tsakaninsu, Abbu ji yake ya samu sabon rayuwa a Nigeria, burinsa bai wuce ya samu amincewa da soyayyar Irfan ba.




"Har kusan sati guda , rarrashin duniya Deejah tayi amma fir Irfan yaki yafe masa,
"Tana tsaye bakin kofar Design room dinsa tana kallonsa yanda yake kan jera pics din mahaifiyarsa. A hankali ta karaso gamida rungumesa ta baya.
"murya can kasa take fad 'in" Baby life is all about forgiveness nasan mijina ba haka yake ba, He always forgive and forget.... Take ya tuna exactly abunda ya fada mata Kenn lokacin da daddyn ta yazo.
"Dan murmushi yayi kafin ya manna mata kiss a goshi yace " I know what are trying to say Baby, ki sani abunda Abbu yayi ma mom was out of line. He don't deserve to be forgiven.
"Deejah ta dan sauke ajiyan zuciya kafin tace " If momy was still here I know she'll forgive him, Baby ka yafe masa pls.
"Yatsunta ya riko gamida yin gajeren murmushi da leben bakinsa kafin yace " Baby let's not talk about this pls....
"Dan murmushin itama tayi kafin tace "Ohk ka min favor guda, rungumeta yayi cikin kafadunsa yana shafan dan shafeffen cikinta kafin yace " matata bazata tambayeni favor ba, ko menene muddin bai fi karfina ba zan mata shi as far as zata kasance cikin farin ciki.


"Murmushi tayi tana dan kallon kyakkyawan fuskar sa kafin tace " So nake mu tafi airport yanzu Abbu zai koma Lebanon muyi masa sallama..
"Saida gabansa ya fadi da jin statement dinta, dan jimm yayi kafin yace alright i'll do it for you Baby. D'gyalgyal tayi tana kokarin kamo tsawonsa kafin ta manna masa light kiss a pink lips dinsa. Murmushi yayi kafin ya wuce sama dauko dan makulli, itama tabi bayansa don shiryawa...




*Moi Nusy luv ban maceki ba fah, muna nan a tare like sosai sosai..... πŸ˜œπŸ˜πŸ˜˜πŸ˜„*




Sameena ce πŸ‘ŒπŸΎ
[11/13, 6:24 AM] 0mmer Farouk: πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’ *Mallakin Waye*


106


*©Sameena Aleeyou... ✍🏾*


_Queen Samy Novels Forum... πŸ“–πŸ“š_





"Abbu rungume da 'yan jikokinsa yanai masu ban kwana, Ammah Engr da kuma Ummi suna tsaye gefe, kaman daga sama suka hango su Irfan. Kwata kwata basu kawo zaizo ba,




"Yana nan tsaye tamkar gunki, Abbu ma kallonsa yake cike da so da k'auna, a hankali Irfan ya soma takowa har ya k'araso gaban Dattijon.... Baisan sanda ya rungumesa ba hawaye na kokarin fito masa yake fadin " *Grandpa*... Wani dadi maras misaltuwa shi ya mamaye zuciyan wann Dattijo haka nan illahirin mutanen dake wajen.
"Rungumesa Abbu ma yayi hawayen farin ciki na zarya bisa fuskar sa yake fad 'in, Oh dear grandson,......
"Irfan yaci gaba da fad'in" Forgive me pls Grandpa, I was stupid by being so mean to you, I shouldn't have

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login