Showing 150001 words to 153000 words out of 190738 words

Chapter 51 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17294

yana nufin ya aminta da ita kuma yana son ta. Kar ki saka haka komai a ranki ki raini cikinki kuma zan kula da ke Babban mutum kuma na miki alkawarin dawowarsa da wuri haka"


"Shikenan Umma na gode amma ko numbersa babu?"


"Zan bincika miki, bari na je a nemo kai da ƙafa"


Mardiyya ta yi saurin toshe hanci ta ce "Don Allah umma ɗan matsa wari kike,ina nufin warin rama" kafin Umma ta yi magana ta fara kelawa amai a saman gadon ko tashi ba ta yi ba.


Umma da kanta ta dinga bulayin neman kai da ƙafa na ɗan taure. Bayan ta gama komai ta kawowa Mardiyya taƙi ce ta ce daman wurin ɗan tauren kawai take son ji. Baba ƙarami ya manta wayarsa a ƙaramin parlorn da yake sashinsa Umma na zuwa ta fara bincike cikin sa a ta samu wata sabuwar number da aka yi saved da Aboki. Ta san Babban mutum kawai baba ƙarami yake cewa.


"Me kike nema ne haka Hajiya Hadiza?"


"Ba komai, cewa na yi baka ce komai akan cikin Mardiyya ba?"


Ya kalleta ya yi murabus bai ce komai ta ce "To murmushin mene kake? Ina tunanin daman babban mutum rabonsa a tattare yake da Mardiyya ya kamata ka ce ya dawo gida haka, tunda ita muguwar mai baƙar aniyyar ba zata dawo ba saboda tana baƙin cikin ta ganshi tare da Karfi in sha Allah sai Ubangiji ya ɗorawa Ridayya soyayyar Ustaz kuma a banza ya mata nisa"


"Amin, hakan muke addu'a "


"Me? Yanzu dai ka faɗa masa"


"Ki faɗa masa da number da kika ɗauka" yana faɗin hakan ya fice ya bar mata wajan.


Ammi abin duniya ya yi mata yawa Junaid ya kasa samun matar aure saboda matsalar Genotype, ga Balkisa ta dawo gida ba lafiya ga Yaya Zuhura miji ya yi mata dukan mutuwa har kwanciya ta yi a asibiti Mami ce ta kula da ita, ko kallonta ta lura Yaya Zuhura bata son yi yarinyar data fi karfin fiye da kowa a yaranta amma yanzu wai gaba da ita, kamar am musu farraƙu ta ɗauki alhakin hakan ta tattara akan Mami ita ce ta yi mata asiri. Gashi ta kwace gida abinda bata ƙauna kenan ga Baffa ya juya mata baya kwana biyu komai cuɗe mata. Ta juya ta kalli Burhan da baya cikin haiyacinsa ta ce


"Yanzu tunda ba Ridayya ga wani sabon plan, Zainura ita ce target ɗina ka san duk yadda ka yi ka samu kusanci da ita, idan har tsarinmu ya yi daidai sai a nan gab da bikinku ka ɗirka mata ciki ka gudu yanzu ba kuɗi ne a gabana ba, kawai rayuwar yaranta nake so na wargtsa kamar yadda komai nawa ya juye na yi nasara akan Ridayya na bata wahala tun tana zanin haihuwa na rabata da iyayenta, na juyar mata da tunani bayan n bata maganin shaye-shaye na ƙona mata harshe da wuƙa, ni ce na dinga assasata akan Zameer wannan shi ne babban abinda ba wanda ya sani, na dinga ƙarfafa mata qiwwa. Daman na ce ba zata taɓa zama wata a duniya ba gashi ba inda ta je ta rabu da mijinta, Bilal ya aureta uwarsa ta saka ya sake ta kaga an fara lissafa mata aure kenan, in sha Allah haka zata dinga aure tana fitowa ko wanne ta je kuma ta haifi ɗa ɗaya, kuma duk ta haifi lalatattun yara"


Ta juya ta kalli Burhan da yake busa sigari ta ce "Wai kana jina ma? Idan kana busa shegiyar abar nan ba komai kake fuskanta ba"


"Na ji, ni ban iya wata soyayya ba"


"To daman ina mashayi ina soyayya ka nutsu ka tambayi abokai"


Ya miƙe bayan ya ɗauki wayarsa ya ce "Bari na doƙa yanzu abinda za a yi ki nemi jauwalarta ki bani shaɗayanta ko?"


