Showing 27001 words to 30000 words out of 190738 words
Chapter 10 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
fara ba ki taɓa ce mana mutuwa za ki ba, mata nawa suke aure su ɗauki ciki, su yi rainonsa kuma su haife lafiya su shayar da abinda suka haifa? Ba za ki mutu ba, da gaske ba za ki mutu ba Fatima" Amma kuka take sosai domin bata taɓa ganin naƙuda irin ta Mami ba, jijjiga take idanunta ya zazzaro waje harshenta ya zazzago sai fisga take kamar mai aljanu, likitoci ne suka fitar da Amma ta nufi reception hankali tashe, Junaid ya tari Ammi da cewa.
"Ammi ya kike kuka haka? Kar ki ce mana wani abu ya samu Mami don Allah" Ammi ta dake ta share ta ce "Junaidu kira mini Baffanku kada ƴar mutane ta rasu na shiga uku"
"Kamarya ki shiga uku Ammi?" Amma ta kalli Zuhura ta ce "Wallahi idan Fatima ta mutu na shiga uku, ba za a taɓa ganin laifin Alhaji ba nawa za a gani, duk duniya gani ake kishiya azzaluma ce, ban san meke damun mahaifinku ba Zuhura wallahi ban sani ba" Hajiya rai ɓace ta kalli Junaid ta ce
"Wa kake da suna? Mu je can wajan uban naku" Ya yi sururu sai kuma ya bi bayanta, mota ya buɗe mata ta shiga, shi ma ya shiga ya nufi gida da ita.
Alhaji Mansur Rano na zaune a parlon ya rasa meke masa daɗi, tun asubar fari ta wayewar garin yau yake jin damuwa a zuciya, ga wani masifaffen ciwon kai dake shirin haukatar da shi, da ƙyar yake buɗe idanunsa saboda nauyin da sukai masa. Rana ɗaya tal a rayuwarsa da komai yake shirin jirkice masa tare da ƙoƙarin raba duniyarsa zuwa biyu ta ƙarfi. A hankali ya ce
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Allahumma inni lima anzalta min khairin faƙir" Ya lumshe idanunsa zuciyarsa na bugawa, tunanin Fatima ne a ransa da son sanin halin da take ciki, da zarar ya yi ƙoƙarin ambatar sunanta yake jin kamar zai mutu ko zai haukace, ransa ya ɓaci. A hankali ya miƙe da nufin tattara files ɗin gabansa yabar garin ya koma wajan aikinsa, yana miƙewa sai ya ji kansa ya sara da zarar ya rufe idanu kuma Amma ke zuwar masa cikin idanu ya ji kawai ita yake son gani a gefensa, wayarsa ya ɗauka yana shirin kiran Amma sai ga su Hajiya sun shigo, ya faɗaɗa fuskarsa tare da ƙoƙarin shimfiɗa fara'a ta maye gurbin damuwar akai. A nutse ya koma ya zauna idanunsa a ɗan zube kan Junaid domin ya kasa kallon Hajiya haka kurum.
"Ni zaka ka kalla ba Junaidu ba, ni ce nan wacce zaka kafe da kallon tuhuma Mansur" Baffa ya juya cikin ladabi ya ce "Wani abun ya faru?" Ta miƙa masa hannu tare da yi masa daƙuwa ta ce "Ubanka ka yi yana can yana dogara wa da sanda, ni zaka kalli tsabar idanuna ka tambaye ni mai ya faru? To ai kafi ɗan dako sanin ta sha Mansur, wallahi wahainiyarka ta kiyayi ramata, karka kuskura na nuna maka ɓacin raina"
Baffa kansa a ƙasa saboda juyawar da yake masa ya ce "Afuwan, ki yafe mini Hajiya"
Ta gyara zama ta ce "Faɗa mini wanda ya tilasta maka wajan auran Fatima?" Jin sunan Fatima ya sa ya riƙe kai da sauri yana mai ambaton sunan Allah ya jima kafin ya ce
"Fatima? Fatima wace haka" Hajiya ta saki baki tana kallon Baffa, ta juya ta kalli Junaid shi ma da mamaki yake kallon Baffansa sai dai bashi da ikon saka baki cikin zancen manya.
