Showing 126001 words to 129000 words out of 190738 words

Chapter 43 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17321

nan Mami ta ƙarasu wajan ta ɗago Ridayya dukda kasancewarta baƙa bai hana yatsun Burhan fitowa ba, duk kawaicin Mami sai da ta ji ranta ya ɓaci sosai domin ba zai kassara mata yarinyar da bata mori komai na rayuwa ba.


"Burhan me ta yi maka da zafi haka?" Ya yi shiru yana bin Ridayya da kallo saboda yadda ta lafe jikin Mami tana kuka kamar ranta zai fita ga wani irin haushi Ustaz daya kamata yana kallo Umma ta ci mata mutunci gashi a ɗakin ta samu ciwon ya yi shiru. Mami ta kama Ridayya har zuwa ɗaki ta zaunar da ita ranta ɓace ta nufi inda Baffa yake domin ya shiga tsakani.


Mardiyya na tsaya ta caɗa uwar kwalliya sai feshe jiki da turare take yau zata zama mace mai ƴanci ta fita daga layin ƴan'mata waya take yi tana cewa
"Kamar yadda kika bani shawara ne, na siyo maganin na haɗa masa a juice, amma fa naga both gender ne maza da mata"


Ta cikin wayar aka ce "Da za ki siyo wannan kema sha za ki yi ne?" Ta ce "A'a ya ce yafi aiki ne da wuri kuma yana da mugun ƙarfi yana iya yin kwana biyu jikin mutum yana aiki, kuma gabaɗaya na juye"


Ta saki salati ta ce "Innalillahi kin kashe ɗan mutane wallahi kaɗan za ki saka fa shi ne kika juye duka zai iya yi masa illa fa" Mardiyya ta saki dariya tana duba gidan maganin ta ce "Kar ki damu yanzu zan je nasan idanunsa ya rufe ni kawai yake jira, ai Umma ta ce daman lafiyarsa ƙalau kiga dole na ja masa aji" sallama sukai ta yi dropping wayar saman mirror ta nufi banɗaki wanke baki. Tana shiga Ustaz ya shigo kai tsaye idanunsa ya sauka akan gidan maganin ya ɗauka ya dinga juyawa kenan shi ne dalilin kawo masa lemo? Kenan shi Ridayya ta sha?


"Ya Allah!" Dole Ridayya ta gigice a ransa ya ji dole su yi wannan game ɗin 1-1 yaga lemon da take sha a saman stool ya zazzage mata raguwar ciki ya juya ya nufi bedroom ɗin Ridayya.


Kwance ya sameta saman carpet tana ta birgima da kuka gefen fuskarta har ya kumbura ya ƙarasa ya ɗago ta zuwa tsaye ƙafafuwanta rawa suke sosai ta ce


"Abbiey ka daina taɓa ni ka bar ni haka" ta faɗa tana shagwaɓe fuska "Ni ne maganin ciwonki Ustaza ki yi haƙuri bani da iko but i can help ki samu nutsuwa" Ya riƙo fuskarta shatin yatsu ya gani da mamaki ya ce


"Waye? Waye da wannan aikin?" Tana kuka ta ce "Ba abinda na yi masa warin taba na ji shi ne na yi amai ya mare ni"


"???" Alamar tambaya ya yi mata da hannu akan waye? Ta ce "Burhan"


Bai ce komai ba amma tana ganin yadda jijiyoyin kansa suka fito bakiɗaya har wani huci yake futarwa ƙirjinsa na harbawa ganin bashi da lokacin magana baya kuma son gardama ya saka ya ɗauketa gabaɗaya zuwa bathroom ta tsayar da ita tsakiyar shower ya sakar mata ruwan sanyi wanda ya sauka har jikinsa. Ta yi saurin ɗauke kanta saboda wata kunya sosai daya kamata, shi da kansa MB USTAZ a tsorace yake domin bai taɓa ba, bai san ya ake yi ba bai taɓa kusanta kan shi da ko wacce ƴa'mace ba sai yanzu, ita kanta Ridayya sauyin data gani a idanunsa Abbiey ɗin nata ya bata tsoro ya damƙe hannunta ɗaya ɗaya hannunsa kuma ya riƙe ƙugunta mai faɗi.


