Showing 120001 words to 123000 words out of 190738 words

Chapter 41 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17278

yi faɗa domin Ridayya ka yi faɗa domin abinda zuciyarka ke so, kuma take son rayuwa da shi. Bani da tabbacin mene a zuciyarki game da ƴar rainonka abu ɗaya zan faɗa maka ka kula ka yi ƙoƙarin ganin ta zama taka ka yi hakan ƙarfin qwiwarka yana ga abinda kake so"


A hankali ya shiga girgiza kansa yana matse hannun Baba ƙarami dake cikin nasa bakinsa na rawa ya cec


"Bana jin zan iya Abba zuciyata a matse take bana fahimtar komai"


"Be strong; ka yi abinda ya fi haka idan abu ya ƙare baya nufin rayuwarka ce ta ƙare, something is over doesn't means yourself is over. Har yaushe zaka zauna haka? Shiru baya maganin matsala ciwo yake haddasawa a zuciya da kuma dana sani mara iyaka ba zan ci-gaba da faɗa da mahaifyarka ba, ba tare dana san kana son Ridayya ko a'a ba?"


Ustaz ya ware idanunsa a lokacin ya kalli mahaifinsa ya kasa furta komai sai zufa da take yanko masa shi gani yake me ya sa dole sai ya furta ba za su gane bane? Me ya sa ake son fallasa masa asirin zuciyarsa "Ka faɗa mini ina jiranka, mene matsayin Ridayya?"


"Abba please"


"Please what?" Ya yi ƙasa da idanunsa zuciyarsa kamar ta fito waje.


"Look Muhammmmd the most important thing is to be yourself. Ni mahaifinka ne don ka fiddo mini sirrinka ka buɗe sirrinka ba wani abu bane, idan kana son Ridayya i most be by your side, idan baka son ta shikenan I'll let her go ta zama free"


Da sauri ya matse hannu Baba ƙarami hatta tsokar jikinsa rawa take ya shiga girgiza kai laɓɓansa na rawa "Say it Muhammmmd"


"Ni daban Abinda ke zuciyar Ustaza daban Abba"


"Ko hakan yana nufin ita ɗin tana amsa sunan matar Muhammad-Bilal Tahir Rano ne?"


"A'a Abba babu kyau kar ka fara wannan zunubi ne na yafe maka kuma"


Baba ƙarami ya ce "Zunubi ko? A wannan lokacin kai Allah zai yafewa bani ba Babana, da gaske nake ina nufin abinda na faɗa. Ridayya Mansur Rano is your halal wife matar sunna"


Ustaz ya kasa tantance halin daya shiga kallon Baba ƙarami kawai yake da wani irin firgitaccen yanayi da shakku dukda a zaune yake amma tun daga kan babban yatsarsa har zuwa saman jikinsa rawa yake fuskarsa ta fara sauyawa zuwa wani launi kamar ba Ustaz ba.


"Allah ya yafe maka Abba Allah ga Abbana"


Baba ƙarami ya yi murmushi ya fahimci Ustaz har yanzu bai yarda ba, ya ciro wayarsa ya kunna video recorded ɗin da aka yi na ɗaurin auren. Play ya danna Ustaz ya zubawa video Idanu ya Baffa ga Baba ƙarami ga Tajj har da Junaid ga Barrister ga kuma General mijin Anuty Kaltum. Sanda ya ji liman ya ce “An ɗaura auren Muhammad-Bilal Tahir Rano da Ridayya Mansur Rano a kan sadaki dubu ɗari biyu”


Tsigar jikinsa ce ta fara mimmiƙewa yana jin wani emotions wanda baya kaiwa ƙasan mararsa a iya zuciyarsa yake tsayawa da gangar jikinsa ƙofofin gargasar jikinsa suka buɗe wani irin sanyi yana shigarsa, zuciyarsa ta buɗe hannunsa ya shiga rawa duk jarumtarsa ta kau ikon Allah kawai yake gani mai yin yadda ya so a lokacin daya ga dama, Hausawa sun yi gaskiya da suke cewa kana iya aurar matar wani amma ba zaka iya haihuwar ɗan wani ba, matar mutum kabarinsa.


"Abba gaske kake?"


