Showing 105001 words to 108000 words out of 190738 words
Chapter 36 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
da goro. Mardiyya har sujjudul shukri ta yi ta mallaki Ustaz cikin ruwan sanyi miji na kere sa'a ta ce ita ko ba'a gama haɗa kayan ɗaki ba zata bi su Mai ran ƙarfe gidan mijinta ta yi masa kyakkawar tarba gabaɗaya ta mance da cewa ya ce bashi da lafiyar ɗa'namiji.
Kullum Ridayya sai sun yi waya da Sadauki ta cikin wayar yake shaida mata ita ce wacce yake so ta bashi dama. Har yanzu bata ce ta amsa ba, ba kuma ta san mene matsayin Sadaukin a ranta ba kullum sai ya yi kamar zai yi mata kuka kalaman soyayya na musamman ke fita daga bakin Sadauki baya tsoron Ustaz ko kaɗan.
Kwana goma kenan da faruwar hakan misalin 11:43 Ustaz ya shigo gidan babu mai cewa shi wata kakkaurar black ɗin jersey ce a jikinsa sai trouser babu ko hirami gabaɗaya a ɗan hargitse yake, babu kowa a main parlour ya nufi bedroom ɗinta ya ɗauki Little ya fita da shi ya kwantar a bayan mota ya dawo cikin ɗakin yaga bacci take sosai ya san baccinta da nauyi, daga ita sai rigar bacci ya sunkuya ya cicciɓeta ya nufi mota da ita yana shiga rufe yana ƙoƙarin yi wa motar key tana farkawa ganinsa ya saka ta buɗe baki za ta yi magana fuskarsa babu walwala ya saka hannu ya riƙe bakin nata tare da murɗe shi da sauri kuma ya ja motar ya fice da wani irin gudu....
🥰🧚🏻♀️ Sannun ku Mar'atussaliha na yaba muku wajan comment da sharing Ubangiji ya raya zuri'a. 👉🏼🤙🏼🤙🏼 Zazzafar muhawara team Sadauki da Ustaz Ridayya dai second hand ce.
*MUNAFUKIN MIJI 31*
Mikiya Writers Ass...
Bright pens free batch
Nimcyluv
Hotel ɗin da yake sauka tare da yin rayuwarsa secret and privacy a Kano ɗin nan ya nufa da ita, a jikinsa yake jin idanuwanta na yawo a kansa ya share fuskarsa babu walwala ta yi jajur a haka driving da gudu dukda kasancewarsa Ustaz baya ƙaunar yin tuki a hankali.
Ustaz ya yi parking a harabar hotel ɗin a hankali ya kifa kansa a kan sitiyarin motar yana fid da numfashi wani irin zafi zuciyarsa ke yi masa, ciwon da ya yi na kwana biyu bayan faruwar abun shi ya hana shi dawowa, so yake ya zama mutum mai uzuri baya son nuna zafin zuciyarsa a kan Ridayya akwai tarin abubuwan da idan ya duba ya ke yi wa Ridayya uzuri. Yanzu ma a hargitse ya fito kuma baya son taga fushinsa domin ya fahimci idan ya nuna damuwarsa kamar hakan take so shi ne abinda take buƙata.
Fitowa ya yi daga cikin motar wani ya zo wajansa da sauri ya ɗan jingina da motar yana sauraren bayanin mutumin wanda tsayin lokaci ya kasa zama ya ji bayanin sai yanzu.
