Showing 30001 words to 33000 words out of 190738 words
Chapter 11 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
daya fito daga cikin mota ba shiri ya ce
"Ke wacce irin mara tunani ce da za ki zo tsakiyar titi kamar kin samu hanyar gidan ubanki, e?" Wani ya leƙo daga mota ya ce
"Da ka yi mata afuwa bana jin data da cikakken hankali fa, ko babu komai a girme ta girmeka sai ta ci albarkacin hakan" Cikin kumfar baki ya ce
"Matsalar ta ce wannan kuma hauka ai bani na ja mata, irin su ne masu yawa mutane bala'i"
Murmushi Ridayya ta yi idanunta akan mutumin ta ce "Rashin adalci da ka yi mini daka hana motarka bi ta kai na, wallahi farin cikina a yanzu bai shige mutuwata ba, inama baka dakatar dani ba? Ina ma ka take ni ka yi gaba abinka, babu mai ce maka don me, mai gata shi ake nema wa ƴanci" Ya yi tsaki yana komawa mota ya ce "zafin talauci hauka ne? Kowa idan masifar yunwa ta masa yawa sai ya nemi kashe kansa aikin banza aikin wofi, wahala ku ta ganku" Ya yi wa matarsa key tare da barin wajan, Ridayya ta bisa da kallo domin kamar ba Hausa yake mata ba, laɓɓansa kawai take kallo ta kasa fahimta. Ɗaya mutumin mai bawa Ridayya wancan haƙuri ya dinga kallon Ridayya, yarda maganarta ke fita a hankali a kuma taushashe da yarda take marairaice fuska a shagwaɓe ya saka ya fahimci yarinya ce masifar wahalar rayuwa ce ta mayar da ita haka. Daga gefe guda yana mamakin wasu mutanen da basu iya taimako ba sai gori da arziƙi kamar iyalan ƙaruna.
Ya fito daga motar ya ce "Sannu baiwar Allah kamar kina buƙatar taimako?" Ta yi masa ƙuri da idanunta ta kasa furta komai saboda kwarjinin da ya yi mata. A hankali ya zaro kuɗi a aljihu ya miƙa mata ya ce
"Gashi kya ci abinci"
Kamar ƙaramar yarinya ta maƙale kafaɗa, ita yanzu ba kuɗi take buƙata ba, wanda zai ja ta ya rungume ta ya rarrashe ta, shi take so. Yin duniya taƙi amsa, sai kallonsa take kamar zata bisa, ya zaro card ɗinsa da number shi ya ce
"Ki kira ni, when you need my help ok?" Ta amsa ya juya a hankali ya ji ta ce
"Abbiey!"
"What? What did you say?" Ta juya da sauri ta bar wajan, ya yi murmushi a fili ya ce
"Ikon Allah" kuɗin daya fito da su ya bada sadaƙa da nufin Allah ya bata lafiya ya kawo mata sauƙi cikin lamuranta. Mota ya shiga daman akan hanyar barinsa garin yake.
Ridayya bata nufi hanyar gidan mijinta ba, tafiya ta cigaban da yi bakinta na motsa wa kamar bai magana, harta ƙarasa gidan Baffa, yanayin yadda taga gidan ya saka ƙirjinta bada wani ƙyakƙyawar sauti, bai yi kama da gidan da mutane suke rayuwa tare da wanzuwa a cikinsa ba, ya dinga kallon cikin gidan daga waje babu mota ko ɗaya sai uwar ƙura duk flowers ɗin sun bushe sun mutu murus ya zama kamar kofai. Ta runtse idanunta sunan Allah take son kira amma ta kasa, me ya sa sai yanzu take buƙatar jin ra'ayin Mami a kan lamarin aure da yardar ta? Me ya sa Mami bata taɓa janta a jiki ba? Me ya sa sai yanzu take son rayuwa da Maminta. _When all is gone...!_
Hannu ta sak ta dinga bubbuga ƙofar gate ɗin a raunace ta ce "Baffa ka buɗe mini ƙofa na dawo, Mamina na dawo gani na zo ba zan ƙara zaɓar kowa a kan ku ba, Mamina buɗe mini ni ce Ridayya" ƙofar take bubbuga wa sosai ta ce "Bakwa jina ko? Yunwa na ke ji Mami shi ya sa muryar tawa babu ƙarfi, Mamina zan ƙara haihuwa za ki samu jika, Baffana wai ka dawo ashe kana nan" Shiru ba amsa, ta dinga buga wa da iyakar ƙarfinta. Ta matsa ɗaya ɓarin ta ƙura wa side ɗin Ustaz idanu tana tuna sanda yake bata abinci ya goyata tana tuna yadda duk wani motsinta yake kan idanunsa. Ta rufe ido tana sauke ajjiyar zuciya a cikin raunatacciyar muryarta mai tsananin sanyi ta ce.