"Da gaske nake Babana hukuncin Ubangiji ne ba namu ba, kuma tsarinsa ne Ridayya matarka ce"


Ustaz kasa magana ya yi sai halin ɗan fari dana autar ya bayyana ya ɗora kansa a cinyar Baba ƙarami wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya ya sauke a ransa yana yin hamdala ga Ubangiji daya ara masa ganin wannan ranar. Bai taɓa fitar da hawaye a rayuwarsa ba bai suna zuba ba sai da Baba ƙarami ya riƙo fuskarsa yana share masa hawaye ya ce


"Kuka? Al'amarin har ya kai haka Babban mutum baka tunanin ka girma?"


Ya ɗan marairaice fuska ya ce "Allahamdulillah!"


"Shi ne abin godiya, zan yi magana da kai idan ka samu nutsuwa"


Ustaz ya kasa tantance wanne kalar farinciki yake ji, tsoron abinda Dr ya faɗa ya wanzu a zuciyarsa anya zai iya? Me ya sa bai samu Ridayya ba sai yanzu da ƙaddara ta faɗa masa ƙaddara mai zafi da munin gaske Ridayya ta saba da rayuwar gidan miji ba zata jure halin da yake ciki ba, domin ba zai amfana mata da komai ba shi ɗin kamar photo haka zai zama. Idan ya ture wannan taya zai fara rayuwar aure da Ridayya? Ƴar cikinsa yarinyar daya raina kuma yana jin ya mata girma, shi da kansa kunyar wannan al'amarin yake yana jin son rayuwa da ita har bayan abada idan akwai amma bai taɓa hango wani nauyi na musamman ba, taya zai iya kwana da ita gida ɗaya ɗaki ɗaya gado ɗaya matsayin matar, su kwana matsayin mata da miji? Ya rufe idanu a hankali yana sauke numfashi nauyin zuciyarsa na raguwa kamar a mafarki haka yake jin batun auren nasu gefen zuciyarsa Ridayya ɗin kawai yake son gani, a wannan karan zai yi mata kallo ne na matarsa kuma halalinsa.


"Tsuguno bata ƙare ba"


Ridayya Sadauki ne a ranta, shi kuma Ridayya ce a ransa Mardiyya kuma Ustaz ne a ranta ga matsalar rashin mazakuta ga matsalar Umma wacce tafi ko wacce illa a zuciyarsa ga matsalar Sadauki ga matsalar ciwon Ridayya ɗin _“What should I do?_”


Allura aka sake yi wa Ridayya mai nauyi ta fara bacci al'amarin ya ƙara hargitsa kwanyarta wacce take a gurɓace har yanzu shocked ɗin ganin Ustaz zube a ƙasa ne bai yar kanta ba.


Kwana biyu a tsakani ta farfaɗo cikin hayyacinta kuma babu abinda ke damunta sai ramar da ta yi ta ƙara yin zuru-zuru ta yi ɗan duhu a kan na baya saboda kwanciyar asibiti. Lokacin da idanunta ya sauka a kan Zainura firgicewa ta yi ta hau salati da addu'a


"Yaya Ridayya ni fa ba fatalwa ba ce ki bar addu'a" Ridayya ta girgiza kanta ta fara yunƙurin guduwa Baffa ya ce


"Fatalan suna da yawa"


Da wani irin sabon tashin hankali take kallon Baffa sai kuma Mami ta dinga nuna su da hannu


"Kun kun mutu an ce kun mutu ko kun zo tafiya dani ne, kar ku bar ni zan biku lahira ɗin an ce...,"


Sai kuma ta sulale jikin Mami a sume daman sun zan za a rina an saci zanin mahaukaciya bayan ta farfaɗo ta fasa wani ihu Mami ta riƙe ta gam a jikinta ita kanta kuka take Zainura ma kukan take Baffa ya sunkuyar da kansa.


"Mami da gaske kece? Kece a gabana kike riƙe ni baku mutu ba aka ce kun mutu? Ashe ƙarya ya yi mini mugu azzalumi ba zan taɓa yafewa Giɗaɗo ba ya saka na dinga wahala ashe kuna raye Abbiey ma ya ce kun mutu to babu ruwana da shi tunda ya yi mini ƙarya"


Ita tana kuka Mami na kuka "Shiitttttt ya isa haka kinga ba ki da lafiya ki bar kukan haka"


"Lafiya lou nake ai tunda na ganku na warke Mami za ki dinga yi mini magana yanzu? Za ki dinga hira dani? Kuma za ki dinga siya mini abu irin n Zainu kin daina bari na cin mutuncin halittata?"


