Showing 42001 words to 45000 words out of 190738 words
Chapter 15 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
wanda na haɗa da jinin al'adata ta kifo da shi" Biba ta ce "Kutimelesi ina ganinta a murguɗe ashe muguwa ce?" Ammi ta finciko Ridayya ta ce "To da fa? Kwana biyu daman bana gane kan Alhaji Mansur cikin bacci zai fara kiran Fatima, Zarahna"
"Riƙe mini ita Biba" wuƙa Ammi ta ɗakko ta ɗora a saman gas, wuƙar nan ta yi jajur da ita kamar a maƙera sai ka ce mai shirin yin walda "Fito mini da harshenta, buɗe bakin nata ki riƙe kafura mahaukaciya da kyau" Biba ta buɗe bakin Ridayya tare da zaro ɗan ƙaramin harshen yarinyar duk miyar data shafi wajan tana nan, babu tsoran Allah babu tunanin zata mutu tabar yaranta a duniya cikin rashin tausayi da imani Ammi ta ɗakko wuƙar nan daga gama yin jaa a wuta ta manna wa Ridayya a harshe......
*Wannan page ɗin na ku ne stepmother Jama'a mutuna a kodayaushe mutuwa na kusantarmu, yanzu ne, anjima, gobe ne jini. Only God knows. Uwar gida da amarya ku ji tsoron Allah, babu amfanin cutar da ɗan kishiya, matsalarki da kishiya daban, babu ruwan yaranku ciki, wallahi wallahi duk wanda ya wulaƙanta ɗan wani sai Ubangiji ya musu hisabi. A cikin Alkur'ani Ubangiji da kansa ya bawa maza damar auren mata huɗu cif, banga dalilinki na shigowa ki kori wacce take gidan ba, maza sun bar mu da wahala, saboda kawai ki mallaki miji sai ki haukata kishiyarki ko ki sabauta ta, ko kuma kai saka tsanarta a zuciyar miji ko ki saka mata warin jaɓa, ko ki musu farraku da ɗa da dukiya Allah kaɗai ya san mai morar su wallahi. Ku ji tsoran Allah ku ji tsoron wallahi cases ɗin da muke karɓa wajan aikinmu Allah ya yi yawa da su mene amfanin yin abinda ba zai maka amfani a lahira ba😭😭🤲🏻*
Bana jure sharing don Allah idan kin karanta ki yi sharing fisabilillahi🌚 idan ba a sharing zan mayar da posting iya wattpad da channel ɗita ko Facebook group nawa.
Domin gyara ko sharhi
sulaimanshuaibunaima@gmail.com
Na'ima Sulaiman Sarauta
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI 15 ✿*
Mikiya Writers Ass.....
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv
_Wannan shafin naku ne masoya Munafukin miji masu ƙaunar Zameer da shalalen Ustaz🤓 Drama section, Munafikin miji fans, Sarautar's Library gidan da aka kusa ƙwace shi daga hannuna🤣su Oum Safna,su Balkisa su Oum shaheed su Mom sani writer ɗin Surukata. Ga na musamman ajin tubarkalla Nimcy paid library, da jama'ar Nimcyluv readers hub. My WhatsApp channel people🥰🥰 much love Bright pens na godiya_
"Biba sake riƙe mini tsinanniya gayyar na ayya gayyar assha, wato ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu ko? Yadda uwarki ke son kwace mini miji, haka kike so wargatsa mini plan na yi biyu babu,uku ba ko ɗaya? Ki zame mini ƙarfen ƙafa mai wuyar fidda wa?" Ammi ta faɗa tana sake ɗora wuƙar a saman wutar gas ɗin. Biba dake riƙe da Ridayya, kamar wacce ta riƙe sa'arta sai haki take saboda wahala ta ce
"Ina ganin ki rabu da ita haka, she's to young da wannan azabar taki Maryam, matsalarki da uwarta daban, matsalarki da yarinyar daban, look at her? Shekara shida amma kamar ƴar shekara huɗu duk ta tsamure kodan rangwamen hankalinta kya saurara mata please"
"Na saurara mata? Kin san me kike cewa Biba, kin san baƙin ciki da takaicin dana ɗanɗana dalilin uwar yarinyar? Kin san halin dana shiga sanadin Fatima? Ai wallahi ko zan ƙarar da komai nawa ba zan saurara ba sai na kai ga gaci, this is my promise" Biba ta girgiza kai domin haka kawai tausayin Ridayya ya kamata, ita kanta ta tsani kishiya ko a mafarki bata fatan ace yau gata da kishiya balle a zahiri? Kuma burinta ta rayu daga ita sai ranta banda ƴaƴan kishiya. Ta kalli Ridayya da wani irin yawu mai kauri ke dalala daga cikin bakin nata,bata zaro harshenta da ya yi jajur yana tsastsafo da jini, fatar wajan ta ciro, idanun yarinyar kamar zai faɗo ƙasa saboda masifar azabar dake ratsa mata jiki, tana kaiwa gurɓatacciyar kwakwalwarta ziyara tare da game dukkan wani sassa na jikinta da suke motsa ji da gani.
