Showing 186001 words to 189000 words out of 190738 words

Chapter 63 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17285

tafka" Zainaba ta taɓe baki ta ce "Jama'a yau ga Zameer a lalace? Ina ita shegiyar yarinyar Khairy take kowa?" Moo ya ce "Ai ita muka zo dubawa, ta yi hatsari ne ga matsala data samu har an cire mata mahaifa ba zata kuma haihuwa ba, shine ta buƙaci ganin Zameer ya yafe mata kan sharrin da ta yi masa na kawowa masa yarinya bayan ta san ba shine ubanta ba, ta buƙaci ya bata yarinyar shi kuma ya ce ba zai bayar ba ya dai yafe mata, kema ta roƙi daki yafe mata"


"Ina ruwana da ita? Allah ya yafe mana bakiɗaya"


"Ridayya don girman Allah ki dawo gare ni wallahi mutuwa zan yi" daidai nan Ustaz ya ƙarasu wajan hannunsa ɗauke da little Bilal, yana zuwa Zameer ya yi saurin buɗe idanu yadda kasan photocopy akai na Ustaz a fuskar little kamar ya yi kaki ya tofar, Zainura ta ƙarasu wajan hannunta ɗauke da Sadauki da Al'hussan. Zainaba ta gai da Abbiey ya jinjina kai ya kama hannun Ridayya suka bar wajan "Daman taya kake tunanin zata dawo wajanka kamar ita ta zalunce ka? Ai kai da ita sai dan irin wannan ganin daga nesa yasin" Zainura ta ce "Wallahi, wannan yaran nata ne ƴan'uku ta haifar jajur" tana faɗin hakan ta bar wajan itama. Hawaye ya shiga sakkowa a fuskar Zameer Hanne bata ganin girmansa ga yaransa sai addu'a musamman macen, ga babu aiki sai zuwa gona abokai duk sun guje shi Moo kawai ya rage da ace Ridayya na gefensa da komai mai sauƙi ne a gare shi, zaman Kano ya fi ƙarfinsa Ridayya ta fi ƙarfinsa a yanzu duniya ta tabbatar shi ne ya zalunce ta tunda Ubangiji ya yi mata sauyi a rayuwa.


Wata biyar bayan dawowarsu suka koma hadaɗɗan gidan Ustaz, Umma sosai take ƙaunar Ridayya da yaran da sukai ƙima sosai da wayo aka haɗa Auren Junaid da wata yarinya Iklas sai Zainura da Burhan akai aure lokaci guda, tsakanin Mami da Ammi mutunci ne kawai Tajj ya samu ya yi aure shima da ƙyar Prof ya bawa Hajja Azizat takardar saki.


Misalin ƙarfe tara na dare ta shigo parlon tana sabga ƙamshi uban ƙamshi kanta a ƙasa ta ɗora mayafi saman ɗaurin ɗan kwalin da ta yi na black and gloden ɗin lace sai walƙiya yake a hankali take ta kawowa har ta zo tsakiyar parlon, tunda ta shigo yake kallon ta da wani expression looking da emotions na shekarun baya da suka shege sai yanzu da suke motsa masa a ƙirji da zuciya ashe ba mutuwa sukai ba kawai dole ta saka suka kwanta. Ya ɗan yi tattausan murmushi irin na manya ya ƙarasa tare da buɗe mayafin kanta ta yi saurin yin ƙasa da kai tana murmushi, bata san cewa dattijon zamani bane sai da ta ji ya rungomo ta zuwa jikinsa ya ce "Allah Allahamdulilah daka mallaka mini Azizatuna.....




Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
*MUNAFUKIN MIJI*


Nimcyluv
49-50


Mikiya writers Association.


"Abba" ta furta cike da kunya shi kuma ya riƙe ta da tafukan hannayensa, dukda cewa ita ta yi requested auren a wajan shi, amma ji yake kamar ta shiga zuciyarsa, dukkan wasu ƙofofi na zuciyarsa a buɗe suke ƙara raya kan su suke da farfaɗo abinda ya kusa macewa a tsakiyar ƙirjinsa. Hajja Azizat ta ce "Congratulations" Baba ƙarami ya saki hannunta baya ya yi mata runguma ƴar sunna ya koma ya zauna a hankali ya ce "Allahamdulilah" ta nemi waje ta zauna ta ɗan buɗe mayafin kanta sukai shiru can baba ƙarami ya ce


"When last rabon dana ganki haka kusa dani Azizat?"