"Ina tare dake Ridayya ki yafe mini na yi kuskure ka cutar dake"


"Na yafe miki ba ki mini komai ba" daɗi ya ishe Ridayya tana tuno maganar Zameer da yake cewa bata da kowa bata da gata to ya zo ya gani iyayenta suna raye.


"Baffa don Allah yau ɗaya ka ce ni ƴarka ce bani na yi kai na da na san inda zan samu farar fata da kyau irin na Zainu dana samu"


"Shalalen Ustaz you're my darling daughter my love you're my favorite person. Na yi laifi da kuskure ban san yaushe ba kuma ba zai daina kukan hakan ba duk wanda yake da saka hannu a kan faruwar komai ba zan taɓa yafe masa ba"


Baffa ya rungume Ridayya yana jin wani tausayinta soyayyar da yake mata tun tana ciki wacce ita ta yi sanadiyyar lalata komai ta dawo masa sabuwa fil a zuciya. Mami kuka take da dukkan ƙarfinta raba uwa da ɗa akwai ciwo kuma dafini mai girma a zuciyar ko wacce mahaifiya idan ta tuna bata bawa Ridayya tarbiyya sai ta ji hankalinta ya tashi shi ya saka wani lokacin komai take yinsa da ka, dukda Ustaz ya taka rawa iya karfinsa wajan gina ta a kan turbar arziƙi. Addini, biyayya, tsare mutunci, suttura da ilimin zaman rayuwa amma tarbiyyar uwa daban take role ɗin uwa is best a rayuwar ko wanne ɗa.


"Mami ni ma ina son kayan irin na Zainu"


"Ridayya ke dai kishi halittarki ne ƙanwarki ce fa, ke ga Little kin ajjiye da abinda kika haifa na fari yana nan da tuni ya yi wayo fa amma kina acting like a baby"


Cewar Yaya Balkisu tana dariya. "Mu dai yanzu baby ce a wajanmu dole ta nuna mata wawta irin ta ƴaƴan fari da kuma sangartata Ustaz ya yi"


Cak Ridayya ta tsaya da murmushin da take sai kuma ta miƙe ta ce "Baffa ina Abbieyna?"


"Ki ce ina Yaya Bilal ko Ustaz ki daina cewa Abbiey Ridayya"


"Shi Babana ne, yana ina?" Baffa ya sauke numfashi ya ce


"Kusa da ɗakin nan ki fita a hankali" da ƙyar ta jira ta saka wula duguwar riga ce a jikinsa wacce komai nata ya fiddo ta yi mata kyau ko slippers bata saka ba ta fita tana ƙoƙarin shiga room ɗin Umma na fito wa


"Ina yini Umma?"


Da faɗa bakinta na rawa saboda kallon da Umma ke yi mata.


"Ina yini ban ganshi ba, umma kuma ke neme ta idan kin zo don ganin Ustaz ne to ki koma domin babu ke babu shi"


Jikin Ridayya ya yi sanyi idanunta ya cika da hawaye ta ce "Abbieyna ne fa don Allah ki bar na shiga"


"Zan ga uban wanda ya isa ya saka ki shiga"


A sanyaye ta ce "Me na yi miki Umma ki yi haƙuri idan na miki laifi"


"Ai kinfi ɗan dako sanin tasha. Ba ki mini komai ba kawai na tsane ki bana son ganinki tare da Muhammmmd"


Mardiyya ta ƙara su wajan ta ce "Umma the car is ready likitan ya bada sallama"


Umma ta ce "Ok ƴar arziƙi irin albarka wanke hannu ka taɓa farar mace alkyabbar mata haske mai haska ko wanne duhu, farar mace baku da yawa a duniya dai a Aljanna, idan mutum bai auri farar mace ba kuɗinsa ne bai kai ba" Mardiyya ta yi wani irin fari da idanu ta ce "Na gode Ummana"


Ridayya ta ji ta muzanta jikinta ya ɗauki rawa ta juya da gudu ta tsaya wani corridor ta yi kuka kamar ranta zai fita sai kallon baƙar fatarta take me ta yi wa Umma haka ne? Idan ta yi mata laifi to a kan me zata hanata zuwa Abbiey? Kukan da ta yi mai yawa ya saka kanta sarawa tare da fara ciwo.