"Da gaske depression yana neman cin ƙarfinka damuwa ta yi wa zuciyarka yawa baka samun yin bacci cikin dare haka da rana ba yi kake ba, zuciyarka a ƙuntace take sosai hatta yawan ciwon kan da kaɗaitar da kake buƙata duk alamomin depression da rashin son maganar ka yi ƙoƙari ka samu nutsuwa ka ɗan ɓata lokacinka a kan wani abun da zai ɗauke maka kewa gudun kar kwakwalwarka ta samu matsala"
Ustaz ya yatsunsa fuska yana jan gemunsa dake yi masa ƙaiƙayi saboda sauyin yanayi baya son zafi weather ɗin Kano dana Lagos are different. Ya jima kafin ya ce
"Ina jin kamar ana kiran sunana ko ana jana wani wajan idan na rufe"
"Dole za ka ji hakan, amfanin zuwa asibitin kenan idan wasu ne cewa za su yi mutanen ɓoye ne ai cutar damuwa haka take signs and symptoms na depression yake you have to be very careful Sir, symptoms ɗin suna da yawa. Feelings of sadness, tearfulness, emptiness, or hopelessness
Anxiety, agitation, or restlessness
Behavior that looks like extreme laziness, rudeness, or disregard for others. Ɓacin rai da kulawa da lokaci, takaici, jin rashin fahimta da rashin kulawa, jin rashin sha'awa da wasu ayyukan al'ada, janyewa daga jama'a rashin mayar da kira rubutu da saƙon imel. Soke wasu tsare-tsare gajiyawa da rashin kuzari rashin samun wadataccen bacci,Jinkirin tunani, magana, ko motsin jiki. Feelings of worthlessness or guilt
Fixating on past failures or self-blame
Trouble thinking, concentrating, making decisions and remembering things"
Dr ɗin ya jinkirta kafin ya ce "Kai namiji ne wanda bai kamata a samu haka daga gare ka ba, i wonder why har ka samu kan ka cikin cutar damuwa dole ka kula kuma.....,"
"Enough!" Ustaz ya furta yana runtse idanunsa ya girgiza kansa kaɗan sai kuma kawai ya jinjina wa Dr ɗin kai tare da bashi damar tafiya.
Gabaɗaya ji ya yi jiri na neman ɗaukar shi, yana ganin mutane bibbiyu a idanunsa ga wani irin sabon ɓacin rai dake wanzuwa a zuciyarsa me miliyan yake nufi? Mahaukaci zai zama ko me sunan Allah kawai yake ambata har ya ɗan samu sassauci ya buɗe bayan motar ya ɗauki Little da har yanzu bacci yake, a nutse ya nufi ɓangaren ɗaya ƙofar ya saka key ya buɗe ya ganta ta kifa kai tana shassheƙar kuka ga rigar jikinta duk ta manne mata a fata da yatsunsa ya fara mata magana taƙi ɗago kanta shi ba zai iya tashin hankali ba ko buɗe baki ya yi zai yi magana har tsakiyar kansa yake jin wani irin dokawa.
Ta ɗago kai ta kasa kallonsa domin duk abinta bata iya kallon idanunsa, a hankali ta fito daga motar Ustaz ya bita da kallo yaga rigar sam ba ta yi masa ba
"Riƙe shi muga"
Amsar Little ta yi sai cin ɗaci take tana ɓata rai jerseyn jikinsa taga ya cire ya zama sai farar singlet a jikinsa da trouser ya zama ƙato a gabanta ya miƙa mata ta tura baki ta ce
"Ni ka mayar dani"
Ya girgiza kansa bai ce komai ba ya gyara tsaiwarsa tare da marsad ya saka mata jerseyn ta rufe mata kirji ya ɗan sauke numfashi maganar ita kanta ba komai take ji ba kamar mai raɗa ya ce
"Za ki komai na ɗauka, banda nuna tsaraici da sura Sayyada"
Ta tura baki ya kalli lips ɗin kansa na juyawa da sauri kuma ya ɗauke kai ya amshi Little yana tafe tana binsa domin ya san halinta babu inda ta sani kuma ba zata iya komawa ba.
A ƙofar wani bedroom ya tsaya ya saka key ya buɗe, yanayin wajan na mutum ɗaya ne komai da komai yana shiga ya kwantar da Little har ya je bakin ƙofa ya ce
"Ina zuwa"
Ta bi shi da kallo ya jima kafin ya dawo, yana shigowa taga idanunsa sun rine ba kuma ja sukai ba tsananin azabar ciwon kai ne. Ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito sanye da islamic jallabiyya mai ƙaramin hannu banda ita ba da haka zai kwanta zafi yake ji sosai.
"Abbiey jallabiyya dai wannan jallabiyyar sai na yayyanka su"
Sarai ya jita amma ko kallonta bai yi ba, ya daddafa ya yi sallah ya yi azkar ya miƙe kamar zai nufi gado ta yi saurin tashi bai kalleta ba ya ce
"Ba ki da kai Ustaza, me kike tunani?"
Ta yi shiru, shirun nata kuma damunsa yake ko bai tanka mata ba yana son jin maganarta ya ji kalar tsraiwar data sake
"Sallah zan yi" Ta faɗa kai tsaye ita idan ta yi wa Ustaz ƙarya har cikin zuciyarta bata jin daɗin hakan
"Kwanan wata 15 yau, yaushe al'adar ki ta rikiɗe?"