RIDAYYA bata san meke faruwa ba ta tsinci kanta da kallon cikin ƙwayar idanun MB USTAZ ɗin da kyau wani abu mai kama da feelings na tattaro mata wanda a kansa ne kawai take jin hakan. Ruwan ya ci gaba da sauka a jikinsu ba zai iya ganinta ba domin bai shirya ba, ganin kuma bashi da wani amfani a tare da shi, bai taɓa jin zafin sabuwar wannan ƙaddarar tashi ba sai yanzu, akwai lokacin da dole sai ta ɓukaci hakƙinta na aure musamman ita data riga ta saba ta san kan abun, yanzu na ya san alkuya kawai take da yadda bata ɗauke shi matsayin miji ba, da kuma yadda bata samu labarin auren nasu ba. Rashin lafiyarta ya taimaka wajan rashin fahimtar abinda yake mata a yanzu ba iya matsayin uba bane ya shige hakan.


Ya rungumota jikinsa ya riƙe ta da kyau yana ji tana sauke ajjiyar zuciya ya ce "I am sorry Little Mama, ki yi mini uzuri"


"Me ya sa ka ce ka tsane ni Abbiey idan baka so na waye zai so ni?"


"Me kika sani game da so ko ƙi? Kin yi rayuwar aure dai kawai Ustaza ba tare da kin san mene auren ba, wahalarsa kawai kika sani am soon za ki san waye mijinki mene kuma aure da daɗin dake cikinsa. Ni ban yi mini al'ƙawarin babu ƙalubale ba domin ko harshe da haƙori ana saɓa wa kuma ko wanne aure ɗan haƙuri ne, ina da yaƙini za ki yi farinciki za ki samu freedom, soyayya, tattali, kulawa zan share miki takaicin da kika wanzu da shi zanja ragamar komai na rayuwarki"


Ta kalli gefen fuskarsa ya mintsini kumatunta ya ce "ba gemuna za ki kalla ba cikin idanuna za ki kalla"


"To me ya sa kake ce mini haka?"


“I dreamt that you were mine, and then I woke up smiling because I realized it was not a dream. You are already mine!”


Ta tura masa ba ta yi aune ba ta ji saukar bakinsa a gefen nata ya yi mata light kiss ya ce


"Love you my dearest wife Mimina! ƴar lukutar Abbiey"


Jikinta ya saki tana ganin zunzurutun iskanci yau yarr haka ta ji bata taɓa sanin akwai wani abu mai kama da haka ba nauyi da kunyar Ustaz ya kamata. Jin tana atishawa kuma yanayin ya ɗan sauka ya kashe shower ɗin ya jata gefe ya ce "Cire kayan kar sanyi ya kama ki"


Fita ya yi a parlour ya same su Baffa yana ta faɗa Mami kuma har kuka ta yi Ustaz na zuwa yama mance jikinsa a jiƙe yake kai tsaye kan Burhan ya nufa lokacin ɗaya ya sauke masa lafiyayyun maruka biyar a gefe ɗaya gefen bakinsa ya fashe ya shaƙe masa wuya ya ce. "Na rabu da kai saboda babu ruwana da kai, amma yanzu ka shiga hurumina ka taɓa iyalina zaka san ka taɓa matar Muhammad-Bilal Tahir Rano, kuma daga kan ka babu wani zai yi gigin dukan Matata"


Hannun Burhan ya kama ya ce "Bada wannan hannun ka mare ta ba? To daga yau ya tashi aiki"


Lanƙwasa yatsun hannun ya yi suka bada sauti Burhan ya yi ƙara saboda jin yatsun sun karye Ammi ta ce "Wai mene haka akan ya mare ta zaka masa haka ba ita ce ta yi masa amai a jiki ba?"


Ustaz ya kalli Ammi ya ce "Shhhh ban saka dake ba, akwai ranar da zan waiwaye ki kuma ko ke yanzu kika dakar mimi mata wallahi sai na watsa miki yatsuna a fuskarki, kuma ki shirya amsa duka tambayoyin da suke jiranki sonna or later, zalincin da kukai mata tun tana ƙarama bai isa ba ko? Waye bai zalunce taba a cikinku duk da kuke tsaye?"