"Mene shaɗaya kuma?"


"Ke ciki ce fa, ana miki inkiya bakya ehhh, number wayarta nake nufi naka yarinyar mai ƙirice matsalar kawai yama sunanta kika ce ta fita haɗewa"


Ammi ta ja tsaki ta ce "Ji wawa ba maganar yayar muke ba ta ƙanwar muke"


"Ohh sure zahabu zahabu ya sunan beb ɗin?"


"Zainura"


Burhan ya lissafa faɗar Zainura ya kasa sunan ya masa wani iye yane. Sai kawai ya ce “Zinu"


Cikin sa a yana fita ya yi karo da ita ta dawo daga makaranta dake weekend ne ana ta kiran sallar magriba tana ganinsa ta haɗe rai bai taɓa tsayawa ya mata kallo sosai sai yanzu ba ya tsaya a hanya ya cake ta haɗe fuska cikin muryarta ta tsiwa ta ce


"Malam ka tsaya mini a hanyar shiga gidan ubana?" Ya yi mata shiru sai warin sigari yake ta yi saurin rufe hanci


Zata shige ya yi saurin kama hannunta tana juyawa ta ɗaga hannu ta kifa masa mari ta ƙara kifa masa wani ta ce "Sakarai shashasha ko an faɗa maka ni irin ƴan iskan da kake bi ne? To ɗabi'ata ta sha bamban da taka jikina mai tsarki ba irin naka ƙazami...."


Hannunta ya fisga da ƙarfi ta yin saurin matsawa kusa da shi saboda yadda ta ya jawo hannunsa idanunsa jajur sai huce yake yatsun hannun Zainura raɗau a fuskarsa ya zaro wuƙa a aljihu nan Zainura ta firgita amma ta dake jiran yadda zai soka mata kawai take. Idanunta rufe ba zato ta ji ya ce


"Ina son ki Zinu ki koyi so na dole" yana faɗin hakan ya sake ta ya fice kamar walƙiyya.


Junaid bai samu faɗawa Baffa uzurin Zameer ba yama manta shaf dake baya yawan zama always yana wajan aiki. A ɓangaren Zameer baya iya bacci ya zama kamar sauna matarsa Ridayya kawai yake muradin gani kusa da shi duk duniya babu wata ƴa mace dake gabansa sai Mai son shi Ridayya kuma zai yi komai saboda ya mallaketa shi kaɗai zai rabata da ko wanne namiji. Ya shirya cikin shadda skyblue ya nufi gidansu Ridayya da addu'ar Allah ya sa ya haɗu da Baffa ko Junaid ko ita kanta Ridayya ƴar Aljanna.


Sadauki ya zama sai addu'a ya kaɗaita sosai sai ya yi kwana da yini a ɗakinsa sosai suma ta taru a kansa da fuskarsa kamar mahaukaci ya daina walwala ko da Mother ne. Tajj ya zo har gidan shi kansa ya firgita da yanayin Sadauki ya faɗawa Hajiya Azizat gaskiyar Ridayya ta yi aure amma kar ta faɗawa Sadauki idan lokaci ya yi zai sani.


Takarar BM USTAZ ta kankama ko'ina an sanya poster ɗinsa da inkiyar Fari mai farar aniyya ya samu karɓuwa wajan jama'a dukda ba a ba a bada damar fara yin kamfen ba. Al'amarin daya ƙara gigita Mardiyya soyayyar Ustaz ta dawo sabuwa fil a ranta gefe guda mata suna fara crushing akan shi. Yayinda shi kuma yake ƙasar Japan zaune da matarsa ko wanne meeting ta zoom yake halatta sai ya sauka a Nigeria har ya koma ba wanda ya sani.


Har yanzu Ustaz ya kasa furta komai akan first night ɗinsa da yake cewa Ridayya ta amshi budurcinsa, duk abinda ya lissafa sai ya ga bai dace da Ridayya ba. Bai jima da shiryawa ba suna zaune akan duguwar kujera daga shi sai wata haɗaɗɗiyar rigaw armless amma mai kauri ya zuge zif ɗin gaban rigar saboda yanayin da yake ciki a yanzu ke haifar masa da zafi a ƙofofin gashin jikinsa. Ridayya kuma na kwance a jikinsa ta miƙe ƙafarta a saman tashi tana wasa da wayarsa shi kuma ya yi shiru yana shafa samar kanta data kunce kitson.