"Tun ranar ɗaurin aure na" ta furta cikin ƙasa da murya ya jinjina kai kamar yadda Abbiey yake idan yana son kawar da zancen addu'a ya yi sosai mai tsayi kana ya shafa ya ce.


"Allah ya bamu zama lafiya"


"Amin"


"Am still on your mind kenan? Wanne qualities kika gani wajan tsoho mai tarin jikoki har kikai sha'awar aurena?" Ta yi masa wani irin kallo kafin ta ce "Tun qualities ɗin dana gani a baya na nace maka, shi ne dai"


"And you left me, har yanzu ban san dalili ba"


Ta ce "Destiny! Ƙaddara mana ita ce dalilin Abba ta raba mu and now we are together, za mu kasance har abada"


Ya yi murmushi yana shafa gemunsa ya ce "In sha Allah" sai ya kalleta sosai ita dai still da garin ƙuruciyarta daman ba wani jikin kirki gare ta, a goge fatarta take ƴar daidai da ita.


"Tahir ɗin da kika sani a baya yanzu fa bashi bane Azizat, ina da yaro mai shekaru wajan 40 gani da jikokai, anya zan iya sauke nauyin ki kowa? Ba ki yi kuskuren zaɓe na a karo na biyu ba?"


Idanunta a kansa ta ce "I'll never regret in sha Allah Abba,in dai kana so na ai komai mai sauƙi ne" bai ce komai ba ya ɗauki wayarsa ya duba, daman tun kiran farko da ta yi masa ya san kwanan zancen yaƙi zuwa wajanta ne sai da ta gama idda, tana gamawa kuma ta masa text via mail kai tsaye, bai tashi zuwa wajanta ba sai da ya tabbatar igiyar aurensa ta hau kanta, bayan shaidu sun shaida. Ya miƙe tsaye ya ce "Zan shige ni" ta ce "Tun yanzu ango?"


"Kina da wajan ajjiye ni ne?"


"Sosai ma" ya girgiza kai ya ce "Kina buƙatar wani abu ne?"


"Babu sai abu ɗaya" har zai tafi ya ce "Me?"


"Bari kaga" ya tsaya ta ƙarasu wajan kafin ya ankare ta rungume shi tare da yi masa kiss a kumatu, ya hangame baki ya zama kamar statue ya ji kamar wani ke jan shi, ta yi masa bye bye yana dai tsaye bayan ya tabbatar ba wanda ya ga wannan abin kunyar ya sauke numfashi ya fice.


Fitowa Abbiey ya yi bayan sun kammala magana da Ridayya ya nufo hadaɗɗan main da yake tsakiya yana gaba tana biye da shi hannunta riƙe da hula, ta dube shi ta ce. "To Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri" a nutse ya ce "Amin, shi ne ma tunda bana jin siyasar a raina"


"Haka ne, kawo na saka maka hular"


Ya rausayar da kansa gefe yana kallon yadda take ɗage amma ta kasa ta bashi hular kuma taƙi shi kuma yaƙi sunkuyo da kansa ƙasa "Abbiey please ka miƙo kan" yaƙi cewa komai sai kallon ta kawai da yake da wani irin yanayi mai fisgar zuciyar duk wata budurwa. Ta ɓata rai sai kawai ya saka hannunsa biyu ya ɗago ƙugunta sama "Saka" tana dariya ta saka masa hular tare da tattare gashin ta tura cikin hular.


"Ka yi kyau sosai kamar karka fita ko'ina" ya lumshe idanunsa ya buɗe "Me zan taho miki dashi?"


"A'a ba komai"


Ya haɗe hannuwanta biyu ya riƙe "Allah ya yafe kiki Mimi, hakan kyautatawa iyali ne kuma koyarwar Annabin tsira ne, kawowa iyali tsaraba muddin akwai halin hakan"


"To ka siyo mini vanilla ice cream"


"Banda kayan sanyi" tai shiru tana tunani sosai sai kuma ta ce "Ok Gashasshen nama mai zafi da kuma L&Z"


"An gama beb"


"Thank you" ya rungume irin side hug ɗin nan ya ce "I love you"


Ta ja gemunsa da yake mata kyau kullum ta ce "You mean the world to me Hayatee" ya ƙara 10 minutes akan yadda tsara zai fita ɗin.