Duguwar jallabiyya ce a jikinsa ta maza saboda aikin da yake mararsa an bashi da wani ɗan sanda yana takawa da shi, fuskarsa a kame baka gane halin da yake ciki furr Umma ta hana shi shiga wajan Ridayya a haka suka shiga mota Junaid ya kai su can gidan Ustaz ɗin. Ustaz hankalinsa yana kan Ridayya a haka ya bar asibitin. Ridayya tana komawa ciki suma aka sallame su ta zama wata so silent maganganun Umma na yawo a kanta lokaci zuwa lokaci tana kallon baƙar fatarta.




Zameer ne jingine da cikin wata jibgegiyar mota ya sha shadda sai ɗaukan Idanu take kamar kodayaushe waya iphone ce a hannunsa ya manna bluetooth magana yake kamar an yi masa dole idanunsa a kan Alhajin ya ce


"Idan ka siyi filin haka to idan bai ba ka bar shi akwai masu siya da yawa"


Mai siyin filin ya dinga kallon makeken filin da girman gidan da zai samar bai ɗauka kuɗin da Zameer ɗin zai buƙata kenan ba domin ya yi sauƙi fiye da yadda ya zata ya ce


"A'a nikam filin ya yi mini idan miliyan 25 ɗin ne matsayarka shi kenan sai ka bani takardun fili ga shaidu ga dillali ni kuma na baka takardar banki ko transfer ko cash"


Zameer ya ɗan taɓe baki yana danna waya a nutse ya ce "No transfer ɗin zai fi" Ya ce "Ok takardun filin?"


Mota Zameer ya je ya buɗe ya ɗakko takarda ɗaya ya dawo ya bawa mutumin shi kuma ya shiga duba takardar can ya ce "Kace sunanka Zameer Mahboob Dollar?"


"Sure; ya akai?"


"This land is owned by Ridayya Muhammad Tahir"


Zameer ya ce "Inji uban wa? To nawa ne halak malak idan zaka siya ka siya idan ba zaka siya ba ka bani takarda ba dole"


Dillalin ya ce "A'a ai ba a yi haka ba kasan duniya ta lalace da ɓata gari masu satar filayen jama'a, ko ka mance ba wannan takardar zaka bamu ba? Domin wannan ma ai original ba ce" gaban Zameer ya faɗi jin ance ba Original bace fake ce kenan ko ya? Me ya sa ya yi gaggawar barin Ridayya ta gudu ne? "Eh maybe mantuwa na yi kawo kawai"


"A'a ba a yi haka ba ina zuwa" Dillalin ya faɗa yana kwafe wasu numbers daya gani a jikin takardar kira uku ya yi kafin a ɗaga ya yi wa Alhaji alama daya kira police.


"Assalamu alaikum kuna magana da Bello dillalin filaye, an kawo wani fili dake unguwar jan bulo kuma an saka Ridayya Muhammmmd Tahir" Shiru ya yi yana jin me ake cewa ya ce "To babu matsala nima naga alama bari a yi hakan"


Zameer na tsaka da danna waya yana jira ya ji shigowar maƙudan kuɗaɗe ya an riƙe shi ya ɗago kai ganin police ya saka shi binsu da Idanu kafin ya yi magana ɗaya daga ciki ya ce


"You are under arrest"


"Arrest akan me kasan waye ni kowa officer kasan waye babana?"


"Sorry sanin waye babanka baya cikin aikina, idan mun je office za ka ji bayani"


Tija ƙeyar Zameer sukai zuwa police station. Suna zuwa suka bashi damar kiran babansa kuma suka zayyana masa laifinsa na sama da faɗi da yake shirin yi da filin wani. "Wani kuma? Filin na matata ne matata kuma hakƙina ce komai nata mallakina ne"


"Ina matar taka take yanzu? Ta zo ta bamu tabbacin kai mijinta ne sai mu sake ta, ku saka shi a ɗaki"


Zameer bai san ta ƙamaimai inda Ridayya take amma dole zata dawo gare shi bata da zaɓin daya shige zama ƙarƙashin inuwarsa haka ya saka a ransa kwana biyu ya yi ya fita daga hayyacinsa ko hauka yake ai ba zai kira gida ba, kuma bashi da ƙarfin qiwwar kiran Moo ko Khalid. Ridayya kawai yake nema idanu rufe.


