Showing 144001 words to 147000 words out of 159062 words

Chapter 49 - MALLAKIN WAYE COMPLETE Document from Queen Samy.txt

20 Dec 2024

10410

99




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*


_Queen Samy Novels Forum....πŸ“–πŸ“š_




*A rayuwa kar ka zamo mai cire tsammani ga rahamar ubangiji*




"Kasa motsawa tayi daga yanda take hawaye bai daina bin k'u cinta ba snn bata daina bin fuskar matan da kallo ba, tabbas wann fuska yanayinta take gani cikin mafarkinta, Allah yau ya nuna mata a zahiri,...
"Hannu Fatimah ta saka ta shiga shafa fuskar Deejah hawaye na bin k'uncinta itama, shakka babu tun ganin Deejah take jin babban al'amari gameda ita, snn ta tab'a had'uwa da ita a lokacin da take cikin jinyar hauka,..."Bakinta na rawa take furta,"Alhamulillah, I met her, I finally met her.. It's exactly 20years, my daughter, I'm here sweetheart, your mum is here...."Kuka mai k'arfi ya kufce masu, tuni Fatimah ta rungume Deejah sosai cikin jikinta, Allahu Akbar banda sautin kuka baka jin komai anparlorn.


"Deejah gani take kaman mafarki ne ba gaskiya ba, kallon ta tayi hawaye na sauk'a bisa k'uncinta kafin ta soma fad'in" *Ummi* meyasa kika haifeni kika gudu, meyasa kika yar dani, meyasa kika bari na girma ba tareda iyaye na ba, meyasa kika bari suka jefeni da sunaye munana, Ummi shin da gaske ne bani da uba....."Kuka mai k'arfi ya kuma kufce wa Deejah.
"Irfan dake tsaye gefe, kasa jurewa kallon wann abin tausayin yayi tuni ya fice ta back door ya kifa kansa yana kuka mai tsuma zuciya.


"Murmushi take hawaye na bin k'uncinta tana tallafe da fuskar Deejah take fad'in" No my dear, no you are not a baster, kinada mahaifi, ke 'yar sunnah ce, kar ki sake wann gurb'ateccen tunani a k'wak'walwarki, Abinda ya rabamu k'addara ne, gashi k'addara ta kuma had'a mu, baby ke musulma ce nasan kinyi imani da k'addara, mu kuma kalan namu jarabawar kenan...."
"Farin ciki maras misaltuwa ya mamaye zuciyar Deejah tuni ta kuma rungume mahaifiyarta suna kuka mai tsuma zukatan masu saurare...


"Saida sukayi mai isarsu kafin ta rik'o Deejah ta k'araso danita gaban Baba Alhaji, hannun tsohon ta kamo wanda tuni hawaye ta wanke masa fuska ta had'a dana Deejah kafin ta soma fad'in" Baba ga jikar ka, jikarka is alive, shes alive, shes here infrot of us, shes a lady now, Allah yaji addu'an mu, Allah ya had'amu....."Rungumesa Deejah tayi tana hawaye shima hawayen yake, kasa magana yayi, saboda heart d'insanis very weak, yanzu haka ma wannan babban abun mamaki da ya gani ya tab'a masa heart, daurewa kawai yake bai so su gane.
"Hannaunsa na rik'e cikin na Deejah yayi alama wa Daddy da ya k'araso, a hankali Engr ya k'araso gabansa. "Hannu Baba Alhji yasa a aljihunsa kafin ya ciro 'yar k'aramar takarda da biro ya d'an rubuta note gamida mik'awa Engr.
"Engr ya karance note d'in kafin ya d'ago ya kallesu gaba d'aya kana yace" Baba Alhj needs some rest regarding his condition, zuwa gobe insha Allah za'a kai masa Deejah su wuni tare, but for now za'a kaisa gida, ya huta, yana tsananin buk'atar hutu. Duk sukayi na'am da batu. Fatimah ta k'araso gamida durk'usawa jikin wheelchair din har lokacin hannunta na rik'e cikin na Deejah kafin ta rik'e hannun Baban ta kana ta soma fad'in" Baba kana so na taho tare da kai...."Da sauri ya girgiza mata kai da k'yar bakinsa na rawa maganar bata fita sosai yake furta" A'a, Fatee ki tsaya da d'iyarki kar damu I'll be fine, idan yaso zuwa dare sai ki dawo gida...."Rungumesa tayi gamida share masa hawayen da zubo masa, Deejah ma tsugunawa tayi gamida rungumesu baki d'aya.