Umma dake sauraron baba ƙarami ba tare data fahimci me yake cewa ba ta ce "Aure kamar wasan yara kai ne ka yi auren ko dai wani?" Ya kame girka ya ce "Ni ke wasan kenan Hadiza?" Ta ce "A'a, abu ne na ji shi gaba-gaɗi" a hankali ya ce "To da gaske aure na yi wallahi Allah, kuma yau za a kawo amaryar kuma ƴar'uwarki"
"Aure dai irin wanda iyayenmu sukai mana kake magana Tahir?" A fili ya maimaita “Tahir” sai kuma ya yi murmushi ya ce "Shi dai, ai ni mijin mace huɗu ne kuma ban taɓa miki alƙawarin zama dake ke ɗaya ba, ban kuma yi auren don na ƙuntata miki ba, ban yi kuma don bana son ki ba Umma Ubangiji ya ƙaddara auren ya kasance kuma ya kasance ɗin, ki bani ƙarfin qwwa please na shaideki a bayan idanunki kan cewa ba ki da wata matsala, tunda nake dake shekaru nawa ban taɓa bijiro miki da maganar aure ba, na aure ki don ina son ki kuma zan cigaba da son ki don Allah ki cire komai a zuciyarki ku zauna lafiya ita sam bata da matsala"


Ta wani kalle shi tana murmushi ta ce "Waka aura? Ina nufin wace kishiyar tawa?"


"Hajja Azizat, mahaifiyar murgayi Sadauki"


Da wani irin firgitaccen yanayi mai ban tsoro da kuma tashin hankali, daya saka Umma miƙewa tsaye ba tare data shirya hakan ba, baki sake kawai take kallo Baba ƙarami kafin ta haɗiye wani irin yawu mai ɗaci ta ce "Now i understand, cewa za ka yi tsohuwar budurwarka ka aura domin ka nuna mini iyaka ta na cewa a rashin ta ka aure ni Tahir" ya dinga kallon ta ya ce "Amma tsakanin ki da Allah tunda muke kin taɓa ji na yi maganar ta?"


"To bayan ta yi aure ta ya ka aure ta?"


"She has been divorced" ya ce yana kame fuska.


Umma ta rushe da kuka sosai ta ce "Mayya ai na sani wallahi tana sane ta kashe auren domin ta aure ka, kawai zan tattara na bar muku gidan domin sai abinda na gani kawai" Baba ƙarami ya yi murmushi ya nufi inda take yana cewa "Zo ki ji"


6 month later
Kuka take sosai tana gogen hawayen da yaƙi tsaya mata shi kuma yana gefe yana ta yi mata dariya abinsa, ta juya ta kalli Al'hussan dake bacci gabaɗaya watan su shida, ta kalli takardar hannunta daya tabbatar tana ciki ta dube shi ta ce "Abbiey don Allah ka rufa mini asiri, na shiga uku wanne irin ciki kuma? Ni a haihuwa zan ƙare kenan" ya ajjiye wayar hannunsa cikin kulawa ya ce "Ba kowa Allah ke wa wannan ni'imar ba Mimi, ki yi farinciki this time around za ki haifa mini me kama da ke" cikin damuwa ta ce "Ai ba za kaga aibu ba, sai da na ce kar ka yi kar ka yi amma ka yi, gabaɗaya watan su Al'hassan shida ya kake tunanin za su lalace? Da wanne ido zan je gida a ganni da ciki?"


"But ba iskanci kikai ba mijinki ne ya miki shi Mimi" ya faɗa a taushashe kawai ta sake rushewa da kuka, shi abin duk mamaki yake bashi mene a cikin yin kwanika to? Girgiza kai ta yi ta ce "Zan zubar da cikin nan gaskiya ka yi haƙuri" tana faɗa tana miƙe zata bar bedroom ɗin, daman dawowarsu kenan daga asibiti saboda zazzaɓin da take hannu ya saka ya fisgota yana wani irin nishi idanunsa sukai jajir ya ce "za ki zubar da me?"