Ta ji yana shige gona da iri ta yi masa banza a hankali ta ji ya ce


"I am very lucky"


"Dame?" Ta tambaya hankali ya ɗago ta bayan ya kalli cikin idanunta ya ce "Ko wanne namiji yana amsar budurcin matarsa ni kuma matana ta amshi nawa dole na yi wa Ubangiji godiya"


Ta ɗaure fuska ta ce


"Magana kake faɗa mini idan na fahimta ka auri bazawara"


Nan da nan fuskar Abbiey ta yi jajur fushinsa wanda bata taɓa gani ba ya bayyana ya dinga kallonta da wani irin firgitaccen yanayi goshinsa ya fara fidda zufa ya kama hannunta duka biyun kamar zai yi faɗa sai ta ji muryarsa a ƙasa ya ce


"Ridha" ya yi shiru ta kasa kallonsa


"Ɗago idanunki ki kalli cikin idanuna" a hankali ta kalle shi abinda ta gani a idanunsa was very different yanayi ne da babu wanda zai iya ganewa amma zuciyarta tuni ta buɗe wani irin son Abbiey ɗinta ya dunga huda mata ƙirji yana shiga zuciyarta


"Na taɓa miki maganar mijinki ko aurenki na baya? Kin taɓa ji na yi magana akan surarki ko wani abu? Balle budurci ko bazawara?"


Ta girgiza kai "Buɗe baki ki yi magana" ta yi shiru cikin faɗa ya ce


"Zan watsa miki yatsu a fuska Ustaza, gaggauta magana Ustaz na jinki"


Muryarta na rawa ta ce "A'a Abbiey"


Yana riƙe da hannunta ya matse alamar hukunci yake mata can ƙasa daidai yadda za ta ji cikin wata kalar murya ya ce


"Ban taɓa damuwa da wannan ba, ba kuma don shi na aureki ba, ba don shi ya sa nake son ki ba. I'm just love you for the sake of Allah for the sake of love Ustaza, ina ta laluban dalilin daya sa nake son ki tun kina jaririya ina goya ki har kika girma na ji ina son rayuwa dake na kasa, nasan soyayyar gaskiya bata da wani dalili" ya yi shiru ya murza tsakiyar tafin hannunta


"A shekeran jiya na samu amsar tambayata, Ridha bayan son tsakani da Allah da nake miki na ji a raina tarbiyyarki kawai na yarda da ita a cikin ƴan matan duniya, saboda ni na tarbiyantar dake na kare mutuncinki har zuwa gidan aurenki, matan yanzu abin tsoro ne wayewa ta musu yawa wasu soyayya da suke abin tsoro ce, Ridha ba kunya za kiga mace tana bari namiji yana riƙe mata hannu. Innalillahi Allah ka yafe musu Allah ka yafe masu wallahi da na auri Iran matan nan gwara na zauna haka, ke kam ina alfahari dake kin riƙe mini kimarki da mutuncinki na ɗiya mace"


Gaban Ridayya ya yi mummunan faɗuwa ƙirjinta ya duka da ƙarfi, wani tashin hankali ya mamaye ta nan take jikinta ya yi sanyi tausayin Abbiey na yardar da ya yi mata ya kamata idanunta ya cika da hawaye.


Ustaz ya saki murmushi har dimple ɗinsa na shigewa yana riƙe da hannunta a hankali ya kai yatsunta zuwa bakinsa ya tsotsa tare da sumbata ya ce
"A gare ni babu wani abu da nake ɓoye miki, babu shi don Allah idan akwai abinda ya kamata na sani tun yanzu ki faɗa mini na san yadda zan fuskance shi, bana son rayuwar ɓoye abu idan na miki abu kawai ki faɗa mini ok?"


A hankali ta ce "Ba komai" ya tsora mata idanu kamar mai fahimta "Are you sure?"


