Showing 102001 words to 105000 words out of 190738 words
Chapter 35 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
yi shiru na rashin abin faɗa banda harbawa da ƙarfi babu abinda zuciyarta ke yi mata, a kullum Ustaz na yi mata kwarjini amma na yau na musamman ne ya sauya mata gabaɗaya babban abin ba wani sauyin kamanni a fuskarsa banda shekaru da ƙasumba daya ƙara da yawan sumar kai, sa nutsuwarsa da tarin kamalar daya sake mamaye gangar jikinsa ga wata Ilham ta musamman. Haka kawai ta ji ranta ya ɓaci da ransa da lafiyarsa hankalinsa kwance yake gudanar da mu'malarsa babu damuwa da tunanin yarinyarsa bata tare da shi bai san hali da ƙuncin data shiga ba.
Baya kallonta a zahiri sai sai dai da idanun zuciya yake kallon yanayinta shi bai ma san yaushe ya riƙe ta taɓa ɗazo kawai yasan ba zai zuba Idanu ta fita riga a buɗe ba. Duk suka yi shiru kowa ya kasa magana sai bugun zuciyarsu dake aiki so yake ya tambayeta ina mijin nata? Ya akai ya neme ta ya rasa.
Mahmah ce ta shigo ɗauke da Little dake kuka sosai tana faɗin "Mimi gashi ya addabi jama'a da kuka kin san halinsa idan ya fara kuka sai kin bashi ya sha hankalinsa yake kwanciya"
Ridayya ta kasa amsar Little ita kunyar Abbiey take yaga wai wannan ita ta haife shi kenan ya san me ta yi ta samu ɗan?
"Ina magana kina jin yaro zai fasa kunnen mutane?"
A marairaice ta ce "Mahmah ki riƙe shi zai yi shiru fa"
Daƙuwa ta yi mata ta ce "ungu wannan dan gidanku idan ke ba ki sha nonon uwa ba sai aka ce shi kar ki bashi? Saboda wa Allah ya hallici nonon banda yaranki? Bafa don a do aka mallaka miki su ba. Naga kullum kina bashi yanzu iyayi ne ko san a sani? Karɓe shi ni"
Idanunta tuni ya yi raurau hawaye ya cika su wacce kalar mafisa ce Mahmah ke shirin janyo mata don abin kunya?
"Don Allah Mahmah wallahi....,"
Ustaz dai da kunne yake ji ko ɗaga kai bai yi, he just pretend kamar bai san mene faruwa ba.
Ajjiye mata shi ta yi a cinya Mahmah na fita da halin yaran yanzu ta yi waje abinta don ita har zuciyarta bata ɗauka ta yi wani laifi ba.
Little ya dinga kuka yana zura hannunsa cikin rigar Ridayya alamar dai a matse take har da haura ƙafa kukan ya yi wa Ustaz wani iri a ka domin har ƙasan zuciyarsa yake jin kukan na Little ya ɗago kai yana haɗe fuska ya ce
"Ba haka na yi miki ba Ustaza da gaske ban raineki haka ba, ko sau ɗaya a ta dalilina ba ki taɓa kuka ba" Ya faɗa yana gyara zama tare da kafe ta da Idanu babu kuma wasa a fuskarsa don shi bai ga wannan dalilin ɗaukan alhaki da zunubin ba.
Ta tura baki taƙi cewa komai ita haka kurum haushinsa ya kamata me ya sa bai taɓa nemanta ba ta kuma yi alƙawarin ba zata yi magana ba amma tuni hawaye sun fara sauka daga idanunta saboda zallar sangarta da ganin kuma Ustaz ɗin a gabanta.
"Ko dai ki bashi abinda ya kewa ko kuma ni na zo na bashi, ko kuma dai ki cire su tunda basu da wani amfani"
Ganin ya miƙe ya saka ta yi saurin riƙe Little ta fara ƙoƙarin fito da shi cikin sauri kuma mai kama da nutsuwa Ustaz ya yi hanyar ƙofa yana jin kansa na sarawa.