"Cikin" ta faɗa ba tsoro. Ya matse hannunta ya yi wani irin murmushi ya ce "Wannan shi ne abinda za ki yi har abada naƙi yafe miki"


"Wallahi sai na zubar yarana watan su shida kawai sai a ganni da ciki? A saboda ba kai kake shiga cikin jama'a ba? Gashi ina tunanin ƙarasa karatuna" yadda take ɗaga masa murya ya fi komai bashi mamaki ya sake ta ya ce "Ridayya kenan, muddin ni na yi cikin nan wallahi tallahi kika zubar anan za ki san waye kike aure a nan za ki ɗaya fuskar tawa, ba maganar saki a tattare dani amma abinda zan miki sai kin gwammace kiɗa da karatu ni Muhammad Bilal Tahir zan ba ki mamaki" ya sauke numfashi yana jin kansa na sara masa ya ce "Idan kuma ke kikaiwa kanki cikin fine kina iya yin abinda kika ga dama" sosai suke cacar baki abinda basu taɓa yi ba, basu yi aune ba su kaga Little ya shigo cikin sauri Abbiey ya koma bayan Ridayya yana saita yanayinsa kana ya ɗan jawota jikinsa, Ridayya ta ɗan dake tana murmushi ta ce "Jarumi na ya akai? Shigowa ba sallama ba neman permission bana hana ba?" Little dai kallon su yake ya san dai ya yi sallama har babu adadi ya ce "Kuna ta faɗa Mimi da Abbiey"


"Faɗa kuma?" Ya ɗaga kai ya ce "Kuna ɗaga murya kinawa Abbiey haka" ya miƙar da yatsar shi yana pointing wani waje, Ridayya ta yi murmushi ta juya ta kalli Abbiey ta ce "Abbiey ka ji wai faɗa muke?"


Ustaz dai ya yi shiru don bai iya ƙarya ba idan muddin ya buɗe baki to e zai ce. Ta kalli little ta ce "Wani abu muke nunawa na Film, scane ɗin ya mini kyau na ce mu yi rihazal da Abbiey amma ba za mu kuma ba" cike da gamsuwa ya ɗaga kai ya ce "To malam ya ce idan an yi faɗa za a sasanta musabawa ake" ya kamo hannun Abbiey ya kamo na Ridayya ya haɗe, Abbiey ya damƙe hannunta dake cikin nasa yana shafawa ya zuba mata idanu, ya fahimci dole ya shiryawa wannan cikin domin ta tsiwa ya zo idan tana al'ada ta yi ƙunci taƙi magana yanzu kuma ciki ya zo mata da rigima dole ya tausasa zuciyarsa ya fahimtar da ita da kyau ya kuma iya controlling kansa ya ja numfashi ya sauke yana sake riƙe hannunta little ya ce "To ku gaisa"


"Assalamu Alaika Abbiey" shi dai kallon ta yaƙe yaƙi cewa komai ganin yadda little Bilal ya kafe shi da idanu ya saka shi cewa "Sannu Mimi" little ya dinga tsalle yaro ne mai shegen wayo da surutu ya ce "Second Mimi ta zo da wata" Ridayya ta ce "Ka cire second ɗin Just say Mimi, idan da amana kuma duniya da gaskiya ai wajan Zainura zaka zauna" ya maƙale kafaɗa ta ce "And this is the last time da zaka shigo bedroom ɗina da Abbiey ba a baka permission ba, a good person never do this ok?" Ya ɗaga mata kai Ustaz dai kallon su yake, little ya fara ƙoƙarin shigewa jikinta ta ce "A'a wallahi muje" sai da ta je bakin ƙofa bayan little ya fita ta juya ta kalli Ustaz ta ce "Kuma da kake maganar saki an faɗa maka ko ka sake ni zan tafi ne? Rayuwa da kai yanzu na fara saboda ina son ka" girgiza kawai ya yi a zuciyarsa yana "Allah ya yafe miki Ustaza" wato idan baka da mace ƴar drama ma da sauran ka, ko babu komai za a saka bakinka ya motsa da surutu.