"Abbiey, i miss You"
Waje ta nema ta zauna da nufin ta jira su dawo ko unguwa suka je, sai dai Ridayya bata san sun yi tafiyar da babu waiwaye balle batun dawowa a cikinta ba, sun je inda ko wanne mai raye sai ya ke ko baya su, sun je gidan gaskiya. Tana ta zaune ko motsi bata yi saboda galabaita ga cikinta daya fara motsi alamar yana cikin wata na huɗu yanzu yana buƙatar ɗaukin gaggawa, a nan wajan bacci ya ɗauketa. Ita yanzu ba kowan kowa ba ce, but an unprivileged woman
Lagas/ Ikeja
Birnin Legas, ko kuma Birnin Ikko, shi ne babban birnin Jihar Legas da ke Najeriya. Legas yana ɗaya daga cikin birane mafi girma da yawan jama'a a Afirka da ma duniya bakiɗaya. Legas ne birni na biyu mafi girma a Afirka, kuma na bakwai a duniya.
Government Residence Area (GRA). Unguwa ce babba mazuna manyan mutane.
Idanunsa a lumshe yake sauraran maganganun da ake yi ta cikin wayar dake saman kujera wacce ya sanya a handsfree. Yadda yake sauke ajjiyar zuciya a hankali yana tura hannunsu cikin kansa za a ɗauka bashi ke yin wayar ba, ɗan gajeren tsaki ya ja a fili yana haɗe yatsun hannunsa wanda suka bada wasu sauti kafin a hankali ya buɗe sanyayan idanunsa masu kaifi da wani kwantaccen sirri a cikin su. Cikin gajiya da maganar mutumin ya ce
"Enough" Ya faɗa cikin kakkausar murya yana mai sauke numfashi da ƙyar saboda nauyin ƙirjinsa da yake ji. Ta cikin wayar aka ce.
"Be patient Ustaz Bilal, ka ɗauki ƙaddara watanni nawa da faruwar hatsarin nan mun yi iyinmu mun faɗa maka gabaɗaya mutanen ciki sun ƙone" Ustaz Bilal ya manta da waye yake waya cikin hargowa ya dakawa DSS (Department of State Security) tsawa ya ce
"Liar, wanne irin hatsari ne a ce kowa ya rasu, my own family? Kana nufin na rasa kowa, e? Mene amfanin (IPO) a cikin police ne?"
DSS ɗin ya ce "Investigating Police Officer" Ustaz ya jinjina kai ya ce "Good, to ya ƙara bincikawa familyna suna raye kar ka sake kira na muddin bada Baffa za ka haɗa ni ko Junaid ba" Ya kashe wayar yana miƙewa tsaya, Nasir ya dinga bin Ustaz Bilal da kallo a ɗan tsorace domin bai taɓa ganin zallar masifar Ustaz irin yau ba, ana cewa masifaffe ne bai taɓa gani ba amma yau shi kam zai bada labarin haka. Ya miƙe ya ce
"Md komai ya yi zafi maganinsa Allah, ka yarda da ƙaddara ka yarda cewa dukkan mai rai mamaci ne, ka yarda cewa aljalinsu ne ya zo lokacin ɗaya, mutuwa wajibi ce hisabi gaskiya ne, rayuwa ƙarya ce kuma wa'adi ce, ina iliminka ina da tauhinka"
"Yana gidan ubanka, na ce yana gidan Ubanka Nasir tsahirta mini" Nasir ya ja baya yana gwaloido ya ce "Asstagafirullah, yau Ustaz da zagi? Wallahi dole na saka Hajiya ta yi maka aure" Ustaz Bilal ya yi kamar zai shiga ɗakinsa yana zuwa dab da Nasir ya saka hannu ya damƙo shi tare da jansa har bakin ƙofa, ya cilla shi tare da rufe ƙofar yana dafe kansa ya ce "Haihuwa za ka saka a yi mini ba aure ba, stupid".