"Ni kake tambaya wace Fatima? Ni zan faɗa maka matsayin Fatima a wajanka Mansur?" Hankalinta duk a tashe yake ya sunkuyar da kansa ƙasa ya ce "Da gaske na yi makkuwa wacece Fatima?" Hajiya ta fashe da kuka ta ce "Idan tururuwa ta so lalacewa sai ta yi fiffiken tashi, lafiya ƙalou kake Mansur ko dai shaye-shaye ka fara bamu da labari?" Ya girgiza kai ya kasa cewa komai idanunsa ya yi jajur, kukan mahaifiyarsa na taɓa shi.
"Bari na tuna maka shuɗaɗɗen tarihin daka manta, Fatima matarka, wacce kukai auren soyayya da ita, kuma ita ce soyayyar farinka akan bata isa aure ba ka jirkinta da aurenta ka fara soyayya da Maryama, matarka ta farko ita ce Maryam uwar su, Zuhura, Balkisa, Junaid, Aliyu, Usman, Umar, Abubakar, soyayyarka ta farko kuma ita ce Fatima, soyayya gaskiya ce musamman first love, har cewa ka yi a aura maka Fatima da ƙuruciyarta kasancewar iyayenta wayayyu ne sun san illar haka suka hana, tana budurwa aka yi mata kishiya duk wani a duniya daka tara kake alfahari da shi sanadin Fatima ne, kada ka manta kuma da Babar Fatima da babbar Maryama aminan juna ne, silar auren Fatima da samuwar cikin da take da shi ya taka rawa wajan samun cigaban kasuwancinka zuwa matakin da kake a yanzu, soyayyar duniya ka ɗauka ka ɗora wa wannan cikin, dukda cewa bata samu ciki da wuri ba, babu wanda ya taɓa jin kansu da abokiyar zamanta, baka taɓa kawo mini ƙarar Fatima ba, yarinya mai haƙuri da ɗauke kai da zurfin ciki, albarkacin Fatima wanne kalar ci-gaba ne baka samu ba? Sai yanzu kwatsam sanda take buƙatarka sanda rayuwarta take tsakanin abu biyu zaka juya baya ka bijiri da abinda ba shikenan ba? Anya kama kan ka adalci? Kasan me kake kowa Mansur? Ko akwai abinda ya haɗaku ne, naga kai da kanka ka kai ta asibiti jiya"
Baffa kuma Abban sama ya yi wa Hajiya ƙuri da idanu kamar mai son tuna wasu abubuwan a hankali murya bata fita sosai ya ce
"Na tuna ta, Fatima matata mene ya faru yanzu Hajiya?"
Hajiya ta ce "Likita ya ce ta shafe sati tana naƙuda, ƙarfinta ya ƙare bata da wani kuzari ba zata iya haihuwa da kanta ba, ga yawon ciwon kai da zazzaɓi da take sun haifar mata da jijjiga babu mamaki ta shafi abinda yake cikinta, bama fatan haka"
Baffa ya ɗauki waya ya ce "Allah ya kyauta"
"Ma ma'anar Allah ya kyauta kar ka saka ni saɓo Mansur tashi za ka yi mu je" Ya numfasa kamar zai yi kuka saboda ciwon kai ya ce
"Na je ina kenan?"
"Asibiti, Fatima na barin wasiyya tana buƙatar ganin ka" Ya runtse idanunsa kamar kansa zai tarwatse ya ce
"Allah ya bata lafiya, idan ta tafiya ce Allah ya jiƙanta na yafe mata"
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Masur, Mansur ka ji tsoran Allah ka tuna duk abinda ka yi wa ƴar wani a rubuce take sai an yi wa taka, shi alhaki kwikwiyo ne, kada ka gina ramin muguntar da zaka rufta kanka a ciki" Baffa ya kasa cewa komai ya kara waya a kunensa ana ɗagawa bai tsaya jan zaren zancen ba ya ce
"Maryam na ba ki mintuna goma ki dawo gida yanzu, minti ɗaya kika ƙara a bakin aurenki" Yana faɗin haka ya kashe wayarsa. Hajiya ta ce "Wannan ba Mansur ɗina bane akwai alamar tambaya, Allah ya shiryaka ya dawo da kai hanya madaidaiciya"
Baffa ya miƙe tsaye sai haura sama ta ce "Idan ni uwa ce, kuma ni na haifeka ka zo mu shige kaga halin da matarka take ciki" Baffa ya ce "Ki yi haƙuri Hajiya nikam ki yi haƙuri ban iya zuwa, wallahi ana takura ni zan iya sakinta"
Kuka sosai Hajiya take Junaid na bata haƙuri ta ce ya kira mata Yaya A'isha wacce ta kasance yayar Mami, Junaid na kira ta ce ai sun jima cikin asibitin.