"Engr da kansa yayi niyyan kai Baba Alhaj amma Sadiq ya matso ya d'an sadda kai kafin yace" Daddy you're exhausted too u need some rest, I'll take care of Baba Alhaj,... "Engr ya bubbuga kafad'un Sadiq yana murmusawa kafin yace "Allah ya maka albarka.




"Fateemah ta kamo hannun Aunty Larai tana murmushi da sauri ta rungumeta a hankali take fadin" Bansan da bakin da zan maki godiya ba, Allah ubangiji shine kawai zai biyaki, na gode k'warai da gaske, Allah ya saka maki da mafificin Alkhairi. Aunty Larai ta goge hawayen da suka zubo mata kafin tace" Ai d'a na kowa ne, Tun tasowar Deejah nake sonta tamkar ni na tsuguna na haifeta, shiyasa ma na saka mata sunan mahaifiyata Khadeejah, snn da naga ta kawo girma na damk'a ta a hannun mutanen da nasan bazasu cutar da ita ba. Da sauri Deejah ta rungume Aunty Larai.


"Fatee ta kuma juyowa ta dubi Ammah da Engr kafin tace Allah ya biyaku da Aljannah, hak'ik'a zukatanku tsarkakku ne babu mugunta balle ha'inci, kun bata good life at the end kun aurar da ita ga d'anku mafi soyuwa a gareku snn yaron arziki wanda aka masa shaida da halin k'warai, hak'ik'a kun cancanci yabo da godiya..."Da sauri ta rungumeta tana murmushi kafin ta soma fad'in" Fateemah ki daina fad'in haka, Allah ya k'addara fad'owar Deejah hannunmu sabida gida ta dawo, Jikar Hindatu jika ce a gareni, haka nan jikan Alhj Ma'aruf jikar Alhj Mumtaz ce ko babu ke Deejah d'iyar mu ce, Allah shine abin godiya da yaye duhu ya bayyanar da haske.
"Hannaye suka d'aga donyi addu'o'i tare da mik'a godiya ga Rabbil Izzah.




"Duk wann abunda ya faru a idanun Azee dake mak'ale saman Stircase ya faru, hawaye na bin k'uncinta, hak'ik'a rayuwar Deejah dana mahaifiyarta na cike da tarin al'ajabi da darrussa game hankali, shin Deejah cousin d'inta kenan, shin dama Deejah 'yar uwarta ne....."Maganan data soma jiyowa daga parlorn ya katse mata tunanin da take.


"Daddy yaci gaba da fad'in" Irfan kenan shine mijin d'iyarki Deejah, Ummi (Fateemah) sunan da Deejah ta soma kirarta dashi kenan, ta d'anyi murmushi kana tace" Like father like son..."Irfan ya d'an murmusa yana satan kallon Deejah gamida sosa k'eya. "Ammah ta d'an dunguri k'eyar sa kafin tace mata biyu ke gareshi da kike ganinsan nan ya kusa zama daddy shima don d'ya matar tasa juna biyu gareta...
"Kirjin Ummi yaba da dumm dan kuwa ita a halin yanzu tsoron kishiya take, tunda kishiyar uwa ta kassara mata rayuwa, Irfan kuwa take annurin fuskarsa ya d'auke, Deejah ma har ta mance da wata Azee sai yanzu da Ammah tayi maganar.
"Daddy ya d'an k'ak'aro murmushi don ya lura da yanayin chanzawan da Fatee tayi, Engr yaci gaba da fad'in" Aff Irfan ina Azeezar tun dawowar mu bamu ganta ba,...."Shiru Irfan yayi take idanunsa suka kad'a sukayi jazur, Ammah ta nud'e murya tace Irfan tambayarka ake ina Azeezar,..."Deejah ta tsaresa da ido tana jiran amsarsa don itama yak'i fad'a mata komai gameda Azee, tana tambayarsa zai bar wajen, ko ya kawar da zance ko kuma ransa ya b'aci...."Basu ankara ba sai hango Azee sukayi tana sak'owa daga stirs kaman Kazar da ruwa ya buga, haka take tafiyar har ta k'araso cikin parlorn...