Nasir ya dinga dariya, koba komai yau ya ja Ustaz da magana a ƙasan zuciyarsa kuma yana mai tausayinsa domin duk wani bincike ya nuna Ustaz Muhammad-Bilal ya yi rashin ahhalinsa yana buƙatar mai kula da shi, ba kowa yanzu Ustaz ke buƙata ba face Mata wajan zata kula da shi, amma shi ganin kansa yake tamkar waliyyi bai taɓa jin ko da wasa Bilal ya yi maganar mace ba, balle kuma aure ko bashi da lafiya ne Ohho ko irin first love ɗin nan bai taɓa gwada yi ba.
Nasir yana ƙoƙarin ficewa mota na shigowa cikin gidan, ya ware Idanu ya ce "Wonder shall never ends, wa nake gani kamar Baita?"
Murmushi ya yi yana buɗe idanu tare da watsa hannu alamar oho maka. Nasir ya daki kafaɗar Baita ya ce "Let's keep a joke aside, when did you came?"
"Jiya" Baita ya ce a taƙaice yana kallon Nasir, sai kuma ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na tashi, wani abu na son fusgarsa da son ɗarsa abun da bai shirya ba. Allah Allah yake ya ƙarasa wajan Ustaz babban amininsa ya yi sharing damuwarsa da shi. "Shi ne ba waya? Ko chat?" Baita ya ɗaga kafaɗa ya ce "Bazata" gaba ya yi abinsa ya ce "Ustaz fa? Md"
"Kamar ka shiga, don baya cikin nutsuwarsa wallahi yau ko Bank bai je ba" Baita ya tsaya cak tare da jin abinda yake faruwa da Ustaz ɗin, don dama yana ta kiran wayarsa bai ɗauka ba. Nasir ya san Baita ba zai magana ba hakan ya sa ya ce "He lost his entire family in an accident" Baita ya zaro ido sai kuma ya runtse da kyau yanzu da me zai ji da rarrashin Ustaz Bilal ko kuma da matsalar yarinyar da ta tsaya masa curr a rai?
Iskar hadarin dake kaɗawa ya sanya Ridayya farkawa daga bacci wahalar daya ɗauke ta, ba tare data shirya ba. Ta miƙe da sauri tana murza idanunta tare da kallon gate ɗin gidansu har yanzu basu dawo ba? Ta juya taga duhu ya fara a hankali ta ce "Ko sai yaushe za su dawo? Mamina, Baffa gobe zan dawo na ganku kun ji?" Ta ja ƙafa ta nufi gidanta ta mance da cewa yanzu ba mallakin mijinta bane. A ƙofar gida ta samu Zameer a zaune ya wanka wani voyel mai laushi har farar singlet ɗin ciki ana gani ya yi kyau, gefensa kuma leda ce sarai ya ganta ya share ya ta nufi ƙofa sai ta tsaya ganin gidan a garƙame da kwaɗo. Ta juya ta kalle shi ta rasa dalilin daya sanya yau ko kyansa bata gani ba, duk yadda ta kai da danne zuciyarta wajan ganin bata ji zafinsa ba. "Ka buɗe mini?"
"Daga ina kike?" Ya tambaye ta yana miƙewa tsaye tare da mayar da wayarsa zuwa cikin aljihu, ta kafe shi da ido taƙi magana. Daram! Ya ji zuciyarsa ta buga, ba tare da sanin dalili ko hujjar hakan ba, abu ɗaya ya fahimta, rashin tsoro da tausayin da suke shimfiɗe a idanun Ridayya yau babu su, tarwai yake kallon cikin idanunta, ya rufe ido ya buɗe wannan kwantacciyar soyayyar babu ita idan har yaren soyayyar daya karanta idanunsa sun faɗa masa daidai. "Daga ina kike? Kar ki bari na maimaita maganata idan ba haka ba, za ki mamamkina"
"Mamaki na nawa kuma ZAMEER?" Ya zaro ido jin ta ce Zameer yau Ridayya ta kalli cikin ƙwayar idanunsa ba shakka ba tausayi, da wannan soyayyarta ta, kai tsaye gatsal ta ce Zameer? "Sunana kika kira Ridayya, sunana Ridayya" Still idanunta a cikin nasa ta ce "Kenan daidai na faɗa ashe, Zameer ko?" Ya shanye mamakin ya san fushi ta yi yana mata daɗin baki zata sakko, sai dai ko a fushi Ridayya bata taɓa tsare shi da wannan rikirkitattun idanun nata ba sai yau.