Baffa ya yi ƙasa da kai domin yasan wannan faɗan har shi. MB USTAZ ya murza hannu ya ce "Na yi shiru ne saboda ba ku ɗinne a gabana ba duka, amma yanzu duk wanda zai taɓa mini mata wallahi shari'a ce zata raba ni da shi for sure idan duk babu mai son ta ni kaɗai na ishe ta,ita ce ni; nine ita so stay away from my darling wife"


Yana faɗin hakan ya juya zuwa part ɗinsa ransa a ɓace kwance yaga Mardiyya a kan gadonsa tana ta juyi tana ganinsa ta miƙe tsaye zata ƙarasa wajansa ya dakatar da ita da hannu "Don Allah ka taimaka mini ina buƙatarka"


"Ba ki yarda bani da lafiya ba? Shi ya saka kika saka mini abu a lemo? Yanzu da kika saka mini mene ya same ni?"


Za ta yi magana ya ce "Bana son na yi insulting naki in any way just leave my room"


MB USTAZ ya nemi hutu wajan aiki suka koma Kano har lokacin Ridayya bata bari ta sake haɗuwa da shi ba, kunyarsa take ji da kansa deep down na zuciyarta tana tunanin Sadauki. Kwanan su biyu da komawa Anuty Kaltum ta zo ita da Yaya A'isha sun jima suna nusar da Ridayya kana Anuty Kaltum ta yi wa Ridayya wasu picture ta turawa wata ta WhatsApp tana gamawa ta yi voice ta ce


"Yamara ga pictures ɗin nan don Allah ki haɗa kayan dana kawo ta a fara komai kafin Ramadan kun kammala na tura kuɗin komai, gyaran ciki da waje" Yamara yana nufin Hafsat a kanuri mazauna barno a Maiduguri. Kiran Yamara ɗinne ya shigo wayar Anuty Kaltum ta ɗaga ta saka handsfree ta ce "Ridayya ɗan jeki waje"


"Ashe haka abu ya faru da ƴar wajan Botula? Ɗazo muke magana da Falmata fa" Anuty Kaltum ta ce


"Wallahi shi ne dalilin daya saka na kira ki, aure ya mutu kuma an sake ɗaura wani kuma yarinyar tana buƙatar ilimin ɗa namiji da rayuwar gidan aure, infact she knows nothing about it kin gane me nake nufi?"


"Ai kar ki damu Kaltum dole mijinta ya san ya auri jinin Kanuri kuma ya san daga wacce jiha dangin uwarta suke, domin ita kanta bata san cewa Dada kakarta asalinta ƴar Barno bace ba hala?"


"Alamu sun nuna haka, ai babu wanda ya taɓa zama ya faɗa mata Dada Ƴar Barno bace a can kakanninmu na wajan uwa suke a can aka haifi babar Dada itama Dada acan aka haifeta ita kuma ta haife mu a Kano ƙaddara kowa da kalar tasa zanen jarrabawar"


Yamara ta ce "Kar ki ji komai zata zama mutum zata dawo new Ridayya in sha Allah kin san komai ba sai na miki bayani ba, babu buka ba malam kawai dai mijinta ne abinda tausayi kuma ayi mana afuwa domin sai mun wana shi sai kuma ji a jikinsa"


Sai duk jikin Anuty Kaltum ya yi sanyi domin an faɗa mata matsalar Ustaz da halin da yake ciki, kawai Ridayya za ta yi sacrifice farincikinta da ƙuruciyarta just to be with him da kuma abinda ya yi mata na alheri, kinga an saka alheri da alheri a inda ya dace ga matsalar uwar miji sai gorin baƙar fata take mata da muni wai kuma ita bazawara ce"


Yamara ta saki dariya sosai ta ce "Kan uba ji wani zunubi za ta yi wa kanta domin wallahi soon zai fara bijire mata, wake tsayawa tunani idan zai faɗa soyayya ita take ganinta a bazawara amma shi kallon yarinya budurwa yake ba, so na gaskiya baya buƙatar dalili ko hujjar yinsa, idan don haka yake son ta to tabbas kawo yanzu daya daina amma ya fasa? Wallahi ta kiyaye zuciyar data kamo da matsananciyar soyayyar mace domin ta fi komai illa kuma bazawara za taga aikin zawarawa"


Anuty Kaltum ta sauke ajjiyar zuciya Mami ta yi kamar bata san me ake cewa ba, domin daman ita magana bai wani dame ta ba Yaya A'isha ce take ta dariya ita kaɗai.