"Ba kyau azaba da wuta, Ubangiji kawai ke da ikon haka, kurman da ita kike son yi ne?". "Ta kurman ce mana Fatima ke da asara bani Maryam ƴar Alhji Shitu ba"
"Malam Shitu dai, don bani da labarin Malam ya je makka, ke fa matsalar dake damunki hadda talaucin daya yi miki katutu a gindi" Ammi bata kula Biba don taga alama tunan silili take ƙoƙarin yi mata. Ta cafko harshen Ridayya tana ƙoƙarin manna mata wuƙar suka ji an ce.
"Ammi, Ammi me kike ƙoƙarin yi haka" Ta yi saurin cillar da wuƙar tana haɗe rai kafin ta ɗauki Ridayya idanunta zube a kan Junaid ta ce "Daga ɗora girki fa na nemeta na rasa, sai ihun ta na ji a kitchen, kasan ta da kwaɗayin nama kamar jikar mafarauta shi ne ta kifo da tukunyar ta ƙona kan ta" Junaid ya kalli kitchen ɗin, kana ya kalli Ridayya dake miƙo masa hannu tana sauke ajjiyar zuciya idanunta ya ƙafe sun ƙara girma, harshen data zaro yake kallo da sauri ya matsa yana kallon wajan ya ce "Me kuma ya sameta a baki?". "Ƙonar da nake faɗa maka ce ai"
"Bai yi kama da wacce ta ƙone ba, sai dai ƙona ta a kai, kalli shatin wani abu fa?" Ammi ta kalli Junaid gabanta na faɗuwa sosai ta ce "Me kake nufi? Ni zan ƙona ta ko kuma Biba data taimaka mini na ɗauke ta? Yarinyar daba hankali gare ta shi ya sa na ce babu mai saka ta a makaranta yanzu, ni zaka ɗora wa alhakin hakan Junaid?"
Ya girgiza kai murya a ƙasa ya ce "Ki yi haƙuri Ammi, bana nufin haka" Yana faɗa ya fice, ta leƙa ganin ya fi ta ta dungurar da Ridayya a wajan tare da yin part ɗinta, Biba ta bi bayanta a ranta tana jinjina abubuwan da suke mata yawo a kan ta.
Suna fita Ridayya ta miƙe tana yarfe hannunta, tare da fito da harshen waje domin samun sauƙin abinda take ji, da zarar iska ta kaɗa sai ta ji kamar yanzu ne Ammi ke manna mata wuƙar, majina, yawu suka haɗe mata sai kuma a lokacin ne ta fara neman hanyar gudu inda bata taɓa yi ba a gidan ta nufa, rashin ƙwari da ƙarfin jikin da bata da shi suke neman yasar da tsamurarren jikin nata. A jikin bishir zugale ta raɓe hawaye na bin idanunta sai nishi take da haki tana son yin kuka a fili ta kasa.
Shigowar shi kenan cikin gidan, tunda ya shigo ya samu kansa da faɗuwar gaba mara dalili. Ya yi jim a daidai mararrabar data haɗa shashin biyun, na Baba ƙarami dana Baffa. Yana ƙoƙarin nufar part ɗinsu ya ji saukar siririn muryarta a cikin kunensa.
"A...aaa.. Abbiey, Abbiey"
Furucin ya yi fitar gurbi daga cikin bakinta, ba tare data san waye a wajan ba, azaba ta saka babu sunan wanda ya zo bakinta da tunaninta sai na Abbiey.
Ustaz ya juyo da sauri har hiramin kansa na faɗuwa, idanunsa da suke kodayaushe a rufe ya sauka a kan Ridayya, ya zuba mata ido ganin sai murza harshe take.