"Sakk'owar Azee yayi daidai da banko k'ofar parlor da akayi aka shigo babu ko sallama. Gaba d'ya suka maida dubansu wajen...


"Yesmin ce sai faman taunar cingam take ga wasu arnan kaya marrasa mutunci a jikinta, cire bak'in glass d'in idanunta tayi kafin ta soma bin mutanen parlorn da kallo d'aya bayan d'aya, tsaf ta sauk'e idanunta kan Azee wacce ke ta faman muzurai, da sauri ta nufi yanda Azee ke tsaye tana huci, ganin Yesmin ta nufo ta yasata saurin yin bayan Ammah ta b'oye...




"Ammaha cike da mamaki take fad'in lafiya, wacece ke..."Yesmin tayi k'araras da cingam kafin ta gyara tsayuwarta tace "Why not ku tambayi wann 'yar iskar karuwan so called in law d'in taku...."Ta k'arashe maganar tana nuni da Azee, Nadiya ware ido sosai tayi tana kallon ikon God, don kuwa ta gane fuskar Yesmin randa ta kamasu suna mad'igo a gidan Irfan"
"Gaba d'aya suka juyo suna duban Azee cike da mamaki, tuni hawaye ya soma ambaliya a fuskar Azee, "Yesmin taci gaba da fad'in" Ke k'aramar karuwa na maki iyaka da mijina Ahidjo kink'iji ko, shekaran jiya ya koma gida jikinsa a farfashe zai min k'aryarku da kuka saba, baisan nasa abincika mun komai ba, Irfan ne ya dawo ya kamaku a d'akin barcinsa a kan gadonsa, Ke bakiji kunya bama, don ba saboda ke Irfan ya daki Ahidjo har ya sakeki ba sabida sharri da tuggu da makirci da kuka ringa k'ullawa Deejah sabida haka yaci uban Ahidjo snn ke kuma ya sake ki, banza mak'aryaciya, asibiti kikaje aka aunaki mahaifarki ta lalace sabida magunguna da Ahidjo ya tapka maki na hana daukan ciki ya lalata maki haifa, shine keda uwarki da tsinanniyar kakarki kuka saye likita akace kinada ciki don ku saye zuciyar Irfan, ko k'arya na fad'?? Ki musa mana, "Azee dai sai rawa jikinta keyi kanta na k'asa tana hawaye..."Yesmin tayi murmushin cin nasara kafin tace "Toh wllhi kinji na rantse now that Irfan is not longer your husband kikayi gigin auren mijina ko kuma na kuma jin an ganku a tare, Tayi wani murmushin bawasa kafin tace" I don't have to explain my self ke dashi duka kunsan saura, ta juyo tana duban mutanen parlorn kafin tace" Ku kuma ya rage kusan yanda za'ayi ku rabo da wann snake d'in... daga haka ta matso daf da fuskar Azee kafin tace" I hope I made my self clear, don't mess with me again you bitch.....




"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un abinda bakunan su ke furtawa. "Ammah ta dubi Azeeza da idon tsana da k'yama kafin tace" Azeeza shin gaskiya yarinyar nan ta gama fad'i????
"Kuka Azee keyi kafin ta tsuguna ta d'aga hannaye tana rok'onsu.."Ammah don Allah ku rufa min asiri, Daddy don Allah ku taimake ni, wllhi ina son Irfan kaman zan mutu, don Allah kar ku bari ya rabu dani ni marainiya ce, banida kowa sai ku..." Caraf Nadiya tace" Allah ya sauwak'e masa yaci gaba da zama da najasa irinki, Ko kin mance randa na kama ku keda wann karuwar da ta fice kuna mad'igo da mata sama da biyar a parlorn gidanki, Allah ya tsare ya Irfan da mace Irinki,..."Da sauri Sadiq ya girgiza mata kai alamun tayi shiru tana k'ara wutar abu ne. Sai yanzu tausayin Irfan ya kama Sadiq ashe abinda ya gani kenan a gidansa, matarsa da gardi, gardinma best friend dinsa, tausayin Deejah ya kuma kamasa duk illahirin mutanen parlorn she went through alot a rayuwa, Allah sarki, tuni Umminta ta kuma rungumota jikinta Deejah kam sai kuka take sosaimda sosai.