Wata kunya ce ta kama Ridayya komai nata ya sani, da gaske bata sallah tashi kawai ta yi da tunanin kwanciya zai yi a gadon
"Uhmm Ustaza kenan akwai matsala a kwakwalwarki ban miki komai ba a baya sai yanzu? Lokaci dai"
"Ni kawai Abbiey ka mayar dani gida na ce ba zan bika ba, ba zan je gidan matarka ba"
Ya nemi waje ya zauna yana tanƙwashe ƙafafuwansa sosai ya dube ta yana jin ciwon kansa na sauka ya daɗe kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce
"Kina da matsala da matata ne?"
A hassale kamar ba Ridayya ba ta ce "E, ina da ita mene ruwanta da kai zata aureka? Kuma ni ba zan je na dinga ganin yadda kuke rayuwa ba"
Nan da nan idanunta ya cika da hawaye sai yanzu Ustaz ya fahimci da biyu ta yi masa abinda ta yi kwanaki idan ya fahimta daidai ya haɗe da fuska sosai kamar ba shi ba a kasashe ya ce
"Oum-Bilal buɗe kunne zuwa gidana da rayuwa dani dole ya zame miki domin ina buƙatar, ina ƙaunar matata kuma ƴar'uwata bisa umarninta na zo gare ki, soyayya da ƙaunarta a zuciyata ya saka nake mata uzuri, idan kika bari ta yi kuka saboda ke za ki ga me zan miki, bana son fushinta kuma rayuwa gidana daban take wacce baki taɓa ganin irinta ba ko a mafarki"
Numfashinta ta ji yana tsayawa ta saka hannu ta ɗan riƙe rigarta bakinta na rawa ta ce "Da gaske wai ka yi aure Abbiey? Waka aura?"
Haɗaɗɗiyar girarsa ya ɗage mata alamar eh don ba zai faɗi abinda bashi kenan ba ya juya a hankali ya ce
"Aure lokaci"
Wani irin kuka ta rushe masa da shi tana durƙushe wa a ƙasa "Amma ƙatuwa dani a ga babana ya yi aure? Kuma soyayya kuke kuma ta haihu?"
A ransa ya ce "Babbar magana" a zahiri ya ce
"Laifi ne idan matata ta haihu? Ke dana aurar dake kika haihu laifi ne? A'a ƙiyayya muke kema mu je ki faɗa mini inda kika baro mijinki a daidaita na ba yar dake, matata jinina ce"
Daga nan bai ƙara cewa komai domin daman dauriyar maganar yake yana ji tana ta kuka ya rasa dalilin kukan nata a haka har bacci ya ɗauketa. Ya tashi ya bi ko'ina da addu'a ya ƙure gudun a.c ya gyara mata rufa bayan ya cire jerseyn ɗin yana ji tana ta sakin ajjiyar zuciya hawaye ya nashe da baƙin fuskarta. Can cikin dare Ridayya ta ji kamar ana buga abu da sautin fitar numfashi sama-sama ta buɗe idanunta daya kumbura a tsaye ta ganshi daga shi sai single ya cire jallabiyya ɗin bata taɓa tsayawa ta yi masa kallon tas ba, gabaɗaya Abbiey ɗin yanayin kamar ruwa biyu haka Ubangiji ya yi masa kalar tashi halittar kamar Balarabe kamar Bature fatarsa har yellow take ta ɗauka Zameer ne kawai mai yin murɗaɗen jikin nan amma sai taga naga Ustaz ya ci uwar na Zameer ko dan kullum cikin jallabiyya yake ne? Baya ya juya mata amma six packs ɗin shi a buɗe yake ko'ina ya rabu ga wasu muscles dake rawa a jikinsa kana ganinsa kasan yana cikin wani hali ji yake kamar ana tsaga naman jikinsa kansa ana sara masa gida biyu gashi ya kasa runtsawa ko kaɗan sama da sati baya iya bacci tsananin azabar ciwon ne ya saka yane buga kansa da bango kaɗan-kaɗan har ya fara da sauri.
A tsorace Ridayya ta miƙe tsaye bakinta na rawa ta ce "Abbiey?"