Ta jinjina kai ya jawota jikinsa ya rungume yana jin yanzu abinda ya yi masa saura gashi ga muradin ransa


"Thanks for the gift, thanks for the virginity, i appreciate it. Ubangiji ya yi miki albarka ya ba ki aljannar firdausi, u make my day kin mai dani cikakken mutum"


Idanunta cike da hawaye ta ce "Ka yafe mini Abbiey, bana jin na cancanta godiya ƙaddara ta zo ba yadda muke tunani ba ban baka.....,"


"Shhhh!!" Ya ɗora yatsarsa a bakinta


"Ni budurci na amsa da gaske Ustaz i feel very comfortable with you ban yi zaton haka ba, ke ta musamman ce Sayyada ki saki jiki Allah yana kallo ina son soyayya ina son romantic love, ba zan ɓoye miki me na ji idan na gamsu baya nufin kema haka karki cuci kanki if u need more, all you have to do is ask I'll be the best husband for you bani da bakin gode miki ba kuma zan yafewa kai na idan zuciyata bata cika da soyayyarki ba"


Kunya duk ta kama Ridayya ta ɗaga kai ta kalle shi ya kashe mata ido ɗaya yana ɗage mata curin girarsa "Na gode"


"Mu je ki kai ni asibiti"


"Baka da lafiya?"


Ya dubeta yana sauya yanayi sosai ya ce "Tun first night ɗina da kika amshi budurci jikina ke ciwo ba ki gasa ni a ruwan zafi ba ban sani ba ko na ji rauni "


"Uhm uhm kai Abbiey "


"Serious Ridha a lokacin ihu nake ta cikin zuciyata" ta yi saurin kifa kanta a ƙirjinsa ya rungume ta sosai da kyau a jikinsa yana shaƙar ƙamshinta a hankali yake sake shigar da ita jikinsa sukai shiru for some minutes zuciyoyinsu na dukawa a tare suna buɗewa tare da amsar yanayin iya wahala Ridayya ta wahala sosai domin ji ta yi kamar bata taɓa sanin ɗa namiji ba, amma dole ta gyara jikinta ta daure tunda ita ba matar novel mace da za a ce miji ke yin komai.


“Ridherh...,"


“Abbiey" ta amsa a nutse tana wasa da dugun gemunsa mai kyau.


“I love you!”


Ya ce a cikin kunnenta ya hura mata iska a kunne daidai lokacin wayarsa ta fara ringing bisa tsautsayi hannun Ridayya ya danna amsa kiran dake wayar nada speaker sosai suke jin me ake cewa banda Ustaz daya ya tafi love world. Ridayya har tsakiyar kanta ta ji kalmar names ya sha faɗa mata sanda suke University bata taɓa jin tasirin kalmar ba sai yanzu,ta ƙara bambance so da birgewa jikinta ya saki ta kasa ɗagowa a hankali wani yawo mai ƙamshi ya fita daga bakin Ustaz ya sauka a kunnen Ridayya muryarsa bata fita sosai kamar zai yi kuka ya ƙara cewa


“I love you ”


Daidai lokacin ta cikin wayar suka ji an ce


"I love you too sweetheart, na kira na yi maka albishir da cewa ina juna biyu ma'ana ka tafi ka bar ni da cikinka......




08164069385
Ga masu buƙatar ayi musu tallah .
*MUNAFIKIN MIJI 41*
Mikiya writers asso...




Bright pens free batch
Nimcyluv




*A yi FOLLOWING CHANNEL ɗina domin samun update akan lokaci na MUNAFIKIN MIJI da wanda suke buƙata daga farko, ƙofa a buɗe take ga masu buƙatar ayi musu tallah*
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T




Ƙoƙarin tashi Ridayya ta yi cikin sauri a nutse kuma Ustaz ya damƙe hannunta yana ƙara kame fuska saboda saukar muryar Mardiyya da ya ji.


Ta cikin wayar Diyya ta ƙara cewa "Baby na yi kewarka sosai na yi kewar mijina, ya kamata ka dawo tunda mayyar data na ce maka ka sake ta, kuma kai ma ka tabbatar mini baka son ta" da mamaki Ustaz yake jin furucin na Mardiyya ya lumshe idanunta zuciyarsa na matsewa yana jin yadda hannun Ridayya ke rawa wanda yake da tabbacin ba iya hannun bane hatta zuciyarta rawa take.