Sadauki na zaune shi da Prof da Mother sai secretary daya shigo yanzu cikin rashin sa'a files ɗin hannunsa suka kwace pictures ɗin zuƙa zuƙan ƴan'mata suka bayyana tare da tarwatse wa a parlourn.
Sadauki ya dinga kallon pictures ɗin da mamaki haka mother. Prof hankalinsa ya tashi ya yi wa secretary alama da idanu cikin faɗa ya ce "Wai secretary how many times zan maka warning akan ka daina bina da photonan masu neman taimakon nan eh? Gabaɗaya baka san aikinka ba ana bata taimako dole ne na ce maka marayu kawai dana kasassu nake bawa tallafi" secretary ya ce "Afuwa ranka ya daɗe wallahi sun takura ne gabaɗaya bikinsu za a yi ke suna buƙatar taimako shi ne suka rarraba pictures nasu, wannan sun fi wata waje na yau na gaji na ce bari dai na yi maka bayani"


"To i can't ba zan iya ba kasan takara nake bana son problem"


"Muga" Sadauki ya faɗa yana amsar pictures ɗin yanayin kayan jikin ƴan matan su kaɗai abin mamaki ne ba su yi kama da masu neman taimako ba shi damuwar neman auren Ridayya ce a kan shi ya bawa secretary pictures ɗin mother ta ce "Daka taimaka shi taimako ba sai an ware wani ɓangare ba, kuma hakan zai taimaka wajan dasa soyayyarka wajan mutane shi ma campaign ne"


Prof ya miƙe tsaye ya ce "Mu je" fita suka yi shi da secretary suna fita ya ce


"Ka kusa kwafsawa wallahi idan Sadauki ya sani na banu"


Secretary ya ce "Wallahi ban san ya aka yi ba"


Prof ya lumshe idanunsa yana sake kallon pictures ɗin hankalinsa duk ya tashi ya ce "Wallahi duk ka firgitar dani a gida na yi niyyar kwana amma ka zaɓa mini guda biyu a yi booking hotel da ɗaki a kula da su ya zama confirmation please i trust you"


Suna gama maganar ya koma ciki ya ce "Yes son ina ne address ɗin yarinyar gobe za mu je in sha Allah kar ka damu har da sadaki zamu tafi"


Murmushi Sadauki ya yi ya ce "Best father thank you darling"


"Anything for you dear, iye angon Ridha"


Tashi ya yi mother ta ce "Badai fita za ka yi ba na haɗa maka abinci"


"No meeting ne dani zan dawo nan da 2hrs love you wife" kafin ta yi maganar ya fice.


Sadauki ya kalli mother yaga duk ta sauya ya san akwai damuwa a ranta, mother tana buƙatar mijinta a kusa da ita kewarsa take sosai ta manta yaushe rabonta da shi matsayin miji da mata Sadauki zai yi magana ta ce "Wanne gida ka ce ka zaɓa ne? Kuma zan tura a fara haɗa lefe"


"Mother nrml fili nake so gidan da zan ginawa Shanshan na musamman ne" Ta yi murmushi ta ce "Oh Allah ya nuna mini wannan rana"


"Wallahi mother ina tsananin son Shanshan Allah ne shaidata i love her with all my heart I so much loves her"


"Allah ya baka ita" da sauri ya ce "Yama bani"




Duk suna zaune a parlour banda Ridayya wacce kullum kuka take sun rasa gane kanta rabonta da Ustaz tun ranar da Sadauki ya zo. Idan ta fara tunanin Sadauki sai tunanin Abbiey ya danne na Sadaukin tunanin yadda zata zama fara shi ne kawai a ranta.
Baba ƙarami ya ce "Allahamdulillah komai ya yi farko yana da ƙarshe kuma in sha Allah zamu tattara mu koma Kano da zama a Babban gidan da aka sauya. Kuma zamu tara mutane a yi addu'ar ɗaurin auren Ustaz da Ridayya kana a yi walima dole jama'a su shaida kuma aurenta ya zama mai ƴanci ba kamar wancan ba. Babban mutum zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login