Showing 144001 words to 147000 words out of 190738 words

Chapter 49 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17311

feed on you.....,


Ya kasa ƙarasa maganar tsoro ya shiga zuciyar Ridayya ta mance yadda ake ta manta sam kuma bata shirya ba, uwa uba ga ɗinkin da akai mata ga kuma gyaran data sha a Maiguduri. Hankalinta ya tashi ta fara shassheƙar kuka Ustaz bai ma san me take yi ba yana ƙoƙarin maida Ridayya matarsa ta halak kuma ta sunna kamar gilmawar walƙiyya haka photon Zameer da Ridayya ya faɗo masa a cikin idanunsa sanda ya gansu turmi da taɓarya cikin hanzari ya miƙe tsaye yana dafe bango ya fice daga ɗakin bakiɗaya....




Barkanmu da sallah🤓
Ku yi haƙuri na jina shiru, wallahi ayyuka ne suka sake ƙaruwa. Kun san me rai da buruka wani aiki da na yi apply tuntuni shi ne na samu aikin yanzu nake ta jigilar zuwa seminer. Bana son fara typing na tsaya, but yanzu Allahamdulillah da taimakonku da haɗinku za mu kai zuwa gaci a ci-gaba da yin comment da sharing. A kuma yi haƙuri da abinda za a karanta marubuci baya fara labari ba tare daya tsara shi ba komai aka karanta daman a haka yake dole zai kasance.




Comments
Share fisabilillahi.
*MUNAFUKIN MIJI 39*
Mikiya Writers Ass




Bright pens free batch
Nimcyluv


*Masu buƙatar Munafikin miji daga farko ku yi following channel ɗina👇🏻*https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T


Muna yin tallah don ƙarfafa kasuwancin jama'a, a saka maka a status mai 1k to above viewers muna sakawa channel mai 2k zuwa sama followers sai kuma a littafi. Idan kayan mata kake shiryawa muna yi mun sanya shi a kayan da tauraruwa ke using dashi, idan bags ne, shoes ne anything... Ku yi magana ta wannan number 08164069385






Ajjiyar zuciya Ridayya ta sauke tana wurƙila idanunta ƙirjinta sai ɗagawa yake ta jima kafin ta dawo daidai ta ce "Na shiga uku Abbiey me kake shirin yi?"


Can ƙasan zuciyarta ta ce "Ke ɗin fa matarsa ce, yana da iko dake Ridayya, idan bake akwai Mardiyya"


Tunawa da ta yi tana da wata wai kishiya hankalinta ya yi masifar tashi, tsoro ya wanzu a zuciyarta yanzu idan ya barta zai iya zuwa wajan Mardiyya yana da wannan ikon, ƙirjinta ya motsa wani abu mai kama da tsoka ya motsa a gefen ƙirjinta hakan ya bata tabbacin bata mace ba, tana da raguwar zuciya a ƙirjinta wacce babu shakka soyayyar Ustaz ce ta mamaye cikin tsokar da wajanta wacce ta haddasa bugawar ƙirjinta da ƙarfi fiye da bugawar agogo.


Sakkowa ta yi jikinta a sanyaye sai yanzu fitarsa ya dame ta, domin har zuciyarta bata da tabbacin abinda ya hana shi idda nufinsa a kanta, tana tsoro da shakka ƙwarai. Jiki a sanyaye ta nufi parlour amma the parlour is empty ba kowa a ciki, sai ɗumin hiter saboda sanyi. Ta bishi?


"A'a Ridayya kar ya yi miki faɗa" zuciyarta ta yi saurin faɗar hakan.


Ta marairaice fuska bata sake bada ƙofar wani tunanin ba, kai tsaye ta nufi ƙofar da take da tabbacin yana ciki. Ƙarar saukar ruwan shower da ta ji ya sa ta san yana ciki da alama kuma wanka yake ta yi can ta zauna. Ustaz ya sauke numfashi sai a lokacin ya lura bai kyautawa kansa da zuciyarsa ba, kokawa yake ta yi da zuciyarsa amma wani irin zafi da yaji-yaji yake ji a tsakiyar ƙirjinsa ɗanɗanon bakinsa ya sauya, bai san me ya sa tunanin abub ya faɗo masa ba, tunda ba zina ya rusketa tana aikatawa ba, sunna ce, sunna mai ƙarfi tunda mijinta kuma koba komai Ridayya ba zata taɓa wofintar da tarbiyyarta ba.