"Shalele" Ya kira ta, cikin sauri ta buɗe idanunta ta kalli wanda ke tsaye a gabanta, bata hawaye da shi ba, amma tabbas muryarsa ta zauna a tunaninta raɗau. Ta shige ƙifta idanunta a karo na farko cikin murya ta sangarta ta fashe da kuka har lokacin kallonsa take. Ustaz ya durƙosa a gabanta ya kasa magana a tsayin shekaru shida ɗin da suka samu basa tare abubuwa da yawa sun faro har girman Ridayya, da kuma yanayin daya rusketa a yanzu. Tattausan hannunsa ya saka ya cira ta saba, tare da ɗora ta a kafaɗa ɗaya hannun kuma ya ja trolley ɗinsa kai tsaye kuma part ɗin Baba ƙarami ya nufa, shiru komai an yi mutuwa ba kowa, ko sallamar da ya yi cikin kamilalliyar muryarsa babu wanda ya yi balle ya amsa bedroom ɗinsa ya nufa da ita, yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya a bayyane.
Ammi dake zaune tana jinjina girman asarar da Ridayya ta saka ta, ta yi ƙwafa ta ce "Wallahi na tsani yarinyar nan, da dukkan alamu uwarta ma malamai take bi gashi nan komai na neman jirkice mini" Biba ta yi murmushi ta ce "Me ya sa kike tunanin Fatima za ta yi miki asiri?" Ammi ta ce "Me ya sa ba zan yi tunanin hakan ba, tunda tana son mijinta dole ce ta saka suka rabu, gashi da baya ƙaunar ko jin sunanta babu wanda yake magana a kan al'amarin auren yarinyar da kuma neman hakƙin Fatiman, kwatsam yanzu Mansur ya tsiro mini da wata ɗabi'a"
"A moral person doesn't lie, cheat, or steal, Fatima ba zata taɓa miki asiri ba wallahi zuciyarta ai ba irin taki bace, matsayin ƴar'uwa take kallon ki ba kishiya ba, babu laifi don ta so mijinta tunda ai sun gina tsaftatacciyar soyayya tun kafin aure, shiga kika yi wajan ganin kin raba su, ki ka yi musu farraƙu kuma kika raba uba da ƴarsa"
Ammi ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Yanzu Biba mene abin yi?" Biba ta yi murmushi ta ce "Nasan bayan na yi tafiya kin je wajan Malam right? Wanne aiki ya yi miki?"
"Kin san wannan yayar Fatimar Kaltum take kowa? Ƴar ta'adda ce wallahi da ƙyar idan bata taɓa yin dabanci ba, gashi mijinta soja ne muƙamin General gare shi, ni da abinda ya shafi hukuma bana son shi, to kuma tana iƙirarin zan gane kure ne"
"Kawai ki faɗa mini wanne aiki malam ya miki, ki riƙe bayaninki" Ammi ta ce "Ok. Na saka ya garƙame mini bakin jama'a da dama, ya kuma ɗauke hankalin kowa daga tunanin samawa Ridayya ƴanci, an rufe bakin Kaltum da mijinta, haka na mahaifiyar Fatima, an rufe bakin Baba ƙarami da matarsa ke dukkan wanda ya shafi Ridayya kuma yake da ikon yin magana a kan lamarin na kai sunansa wajan Malam, na saka an ɗauke hankalin Hajiya da Mai ran ƙarfe daga zuwa Kano, tun ranar basu ƙara zuwa ba, balle kiran waya, ke hatta yarana na rufe bakunan su kuɗi kawai nake kwasa wajan Alhaji Mansur" Murmushi sosai Biba ta yi ta ce
"Wow! That's good dear, amma kin manta malam ya ce Ridayya mai ƙashin arziƙi ce? Ko alherin da Alhji Mansur ke samun albarkacin haihuwarta ne, kuma ya haska mana goben mun gani, ga baiwa da tarin hikima"
Ammi ta miƙe tsaye ta ce "Shi ne abinda ba zai taɓa faruwa ba, idan har ina raye Ridayya ba zata taɓa zama wata a duniyar nan ba, shi ya saka nake bada maganin mayen nan ƙwaƙwalwar ta ƙara sa juyewa, ta yadda ba za ta taɓa fuskantar karatu ba, yadda ban hango future mai kyau a tawa zuri'ar ba, babu abinda zai saka na zuba idanu ƴar kishiya ta zaba wata, zan tabbatar bata samu ilimi ba idan har ina raye"
"Idan haka ne, kar ki sake ki bari Fatima ta dawo cikin gidan nan har abada" Biba ta faɗa tana cewa "kawo kunnenki"
Duk suna zaune a babban parlour mai zaman kansa, banda ƙira'ar Sheikh Afif Taj babu abinda ke tashi, ƙamshin Air-freshnerh ke tashi tako'ina.