Cak ya tsaya da sauri kuma ya saka hannu ya kashe hasken ɗakin kafin ta kunna ya yi saurin shigewa bathroom zata iya cewa zata taɓa shi a wawtar Ridayya domin ya lura ba ta yi girma da hakan ba. Ta yi jigum ƙasan ranta kuma tunanin Sadauki take da halin da zai shiga.
Dab da asuba wayar Ustaz ta fara ringing taga baƙuwar number tunaninta ya bata maybe matarsa ce. Can kuma aka kira da wata number an saka “Friend”
"Babban mutum"
"Yaya ni ce, Ridayya ce Abban Nadra Please ka zo ka tafi dani wallahi ba zan bisa ba"
Tajj ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Bake kika bisa ba?" Ta kasa cewa shi ya zo ya ɗauketa.
"Listen Mimi, ina Ustaz ɗin?"
Ta tura baki ta ce "Na farka na ganshi tsaye yana buga kansa kuma ya shige toilet"
"Subuhanallahi, Innalillahi! Ciwon kanne? Abbiey ɗinki bashi da lafiya Mimi yaƙi bari a faɗawa Hajiya ciwon kai ne wanda yake shirin ɗaukan rayuwarsa ki gaggauta zuwa wajansa ki riƙe masa kan ki yi masa addu'a"
"Yaya Sadauki fa?"
"Ridayya wai wanne kalar tunani ne dake? Me ya sa kwakwalwarki bata faɗa miki daidai ga halin da Ustaz yake ciki kina tambayata a kan wani"
"Bai san na tafi bane, Yaya shi Abbiey bai taɓa nema na ba tunda nake kana ji ma wai ya yi aure ai ya jira dawowata a yi bikin ina nan?"
A nan Tajj ya warware mata komai na irin neman da Ustaz ya yi mata tare da cigiyarta "Ke a iya tunaninki Ustaz zai iya zuba idanu ba tare da ya san inda kike ba? Idan ke za ki iya aikata abinda kika aikata kina tunani shi zai yi, Ridayya kin san waye Babban mutum kowa? Ki yi tunani da kyau ki nutsu ki fahimci shirun shi, kallonsa idan ke ba ki fahimce shi ba waye zai fahimce shi ba, idan ke ba ki zama silar farincikin shi ba da yayewar ciwonsa ba waye zai zama wa yake da shi? Ko biyu ne kawai kuka rage a duniya daga ke zai shi nasan kina sane da cewa iyayenku basa raye, Hajiya ta rage da Mai ran ƙarfe su kuma ba za su iya kulawa da ku ba, idan ke Ustaz ya kula dake shi waye zai kula da shi? Kin san zurfin cikinsa rashin damuwa da abu, sadaukarwa. Kin san adadin matan da suke ƙaunar Ustaz dukda shekarun shi? he is blessing ni da kai na ina ƙaunar zama kamar shi da Nadra ta isa aure ko kuma babba ce wallahi shi zan aura mata ko ta na su ko bata so.....,"
Ya yi shiru yana sauke ajjiyar zuciya kafin ya ce
"Every girl deserves a guy that can make her smile, even when she doesn't want to. Ki buɗe zuciyarki ki ji sunan waye idan kika tuna ko kika ji yanayinki ke sauyawa? Waye bakya jure ganin ƙwayar idanunsa? Waye bakya gajiya da ɗabi'unsa waye za ki iya sadaukar da farincikinki saboda shi? Waye idan ya taɓa jikinki yanayin yake kaiwa har kwakwalwarki? Waye kike jin kishin shi? Waye bakya ƙaunar ganinsa da ko wacce mace sai ke ɗaya? Who sacrificed many things for you?"
Ya yi shiru a hankali Ridayya ta ce "Mene amfanin haka?"
"Idan kika nutsu kika gano waye wannan mutumin to shi ne the best for you shi ne wanda kike so kuma kika cancanci rayuwa da shi"
"To idan na gano fa sai na yi me?"
"Ki faɗa mini waye wanda fitilar ta haska miki, sai ki fara tunanin rayuwa da shi"
Ta yi saurin girgiza kai ta ce "Wai da gaske Abbiey ya yi aure?"