Ya buɗe idanu wanda suka shige ciki a fili ya ce


"Allah ka yafewa Ustaz, na yi rashin uzuri ka yafe mini bisa tunanina"


Gyara zaman bathrobe ɗin ya yi ta zauna da kyau a jikinsa, ƙamshin shower gel na fita daga jikinsa, a baƙin ƙofar toilet ɗin ya cire bedroom slippers ɗin ya saka normal slipper na ɗaki yana fitowa zuciyarsa ta doka da ƙarfi ganninta zaune idanunta cike da hawaye, idan da akwai abinda ba zai jure ba shi ne zubar hawayenta.


Kasancewar shafa baya cikin ɗabi'arsa ya saka ya ƙarasa bakin gadon ya zauna, kamar zai yi shiru sai kuma ya juya ya kalleta a taushashe cikin lallausan harshe da murya mai nutsar da sabuwar zuciya a shiga soyayya ya ce


"Mene? Are you okay?
Lafiya kike?"


Ta yi shiru ya kama hannunta ya damƙe cikin nasa


"The tears? Hawayen mene? Nine? Laifi na yi?


A nutse yake magana, laɓɓansa na ware wa ɗaya bisa kan ɗaya amma zuciyarsa rawa take, bai san me ya sa bashi da ƙarfin qwiwa ko kaɗan akan Ridayya ba, tsoro ne hakan? Ko kuma tsananin soyayyarta ce ta hadda masa, ko raunin dake tattare da yarinyar ne?


"Abbiey me ya sa ka juya mini baya?"


Ya waro manyan gajiyayyun idanunsa masu cike da bacci da kuma abinda ke kai kawo a jikinsa, ya sake shigar da hannunta cikin nasa yana raba musu ɗumin ruwan wankan, ya ware idanu a kanta ya kasa cewa.


"May be i was wrong da nake tunanin zan samu farinciki wajanka Abbiey"


"Shhhh Ridherh"


Ya ɗora yatsarsa a laɓɓanta baya son jin komai, hawayenta ya sake sakkowa bai yi magana ba ya miƙe tsaye ya kashe hasken bedroom ɗin ya dawo ya kwanta tsakiyar gadon, yana daga kwancen ya miƙa mata hannu ta yi saurin cewa


"Ba za ka yi mini komai ba?"


Ta cikin zuciyarsa ya ce "Jaririya ba ki da hankali, ke ɗin halaliyyata ce"


A fili kuma ya lumshe idanunsa ya buɗe alamar “Eh"


Gadon ta hau ya ɗora kanta a ƙirjinsa ya rufe ta da hannayensa, babu wanda ya yi magana cikinsu sai shi da hannayensa suke shafa sumar kanta, ya kasa daurewa saboda ƙamshin turarenta wanda bai taɓa jinsa ba ya addabe shi, haɗin turaren amare ne daga (Hajiya Nana).


Misalin 3 daidai ya zame ta daga cikinsa yana ji tana motsi saboda raba jikinsu da ya yi, ya ja mata pillow. Ustaz bacci ya ƙaura ce masa ya yi alwala ya shimfiɗa ladduma Nafila yake ta yi har lokacin yin Assalatu ya yi.


Samun kansa ya yi da yin addu'a tsakaninsa da Ridayyerh, ya ɗora goshinsa a ƙasa yana kallon Alƙibila da murya ta neman taimako da ɗaukin Ubangiji ya ce.
"Ya Ubangiji ga Muhammad-Bilal Tahir na neman taimakon ka, ni ɗin bawa ne gare ka, mai rauni, mai damuwa, na san ka fini sanin damuwata, ban kuma raina ni'imar da ka yi mini ba, ni Ɗan'Adam ne mai buri da sanya abu a zuciya, ni almajiri ne kuma bawanka mai tsananin tsoron haɗuwa da kai saboda rashin tabbas. Ya Mujibudda'awati ka sanya hannu cikin lamarina. Ina tsananin son matata Ridherh, bana son ya kai ni ga halaka, ina tsoran soyayyar zamani, Allah ka tabbatar da dukkan alheri ga rayuwar aurenmu, idan aure na da Ridherh alheri ne kuma akwai rabo, Ubangiji ka cire mini abinda ke mini yawo a zuciyata, ka rage mini kishinta, ka tsayar mini da zuciyata waje guda, idan alheri ne auren nan namu ka bani ikon mayar da ita cikakkiyar matata ta sunna, ka yi mana tsakani da sharrin mutum dana aljan, ka sanya farinciki da walwala a rayuwarmu, ka sanya mana nutsuwa yarda da juna, ka kaɗe mana fitina, ka sanya matata ta soni ko kwatan son da nake mata ne, domin ba zata mini irin soyayyar da nake mata ba. Idan aure na da Ridherh babu alheri Ubangiji ka fini sanin komai ka mayar mini da mafi alheri ya zuljalalu wal ibkar. Allah buƙatar al'ummar jihata akan zamana gwamna idan alheri ne ke kirana ka tabbatar mini dashi,, idan ba alheri ka nisanta ni daga wannan al'amarin, gani gabanka ya Allah ka taimake ni, ka tausaya mini, ka sanya hannu cikin lamarina"