Suna zuwa asibitin suka tarar da ƴan'uwan Mami manyan mutane masu ilimi da hankali, da zarar Yaya A'isha ta yunƙura za ta yi magana sai Dada ta hanata, Anuty Kaltum kowa idan ranta ya yi dubu ya ɓaci masifaffiya ce ta ajin ƙarshe.
"To, da alama zaman haƙuri kawai Fatima take a gidan Mansur bamu sani ba sai yanzu, ashe mutumin banza ne bamu da labari" Yaya A'isha ta ce "Uhm, ni fa ban yarda da kishiyarta ba haka kurum jikina yake bani akwai wata a ƙasa" Tsaki Anuty Kaltum ta yi ta ce
"Sune asararru, kuma banda abinsa ai ɗauɗar gora, ciki kan shata ruwan daya dake ka shi ne ruwa, duk lalacewar goma ai tafi biyar albarka kuma ko yanzu kura ta faɗi tafi ƙarfin Allah wadai" Duk maganganun da su ke Zuhura na jinsu. Ita kanta Anuty Kaltum da biyu take, jira take Zuhura ta tanka ta ci uwar yarinyar hankali kwance.
Dr ne ya fito ya ce
"Ina mijin nata muna buƙatar yi mata c.s yanzun nan, za mu cire abinda ke cikinta" Anuty Kaltum ta ce "Dr me ake buƙata"
"Sa hannun mijinta ko uba" Ta ce "Duka basa kusa bari na saka hannun" Dr ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya miji muke buƙata ko uba" Ana kiran Baffa ya ce ina ruwansa ne? Duk an addaba masa akan wata Fatima? Duk yadda sukai daidai ne bashi da wata damuwa. Yana gama wassafawa Anuty Kaltum ta ce "Kan uba, wannan mutumin bai san wacece ni ba har ya manta sanda yake bina da Allah da Annabi a bashi auren Fatima? To zan ci kaza-kazan duk tsinannan da yake da hannu a kan wannan abun, shegu gayyar tsiya" Suka rasa yadda za su yi.
"Zan saka hannun madadin Baffa" Su ka ji an faɗa. Juyawa sukai gabaɗaya a hankali yake tafiya kansa a ƙasa, hannayensa a baya, farar jallabiyya ce a jikinsa bai taushi, ga nutsuwa da haibarsa ta bayyana a fili. Dr ya ce "Ashe kana gari?" Bai yi magana ba, bai kuma ɗago kansa ba ya amshi biro ya saka hannun. Yana kammalawa ya yi gaba Dr ya bi bayansa, yadda yake gudanar da abubuwan shi tamkar shi ne jagoran gidan.
"Babban mutum zuwan yaushe?" Nan nan bai tanka ba, shi bai ga dalilin tambayar ba idan zai zo daman sai ya nemi shawarar wani ko umarnin zuwa wajan wani? Addu'a ya yi wa Mami kana aka shigar da ita C.s kamar daga sama haka su kaga Baffa yana zuwa ya kalli wanda ke zaune can nesa hannunsa maƙale da carbi idanunsa rufe ya ce
"Da izinin wa ka saka hannu Bilal?"
Sai a lokacin ya buɗe ido ya kalli jama'ar wajan sai kuma ya yi kicin-kicin da fuska don bai son kallo ya ce "A ceton rai ai ba buƙatar izini Baffa" Baffa zai yi magana Bilal ya miƙe tsaye ya ce
"Kar ka yi mini ihu Baffa, karka mini faɗa a gaban yara" Baffa ya ce
"To tunda har ka yi abinda ba shikenan ba, ka zuba ido za ka gani" Bilal ya ce "Alheri Baffa, alherin ALLAH muke nema" Daidai nan kuma aka fito da Mami sai wata nurse hannunta riƙe da Baby, Baffa ya bi fuskar Fatima da kallo yana jin kamar ya je ya ɗauke matarsa saboda soyayya da zarar ya yi wannan yunƙurin sai ya ji kansa ya sara ransa ya ɓaci, Nurse ta bawa Anuty Kaltum baby ta amsa tana murmushi Dada ta ce "Ma sha Allah, ki bawa angon ƙarni ya yi mata huɗu ba" Ana bawa Baffa Babyn da basu san me aka haifa ba ya ƙura mata idanu sai kuma ya yi murmushi yana mai sakin jaririyar ya ce.