Tajj ya yi shiru ya san ba haka bane sai kawai ya ce "Oh ba ki sani ba ko? Ai ya yi aure kama yana matuƙar son matarsa komai ya ce ita komai ita ba kiga yadda itama take son shi ba, ina tunanin ma ciki gare ta kuma....,"
Ƙittt! Ya ji Ridayya ta kashe kiran ya yi murmushi a ransa yake addu'ar ranar da zai ga Ustaz da Ridayya matsayin mata da miji dukda damuwar dake ransa shi ma amma ganin wannan ranar kamar abu ne mai wahalar gaske.
Ridayya ta kifa kanta tana rufe idanunta "Ciki?" Ta maimaita kalmar haka kawai abin ya zauna a kanta kenan duk abinda Zameer ke yi mata shi Abbiey ya kewa matarsa har ta samu ciki? Wani abu ya tsaya mata a maƙoshi.
Washegari kafin ta farka Ustaz ya yi wanka ya shirya cikin shadda ruwan makuba ta amshi jikinsa ya ɗora zanna bukar a kansa ya yi wani irin kyau amma idanunsa ya faɗa. Yana parlour ya zaune can ta fito sanye da baya mai hijabi ta amshi jikinta idanunta ya kumbura Little na ganin Ustaz ya fara dariya yana zillo tare da miƙa hannu ya ɗauke shi.
Kanta a ƙasa ta ƙarasa ta tsuguna gaban Ustaz da ƙyar ta iya cewa
"Ina kwana? Ya jiki?"
Bai kalleta ba, bai kuma amsa ba ya amshi Little ya miƙe ya yi waje ta bi bayansa da kallo kana ta bisa a jikin mota ta ganshi suna magana da wani ganin ta kusa ƙarasuwa Ustaz ya sallami mutumin ya shiga bayan mota yana rungume da Little itama ta shigo drive ya ja zuwa airport basu ɓata lokaci ba wajan shiga jirgi daga nan suka nufi hanyar Lagos lokaci zuwa lokaci tana kallonsa kamar bashi ba a ranta tana makami daman haka shadda ke yi masa kyau? Yadda Little ke bacci a jikinsa zaka ɗauka uba da ɗana kamar Ustaz ya yi kaki ya tofar.
Da farinciki ya shigo parlourn yaga bata ciki ya kalli Zainura ya ce "Daughter where is your Mom?" Zainu ta ce
"Baffa kullum idan ka zo sai ka ce ina Mami ni baka cewa ina nake?"
"Ke me za ki yi mini me kuma za ki bani banda surutu da amsar kuɗi"
Ta rausayar da kai ta ce "to ai kowa yau ba zan faɗa maka inda take ba"
Baffa ya zaro idanu ya ce "Haba mana daughter rufa mini asiri kar ki ga yanzu na sume muku"
Ta dinga dariya ta ce
"Yanzu ta shiga bedroom tana waya ne"
Ya nufi bedroom ya hango ta tsaye gaban madubi sai kanshi ke tashi a room ɗin ta sha kwalliya waya ce kare a kunnenta sai kuma ajjiyar zuciyar da take saukewa ya ƙarasa ya rungumo ta, ta baya yana ɗora kansa a kafaɗarta
"Zan kira ki anjima Yaya A'isha" ta katse wayar tana juya Baffa ya rungumeta ya ce "Lovely ke kullum kamar wahainiyya" ya sunbaci goshinta da kumatu yana kallon bakinta ya ce
"Albishirinki" Ta ce
"Goro" ya girgiza kai ya ce "Canki kawai ma"
Idanunsa akan jakar wata zuma.
"I have no idea, ka faɗa mini mana"
"Idan na faɗa miki me za ki bani? Idan kin yarda mu ji daɗin wannan zumar tare da ake cutata da ita" Ya kai zumar bakinsa yana sha kallonsa kawai take tana murmushi tamkar ba Alhaji Mansur Rano ba, wanda ya gana mata azaba ita da yarinyarta
"Kin san me? Wahalarmu ya ƙare ba, they are together kuma i have a plan in sha Allah"
Wani irin rungume Baffa ta yi tana fashewa da kuka ta ce
"Allahamdulillah na gode Allah da ban mutu ba zan ga Ridayya Allah ka bani ikon nuna mata soyayyar data rasa Allah ya sa ta amshe ni matsayin uwa ta haife mini"
Dariya kawai Alhji Mansur ke yi mata ya ciro alawa da dabino da goro ya ce "Amshi