Ya jima yana addu'ar har sai da ya ji damshi a fuskarsa ya gamsu kana ya ɗago ya shafa ya fara azkar idanunsa a kanta. Kamar yadda aka ce dukkan wani musulmi idan har Assalatu ta yi dukkan baccin da yake sai ya motsa hakan ce ta kasance ga Ridayya, bakinta ɗauke addu'a da salati ta shiga motsawa har ta buɗe ido, ta shafa ta ji ta ƙanƙame pillow ta kwaɓe bakinta.
Zamewa ta yi daga cikin duvet ta sakko ƙasa, mamakin ganin kayan bacci ya kamata kullum Abbiey baya gajiya da sauya mata kayan bacci? Kenan yana kalle mata jiki? Innalillahi ta yi saurin rufe ƙirjinta.


Bata san yana ciki ba ta ji ya yi gyaran murya ya ce


"Sai dai ki ɓoye wani abun ba wannan daya zama t.v ɗin Muhammmmd ba"


Ta tura baki "Kai Abbiey ba kyau"


Ya cije laɓɓansa yana duba lokaci "Uhm Ustaza manya, bari na je masallaci"


"To Allah ya tsare mini kai"


Ya yi saurin Juyawa ya kalleta ya ji me ta ce fuskarsa ta faɗaɗa duk da haƙurinsa bai bayyana ba. Ya juya ya nufi masallaci.


Alwala ta yi itama ta gabatar da raka'atul fjr kana ta yi sallar asuba, ta yi wanka cikin sauri ta haɗa turaren zama wanda Hajiya Nana ta bata da Anuty Kaltum ta yi mata bayani tare da mata order nasa. Sosai take jin daɗin turaren aduk sanda ta yi sai ta ji jikinta ya sake haɗewa nan da nan kuma za ta ji sauyi bayan ta kammala, ta kunna kwal mai ƙwalli ɗaya ta saka turaren icce ta yi durƙuso ya shiga jininta sosai, cikin sauri ganin har 6 ta kusa ta ɗauki halin oil ɗin da aka yi mata na musamman wanda ke ƙarawa fata laushi da santsi kamar ta jarirai idan kana shafa shi babu buƙatar kana yin dilka duk a haɗin kayan Hajiya Nana yake, bayan ta shafe jikinta ta ɗauki kwalaccar Nana ta shafa, ta ɗauki humura ta shafa, ta haɗa wani magani a cup mai ɗauke da hulba ta ruwa data gari saboda tsaiwar ƙirjinta tunda ta shayar kuma Allahamdulillah maganin na musamman ne domin a sati guda ta yi da fara amfani da maganin abin har tsoro yake bata idan ta kalli ƙirjinta lallai a gaida Hajiya Nana mai da tsohuwa yarinya, duk yadda Zameer ya wulaƙanta mata jiki amma yanzu tamkar ba ita ba.
Idan ta tuna yadda ta komaɗe ta nemi zama tsohuwar ƙarfi da ya ji a gidan Zameer sai ta ji a rayuwa babu namiji da ta yi wa muguwar tsana sama da shi, ya cuceta ya ruguza mata rayuwa, ya rusa gobenta yana son lalata mata career ɗinta, idan haka aure yake zata bugi ƙirji ta bawa ɗiya mace shawarar kar ta sake ta yi aure. But now rayuwarta Allahamdulillah tana rayuwa cike da kwanciyar hankali da mutumin da tun fil'azal ya dace ace shi ne zaɓinta na farko, amma ƙaddarar auren MUNAFIKIN MIJI ya sanya bata fahimci hakan ba.
"Ridayyerh yana da kyau ki nutsu ki rayuwa mai kyau da tsafta da mijinki, hakan ne zai ba ki damar janye hankalinsa daga kan Mardiyya,da kuma macen dake kwaɗayin zama da shi"