Banko ƙofar da aka yi da ashar ɗin da aka zunduma ya katse Ridayya daga bawa Zainaba labarin, ta miƙe da sauri jiki na rawa take kallon Meer, shi kuma yana kallon Zainaba ya ce "Ke wacce uwar ce ta kawo ki cikin gidana?"
Zainaba ta yi dariya sosai ta ce "Au ina abin yake? Ina ƙoda ina romansa? Wannan abin shi kake kira da gida?" Zameer ya ce "Fita munafukar wallahi zan yi maganinki soon, kuma ba ke babu matata" Ta ce "Wallahi tallahi ni da Ridayya mutukaraba, duka kuma shege ka fasa nima tsohuwar ƴar tasha ce ni wallahi ka kiyaye ni" Zainaba bata da burin daya shige ta ji ci gaban labarin, keke faruwa a cikin asibitin me Baffa ya ce da yaga Ridayya a zanin goyo?
"Ki kwashe kayanki za mu bar wannan gidan" A rikice Ridayya ta ce "Ba dai sakina za ka yi ba?" Zainaba ta ji kamar ta dannawa Ridayya ashar ta dinga zabga mata harara ya ce
"Ban sani ba, gidan ba nawa bane yanzu, kai kima nemi wajan kwana yau kafin gobe da safe yanzu masu gidan za su shigo" Yana faɗin hakan ya fice yasan dole ta neme shi, Ridayya ta rasa me zata ce ta dinga sakin ajjiyar zuciya, Zainaba ta kwashe mata abin kwasa ta zuba a gidanta daman babu uwar komai, sanadin caca Zameer ya siyar da duk abinda ta mallaka. Daga nan Ridayya a ƙafa ta nufi gidansu Zameer wajan Mama domin ta kwana a can.
Sheƙeƙe Mama take kallon Ridayya kafin ta ce "Ai bamu da wajan kwana wallahi ki yi haƙuri ki nemi wani wajan" Ridayya ta ce "Mama Meer ɗan'kine ni surukarki ce idan ba ki wani wajan kwana ba waye zai bani?" Mama ta yi dariya ta ce "Yau dai bari na faɗa miki gaskiya, bani da alaƙa da Zameer ban san waye shi ba, kamar yadda kika ganshi haka nima na ganshi, asali Almajiranci ya zo Kano shi ne yake mana aike daga nan muka riƙe shi kamar ɗan'mu saboda yana ɗan taimaka mana kuma kwana biyu ba uwar da yake bamu, ke yanzu kina nufin kafin ku yi aure iyayenki ba su yi bincike ba? Wallahi ban san waye Zameer ba, ban san kuma iyayensa ba don Allah fice mini daga cikin gida......
Ina jiran comment ɗinku, a duk inda kuke🥰🫶🏼
#Munafukinmiji
#Labarin Ridayya
#Masur&Fatima
#Ƙaddara
#Rashin bincike
#Baƙin kishi
#Son zuciya
#Kishiya
Na'ima Sulaiman Sarauta
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI 11 ✿*
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
A rikice Ridayya take kallon Mama, da alama ta kasa yarda da kuma fahimtar zancen nata. Mama ta ce "Wallahi tallahi bani da haɗi da wani Zameer, ba dangin iya babu na baba, ai asali da tushen shi yana ƙauye da ina jin? Almajiri ne sosai a nan makarantar almajirai ta Malam Iro, tun yana ƙarami dai da kashinsa a gindi aka kawo shi, ba kowa zai san ba ɗan Kano bane, tunanin kowa mune iyayensa"
Bakin Mama Ridayya ke kallo, ta kasa sanin ainahin inda zata zuba kalaman nata, har ta fahimta daidai. Da ƙyar ta buɗe baki ta ce "Mama kin gane wa nake magana akai anya? Mijina fa Zameer ɗan'ki"
"A'a gyara kalman bakinki, ban yi cikinsa ba balle na haifa na ba ki shi ki aura, bai kuma sha nonona ba, lafiya ras nake da alama kece tunaninki ya yi ƙaura daga kwakwalwarki, nutsuwarki ta bar gangar jikinki, Zameer Almajirin Malam Iro ne" Ridayya ta fara kallon Mama dishi-dishi hawayen da suka jima da yin hijira daga idanunta suka fara bin fuskarta ba tare data shirya zubar su ba, bakinta na ɓari da ƙyar take iya motsa bakin saboda ƙonan fuskar daya kame tare da tattare wa waje guda.