"Shiru ya ziyarci parlorn sai sautin kuka kake ji,
" Daddy yayi d'an gyaran murya kafin yace" Irfan da gaske ka saki matarka....."Irfan ya d'ago jajayen idanunsa yana kallon Daddy" Ammah tayi caraf tace" Ai ko bai saketa ba zai saketa yanzun nan, kar kuma k'ara masa pressure Nazif, Irfan abinda kayi kayi daidai, Allah ya saka maku kai da Deejah, Allah ya wanke baiwar Allahn da kuka ta faman k'ulla mata tuggu, Allah mun gode maka da kasa cikin k'arya ne ba gaskiya ba, babu mu babu had'a iri da irinki Azeeza, kin bani kunya kin bani mamaki....."Wani ihu Azee ta kurma tana d'ora hannu aka, a guje ta fice daga gidan tana kuka hannu aka.
"Deejah kuwa tausayin mijinta da tsananin soyayyar sa shi yake shigarta a hankali, ji take kaman ta k'arasa ta rungumesa cikin jikinta a halin da yake ciki a yanzu...


*Two days later*


"Deejah kwance cinyar Ummin ta tana shafa gashinta suna hiran 'ya da mahaifiya, Deejah ta d'an d'ago tana kallon Umminta kafin tace" Ummi you went through alot in life, you experiences a horrible tragedy, rungumeta Umminta tayi kafin tace" Habibty kema kin sha wahalhalu a rayuwa, kinyi experiencing rayuwar duniya, Haka Allah yaso jarabtar mu don mu kasance masu sa'a a rayuwa, Deejah ta murmusa gamida gyad'a mata kai, suddenly kuma sai mood dinta ya canza, Ummi ta murmusa gamida rik'o 'yan yatsun hannunta kafin tace" Habibty akwai abunda ke damunki ne? A hankali Deejah ta share hawayen da suka soma zubo mata kafin tace" Idan akwai wanda nafi tsana a yanzu toh mahaifina ne, Ummi bazan tab'a yafe masa ba, shine silan rabuwar mu...."Tuni Ummi ta rungumeta tana fad'a mata kalamai masu kwantar da hankali.


"Suna a haka Irfan ya d'an lek'o gamida yin knocking a k'ofa, Dagowa sukayi sunankallonsa fuska d'auke da murmushi, a hankali shima ya mayar masu da murmushin kafin yace " May I??.
"Ummi ta gyada masa kai kafin tace"Sure come in Habiby, shigowa Irfan yayi gamida zama gefensu saman rug din shima, dan satan kallon Deejah yayi yana so ya sata dariya don ya gane kaman kuka tayi, Ya dan kalli Ummi kafin yace"Ummi na barka da hantsi, Ummi tayi murmushi kana tace barka Habiby, Irfan ya d'an tura k'afa ya tsokali Deejah kafin yace" Ummi what's wrong with your Habibty ko bata so na shigo bane, dariya suka so bawa Ummi kalan soyayyar su na burgeta, dan kallon Deejah tayi kafin tace wai haka Habibty.. "Turo baki Deejah tayi kafin ta jefa wa Irfan hararan wasa...."Shigowar su Nadiya ne ya katse masu hiran tasu..."Gaba daya suka karasa suka rungume Ummi kowa na so taji nasa gaisuwar.
"Nilam ce tace Ummi da gaske ne kin auri Daddy yanzu, kece Ummin mu, Ummi ta rungumeta tace" Yes my little Angel, and nafi sonki fiye da kowa baby na, rungumeta Nilam tayi kafin tace" I love u ummyyy, I love yoy too sweetheart, Gaba d'aya suka zagaye ta dukanyaran, Irfan, Deejah, Nadiya, Nilam, Amir da Kuma Ayman. Hannu Ummi ta bud'e masu gaba daya kana tace "Oya family hug... Gaba daya suka rungumeta fuskokinsu dauke da annuri, Engr dake tsaye bakin k'okfa a hankali yasa hannunsa ya share hawayen da suka zubo masa.