Kitchen ta nufa ta tafasa black tea domin tasan dole ya nema, bayan ta kammala ta haɗa zuma cikin cup da dafaffiyar madarar shanu mai zafi ta shanye a kitchen ɗin duk ƙaunarta da son shan ruwan sanyi haƙura ta yi saboda maganin da take akai yanzu.
Parlour ta koma ta sanye da plazo da kuma t.shirt mai babban hannu ɗaya a zame wajan kafaɗa ɗaya daidai ta ɗora hula ta rufe kunnenta, tana zaune tana azkar wajan 6:34 ya shigo ciki bakinsa ɗauke da sallama muryarsa a nutse wajan ta nutsar da zuciyar Ridayya sosai da kyau.


"Good morning Abbiey"


Ta ce bayan ta durƙushe har ƙasa ta miƙa hannunta, ya yi murmushi mai taushi yana lumshe idanunsa "Oh Allah na, yaushe za ki bani wani gurbin ne Ustaza?"


Ta yi murmushi ya kama hannunta tare da ɗagota saman kujerar ya zaunar kusa da shi, sukai kusa very close numfashinta na sauka a wuyansa ya kama kanta tare da sumbatar goshinta, ya sake sumbatar ƙuncinta a hankali yana kallon fuskarsa dake cikin tafukan hannunsa ya ce


"Kina lafiya Mar'atussaliha?"


"Cikin amincin Abbiey"


Ya jinjina kai yana ta kallonta for long a hankali ya sauke breathing numfashinsa calmly ya ce


"Kin san me?"


"Sai ka faɗa Abbiey"


"Za ki iya rayuwa dani for life? Na dindin ba na wani lokaci ba?"


"Abbiey zan rayu da kai na har abada, zan rayu da kai zuwa ƙarshen numfashina da zan yi a jikinka koda mutuwa ta ruskeni" ya matse hannunta wanda shi ke nuna mata magana ta shige shi da kyau "Allah ya yafe miki Ustaza ya taƙaita miki haka nan"


"Why? Mardiyya kake so? Da ita kake son rayuwa? Baka so na bayan na kasance matarka ko akwai wani abu daka riƙe a zuciyarka Abbiey wanda kake ƙoƙarin hukunta ni da shi, why not me sai Mardiyya? To why i am here? Me ya sa ba Mardiyya ba?......,"


Caraf ya cafke bakinta da yatsu biyu yana juya mata idanu, amma ina idanunta zallar ƙaunarsa suke nunawa, sai ya ji zuciyarsa na matsewa tana tattarewa waje guda a ƙirjinsa wani irin emotions na yunƙuru masa gabaɗaya ƙofofin gargasar jikinsa suka buɗe ya kasa furta komai sai ƙwayar idanunta da yake kallo. Hakan da ya yi mata ya ƙara tabbatar mata zuciyarsa naga Mardiyya sai ta fashe da wani irin makirin kuka wanda ya gigita Magidancin mutumin, Ustaz ya rasa me zai yi sai kawai ya zame ƙasa ya durƙushe gaban Ridayya a saman qwiwowinsa.


A can ƙasa Nigeriya Ammi ce zaune a parlour ta saka Yaya Zuhura a gaba da mita tana faɗin "Ba zan zauna dake a cikin gidan nan ba Zuhura, kina kallo na lallaɓa ɗan wulaƙancin mijin nan naki amma shi ne kika sake dako wani yajin ko? Kina so a yi mini dariya kin kasa zaman gidan miji"


Yaya Zuhura ta yi shiru wani irin haushi kalaman Ammin ke bata wato ta zauna ya kashe ta? "Dan ubanki ina magana kina mini shiru? Shegiya uwar taurin kai"


"Ammi idan kika yi mini baki wallahi ke zan lalacewa ba wani ba, domin sanda muke zuwa wajan malamai ana siye zuciyar mijina yana bani kuɗi Baffa bai sani ba, kuma ni da za ki sani a gaba kina mini mita so kike na koma ya yi ta dukana ya samu jaka?"