Sanda ya fito daga bedroom ɗin Ridayya ya samu Tajj zaune shi da Sadauki daya gama rikicewa ya daddafe kansa da yake masa wani irin ciwo. Shi fa dole yau sai ya fita da Shanshan duk wahala yadda ya nuna masa iko shi ma dole ya nuna masa ya fisa dabara kuma ɗan'yau ne shi. Ya miƙe tsaye ya ce
"Please i want to talk to you Brother"
Tajj ya nuna kansa ya ce "Ni?" Ya jinjina kansa tare da ficewa ya yi waje. Tajj ya miƙe ya bi bayan Sadauki.
"Wannan kiran fa Hamza?" Sadauki ya riƙe hannun Tajj tare da ɗorawa a zuciyarsa ya ce
"Ka ji ko? Ka ji yadda zuciyata take yi to wallahi gab take da bugawa kuma na san ba za ka so na mutu yanzu ban yi achieving komai ba, ban yi aure na haifi kamar Nadra ba, ban san mene daɗin aure da daɗin zama da macen da kake tsananin so ba, ina so aure sosai"
"Duk ɗan sunna ai ba zai ƙi sunna ba Sadauki"
Sadauki ya jinjina kai yana ƙasa da murya har ɗagawar ƙirjinsa ana gani ya kama hannun Tajj ya damƙe cikin roƙo da neman iri ya ce
"Kai ne tsanin da zan hau na cimma gaci, gina soyayya a tubalin zuciyar daya dace da Hamza Sadauki wannan ba matsala ba, magance abinda zai iya kawo shamaki a rayuwar Sadauki da matar da yake da burin rayuwa da ita shi ne matsalar, Yaya help me please allow me to go with her"
"Ita wa?"
Sadauki ya hargitsa kansa kamar ya make Tajj haka yake ji ya ce "Haba Yaya haba Baban Nadra ya kake haka ne ka fahimta mana"
Tajj ya girgiza kai ya ce "Ban fahimta ba Sadauki"
"Ka fahimta mana da Hausa nake magana bada yaran Jamus ba, balle ka ce don na rayuwa a canne. Ka bani izini na fita da Ridayya akwai magana mai muhimmanci da zamu tattauna da ita ka tausaya mini"
"Wacce magana bisa wanne dalili kake son fita da ita?"
"Saboda ina son ta, ina son ta, ina son Ridayya Yaya kuma aurenta nake son yi" Tajj ji ya yi jiri na neman yar da shi zuwa ƙasa ya yi saurin jingina da motar Sadauki yana karanto Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! A zuciyarsa ga Amini da ɗan'uwa ga kuma shi shi bai tsaya ya nutsu a kan qualities ɗin Ridayya ba kawai ya ji yana son rayuwa da ita ko dan yadda Nadra ta samu farin ciki, yana tsananin tsoron macen da zai aura wacce zata riƙe masa yarinya saboda Allah..
"Ka yi shiru, akwai matsala ne?" Tajj ya girgiza kai ya ce
"Gare ni babu, amma wanda ya ce ta koma cikin nan shi ne problem ɗin. Shi ne komai nata shi ne yake da ikon baka ita da amincewa da kai, idan ka ji ance Ridayya Muhammad-Bilal Rano to ita ce sunansa ne maƙale a nata. Idan na faɗa maka halin da Ustaz ya shiga da babu ita zaka ƙaryata domin tamkar ƴa haka take wajansa"
"Da sauƙi ai ka ce kamar ƴa ina tunanin problem kaɗan ne"
Murmushi Tajj ya yi yana taɓa kafaɗar Sadauki ya ce "Soyayya gaskiya ce Hamza, kuma dukkan inda soyayya ta gaskiya take tana nuna kan ta duk yadda mutum ya kai ga zurfin cikinsa, wani irin abu ne da yake fitar da kansa ba tare da mutum ya shirya ba. Akwai bambanci tsakanin _i have a feelings for you ko you're my crush da i have falls in love with you_. Sadauki ba kasancewar Muhammmmd uba a wajan Ridayya ne matsala ba, Ridayya ita kanta ita ce rayuwar Ustaz wallahi Allah ba zan yi san zuciya ba, ko dan kasancewarka jinina. Ustaz yana tsananin so da ƙaunarta bai taɓa faɗa mini amma halin daya shiga ya nuna, yanayin daya samu kansa daya ganta ya fallasa sirrin zuciyarsa ina tunani ka yi haƙuri ka nemi wata ko a family ne"