"Gaba d'aya sukayi shirin tafiya asibiti duba Laila da Haj idan ka dauke su Nadiya da k'annenta wanda suka ce bazasu je wari ya cika masu ciki ba, Nadiya ta cika su a mota suka wuce WONDERLAND,


"Azee na zaune reception din asibiti sai habaici mutane ke mata wai iyayenta sun cika masu asibiti da wari, waya ta ciro ta shiga neman layin Safwan , Yussy ce ta dauka kafin ta soma fad'in" Azeeza kike ko, Azee murya a sanyaye tace "Eh, Yussy tace fad'a mun yanda kike inada sak'o da zanzo na fad'a maki, snn Safwan kuma baya nan don 'yan sanda nemansa suke wanted. Jiki a sanyaye Azee ta share hawayen idonta kafin tayi kwatancen asibitin da takwa Yussy, Murmushi Yussy tayi kafin tace"This is the time Yusrah now or never, daga haka ta dau mayafinta ta fice.

"Safwan dake lab'e bayan k'ofa ya gama jinta, tuni ya fiti ya hau jibgarta yana fad'in" wata uwsr zaki fada wa Azeeza dan ubanki, Yussy ta fizge bulalan tana hararar sa ta dauko DV ta rusa masa a ciki tuni ya tsuguna yana murk'usoso, Kallonsa take vabu tausayi kafin tace"The whole truth, zan fad'a mata wacece ita, duk gaskiyar da na sani.... daga haka yussy ta fice a guje... Safwan na jan gindi yana k'walla kira wa yussy inaa ta fice....




Sameena ceπŸ‘ŒπŸΎ


πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’ *Mallakin Waye*


100


*©Sameena Aleeyou...✍🏾*


_Queen Samy Novels Forum...πŸ“–πŸ“š_


*"Assalamu alaikum my wonderful n amazing fans, Na gode k'warai da addu'o'inku a gareni, Allah ya bar k'auna...😍😘*


_Wannan shafin sadaukarwace ga duk wani Masoyin Sameena, Na gods k'warai Habibtee's😘_


*Zakiya Maliki sak'onki ya Iso min Na gode k'warai....😍*


"Gudu Yussy keyi har ta samu ta fice daga layin. Da k'yar ta sami adaidaita ta tare tana haki take mar bayanin yanda zai kaita.
"Gaba d'aya Yussy ta d'aid'aice ta fita hayyacinta, ga cikin da take d'auke dashi ga rashin kula daga mijinta, kuka take tana tuno irin abubuwanda tayiwa Deejah tabbas Allah baxai barta ba dole taga consequences a rayuwa...


"Da k'yar Da dafe bango Safwan ya samu ya mik'e hannunsa na dafe da cikinsa yake bin garu da gani kasan yana jin azaba. Koda corps are after him gwara masa ya fita yayi stopping Yusrah from revealing the truth to his very own daughter Azeezah. Mashin ya samu a bakin layinsu ya d'ale....




"Wasu luxurious cars guda biyu naga sunyi parking a harabar asibitin. "Sanye take cikin Wata leshi royal blue Mai jajayen duwatsu red Vail DA jaka da takalmi ta saka tayi kyau har ta gaji, tsan tsan kayunta ya kuma fitowa. "Engr na murmushi ya bud'e Mata marfin motan gamida mik'a Mata hannunsa na dama,
"Murmushin ta maida masa kafin ta mik'o masa nata Hannun, Da taimakon Engr ta sauk'o daga motar. A hankali ya manna wa hannun light kiss murya can k'asa ya furta" you look beautiful Hayaty,
"D'an far tayi da idanunta kafin ta masa nuni dash Irfan da Deejah dake k'ok'arin taimaka wa Baba Alhj ya hau wheelchair d'insa.
"Rik'o hannunta ya kuma yi gam cikin nasa saitin kunnenta yake rad'a mata" let them see Hayatee, besides we are not doing anything wrong, hakanma saidai ya k'ara masu dank'on soyayya susan cewa soyayyarsu rapetation ne na iyayensu...
"Kallonsa take soyayyarsa na ratsa b'argo da tsokanta..."A fili ya furta "I luv you Fateemah with all my heart, a hankali ta furta "and I luv you too....


"Irfan ne yayi d'an gyaran murya kafin yace" Daddy Ummi your love is extra ordinary, may u live together forever, rik'o Deejah yayi cikin arm dinsa yana mai kallon kakkyawar fuskarta yake fad'in" I pray that zamu zama tamkar Ku, no matter what comes our way we will never be apart.
"Murmushi Baba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login