"Me ya sa Mama? Me ya sa kika ɓoye wa iyayena gaskiyar al'amarin? Kun rufe ni kun cuce ni"
Mama ta buga cinya ta ce "A'a a hir ɗinki wallahi kar ki kuma cewa mun cuce ki, idan akwai wanda ya cuce ki bai shige iyayenki ba, da suka kasa yin bincike a kan wanda za ki aura, sai kuma zuciyarki data zama kurma akan Zameer ɗin, don me ake cewa a yi bincike kafin aure? Ai saboda irin haka ka je ka auri ɗan fashi ko kidnapa babu uban wanda ya sani, kinga ni fice mini daga gida kada ki saka bakina ya yi tsini" Kuka Ridayya take kamar ranta zai fita wannan wanne irin lamari ne? Ikon Allah da ƘUDIRAR ALLAH ke riƙe da rayuwarta a yanzu. Waye Mijinta? Ina ne garinsu mene mafita? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un.
"Mama kin cutar da rayuwata ki sani Allah ba sai bar ki ba, na san ba za ki so a yi wa ɗiyarki dake gidana haka ba, domin aure ba abin wasa bane" Sheƙeƙe Mama ke kallon Ridayya kafin ta ce "Wacce ƴar rawa ce a gidan ki?"
"Khairiyya!"
Ta bata amsa a raunace ƙirjinta na ɗaga wa sama, kamar wacce Asthma ke shirin kama ta. Mama ta ce "Tab, wata aba ce haka kuma? Bani da wata yarinya mai irin wannan sunan nikam" Dam! Ƙirjin Ridayya ya bada sauti juwa na ɗaukar ta, ta sulale a wajan tana riƙe da ƙirjinta sunan Allah take son kira ta gagara furta komai. Ganin haka ya saka Mama figar hannunta ta ce "A'a ba za ki mace mini a gidana ki ja mini jarfa da zunɗe, ke da can ba ki yi tunani da nazarin wanda kike tare da shi ba sai yanzu da masifa ta faɗa miki? Ni duk wani Almajiri nawa ne ba ruwana da sanin waye shi" Ta hankaɗa Ridayya waje ta rufe ƙofar gidan. Tana faɗin
"Yaran zamani da masifar kwaɗayin abin hannun samari, da shegen iyayi da kinibibi da kunga namiji yana murza shadda ya kafa hula kyakkawa da shi sai ku liƙe masa? Ba kusan kura ce da fatar a kuya ba, yawanci cima zaunane masu burin tsiya, su kuma iyayinki ganin Allah ya rufa musu asiri suka bashi ke da tunanin ya cancanta, ko kuma tunaninsu arziƙi gare shi?" Ta yi ƙwafa tana komawa tare da zama ta ci-gaba da yanka albasa da kabejin awarar daren da take yi almajirai da ƴan unguwa na siye, ta girgiza kai ta ce "Ai bada kuɗi ne kawai arziƙi ba, hadda miji na gari a wannan zamanin arziƙi ne, ni kuma mene nawa? Kuɗi kawai ya biya ni ya ce na yi masa komai a matsayin uwa" Haka kurum ta ji kamar bata kyauta ba na ɓoye gaskiyar waye Zameer da ta yi, kila a kyau masu sonta wanda suka fishi nagarta da komai, idan ta tuna kuɗi ya bata fa sai ta ji ko a jikinta. Ta share batun Ridayya tare da ci-gaba da aikin gabanta domin a yanzu bata da wani abu daya dameta.
Ƙafafuwanta kawai take cillawa ba tare da sanin inda take saka su ba, wani irin duhu ne ya mamayewa idanunta jiri na ɗaukar ta tare da ƙoƙarin yasar da tsamurarren jikin nata, har ta ƙarasa tsakiyar titi bata sani ba, dukda irin horn da masu abeben hawa suke mata. Wawan burkin da aka ja, da kuma sauke mata lafiyayyen marin da aka yi ya saka ta dawo cikin hayyacinta mutumin