A zaune ta samu Zainura da Zainab suka gaisa sosai nan da nan ta dafa musu taliya fara da mai da haɗin salad domin bata iya dafa komai. Ta kalli Zainura ta ce "Amarya bata lefi" Zainura ta ce "Sallama na zo miki zamu shige Lagos"


"Lagos ke da wa?"


"Da mijina mana yaya" Ridayya ta ce "Ikon Allah, to Allah ya tsare ya kai ku lafiya sai na tuna zuwana Lagos sai ki dage da sana'a garin neman kuɗi ne ba mugunta, ki fara business nima za kina turo mini da kaya" har compound ta raka Zainura sai a lokacin ta lura da Burhan tace "Kake ta zauna a mota? Ban san tare kuke ba"


"No ba komai yaya"


"To Allah ya tsare ya kiyaye" suna tsaye Ustaz dake balcony yana waya ya ƙarasu suka gaisa da Burhan kana ya musu fatan alheri ya yi Zainura faɗa sosai. A haka suka fice daga gidan "Baby lafiya naga ka ɓata rai?"


"Kin bar marayan Allah a waje shi ɗaya haba sweet" ta juya idanu tana shafo fuskarsa ta ce "A yi haƙuri mazaje ba za a kuma ba" ya juya ya kalleta ya ce "Zinu....." Sosai Zainaba ta yi wa Ridayya faɗa na wawtar da take shirin aikatawa ta bata shawarwari masu kyau, da Zainaba zata tafi Ridayya ta haɗa mata goma ta arziƙi kayan abinci da kayan miya suna nama da kuɗi dubu hamsin ta saka drive ya kaita gida.


That's how life is....
Har gidan Ridayya Ammi ta je ta bata haƙuri Ridayya ta ce ba komai ƙaddara ce, ta nuna har zuciyarta komai ya shige. Umma ta yi ƙunci sosai kafin ta sakko Hajja Azizat ta nunawa baba ƙarami soyayya irin wacce ta yi masa tanadi tun suna samari, ya kuma sha mamaki ainun har wani fresh ya yi ya ajjiye tumbi ta ce Abba ya ce Zauja kullum kuma sai ta gai da Ammi bata da matsala hankalinta ya kwanta bata taɓa sanin haka zama yake daɗi idan ka samu caring husband ta ji ita kamar bata taɓa soyayya ba, bata san mene auren ba ta fara business sosai bai kuma hanata ba. Mami hankalinta kwance ita da mijinta Baffa sai junior babu abinda ta nema ta rasa a rayuwa, sosai take kula da su Aliyu Yaya Zuhura tana nan tana zuba zawarci abinta Balkisa ta samu suka daidaita da mijinta. Junaid ma lafiya suke zaune da Iklas hankali ya kwanta kowa ya amshi ƙaddara da Ubangiji ya jingina masa da rayuwa. Ridayya ta haƙura ta fara rainon ciki Mami kuma ta amsu yaran gabaɗaya abin mamaki kuma basu wani lalace ba girma suke sosai, a haka ta ce zata koma makaranta Abbiey ya ce ta bari ta haihuwa sun kusa komawa Japan ai ya mata settling komai a can ta yi masa godiya, sosai arziƙinsa yake ƙara yawa business yake sosai na motoci da da gidaje ya gina ya siyar ya buɗe babban shago a kantin kwari ya saka hannun jari ta ko'ina abubuwa sai addu'a da godiya ga Ubangiji a yadda ya ce Ridayya ce ƙashin arziƙinsa tunda ya same ta komai yake buɗe masa. Basu da matsala sai irin na samun saɓani da ko wanne ma'aurata suke samu a zamantakewa. Mardiyya ta auri Yaƙub babban gidana wajan sama da mutane ashirin tukunya ɗaya ake ɗorawa sosai ta rame ta zabge ta shiga damuwa amma bata da wata mafita data shige zaman gidan mijinta.


Prof komai ya ƙare a wajan Talatu ƙarin kunama ya zama bashi da komai komai ya lalace masa da ƙyar ya samu mace ya aura itama ƴar kanta yana fita take sakawa takalminta igiya ba ita zata dawo ba sai dare, tana dawowa ba maganar abinci za ta yi kwanciyarta idan ya tashe ta kan haƙƙinsa ta ce "wallahi kai kamar bunsuru haka kake, ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login