Wata kalar dariya Sadauki ya yi yana fesar da iska daga bakinsa yana dinga tafiya yana dawowa sai kuma ya girgiza kai ya ce
"Idan shi yana son ta ita tana son shi ne? Idan yana son ta mene yasa ya barta ta auri waninsa? This is unbelievable"
"Ƙaddara ita ce silar faruwar komai, ƙaddara ita ta sanya Ridayya yin aure kuma har ta haihu kuma ƙaddara ita ta saka mijin ya sake ta. Kasancewar littafin da zanen ƙaddararsu ɗaya ne ya saka shima bai yi aure ba har yanzu, kuma ƙaddara ta ɗauki rayuwar iyayensu ta bar su, su kaɗai a duniya, ƙaddara ita ta saka muka buge Ridayya kuma na kawota gidana zuwan Ustaz nawa bai taɓa ganinta ba, kuma ƙaddara ita ta haɗa su yanzu bana son wannan ƙaddarar ta yi silar rayuwarka Hamza You are my young brother kabar maganar iya mu domin ko Ridayya bata so a wannan karan bata da zaɓin daya shige Muhammad-Bilal"
Sadauki ya zame hannun Tajj ya ce "This is serious. Ni kuma na ɗaukar maka alƙawari ƙaddarar aurena ita ta rabata da mijinta, kuma wallahi ba zan taɓa haƙura ba, bana faɗuwa ko a makaranta ba kuma zan faɗi a Soyayya ba, ko zan rayu da Ridayya na kwana ɗaya a matsayin miji da mata wallahi sai na aureta kuma zan tabbatar mata a yanzu soyayya take buƙata ba zaɓin wani ba, dole ta bi abinda zuciyarta yake so"
Tajj ya yi murmushi ya ce "I wish you all the best Romeo"
"What ever; na ji na yar da kuma zaka sha mamaki Commissioner"
"Commissioner? Yayanfa?"
Sadauki ya haɗe rai ya ce "Ba zan faɗa ba, tunda ka kasa taimakona bana ma buƙata kuma duk sanda ka ji an ce alfatiha ni da Shanshan daga ranar ni ne babba"
Ciki ya koma ya samu Ustaz riƙe da Little yana jijjiga shi ya kalli Mahmah ya ce "Mahmah please za mu fita tare da Ridayya"
"To Allah ya tsare ya kiyaye" Sosai mamaki ya cika Ustaz jin furucin Mahmah sai ya share kawai. Yana zaune yaga sun fito tare da Ustaz kafin ta yi magana Ustaz ya miƙe fuskarsa kamar an yi masa wahayi da ranar mutuwarsa ko an ce masa Hajiya ta rasu ba walwala jijiyoyin kansa duk sun fito ya ajjiye Little ya kalli Sadauki dake bisa hanya. Hannun Ridayya ya damƙa tamkar zai ɓalla shi biyu ya yi ciki da ita suna shiga ya ɗauki akwati ya fara zuba kayanta ciki sai kuma ya fasa ya cire mayafin kanta ya jawota gabansa ya saka mata hijabi ya sake damƙo hannunta ya sunkuya ya ɗauki Little.
"Lafiya Ustaz?"
Wayar hannun Ridayya ya amsa ya bawa Tajj ya ce "Tajuddeen Allah ya yi maka albarka mun gode"
Ya juya ya kalli Mahmah ya ce "Mahmah tarbiyar ƴa'mace akwai wahala musamman lokacin ƙuruciya da matakin girma bai cancanci ana barinta fita ba, ban yi zaton haka ba"
"Ayya Ustaz ai naga Sadauki ne shi ɗin kuma ɗa ne a waje na shi ya sa"
"Muharraminta ne? Ba haka na raini yarinyarta ba, ki yi haƙuri Mahmah amma ban ji daɗi ba Ustaza bata taɓa fita da wani ba sai lokacin da aka yi mata aure, ina son ruɗin samarin da yaran zamani na yanzu kar su lalata mini ita. Dole za ki ji ba daɗi amma gaskiya ce bana barinta, a kiyaye hakan ko dan Nadra maza basu da tabbas haka ɗiya mace bata da tabbas akan soyayyar zamani, ni na yarda da yarinyata. Babu komai na yafe miki Allah ya kankare zunubanki"
Tajj ya girgiza kai abin dariya abin takaici.