"Daga ina kike?" Kai tsaye ta ce "Gidan iyayena, gobe ma zan koma don ban tarar da su ba" Ya yi wani murmushi ya ce "Opps sorry, ai na manta ban faɗa miki ba iyayenki duka sun mutu babu kowa da ya yi saura hatta wannan farin mutmin Bilal ko? Shi ma ya mutu?" Murmushi ta yi dukda jiriri ta ji yana kwasarta ta ce "Tom, buɗe mini gidan" Don ita ta san babu yadda za a yi kowa nata ya mutu yabar cikin wannan rayuwar.
"Na faɗa miki Baffa mota ta bi ta kansu ta, an ce ma kansa ya gutsire kuma huta ta babbake su kamar yadda ake babbaka taya....," Saukar wani lafiyayyen mari Zameer ya ji a fuskarsa, tunda yake a duniya ba a taɓa marinsa ba, marin daya shige shi irin yau ba, ya juya ya sake juyawa yaga babu wanda wake gani a gabansa sai Ridayya. "Ke! Wa kika ga ya mare ni ya gudu?" Kai tsaye ta ce "Ni ce, kuma ban gudu ba" Ta faɗa tana shigewa gidan Zainaba. Zameer ya bi Ridayya da kallo domin ya san ba zata taɓa marinsa ba, ƙarya kawai ta yi kansa har wani za fi ya ɗauka.
Zainaba na zaune kamar daga sama taga Ridayya ta shigo a rikice domin ta ɗauka Zameer ya biyo ta, bata taɓa tunanin zata yi wa Zameer ko da tsawa ba amma sai gashi har mari, ba zata taɓa cewa ga sanda ta mari Zameer ba. A gigice Zainaba ta bawa Ridayya ruwa ta sha, ta bata abinci amma taƙi ci hannunta ƙanƙame da card ɗin da mutumin ya bata. "Tunda ba za ki ci abincin ba, kwanta ki huta idan kin tashi sai ki yi wanka"
"Ina son Zameer ya sake ni, hallayarsa bata irin mijin da nake so ba ce" Wani farin ciki ya mamaye zuciyar Zainaba amma ta ɓoye ta ce "Saki kuma? To idan ya sake ki ina za ki?" Ta ce "Wajan Baffa da Mami ko Abbiyena" Zainaba ta jinjina kai ta ce "Kuma zai sake kin?"
Wani irin kallo Ridayya ta yi wa Zainaba sai kuma ta yi murmushi ta ce "Wallahi wallahi Allah na gama zama da Zameer wallahi sai ya sake ni" Zainaba ta yi hamdala tana ƙoƙarin tashi Ridayya ta ce "Zauna na ƙarasa miki labarina wanda na fara, zan baki gabaɗaya labarin a daren nan, domin daga gobe ba za ki ƙara gani na ba" Zainaba ta gyara zama sosai, Usman mijin Zainaba da sauri ya dawo ƙofar ɗaki ya zauna cike da zumuɗin jin cigaban labarin Ridayya. Ridayya ta lumshe idanunta a hankali ta ci gaba da bawa Zainaba labarin.....
Back to story
Baffa ya saki babyn tana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa, Bilal ya yi saurin tare ta, ta faɗa hannunsa ya yi saurin rungume ta a ƙirjinsa saboda jin ta tsala ihu. Gabaɗaya suka kalli Baffa wanda har lokacin babyn yake kallo wacce take ƙirjinsa ya yi girgiza kai ya ce
"Bana ƙaunarta wannan ba ƴata ba ce a kaf zuri'ar Mai ran ƙarfe babu baƙin mutun babu mai munin wannan jaririyar, ni Alhaji Mansur Rano bani na yi cikin wannan yarinyar ba a nemi ubanta wani wajan....