Mardiyya ta gyara zama idanunta akan wata ƙawarta data zo gidan ta ce "Ni daman na san bakai ka zaɓi Ridayya ba cusa maka ita aka yi,kuma gashi Umma ta saka ka rabu da mugun iri. Da ina cikin damuwa yanzu na samu nutsuwa ganin ka zama nawa gani ɗauka da cikinka wanda nake ƙoƙarin haifa maka, baby naga ka fito takara ashe kaga zan zama matar gwamna her Excellency na ji na ƙara son ka"


Barin ta ya yi ta yi magana son ranta don baya katse mutum a tsarinsa ya sauke numfashi kamar zai yi magana sai kuma ya kashe wayar domin ba ita ɗince a gabansa ba yanzu. Ridayya da sauri ta ƙwace hannunta ta miƙe jikinta na rawa kuka ne ke ƙoƙarin kwace mata amma ta hana faruwar hakan, sosai batun cikin Mardiyya ya saka ta cikin firgici da kaɗuwa da kuma jin ta furta wai Ustaz baya son ta, Umma ta saka ya sake ta duka wannan abubuwan mene gaskiyar batun?


So da Abbiey ke cewa ta amshi budurcinsa faɗa kawai ya yi don ta yi farin ciki ko mene? Kar dai ya munafurce ta ne? Ta rabu da MUNAFIKIN MIJI kuma wannan da take saka ran ya zame mata bango abin jigina ya zama silar yaye war baƙin cikin data ƙunsa a gidan Zameer shi ma ya kasance MUNAFIKIN MIJI. Innalillahi wa'inna ilahir raji'un dunƙulewa zuciyarta ta fara yi tana matsewa waje guda ɗacin da ranta ke yi mata har saman harshenta take jinsa.


Ustaz ya yi shiru shi kansa maganar Mardiyya ta jikkita masa zuciya yana son rikicin Ridayya bai kuma shirya rufe ta ba, babu ƙarya a zaman su. Yana ƙoƙarin miƙewa ya bi bayanta ya ji ƙarar faɗuwar abu dimmm! Yana juyawa ya ga Ridayya kwance a ƙasa goshinta ya daki gefen center table nan take ya fashe glasses ya caki gefen goshinta jini ya fara zuba.


Idan ta yi yunƙurin tashi sai ta sake yanke jiki ta faɗi, jikinta ya fara karkarwa tana kanannaɗewa kumfa ya fara fita idanunta rufe amma hawaye ne ke fita sosai nan da nan ta fita cikin haiyacinta rabon da farfaɗiyya ta tasar mata har haka shi kansa Ustaz ya mance yama ɗauka ko ta daina.
Ya riƙe kansa da kyau cikin sauri ya kunna karatun Alkur'ani ya ɗakko ladduma ya rufe ta gabaɗaya bai san wanne irin mataki zai ɗauka akan Diyya ba, ba zata ja masa masifa kullum rabin ransa tana faɗuwa ba. Ya jima durƙushe a gefenta idanunsa ya sauya ƙirjinsa ya ƙara buɗewa a hankali ya ga fitsari na jiƙa laddumar can ya ji ta saki ajjiyar zuciya bacci ya ɗauke ta.


Bata san adadin lokacin data ɗauka tana bacci ba, ba kuma ta san mene ya saka ta bacci har haka ba ta farko tana buɗe idanunta da suka mata nauyi sosai ɗakin duhu sai ɗan ƙaramin haske ta miƙa hannu ta kunna haske a hankali ta jikin gina da jikin frame fuskar gadon sai a lokacin ta lura da sauyin kayan jikinta ga ƙamshin Abbiey ya mamaye ɗakin wanda hakan ke tabbatar mata bai jima da barin wajan ba. Bata son tunawa amma kamar yanzu furucin ke fita ta ci kuka son ranta wataƙila bata cikin matan da suka yi dace da gidan miji wataƙila bata cikin mutanen da za su rabauta da farinciki a nan duniya.


Zuciyarta ce ta ce "Kar ki zama mai butulcewa rahamar Ubangiji, gode masa da iya abinda ya ba ki da kuma abinda kike dashi, ki tuna rayuwar da kika yi a gidan iyayenki babu mai son ki sai Abbiey, kin zama mujiya gidan ubanki, mahaifinki ya ce ke ƴar zina ce, matar uba ta shayar dake uƙubar da ba za ki manta da ita ba, wacce ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login