A hankali ta ɗaga kai tana kallon wacce ta fito daga cikin ɗakin, cikin nutsuwa ta ajjiye azkar ɗin hannunta tana sakin murmushi ta ce
"Autana ta fi ta kowa ya aka yi?" Mami ta ɗan juya idanunta sai kuma ta miƙa wa Dada wayarta idanun Dada ya sauka akan number da aka saka "Zaujina"
"To ki ɗaga mana" Mami ta zauna kusa da Dada ta ce "I won't pick it, six years bai kira ni ba sai yanzu?" Murmushi Dada ta yi ta ce "Ikon Allah, Autana shin sau nawa zan faɗa miki ki wa Alhji Mansur uzuri ne? Ita addu'a bata taɓa faɗuwa a ƙasa dole akwai ranar da za ta yi aikin ta, ki ɗauka yanzu ne ta yi nata aikin ɗauki wayar mijinki Fatima"
"Dada please"
"Just pick up dear" Mami ta ɗauki kiran tare da saka wayar a handsfree ta cikin wayar Baffa ya sauke wani wahalallen numfashi mai nauyi ya ce "Batuluna kin azabtar dani, kiran waya ba ɗagawa kamar na miki laifi?" Mami ta yi saurin kallon Dada, Dada kuma ta yi murmushi tana ci-gaba da duba azkar ɗin ƙasan zuciyarta tana hamdala ga Sarkin sarakuna Ubangijin talikai, Ubangijin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ta wanzar da ƙudira da buwayarsa a lokacin da suke tsananin buƙatar taimakon shi.
"Kin yi shiru? Wallahi ɗan tafiyar da na yi a kan kwangilar da mukai magana last month ji nake kamar na yi shekara ɗari bakya kusa dani, i feel nothing but empty without you Zahraahna" Mami jin abin take kamar a mafarkin data saba yi na mijinta da tilon ƴarta, dukda babu wanda take nunawa abin yana damunta tasha wahala ƙwarai da gaske har kukan mutuwarta an fasa, amma dake mai dokin rai ce ta miƙe jijjigar da ta samu bata sake ta har yanzu. "Fatima, are okay?" Ta yi shiru can ya ce "Ok fine ki yi mini tuwon shinkafa miyar kuka ki tanadar mini man shanu, ki yi mini wannan kyakkawar shigar taki" Nan ma murmushi Mami ta yi idanunta na cikowa da hawaye a hankali ta ce
"Kamar baka cikin hayyacin ka naga alama, har ya sa ka manta cewa ni ba matarka bace ko?" A rikice ta ji muryarsa yana buga tsawa ya ce "What kamar ya? wanne irin mummunan furuci ne wannan wanda girman dafinsa na iya tarwasa zuciyata na roƙe ki da ki daina" Mami ta ce "Wallahi tallahi ni ba matarka bace, shekaru shida da suka shige ka sake ni ka rabani da jaririyata" Cikin sauri shima ya ce "Na rantse da girman Allah ke matata ce ban sake ki ba" Sai kawai ta kashe wayar tana kifa kanta a cinyar Dada tare da rushewa da wani irin kuka mai cin rai. _So the real love is never gone..?_
Dada ta dinga shafa kan Mami tana ganin yadda Baffa ke kira ba tsahirta wa wani na korar wani har number Dadan ya kira suke suka ƙi ɗagawa.
Ustaz ya dinga bin Ridayya da idanunsa masu laushi ganin yadda take ta murmushi a bawon wankan daya saka ta a ciki, ya ɗaure mata ƙugu da towel ƙarami ya jiƙe ta shakaf da ruwa, hakan ya yi ma Ridayya daɗi tana wasa irin wannan yadda ta nuna tamkar ba a yi mata wanka. She's so happy.