*Haba don Allah yanzu idan ka karanta littafin nan ba zaka iya sharing to others groups ba? Mutanen da suke tambayata Allah ya yi wa da su, ina neman alfarma duk wanda ya karanta ya ya yi sharing saboda ALLAH👏🏻*
Na'ima Sulaiman Sarauta
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI 12 ✿*
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Anuty Kaltum ta ce "Alhaji Mansur me kake nufi da jaririyar ba ƴarka ba ce?" Baffa ya yi wa Anuty Kaltum kallon ki shiga hankalinki kafin ya ce "Ina nufin abinda na faɗa, wannan yarinyar da Fatima ta haifa a nemi ubanta wani wajan, bani da haɗi na jini ko gamuwar ƙwayar halitta, ita ɗin ba jinina na ba ce, I'll never accept her as my biological daughter, kuna iya neman ubanta wani wajan"
"Kam bala'i, wa kake da suna Mansur ko wa? To wallahi ƙarya kake idan ma shaye-shaye ka fara ka zo zaka mana maye a nan to yanzu zan dawo da kai cikin hankalinka, kana da yaƙini da tabbacin Fatima bata taɓa yin wani saurayi bayan kai ba, balle ka ce wani abu ko ka saka kalmar zargi a ranka, wannan kuma jaririya bata da wani uba daya shige kai Alhaji Mansur Rano, kamar yadda su Junaid su Zuhura suke ƴaƴanka, wanda ka yi cikinsu to haka wanann jaririya" Anuty Kaltum ta ƙare maganar cikin masifa da kumfar baki, ita daman faɗa ba nata bama siya take balle ya shafi jikinta da suke uwa ɗaya uba ɗaya?.
Baffa ya yi kicin-kicin da fuska kana ya juya ya kalli yaransa da suke tsaye a wajan ya ce
"Wa kika gani baƙi ko mummuna a nan cikin jerin yarana? Tunda nake haife-haife ba a taɓa haifar mini jariri mai munin halitta da baƙin kamar kalwa ba sai wannan mummunar jaririyar, babu ta inda na zama ubanta ba zan taɓa zama ba" Anuty Kaltum ta ce "Ok sai ka faɗa mana waye ya amshi budurcin Fatima a daren aurenku?"
Baffa ya ɗaga kafaɗa ya ce "I am the one, but this baby will never be my daughter" Yaya A'isha dake tsaye itama ta ce "Sai a yi DNA TEXT, a nan gaskiya zata fito"
Baffa ya ce "Ba DNA TEXT ba, ko cikin yarinyar zan ƙara a sake haifar ta, ba zan taɓa amsar ta, ku je ku nemi ƴar'uwarku ta yi muku explanation uban yarinyar sai a kai masa, amma....,"
Maruka aka shiga saukewa Baffa ta ko'ina, ya runtse idanunsa ganin yadda aka mare shi a kan idanun yaransa. Rai ɓace Hajiya ta ce "Ba shakka, dole ka nuna mini ka isa wannan shi ne kalar adalci da halaccin da zaka yi wa Fatima? Yarinyar da sadaukar da soyayyarta ga ƴar aminiyar babarta, ta haƙura har sai ta girma ta kai shekarun da iyayenta suka ɗiba na girmanta, a bayanka; wanne kalar samari ne Fatima ba ta yi ba, wanda suka fika kyau, arziƙi na saba, cancanta? Amma duk ta saka kamar ta share su, tana ganinsu tamkar mata kai kaɗai ta kewa kallon namiji, wanda zai wadata mata da komai? Zai bata farin ciki, ta dinga jin kalaman soyayyar su, kamar busar sarewar Audu" Hajiya ta share hawayen idanunta ta ce
"Cikin daka ƙwallafa rai a kan shi, ka ɗauki burin duniya ka saka wa cikin, har kake cewa duk abinda Fatima zata haifa maka tabbas mai ƙashin arziƙi ne, Mansur yau a gaban iyayen Fatima akan idanun surukarka kake aibata abinda ɗiyarta ta haifa? Kake ƙoƙarin liƙa wa ƴarta kalmar zina? Ina tunanin ba abinda Fatima ta haifa ba ko wata ta ɗakko daban zaka saka hannu bibbiyu ka riƙe, Mansur! Mansur! Wallahi ka haukace"
Baffa ya ce "Lafiya lou nake, wallahi Hajiya ina cikin hankalina a nemi uban yarinyar, matata Fatima kuma a mayar mini da ita gidana"
Jama'ar wajan sun fi yarda Baffa ya samu matsala da tunaninsa, duk wani wanda ya san Baffa ya san labarin soyayyarsa da Fatima-zahrah bashi da wani sukuni sai nata, har ya yi aure jinsa yake empty without his Fatima Batool. Ammi har