"Ke dai Allah ya kyau don ma na bugi cikin yarinyar data haifi Little an yi mata ɗinki ita fa empty head ce a ɓangaren soyayya da zama da miji karatu na musamman nake so ki yi mata idan mun zo Barno"


Sun jima suna tattaunawa sukai sallama Yaya A'isha ta ce "Wallahi ina jin tausayin Ustaz wannan a corner zaku saka shi"


"Bari uwarsa ta ja masa wallahi kwana nan zai zama Munafukin miji akan Ridayya don wallahi zai ta share masa wannan tuzuruntakar tashi zai yi alfahari da ita"


Kafin su tafi Anuty Kaltum ta je ta samu MB USTAZ a part ɗinsa na gidan domin tuni ya tsara yadda yake so a yi masa ginin gidansa Mardiyya tana nan tare da shi Ridayya kuma ta gudu wajan Mami yana zaune saman kujera ya kame nutsuwarsa da ilhmarsa ta bayyana bayan ya gaishe ta, ta numfasa ta ce "Alfarma nake nema za mu ke je a nuna matarka a dangi tunda ba a santa ba"


"Ina?" Ya ce a taƙaice ta ce "Nan cikin garin Kano mana" Ya dinga mamaki bayan su daya sani Mami na da wasu dangin kenan


Jin ya yi shiru ta ce "A bamu permission ba riƙe maka mata za mu yi ba"


Ya duba agogo ya ce "Ok kar ta yi dare"


"Wanne dare kuma ai kwana za ta yi wata guda ma za ta yi ai dangin da yawa wasu basu taɓa ganinta ba, to kafin ayi bikin muke buƙatar su ganta basai an kai musu katin bikin ƴar wajan Fatima ba su ga ba a kyauta musu ba"


Ya miƙe tsaye yana gyara zama babbar rigarsa idan ka kalli Ustaz zaka ɗauka yana da tarin zuri'a saboda tunaninsa da kamalarsa da kuma tsare gira banda tsantsar kishin tafiyar babu abinda take gani a idanunsa.


"Wannan cutarwa ne ai haramun kuke son aikatawa"


"Subuhanallahi haramun kuma?"


"A'a kifa daina salati kamar ba ki gane ba, yanzu don Allah ya General zai ji ki tafi ki barshi har wata guda?"


Anuty Kaltum bata taɓa tunanin ya san sunan mijin nata ba sai yanzu furr ya sakawa idanunsa toka yaƙi yarda.


"Wannan mijin na Ridayya akwai taurin kai da miskilancin tsiya kinga yadda yake mitsi-mitsi da Idanu wai idan ni ce zan tafi wata guda ya General zai ji kamar wanda ya san daɗin mace"


Murmushi kawai Mami ta yi ta ce "Babban mutum kenan zai aikata"


Washegari ya shirya tsaf cikin wagambari mai tsadar gaske zai je meeting ɗin da aka yi inviting nasa na Madugu daga nan sai ƙarasa police station. Fuskarsa fau tana wani yellow saje da ƙasumbarsa sai kyalli suke da sheƙi suke ya yi wani irin kyau ya rusuna ya ce "Abba Umma barka da safiya"


"Barka Babban mutum an fito?" Ya jinjina kai Umma taƙi amsawa "Sai ina?"


"Zan ɗauki Ustaza za mu ɗan je wani waje"


"Bada yawo na ba, idan har nono na kasha wallahi babu inda zaka fita da ita"


Ustaz ya kalleta ya ce "Asibiti za mu ga? Hakƙina ne kula da matata idan ba Ubangiji kike so ya yi fushi dani ba, wallahi Umma ba kyau shiga tsakanin ma'aurata"


"Ni kake faɗawa haka? Ina faɗa kana mini bita tare da ɗora mini hadda? To wallahi sai ka sake ta a yanzu maza ka sauwaƙe mata"