"Shalele, fita dai" Ta yi murmushi mayan dimples ɗinta suka loma duka lokaci ɗaya, ta fiddo masa da manyan idanunta masu zara-zaran gashin Idanu, baƙin fuskar nan kamar a saka ruwa da audiga a laso tamkar ya yi magana, yanayin farin idonta ke ƙara fidda baƙar fatarta ta a fili, a zahiri babu wani abu mai jan hankali a fuskar Ridayya duba da yadda bakinta ke tamkar a karkace ga yawu na fita ta gefe. "Abbiey"
Ta ce tana ƙifta masa ido, ya mata ƙuri a hankali kuma ya kai yatsa yana taɓa dimples ɗinta both sides.
"Ƴar gidan Abbiey" Ya furta a kasalance hana rufe ido, shekarun Ustaz 25 yayinda Ridayya take shekara 6 a duniya.
Tafiya karatunsa ya sauya sosai da gaske daman yana da girman jiki, wannan dalilin ya sa yake ganin idan aka faɗi shekarunsa jama'a za su raina shi, yanzu komai nasa ya sauya girma, nagarta, nutsuwa miskilanci da rashin son magana, baya damuwa da komai kamar yadda baya ɗaukan raini daga wajan wanda ba zai lamunta ba. Ya ajjiye ƙasumba mai kyau wacce ta yi daidai da tsayayyen gemun da Ridayya ke yawan jaa masa tana murmushi. Yana cireta daga cikin ruwan ta haɗe fuska ita ba haka ta su ba, ya shafe ta da Rob, ya ɗauki kaya masu nauyi yasa mata, da zai cire towel ɗin jikinta sai daya rufe ido yana faɗin "Haza haramun" bayan ya kammala shiryata cif ya kalleta ya kalli sumar kanta, bai ma iya tazar ba sai kawai ya ƙuƙƙulle ya saka mata hula. Ruwan zam-zam da rubutu ya ɗauka ya yi addu'a ya bata kana ya bata ruwan bagaruwa da zaiton yana jin tana da ajjiyar zuciya.
Bacci ne ya ɗauketa ya shirya shima cikin jallabiyya mai taushi ya naɗe kansa da hirami kana ya kunna karatun Alkur'ani mai girma ya rufo ɗakin. A parlour ya samu Umma da Baba ƙarami ta ce "Ikon Allah saukar yanzu hala?"
Ya jinjina mata kai yana zama saman kujera kana ya lumshe idanunsa hannunsa ɗaya yana murza goshinsa da gumi ke yanko masa da ƙyar ya iya cewa "Umma, Abba sabahur khair"
"Sannu da hanya Babban mutum ya karatu? A zo lafiya" Ya jinjina kai. "Baka ce kana zuwa ba, gashi bani da abinci" Ya girgiza kai ya ce "Nikam yunwa ina ji, da gaske yunwa Umma"
"To Babana girki ya kamani, Ustaz guda da jin yunwa?" Baba ƙarami ya yi murmushi kawai. "Ustaz bani ruwa a fridge mana" Miƙewa Ustaz ya yi ya ɗauki ruwan gorar kana ya nufi ɗakinsa ruwan rubutu ya zuba a ruwan ya girgiza kana ya koma parlour ya bawa Baba ƙarami ruwan, tunda ya sha yake jin zufa na yanko masa jikinsa ya yi sanyi ya ce
"Ka dage sai ɓangaren banki, yanzu gashi ka kammala karatun wanne banki kake tunanin za su karɓe ka?" Ustaz ya yi shiru, ganin haka ya sa Baba ƙarami cewa "Sai kuma maganar aure, yana da kyau ka ajjiye zuri'a" Ustaz ya yi saurin buɗe ido sai kuma ya ce "Aure? Asstagafirullah Allah ka yafewa Abbana" Yana faɗin hakan ya fice daga parlourn.
Da mamaki Ammi ke bin Bilal da kallo irin yaushe ya dawo ɗin nan? Sai kuma ta dake tana kallon Biba data sake zuwa za su wajan Malam domin ƙarasa aiki. Tunda Biba ta kalli Bilal ta ji wani abu ya saukar mata komai nata ya nemi kuncewa ta jima ba taga mutum mai kwarjinin Bilal ba.
Ustaz ya juya ya kalli Zuhura wacce gaba take da shi, ganin kallon da yake mata ya sa ta ce
"Ina yini Ustaz?"
"Ina Balkis?" Ta ce "Ta fita makaranta" Ya haɗe fuska ganin Junaid ya ce "Kai don ubanka jira kake na gaidaka?" Junaid ya ce