"Jakar ce mana tunda ba za ki iya haƙuri da zaman gidan miji ba, tunda kike duk wahalar da Ridayya ta sha kin taɓa ganin tayo ya ji a gidan? Ba kalar uƙubar da bata shiga ba, yarinya ta zama kamar dabba don azabar gidan miji...,"


Yaya Zuhura ta miƙe tsaye ta ce "Ni da ban Ridayya daban, ba zan iya ba kuma ba zan jura ba, ya ce a biya shi kuɗinsa daman duk kuɗin da nake amsa ke nake bawa, wallahi ki nemi kuɗinsa ki kai masa babu ruwana ficika ban ci ba" a fusace Ammi ta miƙe tsaye zuciyarta na tafasa ganin Junaid a tsaye da kuma Zainu ta ce


"Zuhura har wuyanki ya yi kaurin da ina uwarki za ki dinga faɗa mini haka? To oya zoki shige ki tafi gidan mijinki kafin na yi miki baki yanzu"


Ƙunƙuni Yaya Zuhura ta fara ta ce "Duk wata masifa bake kika ja mini ba, idan don ina kwana a gidan nan ne sai na daina kima daina ganina bakiɗaya a gidan, sai na daina kulaki mu daina magana da juna"


Junaid ya ce "This is serious, kin san me kike cewa kowa?"


"Ina cikin hankalina ba hauka na yi ba, ni wallahi ban san me ya sa ba amma ji nake inama ba Ammi ce uwar data haife ni ba, dama ace Mami ce" Wani irin mari Ammi ta kaiwa Yaya Zuhura ta yi saurin kaucewa Ammi ta yi luuu ta kifa zuwa ƙasa bakinta ya daki jikin kujera nan take bakin ya fashe, ya fara fidda jini haƙori ɗaya ya gutsire. Da sauri Yaya Zuhura ta tattara kayanta tas ta koma part ɗin Mami da zama, Junaid da Abdullahi ne suka kama Mami tare da kiran family Doctor.


A daren bakin Ammi ya haye ko magana bata iya yi, wai yau ƴarta da duk duniya ta fi ƙauna cikin yaranta ita ce ta yi mata haka? A gaske hakan ya faru ba zahiri ba? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un babban tashin hankalin Ammi bai shige tunani wai Yaya Zuhura ta koma part ɗin Mami gabaɗaya ba, ta daina mata magana gaba take da ita suna rayuwa kamar Musa da fir'auna. Ammi ta manta yadda ta raba ƙaunar dake tsakanin uwa da ɗiyarta tun tana jaririya ta raba ganawa, ta yi musu farraƙu gida ɗaya suke amma Mami taba iya ganin Ridayya ta yi mata magana kamar ba yarinyar da ta yi dakon cikinta ba har wata tara da wasu kwanaki, yarinyar data kusa mutuwa wajan haihuwarta. Wataƙila shukar da Ammi ta yi ce ta fara girba amma duhun dake cikin kanta ya mamaye ƙwaƙwalwarta har ta kasa lura da hakan.


Daman Zainu jininta bai haɗu da Ammi ba, wani lokacin a dole take gaishe ta. Mami dake zaune cikin baƙar abaya wacce ta rufe mata tsohon cikinta, mace mai tsananin haƙuri, kawaici ɗauke kai, da nuna damuwa akan damuwar wani, ga kyau ga kyan hali ga kula da miji da tsantsan biyayya ta dubi Zainura ta ce


"Mr tsiwa je ki duba abinci idan ya nuna, ki shirya dinner ok?"


Zainu ta kwaɓe fuska tace "Mami wai tsiwar me na yi ne haka, Allah ki daina mini wannan shaidar ba kyau ke uwa ce"


"Na ji uwar ƴan tsara zance"


"Mami" Mami ta ɗaga Idanu ta kalli Zainura sai bata ce komai ba, Zainu ta ce


"I love u Mami, u looks so young na matso a yi mini ƙani kowa yana da ƙani ban dani"


Mami ta zare idanunta da suke farare ta ce "Na shiga uku, waye zai miki ƙani?"


Da hannu Zainu ta nuna cikin Mami ta ce "I saw it, wallahi cikin haihuwa ne bana abinci ba"


"Get out Zainu"


Fita Zainu ta yi da gudu saboda ta san halin Mami bata ɗaukan nonsense akan abu, musamman tarbiyya ta yara, Zainu akwai karabbani bata ɗaukar raini kana yi mata zata maka nan take tana da wani irin kishi da uwarta da ƴar'uwarta Ridayya. Mami ta girgiza kai kawai ta sauke ajjiyar zuciya how long zata kasance tana ɓoye cikin? Bayyanar cikin na nufin abubuwa da yawa ta gwammace ta yi ta ɓoye wa har zuwa haihuwa tunda tana da jiki da tsayi cikinta baya bayyana sosai. Waya ta yi da Mahaifiyarta Dada tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login