"Ni ba zan taɓa lalata Shanshan ba, ka bani dama a matsayinka na uba mu fita tare da ita zan dawo maka da yarinyarka cikin salama kawai Restaurant za mu, mu yi abu very important.....,"
Wani irin mari Ustaz ya saukewa Sadauki a fuska yana nuna shi da yatsa zuciya ta ɗauki Sadauki ya dunƙule hannu zai naushi Ustaz Ridayya ta yi saurin dakawa Sadauki tsawa
"Mene haka? Dukansa za ka yi?" Ya sauke hannun ƙasa idanunsa jajur jikinsa na rawa ƙwayar idanun Ridayya yake kallo kuma ya fahimci komai ba.
"Shanshan ya zan yi? What do you want me to do? Kin mini alƙawari Shanshan" Juyawa ta yi zata shige ɗaki Ustaz ya riƙe ta ya ce
"Mu je"
Da wani irin expression Ridayya ke kallon Ustaz hawaye ya cika idanunta ta ce "Ba zan bika ba, ba zan taɓa binka ba" sai kuma ta fashe da kuka sosai. Ustaz kallonta yake yana ɓoye tashin hankalinsa.
"Ustaza gidana zan kai ki mu zauna tare"
"Bana son zama da kai bana son ganinka Abbiey baka damu dani ba, baka damu da halin da nake ciki ba, kalle ka ka yi kyau ka ƙara fari ka yi ƙiba kana zaune cikin kwanciyar hankali ka kwanta ka yi bacci, babu mai hattararka babu mai saka abu ya ƙona ka babu mai hanaka abinci babu mai zagin halittarka babu mai ce maka maye, baka taɓa nema na ba ko sau ɗaya babu inda ban shiga ba akan nemanka Abbiey ban ganka ba, bana da kowa bana da dangi babu mai kulawa da maraicina babu wanda zai faɗawa damuwata. Sai yanzu sama taka ka zo ka ce na bika? Ka barni ka rabu dani na ƙare rayuwarta a rashin gata da ƴanci kamar yadda na fara ka bari na mutu ka zo ka ɗauki gawata"
Ba zai ce ƙiyayya ya hangu a idanun Ridayya ba amma ya hangi rashin yarda damuwa tsoro ransa abu, haushi, takaici uwa uba kewa. Fargaba ta kama Ustaz ya rasa me zai ce. Ridayya na kuka ta ce
"Ka kai ni gidanka? Abbiey kenan aure ka yi ban sani ba? Shikenan ka je ka zauna da matarka bana son ƙara ganinka wallahi wallahi Allah ba zan bika ba"
Tajj ya ce "Ridayya You misunderstanding babu..."
"No Tajj" Ustaz ya faɗa a hankali yana miƙa mata Little ta amsa ya juya ya fita daga gidan bakiɗaya. Ikon Allah ne kawai ya kai shi masaukinsa wani irin kuka Ridayya take wanda ita kanta bata san dalili ba. Mamakin wawta da rashin hankalin Ridayya ya gigita Tajj taya tunaninta ya bata Ustaz bai neme ta ba? Har ta kafa hujja a kan haka, ko Ustaz zai yi fushi dole ya faɗawa Ridayya halin da ya shiga. Ganin abinda ke faruwa ya saka Sadauki fita hankali tashe ya nufi gida.
Sama da kwana uku duka wayoyin Ustaz a rufe suke kuma Tajj bai san inda ya sauka ba domin Ustaz mutum ne mai sirri da son rayuwar sirri da keɓewa waje guda.
NAHUTU/BATSARI
Kallon yaron yake cike da damuwa da takaici ganin babu wanda yake ɗaukan shi saboda tsananin muni da ƙazanta, ya ƙara yin wani irin baƙi idanunsa daƙwa-daƙwa ga wani rafkeken hanci gashi gashi ko ɗaya babu a kansa kamar an yi masa ƙwal kwabo tamkar ɗan'ruwa. Ga masifar kashi a wando kuma babu mai ɗaukar shi shi fa duk inda Ridayya take dole ta zo ta amshi ɗan'ta ta bashi nata yana da tabbacin Little shi ne yaron da suka haifa da Khairiyya Harazimi kuma Ridayya ta haife shi, saboda babu yadda za a yi baƙa mummuna kamar Ridayya ta haifi yaro kamar Balarabe.