Baba ƙarami ya tashi ya ce "Hadiza ban hanaki kar ki tursasa Babban mutum wajan sakin matarsa ba, amma ki sani sai dai ku yi zawarci tare da Ridayya yana sakinta zan ɗora miki naki saki ukun, kuma zan buɗe idanu na zaɓo kyakkawa budurwa dal na aure ki daina ganina da furfura kyakkawa ne ni domin a waje na Muhammmmd ya kwashi rabin kyau, wallahi da gudu za a fara rububina zan auri budurwa mu sha soyayya, idan wacce zata ƙwace ni har abada ne sai na nemo ƴar Maiguduri, idan ilimi nake so na nemo ƴar Abuja idan wayewa ne na ɗauki ƴar kaduna, idan soyayyar ce ƴar Kano,idan biyayya ne Zamfara idan kishi ne Sokoto ko Katsina don haka ki bi a hankali, wallahi wallahi Allah kika saka ya saki Ridayya sai na sake ki kuma na auri budurwa sai ki zaɓa zawarci tare da surukarki ko haƙura da ƙaddarar Ubangiji"


Baki Umma ta saka Baba ƙarami ya ce "Jeka Allah ya tsare Babban mutum"


MB USTAZ ya sauke numfashi ya nufi ɓangaren Mami lokacin suna zaune a parlour Zainura sai ƙoƙarin haɗa breakfast take ya shigo ta ce "Yaya Bilal good morning?"


Bai kalleta ba bai amsa ya nufi wajan Mami yana durƙusawa ya ce "Barka da safiya Mami"


"Barka Babban mutum ka wayi gari lafiya?"


"Cikin aminci Mami" kunyar surukai duk ta kamata shi kam ko a jikinsa ya juya yana miƙewa ya ce "Ustaza bata shirya ba?"


"Tab ai dai ka je ka taso, da alama ka sangartata da baccin safe tun ɗazo nake abu ɗaya" MB USTAZ ya zaro idanu yana duba agogo ta nuna masa direction ɗin bedroom ɗin ya tura yana yin sallama underneath his breath. A kanta idanunsa ya sauka tana tsaye gaban wardrobe tana ƙoƙarin maƙale bra ɗinta bata ji sallamar ba balle ta ji zuwan shi, sai saukar lips ɗinsa ta ji a tsakiyar bayanta da laɓɓansa masu sanyi ta yi saurin sakin rigar tana juyawa a tsorace bakinta na rawa ta ce "Abbiey" ya yi saurin ɗora yatsarsa a bakin "Why Ustaza? Ni kike gudu" ta yi narai narai da Idanu ya sunkuya ya ɗauki rigar ya juyar da ita ya saka mata yana ɓalle ɓallin ta ce "Ba kyau fa Abbiey" idanunsa duk wani ya kala ya ce "Mene babu kyau?" Ta ce "Ganin jikina da gaske ba kyau haramun ne"


A taƙaice ya ce "Bari na yi abinda yake mai kyau kuma halal" zillawa ta yi ya girgiza kai ya nufi waje ya zauna yana danna wayarsa shiryawa ta yi cikin brown colour ɗin Abaya mai ɗan faɗi ta saka igiya ta ɗaure ta yi rolling kanta ta saka pech ɗin lipstick ta yi fresh da kyau a hankali ta dawo ta tsuguna ƙasa ta miƙa masa hannu ya ajjiye wayar ya miƙa mata nasa hannun sukai musabaha ta ce "Good morning Abbiey"


"Kin tashi lafiya?" Ta ce "Lafiya lou, ya jiki?"


"Uhm bakin ki ne jikin zan gwada miki ƙalau nake"


Ta kasa kallonsa ya ɗagota ya ce "Zo mu yi special gaisuwa" a kan ciyarsa ya ɗora ta ya juyo da ita ya sunbaci goshinta da kumatunta a hankali ya ce "Allah ya yi miki Albarka Ridherh" Ta yi ƙasa da kanta ya ce "Ki faɗawa wannan masifaffiyar Anutyn taki ta zo ta ɗauke ki ku je unguwar za ki bani address wata ɗaya ya yi yawa, daga nan zamu je asibiti idan mun dawo za a yi bikina da matata"


"Wanne asibitin?"


"Za ki gani ne, sati biyu za mu a asibitin bana son a sani fa appointment nake jira na asibitin"


"To wa za a kai?" Da yatsa ya danna ƙirjinta tsakiya ya ce "Mijin Ustaza"


"To bikin naka Mardiyya ce matarka?" Ya ɗage mata kira sai ta shagwaɓe fuska ta fara kuka wiwi "Wallahi ka nemo wata matar ni bana son ta ka zauna kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login