Ya sauke ajjiyar zuciya saboda masifar yunwar dake cinsa Iya ta ce
"Ka yi hamma ta yi dubu har wannan kar ka cinye ni idan iya ɗan'ka za ka ci da sauƙi, ai muddin ba zaka shiga gona ka taya babanka aikin gona ba ko kayo ita ce kana cikin garari wallahi tallahi yunwa yanzu ka fara zama da ita. Abin tausayi ka saba da cin lemo zubu da biredi da jar miya"
"Giɗaɗo magana nake"
"Haba Iya sau nawa na ce miki Zameer sunana ko Meer? Yunwa nake ji sosai"
"Sai dai kaci kanka ƙandas wallahi dan ko ƙwayar gero babu balle mu yi gero da wake" Ta faɗa tana ƙarasa watsar garin hannunta zuwa baki. Wani irin yanayi ya ji saboda tunanin Ridayya, ko ta ci ko bata ci ba haka zata ɗauki abinci ta bashi ya ci ya sha ruwa, amma gashi uwar data haife shi ta gaza bashi abinci, Ridayya ta yi masa wanki guga ta dafa masa ruwan wanka haka kuma zata faskara ice a fili ya ce "Da sake"
"Wanne saken? Wai ba zaka nemo yarinyar nan ba? Nifa hankalina yana kan zuwa makka ɗin nan na shiga sararin subuhana na sauka ƙasa mai tsarki, gashi ka ajjiye takardu"
"Iya dole duk inda Mai sona take zata dawo domin bata da wani zaɓi daya shige rayuwa dani, bata da kowa babu kuma wanda zai ce yana son ta domin ta tashi daga aiki ni na fara kuma ni zan ƙarar bata da wata marmora ai na faɗa miki tun kafin na aureta ta bani a kanta, tana masifar so na ba zata iya rayuwa babu ni ba dukda abinda na yi mata, balle yanzu da bata da wani gata duk iyayenta sun mutu har mariƙin nata ko tana da gatan ma ai basa son ta, kinga dole mu mayar da aurenmu a lokacin ma idan ta zo sai na ja ajina"
"Sakinta ka yi ne Giɗaɗo?"
"A'a ba wani saki guduwa ta yi na san Khairiyya ba zata dawo gare ni ba zan lallaɓa na je wajan Hanne kafin Ridayya ta dawo, kuma zan ɗauki takardun kadarorin nata a satin nan na shiga Kano na fara siyar da fili ko guda uku ne"
Ya miƙe da ƙyar ya fita yana jin Harazimi na kuka. Iyanti ta ce "A yi dai mu gani idan tusa zata hura wuta"
Iya ya leƙo ta ce "Zata hura mana sai dai ba daga Babban ɗuwawu ta fito ba"
Zameer na fita gona ya nufa Moo ya kira shi ya ɗaga ya ce "Haba Zameer tafiya shiru shiru har yanzu daga Germany ɗin?" Zameer ya fara hura iska ta cikin wayar ya ce "Daddy ɗina abubuwa sun masa yawa yanzu ma muna airport daga Germany za mu shige England a duba lafiyarsa nan da sati za mu dawo"
Moo ta cikin wayar ya ce "Ayya Allah ya bawa Daddy lafiya Gaskiya ne ajeebo kana saurarawa"
Kafin Zameer ya yi magana Moo ya ji ta cikin wayar an fasa ihu ana faɗin "Giɗaɗo wai ka zo maciji ya sari Baffa"
Ganin an haura sati ya saka Hajiya zuwa Rano ta siyar da gona ta saka aka haɗa kayan lefe ta ware kuɗin sadaki da komai da komai.
"Goben nan idan kun je wajan iyayen Mardiyya kawai a ɗaura auren sai na fi samun nutsuwar zuciya ina tausayin Ustaz burina bai shige ya yi aure ba"
"Matar anya ba ki yi gaggawa ba? Ki bari ya dawo" Ta ce "A'a ba wata gaggawa ni ban santa ba, In sha Allah sai dai ya dawo yaga matarsa a ɗaki zamansa ya fara dundirata haka"
Hajiya ta kafe Mai ran ƙarfe da wasu mutane suka nufi gidansu Mardiyya nan take kamar auren bazawara aka ɗaura auren Mardiyya Salis da Muhammad-Bilal Tahir Rano a kan sadaki dubu hamsin bisa tsari na Muslunci aka raba alawa